Chapter three
by @aysharano22
🤍SIRRIN ZUCIYA🤍
By Aysha Rano✨
Book 1.
03
Cikin wani lecture hall mai ɗauke da students da bazasu fi irin 30 ba zuwa 35, gaba ɗaya hankalin students ɗin na kan lecturer ɗinsu dake bayani yana rubutu akan board. Ba ka jin karar komai sai sautin voice ɗin malamin dake fita cikin english ɗinshi mai ɗauke da accent ɗin yarbawa.
Final year students kenan masu studying International Relations a nan University of Lagos dake cikin jihar Lagos. Sosai suka maida hankali suna ɗaukan lectures ɗin har sai da malamin ya gama bayanin da yake yi tsaf sannan ya ɗora da cewa yana facing ɗinsu
“So class concerning research ɗin da na baku kuyi last week, ya nuna almost all of you here are going to fail in your upcoming final year project, cause clearly only few of you are ready for the project.”
Shiru duk class ɗin sukayi suna kallonsa, shi kuma ya ci gaba da cewa
“I think only 3 people among you scored 45 and there’s one person... just one person that scored 83 out of 100.”
Shirun dai suka sake yi suna sauraronshi kafin ya ci gaba
“Any guesses who this one person is?”
Ai tun bai ƙarasa rufe baki ba gaba ɗaya class ɗin suka haɗa baki suna cewa
“Sir Mr India... it’s Mr India.”
Already dama sun saba shi yake topping a kowane course.
Wani murmushi lecturer nasu ya saki as sun faɗa daidai, domin ba ma class ɗin ba kadai ba, kusan kowa da yake department ɗin nan tun daga kan lecturers zuwa students babu wanda bai san waye Mr India ba saboda suna da yayi ta fannin kyau da ƙoƙari.
Yana da ƙwaƙwalwa sosai fiye da duk yadda zan yi muku bayani, shi yasa duk da kasancewarshi ba mai shiga cikin mutane ba, mutane da yawa sun sanshi.
Bai sake ce musu komai ba ya ɗauko wata paper ɗaya ya ajiyeta separate bisa lecturer’s desk ɗinsu sannan ya nufi extreme end of the class, as ko ba’a faɗa ba yasan definitely a ƙarshen class zai sameshi saboda tun 100 level baya da wurin zaman da ya wuce last seat saboda tsabar rashin son mutane.
Sai da ya isa last seat of the class sannan ya tsaya bakin seat ɗin ya shiga kallon wanda ke zaune kansa a ƙasa.
Jin tsayuwar lecturer a gabanshi ya sashi dole ya ɗago kai ya ɗan kalli malamin sau ɗaya kafin ya janye idonshi.
And my people bansan sanda na furta La hawla wala quwwata illah billah ba saboda tsananin kyawun halittar dana gani.
Ya Subhanallah.
Saurayi ne da akalla zai kai 25 zuwa 26 years. Yana da haske sosai, don a kallon farko da kayi mashi zaka gane ko dai he’s Indian ko kuma ya haɗa jini da Indians saboda ba ƙaramin kama yake da su ba.
Hatta gashin kanshi da eyebrows ɗinshi sak irin nasu ne mai wannan laushin da santsi, gashi kuma very thick ga tsayi, don ma shi bai barin nashi ya taru yake ragewa.
Yana da doguwar fuska da dogon hanci ga wasu idanuwa dara-dara tubarkallah. Kana ganinshi zaka ga kyanshi saboda manyan kyau gareshi.
Cikin idonshi na da haske sosai kamar madara sai wajen baƙin kuma nashi ya kasance light blue.
A taƙaice dai kana ganinshi zaka san ba African bane domin tun daga kan sumarshi, skin color da kuma blue eyes ɗinshi ko kusa baiyi kama da na ɗan Africa ba.
To cut long story short Mr India kyakyawa ne na gaban kwatance wanda ko a Indian ma ba ko ina ake samun irinsu ba.
Sunanshi lecturer ya kira kamar yadda kusan kowa a makarantar ke kiranshi wato Mr India.
Ɓata rai yayi sosai don ko kusa baya son wannan Mr India da suke kiranshi da shi. In fact ya tsani sunan.
Don haka without wasting time ya ce ma lecturer ɗin yana ɗan pouting thick lips ɗinshi
“My name is AYAAN.”
Murmushi malamin nasu ya saki domin kaf lecturers ɗinsu babu wanda bai saba da wannan halin nashi ba, so bai damu ba ya miƙa mashi paper ɗin dake hannunshi yana ci gaba da smiling
“You did amazing as usual, I’m super proud of you.”
Amsan paper ɗin yayi kuma har yanzu bai ɗago ya kalleshi ba yace
“Thank you sir.”
Malamin ya ɗan yi patting shoulder ɗinshi yace
“Keep it up.”
