SIRRIN ZUCIYA

Chapter ten

by @aysharano22

🤍SIRRIN ZUCIYA🤍

By Aysha Rano✨

🤍YOTA🤍

Kallonsu kawai Suhana keyi lokaci daya saiga hawaye suna wanke mata fuska, saidai wnn karon hawayen farin ciki ne bana baqin ciki ba…na farin cikin samun qawaye kmr su biyun nan da komai wahala komai runtsi basu taba yunkurin barin side dinta ba.

Hannu Lilly takai tana wiping mata tears din tace “enough of all these tears butter yanxu lokacin kukan wancan bastard din ne ba naki ba”…Esther ma tace “yes ya zama dole mu nuna mashi bai isa ya taba butter yaci banza ba, sai ya biya for what he’s put you through”…kai Suhana ta shiga gyadawa as itama sai yanzu taga ya zama dole tayi maganinshi sam bai kamata ta bari ya tafi scot free da wnn humiliating dinta da yayi ba.
Rungumesu ta sakeyi duk su biyun tana cewa  â€śi love you so much girls, i don’t even know how to thank you”…rungumeta back suma sukayi kafin Lilly tace “you don’t have to thank us girl remember the rule of friendship, no sorry no thank you”…dariya ta saki da wet face dinta tana sake kankamesu cox she actually feels better mgnr da tayi dasu yanzu, tace  â€śyes no sorry no thank you, but still i have to thank you guys…thank you so so much i really love the both of you”…sukace “we love you too butter”…bayan sunyi breaking hug din Esther tace “bamu kadai ma ya kamata kima godiya ba hadda fans dinki da suka tayamu boycotting and reporting…snn plss Su if it’s possible ko small video kiyi dominsu kiyi posting, bakiga yanda suka damu sunaso susan halinda kike ciki ba”…nanny da tun daxun take kallonsu with admiration itama sai murmushi take jin an samu sauqin matsalar sai yanxu tasa baki cikin mgnr nasu tana cewa “Esther is right Suhana you have to do that video ko don ki nunama haters cewa you are a very strong girl that ba ko wane small abu ne zai iya breaking dinki ba…suma fans dinki hakan zai nuna musu you are okay snn ki gode musu kan abinda sukayi”…kai Suhana ta hau gyadawa kafin tace”ok nanny I’ll do the video”…nanny ta matsa kusada ita tareda pecking head dinta da murmushi tace mata  â€śthat’s my strong girl…now let me go to the kitchen and prepare something really nice for you girls coz you deserve it”…murna su Lilly suka hau yi don sunason abincinta suka amsa mata da toh ita kuma ta juya ta fita daga dakin har cikin ranta tanajin dadin yanda kafin abun yayi nisa akayi tackling dinshi, dukda dai baa isa a hana mutane fadar ta bakinsu ba kmr yanda baa isa a hanasu posting abinda sukaga dama ba, at least dai tasan she’s not alone,  and all thanks to Esther and Lilly sai kuma Fans din Suhana da sometimes take kiransu da butter gang.

Tana fita parlor sukaci karo da Desmond, shima kana ganinshi zakaga damuwa tattare dashi yana ganinta ko gaisawa basuyi ba yace  â€śnanny is she okay pls?”…da murmushi nanny ta amsa mashi da “yes she is”…kai kawai ya gyada ba wai don ya yadda da mgnr ba yace “alright bari in ganta”…nanny ta amsa da”ok”…snn tayi kitchen abunta shi kuma ya nufi dakin Suhana.

Duk wnn budurin da ake daddynta bai saniba don baya garin ma gaba daya ya tafi Abuja tun around 8 na safe.
Yana shigowa dakin kai tsaye inda suke zaune ya nufa ya kama hannunta ya mikar da ita tsaye duk yabi ya daurama kanshi damuwa yace  â€śbaby are you ok?..are you fine?”…hannunshi Suhana ta kama tana dubanshi tace “yes am fine babe, don’t worry”…kallon fuskanta kawai yakeyi kmr bai yadda da abinda ta fada ba kawai saiya rungumeta tsam a jikinshi yana shafa kanta a hankali yace “trust me babe i’ll show no mercy to duk wanda sukayi posting video nan…my boys are already on it nasan before the end of today duk zasu shigo hannu, daga nan ni kuma zan nuna masu no body messes with a soldier’s property…saina dauki fansan duk hawayen da suka zuba a idanunki, i will show them hell”…kana ganin karasa mgn fuskarshi na daddaurewa zaka san ba karamin 6ata ran sojoji akayi ba…murmushi Suhana ta saki bayan ta dago daga jikinshi ta kama hannunshi suka zauna kan sofa kafin cikin kwantar da murya tayi mashi bayanin duk yanda sukayi da su Esther yanxun nan…hankalinshi yaji shima ya dan kwanta jin bata dauki abun kmr yanda yake tsammani ba amma dukda haka baiji zai iya yafema duk wanda keda hannu cikin abun ba don haka yace  â€śbut i will still deal with them”…sake lankwasa murya tayi tana ce mashi  â€śbaby plss no…kaga wanda sukayi posting fa ba sune the main issue ba su posting kawai sukayi maybe don su samu viewers da followers, the main villain here is the guy in the video”…shiru taga yayi kmr yana tunani lokaci daya kuma kmr ya tunada wani abun yace “yes that bastard…that guy will definitely pay for this”…yana rufe baki tace “exactly my point baby but please i don’t want you to do anything to him just let me handle him myself?”…wani kallo yake binta dashi kafin yace “how do you think you can handle him baby kawai ki bari insa boys dina su kamashi su kullemin shi a barrack sai na tabbatar da yayi learning lesson dinshi zansa a sakeshi”…sake kwantar da murya tayi tana cewa  â€śno baby ba sai anyi haka ba pls, kasan i know you kuma nasan abinda zaka iya aikatawa, so i don’t want you to touch him at all…please!”…ta karasa mgn tana begging dinshi don a rashin imani irin na sojoji tasan tsaf zai iya sawa ma a kasheshi don ta lura su kisa ba wani babban abu bane a wurinsu yanxun nan zasuyi kuma bazasu bar duk wani evidence da zaisa a kamasu ba…kallonta yakeyi jin abunda take fada yace “why?”…tace”sbd banason kayi committing crime because of me…i told you i can handle him myself trust me”…shiru yayi kmr bazaice komai ba kafin can yace “alright then..but duk kikaga abun is getting out of your control kawai ki kirani, nayi alkawarin saina dawo dashi cikin hayyacinshi”.

