Waheedah

Chapter 7

by @deejarthabdoul12

Cikin sanyin murya Waheedah tace 

“yi haƙuri Dada.”

Hakurin uban ki zaki wuce kije ki ƙarasa min aiki ne ko zaki cigaba da tsayuwa a kaina . Wallahi idan na sake ganin kin tsaya kina kallona sai na karya miki ƙafa munafuka kawai.

Da sauri Waheedah ta juya ta koma bakin murhun.

Dada ta bita da wani irin kallo tare dayin kwafa.
Tashi tayi daga kan tabarman da take zaune ta wuce daki a kwance akan tsohuwar katifan su ta samu Waseela waya kare a kunne ta sai faman kashe murya takeyi tabe baki Dada tayi ta dauki mayafinta ta fita daga dakin.

A tsakar gidan ta tsaya tana kallon Waheeda dake tsince shikafa tace kina gama girkin nan akwai kayan dattina dana Wasila a daki ki tattara ki wanke min su kuma wllh karki kuskura na dawo gidan nan na samu bakiyi ba tana gaba fadin haka ta nufi hanyan fita daga gidan abunta.

Bin bayan ta Waheedah tayi da kallo tana jin zuciyan ta na zafi shikenan ita kam haka rayuwanta zai kare tanayi musu bauta ko kadan bata da hutu a gidan kafin ta gama wani aikin an sake sata wani kuma dolen ta tayi duk da karancin shekarun ta komai ita take yi a gidan girki idan tayi sai an gadama suke sammata randa basu bata ba kuma haka take kwana da yunwan ta sai dai idan Allah ya taimake ta wani lokacin Baba idan ya dan samu kudi yake sayo mata gurasa ta naira dari idan zai dawo.
Ajiyan zuciya ta sauke a cikin sanyi murya tace

"Mami ke kika ce na ringa hakuri komai zai wuce, to Mami sai yaushe ne komai din zai wuce?

Sanin bata da mai amsa mata tambayan nata ne yasa ta share hawayenta ta cigaba da tsince shikafan.

Dada na fita ta nufi hanyan fita daga layin nasu tayi tafiya sosai bayan fitan ta daga layin kafin ta isa wani gida a bakin kofan gidan ta tsaya tana haki saboda uban tafiyan da tasha sai da taji numfashin ta ya dawo daidai kafin ta kutsa kai cikin gidan ba kowa a tsakar gidan hakan yasa ta fara sallama tayi sallama ya kai sau biyar kafin wata mata ta bude labulen daya daga cikin dakuna biyu da suke gidan.

Tana ganin Dada ta washe bakin ta kai Aminiyar dama kece tafe kike ta rangwada sallama haka kaman wata bakuwa ta karasa fada tana kallon Dada dake wurga mata harara.

Tsaki Dada tayi tace ai dole ki fadi haka dama kina jina amma saboda iskanci kika share ni koda yake laifina da na dauko kafa nazo gidan ki me shegen uban nisan nan.

Dariya matar tayi tace haba Aminiyar kinga wannan abun Sauden na makala a kunne na wllh gaba daya ya toshen kunne na ta fada tana nuna Dada earpiece da karamar wayan daya ke hannun ta.

Tabe baki Dada tayi tace to ni yanzu zakimin iso ne ko kuma na juya nayi tafiyata na kwaso uban tafiya da kishin ruwa kinzo kin tsaida ni kina min zance to da Allah ya taimake nima dai ba rana shiyasa ban wahala sosai.

Kamo hannun Dada matar tayi tana cewa ke dai Aminiyar ba'a raba ki da mita wllh to mu shiga cikin dakin ki fada mini meke tafe dake dan nasan wannan zuwan naki bana haka kawai bane.

Dakin suka shiga ta kawowa Dada ruwa tasha bayan Dada ta gama sha ta gyara zama tana kallon matar dake kallon ta itama tana murmushi.

Balaraba wata magana bazo da ita kinsan dai bani da wanda nake shawara da ita bayan ke saboda amintakar dake tsakanin mu Dada ta fada.

Gyara zama Balaraba tayi tace to ina jinki Aminiya.

Kinsan yar guri na Waheedah ko?