Yana gama faɗan haka ya juya ya koma inda ya ajiye sauran papers ɗin ya ba class rep zai ba kowa nashi sannan ya ɗora da cewa
“So I think you guys are going to have to get Mr India to teach you how to do this research cause it’s gonna be very very helpful for your upcoming project and everybody has to learn before our next class.”
Amsa mashi class ɗin sukayi da
“Yes sir.”
Daukan stuffs ɗinshi yayi dake ajiye kan desk yana cewa
“Alright let’s call it a day. See you guys in my next class.”
Daga haka ya fita daga lecture hall ɗin.
Yana fita class rep ɗinsu ya mike yana cewa
“Listen class, Miss Funmi just texted to inform me that she postponed her lecture to next week. So I was thinking why don’t we use this opportunity to learn about the research now? What do you all say?”
Gaba ɗaya class sukayi na’am da wannan shawara na monitor ɗinsu don haka monitor yace
“Ok over to you Mr India, the class is in your hands now.”
Yana gama faɗan haka ya koma seat ɗinshi ya zauna.
Duk zuba ido suke suga Mr India ya taso amma ko motsawa daga inda yake baiyi ba.
Class rep ne ya juya yana kallonshi ya ɗan daga murya yadda zai jiyo daga inda yake zaune yace
“Hello Mr India we ar...”
Tun bai ƙarasa ba cikin ɗan fada-fada yayi saurin katseshi da cewa
“My name is Ayaan okay? Not Mr India.”
Gyada kai class rep yayi kafin yace
“Okay Mr Ayaan Agnihotri, we are all waiting for you plss.”
Agogon hannunshi ya duba. Lokaci ɗaya ya wara blue eyes ɗinshi tare da tashi tsaye da sauri ya ɗauki wayanshi don bai san lokaci ya ƙure har haka ba.
Ya fito daga seat ɗin, kamar zai fita daga class ɗin sai kuma ya juya ya nufi seat ɗin da class rep ɗinsu ke zaune.
Ya ɗan rage tsayi yana dubanshi murya ciki-ciki kamar baya son magana yace
“I have something really important to do right now maybe some other time.”
Da sauri monitor yace
“Not some other time Ayaan, you heard what the lecturer said right?”
Lumshe blue eyes ɗinshi yayi ya buɗe kafin yace
“Okay tomorrow. I’ll teach you guys tomorrow, is that okay?”
Kai monitor ya ɗaga yana cewa
“Yeah it’s fine. See you tomorrow then.”
Da sauri ya juya ya fita daga class ɗin ko amsawa baiyi ba duk suka bishi da kallo.
Class rep ya tashi ya musu bayanin change of plan da aka samu sannan ya koma yayi zamanshi.
Su kuwa dama basuyi mamaki ba don kaf ɗinsu babu wanda bai san Mr India da baƙin hali ba.
A cewarsu tsabar baƙin hali ne yasa ko associating da mutane baya yi. Bai shiga harkar jama’a, kai ko hira da mutane baya yi balle a ga dariyarshi.
Ko aboki basu taɓa ganin yayi ba tun daga level 1 kullum haka zai shigo school ya tafi can ƙarshen aji ya zauna.
Da zarar an kammala lectures kuma shine wanda ke fara fita daga ajin.
Duk da haka kuma bala’in ƙoƙari gareshi.
Ba ƙaramin abu bane zai sa kaga yayi magana da wani a class ɗin idan aka cire class rep da shima kusan dole yake mashi saboda ba da son ranshi yake tsayawa dogon magana da shi ba.
Wannan dalilin yasa banda sunanshi babu abin da course mates ɗin nashi suka sani game da shi.
Sunan nashi ma da yawa ba riƙewa suke ba saboda Mr India kusan kowa ke kiranshi saboda tsananin kama da yayi da Indians ga kuma surname ɗinshi dake sake indicating musu cewa lallai ya haɗa jini da Indiyawa.
Yana fita kai tsaye parking space ya nufa. Sai sauri yake kamar zai tashi sama.
Sanye yake cikin black jean da light blue hoodie a jikinsa saboda yanayin weather ɗin garin akwai ɗan sanyi.
Yana da tsaho sosai amma fa bashi da ƙiba at all kuma kana ganinshi zaka gano yarintar dake tattare da fuskarshi.
Wata ash 406 ya buɗe ya shiga bayan ya ƙarasa parking lot ɗin. Yayi reverse ya fito daga tsakiyar motocin dake gefen tashi sannan ya kama hanyar fita daga makarantar.
Yana hawa titi ya sake duba agogo dake cikin motar. Duk hankalinshi yayi kanta. Bai san lokaci ya ƙure har haka ba gashi yanzu da ƙyar idan bai haɗu da mummunan traffic ba kafin ya kai school ɗinsu.