Sai a snn hankalinta ya kwanta ta saki murmushi tana gyada mashi kanta tace “zan ma iya babe, i love you”…pecking lips dinta yayi shima yana cewa “i love you too”.

Dan wulakanci ashe video Esther ta shiga musu sai hailing dinsu take tana cewa itama Allah ya bata boyfriend kmr Capt Desmond sukaita mata dariya…sai a snn ya samu yayi musu godiya kan abunda sukayi su kuma sukace ai it’s nothing, they did it for their best friend.

Sallama suka musu wai zasu tafi Suhana ta wani bata rai tana cewa “aah ina zakuje kuma?…i thought you guys are gonna stay here with me?”…Lilly ce tace “well, da munyi tunanin haka, but now that your boyfriend is here i think gara mu tafi kawai”…tana rufe baki Suhana ta sake cewa “no noww…baby has no problem with you guys staying, right baby?”…tayi referring question din to him da sauri ya amsa mata da”yes as long as my baby wants you guys to stay, banida matsala da hakan”…sake kallonsu Suhana tayi tana cewa”see, yace bashida matsala da haka so plss karku tafi, i want to spend the rest of today with all three of you since it’s public holiday ba school…with my best friends and my boyfriend”…Esther ce tayi saurin cewa  â€śok if you insist, zamu zauna as long as baza muyi inconveniencing dinku ba”…tun kan ta rufe baki Desmond yace “no there’s no any inconvenience at all”…nan dai sukace sun hakura zasu zauna shi kuma yace “fantastic, so what do you guys have in mind?…do you want us to hang out or stay indoors?”…ai tun bai karasa rufe baki ba suka ce “hang out”…Suhana dake kallonsu da murmushi juyawa tayi tana kallon Desmond din tace “this girls really like hanging out with me”…jan cheeks dinta yayi yana cewa “don’t blame them baby you are too cute that even i like hanging out with you”…ya karasa mgn da manna kiss a goshinta.

Su Lilly suka hada idanu hadda wani gyaran murya irin wai asan suna nan…Suhana ta hararesu kafin tace “so yanzu ina kukeso muje?, cinema..or parks or restaurants?”…da sauri Lilly tace “Cinema”… Esther ma tace “yeah Cinema will do”…kai Desmond ya gyada yana cewa “Cinema we do then”…Suhana tace “alright let me come and start getting ready”…Esther tace “yes you should…yanxu dai zanje kitchen wajen nanny inga me take dafa mana, i can’t wait to taste it”…tana rufe baki Lilly ma tace “me too”…haka dai suka juya suka fita leaving only the lovebirds a cikin dakin.

Kmr jira yakeyi suna fita ya dagata cak ya zauna gefen bed dinta ya ajiyeta a jikinshi kafin ya shiga kokarin hade lips dinshi da nata har wani lumshe ido yake murya a rarrabe yake cewa “oh..my..God..i missed this baby..i missed you”.
Jamye bakinta tayi cikin dabara ta wani shagwabe fuska tana dubanshi tace”i missed you too babe”…daga haka kuma saita rungumeshi, cikin ranta tana addu’a Allah sa wani abu bazai biyo bayan rungumar ba.

⸻

Lee ne yayi parking cikin compound dinsu, kai da ganin yanda yayi parking din zaka gane ba karamin sauri yake ciki ba…agogon hannunshi ya duba yaga its past 11 am already, yaja dan siririn tsaki ganin ashe dare ya farayi har haka kamata yayi ace idan ma bai isa club ba yanxu to yana dab da karasawa amma gashi dalili yasa dole saiya dawo sunyi mgn da Ayaan.

Bude motar yayi ya fita bayan ya kasheta ya nufi hanyar da zata sadashi da staircase sai sauri yake kmr zai tashi sama…yana gama haurawa ya tura kofar yaji a bude ma yake hakan ya tabbatar mashi da cewa bai kwanta ba kenan don haka yana shiga ciki direct ya nufi dakin Ayaan a daidai lokacinda shima ya fito sanye da gym outfit dinshi don dama sai dare yake workout dinshi kmr dai yanzu da ba mutane cikin gym din…karo sukayi a bakin kofa Ayaan yaja da baya yana dubanshi da mamakin dawowarshi by this time don yasan duk ya tafi club yana iya kaiwa 3 to 3:30 na dare a can yau kuma sai gashi ya dawo before 12, ya tabbata da akwai wani abunda ya dawo dashi.




Rano✨