Chapter Six
Hajiya Sarah ta jima tana zaune a gurin kafin a hankali ta tashi ta nufi corridor dazai sada ta da elevator so take yi taje hotel din da ta sauka ta huta tunda dama ba'a zaman jinya a asibitin sanna ba'a bari relative din patient su ringa zirga zirga akan mara lpia.
A hankali Hajiya Sarah ta ci gaba da tafiya cikin faffadan corridor ɗin asibitin cikin takun ta me cike da natsuwa yayin da nurses da doctors ke wucewa lokaci zuwa lokaci suna gudanar da ayyukansu.
Tana isa gaban elevator, ta danna button ɗin jiki bayan wasu seconds kaɗan, ƙofar elevator ɗin ta buɗe shiga ciki tayi da wasu visitors guda biyu ƙofar ta rufe, elevator ɗin ya fara saukowa a hankali
Jingina tayi da bangon elevator ɗin tana lumshe idanunta.
She was tired.
Tun bayan da Muhammad Rayyan ya kwanta a wannan hali, rayuwarta ta canza gaba ɗaya duk lokacin da ta kalli ɗanta, zuciyarta kan sake karyewa.
Ta san cewa dukiya, matsayi da ƙarfi ba su isa su cire wa mutum wata jarabawa idan Allah bai yarda ba.
Sautin elevator ne ya sanar da isarsu Ground Floor wanda hakan yayi sanadiyan dawowan ta daga duniyan tunanin data shiga a hankali ta buɗe idanunta sannan ta fita da elevator din.
Babban reception area na asibitin ya bayyana a gabanta. Mutane daban-daban na shiga da fita, daga fararen fata harma da bakaken fata ta gyara mayafinta sannan ta fito daga main entrance na asibitin.
Wani sanyayyar iska ta bugi fuskarta daya sata lumshe idanunta kafin a hankali kuma labbanta suka motsa
"Montreal weather is something else.
Ta faɗa a hankali tana kallon sararin samaniya.
Parking area ta nufa inda wata black SUV ke jiranta. Driver ɗinta na hango ta da sauri ya fito ya buɗe mata ƙofar mota.
"Good afternoon, ma'am."
"Afternoon."
Ta amsa a taƙaice kafin ta shiga.
Da sauri drivern ya zaga ya shiga motar ya dauki hanya, jingina kanta tayi jikin seat tana kallon city ɗin Montreal ta cikin window.
Manyan buildings ne dake ƙarawa birnin kyau da tsari, yayin da mutane ke ta harkokinsu ba tare da sanin irin yaƙin da wasu ke yi da rayuwa ba.
*Nigeria Bauchi State Kauyen kafin lemo*
Waheedah ce tsungune a bakin murhu sai aikin fifita wutan daya ki kamawa take kasancewan itace danye ne saboda yanayin damuna ga murhun ma ruwa yamai duka.
Idanuwan ta sun kada sosai sunyi ja saboda hayaki daga can gefe kuma kasan bishiya Dada ce zaune akan tabarma tare da waseelah hira suke yi suna shewa harda tafawa kaman wasu kawaye.
Gyara zama Dada tayi tanayin kasa da murya tace nikam Waseela ina alhajin kine kwana biyu naji bakya maganar sa.
Tabe baki Waseela tayi cikin rashin kunya tace Aa Dada nifa bana son gulma Ina ruwan ki dashi da zaki wani tambaye ni inda yake.
Marairece fuska Dada tayi tace haba yar albarka daga tambaya gani nayi kwana biyun nan dan kudin da kike bani kin daina shiyasa nace ko Alhajin naki ne baya nan.
Tsaki Waseela tayi ke dama koda yaushe baki sa aiki sai na maganan kudi Dada to nida harga Allah na daina baki kudina tarawa zanyi saboda nasan idan aure na da Alhaji ya tashi daga ke har Baban babu abun da zaku tsinana sai ma kusa naji kunya a gaban kawayena, ta gama fadin hakan ta mike ta shiga daki abun ta.
Kwafa Dada tayi ta juya tana kallon Waheeda dake fama da wuta kare mata kallo sosai takeyi Waheeda fara ce amma ba sosai ba sai kuma yanayi na talauci da wahala yasa farin nata sake disashewa gaba daya tana da manyan idanuwa da dogon hanci wanda hakan ya sake kawata fuskan ta giran a cike yake sosai da gashi a yanayin jiki kuma duk da kananun shekarun ta komai nata a cike yake Masha Allah dan idan ba an fadawa mutum shekarun taba za'a dauka takai 17yrs saboda girman jikin da Allah ya bata a takaice dai Waheeda tana da kyau daidai gwargwado duk da tana cikin wahala hakan bai hana kyawun ta baiyanuwa ba sam.
Wani munafukin murmushi Dada ta sake bayan ta gama kallon ta a fili kuma yadda ita kadai zata ji tace oh ni Mairo ga kadara a gabana ashe tun tuni nake wahalan samun kudi dama na dau alkawarin wulakanta rayuwan ki Waheedah kuma indai ina raye saikin wulakanta wllh ta fada tana cigaba da sakin murmushi.
Juyowa Waheeda da ta tashi a gaban murhun tayi da ta samu ya kama dakyar tana kallon Dada jin kaman magana takeyi ita dai bata ji ba kuma bata san da ita take ba ko bada ita ba dan haka a hankali ta taka zuwa gaban Dada tace Dada magana kike yi ne.
Dagowa Dada tayi ta maka mata harara tace to munafuka ce miki nayi dake nake ne zaki zo kaina ki tsaya kamar wata mayyah.
Girgiza kai Waheedah tayi tana dan ja da baya dama abun da take gudu kenan ace da ita Dada take kuma bata jiba tasan zagi zata sha gashi dai bata tsira ba yanzun ma.
#Waheedah
#***