Haka yayita ƙurdawa yana bin hanyoyin da yasan zai samu rangwamen traffic tunda Lagos dai ba rabuwa yake da traffic ba sai dai ace na wani wurin bai kai na wani wurin ba.
Tafiyar kusan 37 mins ne ya kawoshi gate ɗin wata makaranta da a jikinta aka rubuta Super Genius Academy.
Parking yayi daga gefe sannan ya buɗe motar ya fito direct ya nufi gate ɗin shiga makarantar.
Kafin ma ya ƙarasa shiga ya hangota tana tahowa goye da school bag ɗinta a baya sai lunch bag riƙe a hannunta.
Yarinya ce da bata fi 5 years ba, ita ma doguwa mai kama da shi sak har blue eyes ɗinsu iri ɗaya kamar yayi kaki ya ajiye.
Wani haɗaɗɗen murmushi ne ya subuce masa as seeing her alone makes his heart giggle.
This girl is his absolute weakness and his biggest strength at the same time.
She is his whole heart as his whole life revolves around her.
His every little happiness depends on her as he loves her way more than he loves himself.
Tana hangoshi ta taho da gudu zuwa inda yake tana cewa
“Papaaaa!”
On top of her voice.
Da sauri shima ya nufeta as gudun da takeyi sai yaga kamar faɗuwa zatayi kafin ta ƙaraso wajenshi.
Suna haɗuwa ya dagata cak ya rungumeta a jikinsa ya ɗan ɓata rai idanuwa a lumshe yana shafa bayanta yace
“Pookie manaa, ban hanaki wannan gudun ba?”
Yadda Hausan ya fito a bakinshi raɗau sai da nayi mamaki saboda by his looks dai bazaka taɓa tunanin ya ma san menene Hausa ba balle ya iyashi.
Amma sai ga Hausan rangadaɗau a bakinshi kamar jakin Kano.
Murmushi har yanzu yarinyar ke yi tana rungume a jikinsa tace
“Sorry Papa.”
Dagota yayi yana duban cute face ɗinta yace
“Ki daina, banso kinji ko?”
Kai ta gyada mashi tana murmushi cikin yaren Hindi tace
“Theek hai meri Papa.”
(Okay my Papa)
Murmushin shima ya saki kuma har yanzu tana riƙe a hannunshi yayi pecking forehead ɗinta yana ɗan jan cheeks ɗinta da free hand ɗinshi yana cewa
“That’s my Pookie. Now tell me who’s Papa’s best friend?”
Tun bai rufe baki ba ta hau nuna kanta tana amsa mashi da ƙarfi kuma full of excitement tace
“Kiara Agnihotri!”
Yace
“Who’s the best daughter in the world?”
Nan ma da saurinta tace
“Kiara Agnihotri!”
Yace
“And who’s the best Papa in the world?”
Da saurinta kuma cikin excitement tace
“Ayaaannn Agnihotriii!”
Ta ƙarasa tana jan rii ɗin na ƙarshe kamar yadda ya saba mata tun ma kafin ta iya magana, don hakan ya zama little routine ɗinsu ko ince signature ɗinsu.
Peck ɗin ita ma tayi mishi tare da jan cheeks ɗinshi kamar yadda yayi mata ɗazu tace
“I love you Papa.”
Rungumeta ya sake yi tare da lumshe idanuwa.
Cikin ranshi yana jin kamar har duniya ya tashi bazai taɓa son wani abu kamar yadda yake son yarinyar nan ba.
Yana sonta fiye da duk wani hasashen mai hasashe har yana ganin kamar duk duniya baza’a samu uba dake son ’yarshi kamar yadda yake son Kiara ba.
She’s his everything.
Murya can ƙasa kuma still yana rungume da ita yace
“You are the only thing that made my life worth living.”
Yana iya jiyo sautin giggling ɗin da tayi kafin tace
“Thank you Appa.”
Murmushi ya ƙara saki kawai yana jinjina kai jin yanzu nan ta kirashi Papa, next minute kuma tace Appa.
Haka nan take tun suna India ta saba duk wanda taga dama kiranshi da shi take.
Shima kuma bai taɓa yunƙurin hanata ba saboda da Papa da Appa ɗin duk yana so indai ita zata kirashi da su.
Dagota daga jikinsa yayi yana dubanta ya shiga daga mata girarshi duka biyun ya juya yare zuwa Hindi before yace mata
“Ab ghar chalee?”
(Can we go home now?)
Yana rufe baki ita ma cikin Hindi tace
“Haan chalo.”
(Yes let’s go)
Bai sake magana ba ya sunkuya ya ɗauki lunch bag ɗinta data yar a ƙasa sannan suka nufi inda yayi parking.
Suna isa ya buɗe back seat yasa school bag da lunch bag ɗinta a ciki, ita kuma ya sata a gaba.
Ya daura mata seatbelt sannan ya zagaya ya shiga driver seat ya tayar da motar suka bar harabar wurin.
Rano✨