Chapter 12
by @reza12
MATAR MAZA 12
(Life story)
A lokacin da ta tabbatar da an ɗaura auran sai kuma wani irin tsoro da farg5 ya fara shigar ta, sai take jin kaman tayi kuskure, bata taɓa jin irin wannan yanayin a sauran auran nata ba, hakan yasa tayi kamar bata da lafiya, tunanunnunka ne suke tai mata shawagi a zuciya. Har suka iso cikin gidan nata tana ganin abun Kamar wasa kumar kamar ba wasa ba. Ya fara sakƙowa ya buɗe mata mota ta fito tana jin gabanta na cigaba da luguden faɗuwa da sauri da sauri har fiye da ɗazu. Har suka shiga cikin palon gidan ta na ta mamakin wannan auran da ko ita da kanta tsoron sa take. Har cikin ɗaki ya kaita ya zaunar da ita shima ya zauna yana cigaba da yabonta da kuma ƙara nuna mata cewar yayi dace da ya sameta a matsayin mata, ji yake kamar ya cinyeta ɗanye ba tare da an soya ba. Daga yadda yake rawar ƙafa kawai ta sake tabbatar da cewar da matsala. Tashi tayi da sauri ta shiga toilet ganin ya fara ƙoƙarin cire kaya, ta na shiga ta lalubo number Sadiya ta rangaɗa mata kira, sai dai taji murya Ummi ta ɗaga. Da yake itama Ummi ɗin tana fahimtar ta sosai, domin bayan Sadiya itama tana iya yin sirri da ita, har ma tafi Sadiya ɗin fahimta, kawai dai saboda ita bata girma sosai bane amma a kwai wayo.
Ta ce "Ummi ina Sadiya?"
"Hajiya ta aikota gidanki, shine ta manta da wayar, bata ma daɗe da fita ba".
"To ina Hajiya ɗin?"
"Gata cen tana cin abinci, ko na kai mata wayar ne?". Sai ta sauke ajiyar zuciya
ta ce "Tom a'a Ummi, kawai kice ina gaidata, kuma kice mata anan Sadiya zata kwana idan tazo, zuwa gobe sai ta dawo". Ummi ta ce "To Anty, idan zata dawo ki bata wannan kayan nawa da kika bani, na manta dasu a cikin dakin ki".
Daga haka ta kashe wayar domin jin yana kiranta daga waje. Ta amsa, ta na fitowa kuwa ya rungumeta yana faɗin mai taje yi a toilet bata gayyaci shi ba, ko so take ya mutu da kewarta. Ya faɗi maganar yana shige mata kamar maye. Azima taji kamar ta ture ɗan iska jin tambar banza wai mai taje yi, ko uwar mai ake yi a ciki idan an shiga toilet. Ta ce "Yanzu dai mu zauna muyi magana, bayan aure a kwai abubuwan da ake yi da yawa wanda bamuyi maganar su ba, kaga akwai kayan aure, kuma ya dace ace ka san wasu abubuwa na addini da kuma batun..." Tun kafin ta ƙarasa ya ce "Duk na sani, zuwa gobe zamuyi wannan maganar, yanzu dai barci nake ji, babu abun da zan iya fahimta wallahi, ba dai anyi auran ba, kuma dai na musulunta ɗin ba, komai zai warware in sha Allah". Tana jin haka hankalinta ya ɗan kwanta, domin ita a tunaninta barcin gaske dai yake nufi da yace barci yake ji. Sosai ya nuna mata ƙarara abun da ya ke so, domin daga karshe ma a fili ya faɗa mata ganin tana bashi wahala. Har sun fara abubuwa suka ji ana buga musu ƙofa, har ta manta da zuwan Sadiya. Ta gyara kanta kafin ta buɗe sai ga Sadiya tsaye fuskar nan a turɓune daga gani bata son aiken, ta matsa mata ta shigo tana faɗin "Ban san yaushe kika fara barcin wuri da har zaki rufe gida ina ta bugawa tun ɗazun bba". Ta ƙarasa tana zama a palo. Azima ta ce "Ba barci nake yi ba, kawai banji da wuri bane". Jin yanayin muryarta yasa Sadiya ɗin ta kalleta kafin ta ce wani abu tayi saurin faɗin "Sadiya nayi aure fa ɗazu". Ta na rufe baki kuwa sai gashi ya fito daga cikin ɗakin daga shi sai gajeren wando yana kiran sunanta ganin ta daɗe. Gaba daya suka tsaya suna kallon juna. Sadiya na kallonsa, Azima