Gyada kai Balaraba tayi kafin tace kema dai Aminiya da wata magana Waheedan ce ban sani ba yar wajen maragayiya matar Malam musa Mijin ki.

Hade fuska Dada tayi tace to bance kimin dogon bayani ba tambayan ki kawai nayi.

Murmushi Balaraba tayi dama tasan yadda Dada ta tsani Waheeda da mahaifiyarta da ko maganan ta bata so ayi mata kafin tace to Aminiya meya faru da Waheedah din.

Gyara zama Dada ta sake yi a karo na ba adadi tace Balaraba kinsan yadda na tsani yarinyar nan kamar yadda na tsani uwarta bana sonta bana kaunar ta ke ina gaya miki me sonta ma na tsane shi zaman da take yi a gidana ma wllh ba yadda zanyi da ita kuma kinsan Malam Musa duk irin asirin da nake masa a kanta saboda ya tsane ta asirin baya cinsa na rasa me yasa dan haka Balaraba na yanke hukunci zan kai yarinyar can birni gidan karuwai so nake ta zama karuwa ta yadda zata na samomin kudi tunda dai dama babu abun da take tsinana min a gidan sai bakin ciki.

Balaraba da tunda Dada ta fara magana ta zuba mata ido tana sauraren ta jin Dada tayi shiru sai ta sauke ajiyan zuciya dan ita kam duk jikin ta yayi sanyi bata dauka rashin imanin Dadan harya kai haka ba da take tunanin tura yar mutane karuwanci akan wani dalili nata na banza da wofi.

Jin shirun nata yayi yawa yasa Dada zungurin ta da kafanta tana cewa wai Balaraba baki ji abun da nake fada bane kinyi shiru kin mai dani mahaukaciya.
Murmushi Balaraba ta kirkiro tace naji mana Dada shawaran naki ne baimin ba wllh to yanzu idan kika turata birni karuwanci shi Malam Musa me zaki ce masa idan ya tambaye ki ina take.

Tsaki Dada tayi kefa dama wani lokacin ba'a abun arziki dake wllh ina ruwa na da wani Malam Musa tuni zan kaishi gurin Malam na kan dutse ya rufe masa baki karya tambaye ni ita take kuma da kike cewa shawara na bai miki ba ai dama bance dole sai ya miki ba shawara ce dai na yanke kuma banga uban da ya isa ya hanani ba wllh.

Shiru Balaraba tayi ta rasa abun da zata sake cewa kuma can kuma wani tunani ya fado mata a rai da sauri ta kalli Dada dake faman karkada ƙafa tace Aminiya na tambaye ki.

Kallon ta Dada tayi ta tabe baki tace Ina jinki.

Yanzu ke a ganin ki karuwan cine kawai zatayi ta samo miki kudi Balaraba ta fada tana kallon ta.

To Balaraba ki fadamin me zatayi ta samu kudi idan ba karuwanci ba yarinyar nan a yadda take da jiki me kyau tuni zatayi kasuwa wllh.

Murmushi takaici Balaraba tayi kafin ta gyara zama tana kallon Dada da kyau tace to bari na fada miki wani abun da baki sani ba Aminiya wllh ba'a samun kudi ta karuwanci a birni abun da sai suje su kwana bai wuce dubu biyar za'a basu ba to ki fadamin dubu biyar nawa yake a wannan zamani a karshe sai ka kare kai bada kudi ba kaida kwasan zunubai a gurin Allah shiru tayi tana kallon Dada da itama tayi shiru tana sauraren ta itafa bawai zunuban da Balaraba ta fada bane damuwan dubu biyar din da tace to ita me dubu biyar zai mata ita da take tunanin samu dubbannin kudi.

Dan tabo ta Balaraba tayi ganin ta tafi tunani ajiyan zuciya Dada ta sauke tace to Balaraba yanzu me kike nufi.

Gyara zama Balaraba tayi tace ina da wata shawara da idan kin bita zaki samu kudi fiye da zaton ki kuma zaki rike kudin da baki taba rikewa ba tunda kika zo duniya.

Da wani irin sauri Dada ta riko hannun Balaraba tace Dan Allah ki fadamin wani kalan shawara ne Aminiyata.

#Waheedah 
#***