Chapter five
Canada
Montreal General Hospital shahararren asibiti ne dake birnin Montreal a ƙasar Canada. Asibitin ya kasance ɗaya daga cikin manyan asibitocin da ake kai marasa lafiya masu buƙatar kulawa ta musamman.
Room Number 312
Wani dogon matashine da a kalla zai kai 35yrs kwance akan gadon marasa lafiyan dake dakin baza a kirashi da baki ba sannan kuma baza mu sashi a layin farare ba kalan fatan shi kalan fatan nan ne da ake kira da caramel.
Kwance yake yana sauke numfashi a hankali da taimakon oxygen din dake makale akan hancin sa jikin sa kuwa kota ina nakura dake taimakawa sassasan jikin sa.
Fuskan sa cike yake da gashi wanda hakan bai hana tsantsan kyawun da Allah ya masa baiyanuwa ba.
A hankali aka turo kofan dakin da ya kasance ba haske sosai a cikin sa sai wani kalan sanyi da dakin ya dauka da kuma kamshi kaman ba dakin mara lpia ba koda yake dama komai na kasan waje daban yake dana nan namu gida Nigeria.
Wata babbar matace in her 50s ta shigo dakin sai dai kuma a yanayina jin dadin daya baiyana a jikin ta zaisa ayi tunanin bata kai wannan shekarun ba.
A hankali take taka kafafuwanta zuwa cikin daki kai tsaye ta nufi gadon daya ke kai tana kare masa kallo medicated glass din daya ke fuskan ta ta cire wanda hakan ya bawa hawayen daya ke fuskan ta baiyana sosai suke kama da mara lafiyan sai dai sabanin shi daya ke caramel in complexion ita fara ce sosai.
A bakin gadon ta zauna ta daura hannun ta akan nasa tana shafawa a hankali dayan hannun ta kuma tana share hawayen dake zuba akan kamilalliyar fuskan ta.
Cikin muryan dake nuna tsananin rauninta ta kira sunan sa.
"Muhammad Rayyan"
Sai kuma tayi shiru na wasu dakika kafin a hankali tasa hannun ta ta shafi gefen fuskan sa wani kyakkyawan murmushi na bayyana akan fuskan ta cikin sanyi murya kuma ta sake cewa.
"Son" your Mommy is here please ya kamata ka tashi daga baccin nan haka Ina kewan ka sosai Rayyan.
Ta fada tana mai cigaba da shafa fuskan sa this is almost three years da kake kwance Son, na gaji da kallon ka haka please Son ta fada hawaye masu zafi na sauka akan fuskan ta.
Da sauri kuma kaman wacce aka tsikara ta cire hannun ta akan fuskan sa ta daga hannayen ta duka biyu sama cikin raunin murya ta fara magana.
Allah ga bawan ka nan ya Allah kai kadai kasan abun dake damun sa ya Rabbi ka yaye masa ka kara mana hakuri da juriyan wannan jarabawan ta karishe addu'an kuka na subuce mata tabbas tana tsananin son danta duk da kasancewan bashi bane kadai dan da Allah ya bata amma soyayyahn shi a gare ta daban yake sai dai duk wannan soyayyahn hakan bai hana Allah jarabtan shi da ciwon da har yau aka kasa gano kansa ba tsawon shekara biyar kenan yake kwance babu wani abu dake motsi a jikin sa.
Karan wayan tane ya dawo da ita daga duniyan tunanin data lula da sauri ta share hawayen ta tare da mikewa a hankali kuma ta duka ta sumbaci goshin sa sannan ta juya ta nufi hanyan fita daga dakin tana daga wayan nata dake cigaba da ruri.
Akan kujeran dake can gefe da dakin ta zauna tana duba wayan ta ganin wacce ke kiran ta yasa tayi gyaran murya ta kara wayan a kunne ta.
Sallama akayi daga can bangaren ta amsa suka gaisa cikin mutuntawa kafin Hajiya Sarah mahaifiya agun Muhammad Rayyan tace Hajiya Jamila nikam ya maganan da mukayi ne na jiki shiru gashi next month su Hibbah zasu koma school.
Hajiya Jamila tace wallahi ban manta ba dan dazu ma muka gama waya da karima wacce take kawo min yan aiki tace a cikin week din nan zata kawota kin san samun yan aiki anan gida Nigeria sai a hankali wllh.
Ajiyan zuciya Hajiya Sarah ta sauke to shikenan ba damuwa i think nima zan shigo Nigeria Next week Insha Allah.
Sallama sukayi ta maida wayan ta cikin jaka kana a hankali ta juya tana kallon kofan Room din da Muhammad Rayyan ke ciki.
#Waheedah
#***