kuma na kallon Sadiya, shi kuma Abraham yana kallon Azima. Kusan minti biyu kowa ya kasa magana sai bin juna da kallo. Shine ya samu damar faɗin "Bakuwa muka yi ne a daren ga?" "Eh ƙanwata ce Sadiya, zata kwana anan ne, nice na kirata". Sadiya tayi saurin faɗin "No yanzu ma zan tafi, dama sako ne na kawo mata, Allah ya bamu alkairi". Ta faɗa tana miƙewa tayi waje. Da sauri ta bi bayanta tana kiranta. Suna isa waje kuwa Sadiya ta juyo a fusace ta ce "Wallahi sai Hajiya taji wannan abun, haba anty Azima, Arne fa, wani irin son zuciya da son kuɗi ne haka, to wallahi sai na fadawa Hajiya na rantse da girman Allah, haba dan girman Allah, ai abun yayi yawa, mai kuma kike nema a duniyar ga?". Ta faɗa kuka na son kufce mata. "Ke wallahi ya musulunta, dan Allah tsaya kiji, ba arne bane, sunansa Ibrahim". "Ni ba abun da zaki faɗa min, ko ya musulunta ai sai kin bari ya fara samun komai na addini, kuma yazo gida amma haka kawai, daga mudulunta sai aure, wai ma ke baki tunanin wani abu ya faru ne, Allah sai na fadawa Hajiya na rantse miki da Allah, abun yayi yawa". Jin ta dage ne yasa ta ce "To kije ki faɗa mata ɗin, dan Allah kiyi sauri kar ƙuda ya riga ki, amma ki sani idan kika kashe Hajiya kune a cikin babbar matsala domin ni ko yanzu nayi gaba na barku, ke kuwa da sauran kune masu bukatar ta har fiye da ni, ko tunaninki ban san abun da nake yi bane, ni dake duk mun san irin ciwon Hajiya, ƙaramin Abu zai iya Kaita har kushewa, dan haka idan kin shirya rasa ta ga fili ga mai doki dan ubanki, Allah ya bada sa'a, sai da safe". Ta na faɗa ta rufe kofar ta barta tsaye ranta na ɓaci. Har yaushe ma Sadiya tayi hankalin da zata faɗa mata haka, komai da takeyi ba dan su bane, ko tafi so ta dinga bin maza ne ko Shaye-shaye. Sosai ta shiga tunani da kuma tsoron kar Sadiya ta faɗa, ko hakan da tayi barazana ce kawai amma har zuciyarta tana tsoro sosai, domin tana jin ma tafi su son Hajiya wallahi. A cikin wannan daran dai Abraham ya angwance da matarsa kaman yadda ya ƙwallafa rai, sosai ya ɓarji angwaci ya kawar da ƙishin da yayi masa katutu a rai da zuciya. Har washegari tana ta addu'a a ranta akan Sadiya, haka ta saka waya a gaba tana jiran kiran Sadiya ɗin ko na Ummi ko Hajiya, amma shiru babu ko ɗaya, ita kuma ta kasa kira, gashi bata son kiran Sadiya ɗin saboda kar ta ga lagonta. Shi kansa Abraham sai da ya tambaye ta ko dai wani abu na damunta ne, ta ce masa ba komai. Tana cikin wannan tunanin kuwa sai ga kira daga number Sadiya ɗin wanda yasa hantar cikinta kadawa da wani irin sauri, tana kallo har ta tsinke, sai ga wani kiran, hakan yasa ta ɗaga tana addu'a a ranta. "Kin faɗa har ta mutu ɗin ne kika kira ni ko dai yaya?" Ta faɗa a dake babu wasa. Sadiya ta ce "Sakon jiya ne dama da na manta ban faɗa miki ba, Hajiya ce tace duk lokacin da kika samu dama ki tambayi mijinki tana son ganinki". Ta ƙarasa a sanyin murya. Azima ta ce "Mai ya faru? Kin faɗa mata ɗin kenan ko yaya?" Ta tambya domin ita ba wannan take son ji ba. Ta ce "Ba ke kika ce na faɗa ba, to meye kuma na tambayar?" Ta kashe wayar abun ta. Tayi jim kaɗan tana tunani. Tabbas idan da ace ta faɗa da ba wannan maganar ake ba, hankalinta taji ya ɗan kwanta kaɗan. Tashi tayi ta koma cikin ɗakin da yake, har zata shiga taji kamar ana magana, hakan yasa ta tsaya tana surara, sai dai bata jin abun da yake cewa amma ta fahimci da mace yake waya, a ranta ta ce kwana ɗaya da aure har ya fara magana da wata. Ai kuwa da karfi ta tura kofar daidai lokacin ta tura wayar a karkashin fulo. Azima da rashin hakuri ta ce "Dawa kake waya?" Ta faɗa tana tsare shi da ido kamar zata kai masa duka. Tuni ya fara kame-kame na rashin gaskiya. Ta ce "Bani wayar mu gani?" Ya kalleta da kyau sai kuwa ya mike ya ce "Baki yarda dani ba kenan?" "Eh ban yarda ba, amma idan kana so na yarda bani na gani?" Ta sake faɗa ƴan kishin na sake zuwar mata. Ya ce "Ina magana ne da manaja akan..." "Bani wayar na gani koma da waye?" Ta katse shi daga dogon jawabin da ya kinkimo. Sai ya sa hannu ya ɗauko wayar ya mika mata. Ta karɓa ta ce ya cire mata ki ɗin. Ya amsa ya cire. Sai dai kafin ya bata ya goge duk inda ya shiga a wayar ta hanya mafi sauki. Ta gama dubawa bata ga komai ba, kuma ta gane gogewa yayi, domin bata ga kira na yanzu ba, sai ta miƙa masa tace "Muddin kana son zaman lafiya dani to babu kai babu kowacce shigiya a waje, idan kuma ba haka ba zaka ga asalin fuskar Azima". A lokacin dai ya lallabata komai ya wuce har ma ya samu abun da yake so.
Haka dai zaman nasu babu laifi har bayan sati biyu, ta koma kasuwancinta shima ya koma aiki, sai dai ko sati ba'ayi ba ya koma suka jone da Mera da sauran matan nasa na titi, duk da auran sha'awa yayi amma kuma ta manne masa a rai, sosai yake ji da ita, baya ko so ta gane cewar yana bin mata shi yasa muddin ya shiga cikin gida to ya gama da ko wacce shigiya. Sosai yake kiyayewa kar ta gano, domin yana jin sonta tun da ya sameta. Bangaren Mera kuwa so take ta rama abun da tayi mata, hakan yasa take yin nata shirin yadda Azima da kanta zata gane cewar shuka tayi a idon makwarwa, koda za'ayi aihuwar guzuma wallahi sai kowa ta rasa, wannan dalilin yasa ta sake manne masa har suka sake yin sabo fiye da baya. Bangaren Sadiya kuwa bata iya faɗawa Hajiya ba, domin dai ta yarda da batun Azima ɗin na cewar idan har ba so take ta kashe ta ba to kar ta faɗa mata. Hakan yasa itama ta ɓoye aka tafi a haka, sai dai itama tayi sabon saurayi wanda suka haɗu a super market mai suna Ali, kusan sati ɗaya kenan, sai dai irin yaran nan ne da basu da yancin kansu, domin dai sai suna cikin hira taga ya ɗaga waya yace gashi nan, hakan yasa ta tambaye shi ko waye ke yawan kiransa, nan ya sheda mata cewar yayansa ne, anan ya bata labarin cewar basu da iayaye, daga shi sai yayarsa Mace tayi aure sai yayan nasu wanda shine komai nasu, shi ya ɗauki nauyin karatu da komai nasu, ko aikin ma da yake yi shi ya samo masa. A lokacin da yake bata labarin kawai Azima take tunawa, kamar dai su da ita, itace komai nasu duk da kuwa ita mace ce kuma a lokacin ma ba wata babba ba, amma ta ɗauki nauyin su, take taji wani irin son yyar tata da kuma ƙaunar ta na ƙara shigar ta. Tun daga lokacin ta daina jin haushin yayan nasu, wani lokaci ma ita da kanta ke tambar sa yau Yaya bai kira ba ne. Sosai suke soyayya har ma Hajiya da Azima sun san da shi, kowa yayi na'am da shi Ali, domin bashi da wata matsala kuma yana da abun yj, Mansur kuwa tuni uwar tasa ta samo masa wata, duk da baya so haka dole ya aura, bai daina bin Sadiya a ɓoye ba, ita kuma ta yi alkawarin babu ita babu shi tunda har uwarsa tayi masa baki kuma yayi aure abunsa, mantawa ne dai ba zata taɓa iyawa ba domin ya taimake su sosai a lokacin da basu da kowa, shi yasa ta ajiye shi a wani guri da ban a ranta.
Fitowarta daga wanka kenan taga wayrsa na ƙara, kuma bata ganshi a ɗakin ba alamar dai ya tafi, hakan yasa ta daga tayi shiru. Sai kuwa ta tsinkayo muryar mace na faɗin tana ta kiransa dan Allah ko ya manta da ita ne. Ai kuwa Azima ta ce "Ya manta da uwarki ne, yar iska wawiya mara mutunci, idan kika ƙara kiran wannan wayar sai na sa an kulle min ke, dan ubanki baki san yana da mata bane?" Tana cikin haka ya shigo gidan alamun dai wayar ya manta. Ya tsaya yana kanllonta. Ya ce "Meye haka kike yi, kin san wacece ita? Abokiyar kasuwanci ce fa, wai mai yasa ke baki da yarda ne dan Allah?" "An ki a yarda ɗin, abokiyar kasuwanci ce zata ce ka sahreta, ko kai ɗaya ne a kasuwar da ba zata nemi wani ba?" Ya ce "Bani waya ana jira na na makara?" "Ba zan bayar ba sai ka faɗa min wacece?" Ya kalleta ya kawar da kai yana huci ya ce "Abokiyar kasuwanci ce, suna son abu ne ni suke jira, idan baki yarda ba kizo mu tafi ofishin nawa zaki same su acen". Ya faɗa da wasa sai kuwa ta saɓo gyale ta ce su tafi. Ya ɗan kalleta yana girgiza kai. Tabbas lamarin yarinyar nan sai ya sake taku, shi ba dan ma yana sonta ai wallahi tun washegarin auran zai saita mata hanya, amma ina ba zai iya ba, sai ya more sosai lokacin da ya gama da ita sai ya sallameta, yanzu kam dole ya lalaɓata. Haka suka kama hanya har kamfani. Kuma kaman yadda yace ne mutane ne ke jiransa, sai dai ba haka bane, suna kan hanya ya shirya komai domin dai wata yar balaja'u ya samu suka shirya har ya kama mata daki shine zai je. Itace a gaba ta buɗe ofishin sai ga mata biyu da wani na miji zaune suna shan shayi, ga kuma ɗaya daga cikin ma'aikatan kamfanin na zaune tara da su. Suna ganinsu kuwa suka fara gaida shi suna musu Barka da zuwa, haka dole ta hakura. A lokacin suka haɗu da Namra tun bayan aure. Ta ce "Hajiya Namra Sarkin fushi". Tayi yaƙe kawai tana son nuna mata babu komai. Sosai ta nuna Mata ba komai suka sha hira har lokacin ta shi yayi. Sosai yake bata kuɗi, duk abin da take so, sannan yadda yake ji da ita Kamar dai yana tsoranta, gashi ya fara jin yana sonta, hakan yasa yake tsoron baiyana mata abun da zai iya kawo musu matsala, duk yadda yayi zaton samunta sai ya samu tafi hakan ma, shi yasa yake kara jin son kasancewa da ita a kowane lokaci.
Ta shirya tsaf domin zuwa gidan Hajiya tun wannan lokacin, hakan yasa tayi shigar matan aure, ta saka katon hijjabi har ƙasa, tayi musu tsaraba sannan ta nufi gidan. Sosai tayi kewar uwar tata, su kuwa dama ƙannen nata kullum suna tare ko a way ko suzo. Tun daga ƙofar gidan ta fara tabbatar da cewar akwai matsala ganin kusan yan uwanta maza a Kofar gidan, haka ta wuce su babu ko sallama bare gaisuwa. Ko tsakar gida ma ta samu wasu da yawa kaman dai abu ake yi a cikin gidan. Da gudu Ummi da take zaune a kofar daki ta nufeta hakan ya dawo da hankalin yan gidan gaba ɗaya gurinsu. Azima na ɗaga kai suka haɗa ido da Anty Yayar Musu, tayi kaman bata ganta ba ta shige sashen su abunta. Tana shiga Hajiya kuma na ƙoƙarin fitowa suka haɗu. Da karfi ta rungumeta tana faɗin "Hajiya nayi kewar ki, duk ina jin kamar ban cika daidai ba. Itam ta rungumeta tana binta da kallon burgewa da kuma jin daɗin yadda ta dawo. Ta ce "Ko ke fa Azima, ji fa yadda kika yi kyau yanzu da kika zauna a gidan mijinki, yanzu da na kwana biyu ban ganki ba ji yadda kika dawo wata babbar Mace mai kamala da mutunci, gashi harda hijbi, kai alhamdu Lillah ma sha Allah, ko kefa. Haka Hajiya ta dinga murna tana farinciki. Bayan ta zauna ta ce "Yanzu dai ga yan uwnki a gida gaba ɗaya kije ki gaida su kafin kowa ya tafi, naji daɗin ma zuwan naki a wannan lokacin wallahi". Azima ta ce "Hajiya wallahi babu wanda zan gaida, yadda babu ruwansu damu haka muma, dan haka kar ma ki wahalar da kanki ba zan gaida kowa ba wallahi". Hajiya ta ce "Ban isa ba kenan Azima?" "Kin isa har ma kin fi, amma dai ba zan gai da kowacce shigiya da shige ba, duk cikinsu waye ya damu dani za wa ya taɓa kirana ko ya zo inda nake, nifa bayan ku bani da wani ahali ato". Jin haka yasa Hajiya yin shiru tana fatan Allah ya shirya Azima, domin tunda tace haka to kuwa ba zata yi ɗin ba. Haka kuwa kaman yadda tace ba wanda ta gaida harda kuwa su Ammy da Mama. Sannan haka ta shiga kichn ɗin cikin gida tayi musu girki mai rai da lafiya yaji nama, a lokacin ta tuno da Baba harda hawaye tayi domin kawai ta tuno da girkin da take masa a cikin kiching ɗin ne, ta gama ta kwaso musu suka ci, ta sake tambayar Hajiya magani tace tana sha kullum, nan ta duba abun da basu da shi ta rubuta saboda kar ta manta. Sai kusan magriba ta dawo gida, lokacin ya rigata da dawo. Bayan sallar Isha suna cin abinci suka ji ana buga musu ƙofar palo, suka kalli juna sai ta mike tana tambayar waye. Taji Muryar mace, hakan yasa ta buɗe suka haɗa ido da Mera cikin wata yar banxar shiga irin ta mazu nema a titi. Ta ce "Nazo gurin baby ne, ina fatan yana nan?" Azima da ta ji wani abu ya tsaya mata wa makoshi ta ce "Eh yana nan shigo". Ta bata hanya a ranta tana jin dole yau sai ɗaya ya mutu a cikin su uku wallahi. Mera kuwa ta karaso har Palon tana kiran sunansa. Yana ganinta kuwa ya mike tsaye cike da mamaki har yana kwarewa domin dai ta bashi mamaki. Ya ce "Meye haka Mera, baki da hankali ne?" Ta ce "Kawai dai nayi kewar ne shi yasa na biyo ka". Tana rufe baki taji sauƙar abu kanta wanda bata ma kula ko menene ba. Ya buɗe baki zaiyi magana shima ta buga masa tana faɗin "Tsabar rainim wayo har cikin gida na, to wallahi sai na kashe ki Mera, daga yau zaki gane ni ba sa'ar uwarki bace, iskanci har cikin gida na...📝
To yan amana mun gama free page, daga wannan page ɗin Matar maza ya koma prvt, group ɗari biyar ne, vip Kuma 1k. Babu dogon jawabi duk wacce ta shirya bin wannan labarin tayi magana ta wannan number *** please iya whasop banda kira. Daga yanzu a iya Arewaapen za'ayi posting da kuma group ɗin wanda suka biya. Ƴan amanar S Reza sai mun haɗu daku. ina muku fatan alkairi.