Chapter 8
Murmushi Balaraba ta sake ganin yadda Dada ta rude saboda taji maganan kudi kafin tace ai Aminiyar in dai zaki bi shawarata to keda talauci sai gani sai hange daga nisa.
To ki fadamin mana sai faman jamin rai kike haba Balaraba Dada ta fada cike da zakuwa.
Gyara zama Balaraba tayi tace kanwata karime da take birni nasan kin santa, to aikin ta dama acan birni tana bin gidanjen masu kudi ne tana kai musu yan aiki, kuma ba karamin kudi ake biyan su ba a yadda tace min ma kudin yana kai dubu dari zuwa dubu dari da hamsin.
Wani irin zaburan da Dada tayi sai da tasa Balaraba ta tsorita, dubu dari da hamsin fa Balaraba hanya kinsan me kike fadi kuwa.
Tsaki Balaraba tayi tace to na taba miki karyane Aminiya idan baki yarda ba yanzu sai na kira Karimen kiji a bakin ta.
Yauwa kira ta kawai Balaraba ai gara naji ta bakin ta Dada ta fada tana zama gefen Balaraba.
Girgiza kai Balaraba tayi ta dauki wayanta ta fara latsawa kafin takai wayan kunnen ta har saida wayan ya kusa katsewa sannan aka dauka daga can bangaren a handsfree Balaraba tasa wayan saboda yanda take ganin Dada ta zaku nan tsab zata kwace wayan daga hannun ta.
Gaisawa sukayi da Karime kafin Balaraba tace Karime dama wata yarinya ce aka samu Babar ta tana son tura ta birni aikatau a birni shine nace bari na miki magana saboda nasan baza ki rasa inda zaki kaita ba acan birnin.
Daga can bangaren Karime tace to Alhamdulillah Yaaya ai faduwa tazo daidai da zama dan dama akwai wani gidan da suka sani nema masu me aiki to harma ina shirin na kira su nace musu suyi hakuri ban samu ba sai kuma gashi kin kira gaskiya naji dadi wllh.
To Masha Allah Karime nima naji dadi kinga saina fadawa Babar tata su fara shiri.
Eh hakan za'a yi Yaaya, amma sai dai wani hanzari ba gudu ba sufa inda suke neman me aikin ba'a nan kusa suke ba suna birnin Abuja ne kinga zaiyi wuya subar yar su tayi nisa dasu haka.
Ai kafin Balaraba tace komai Dada da tunda suka fara magana ta kurawa wayan ido ta kwace wayan daga hannun Balaraba tace yauwa Karime kina jina nice nan Babar yarinyar Waheedah ce yar gurina ai kin santa kuma ko nan da birnin Sin ne zan turata sannan Balaraba tace min kudin da za'a biya ta yakai dubu dari da hamsin ko?
Karime da ta gane muryan waye ne tace eh hakane Yaaya Mairo kinsan gidanjen manya ne sosai kuma inda son samu ne tunda har kin amince to ki shirya yarinyar zuwa gobe zan zo na dauke ta saboda suna son yar aikin ne a cikin wannan sati kuma kinga yau Alhamis gobe kawai sai nayi sammako nazo gidan ki na dauke ta mu wuce.
Cikin zakuwa Dada tace to shikenan Karime bari yanzu nan ma zan tashi na koma can gida nasa ta ta fara shiri wannan abun Alkhairy ai bazan yi wasa dashi ba tana gama fadin haka ko jiran abun da Karimen zata ce batayi ba ta kashe wayan tare da mikewa tsaye tana kallon Balaraba da itama take kallon ta, washe baki tayi tace to nifa Aminiya tafiya zanyi banga ta zama ba yanzu zanje nasa ta shirya tsunmokaran ta a buhu zuwa dare kuma naje gurin Malam nakan dutsu ya rufemin bakin ubanta.
Tabe baki Balaraba tayi tace to shikenan Aminiya a gaida gida.
Ko kulata Dada batayi ba tayi waje abunta ta nufi hanyan fita daga gidan cikin sauri kamar sabuwar kamu.
*Abuja State, Asokoro*
House No. 18, Yakubu Gowon crescent, Asokoro, katafaren gida be Mai hawa biyu wato up stairs. Babban gida ne sosai da ya gaji da haduwa daga gani kasan ba karamin dukiya aka kashe a gidan ba haka kuma duk wanda ya mallaki gidan to ba karamin hamshakin me kudi bane a kasar mu Nigeria harma da kewaye.
Babban compound din gidan cike yake da shuke shuke na flowers masu tsananin kyau da suka kara kawata gidan a gefe kuma parking lot ne wanda manya motoci ke jare har guda biyar a takaice dai gidan nan ya hadu iya haduwa.
Wata kyakkyawar yarinyace da baza ta wuce shakaru 20 ba take saukowa daga upstairs cikin natsuwa waya kare a kunne ta tana magana a hankali idan ba a kusa da ita mutum yake bama ba lallai yaji me take fadi ba.
Akan manya kujerun da suka kawata parlorn nasu ta zauna a hankali muryan ta yake tashi tace to Mom yanzu yaushe zaki dawo din kinsan fa zan koma school kuma bana son na tafi ban ganki ba.
Sautin murmushin Mahaifiyarta da take waya da ita ne ya fito daga wayan kafin tace Hibbah bana son rigima fa i thought kince next month ne zaki koma school din why kike damu na yanzu.
Shagwabe fuska Hibbah tayi kaman Mom din nata na ganin ta tace buh Mom you know I Miss you so much ko this is almost two months baki zo gida ba fa ta fada kamar zata yi kuka.
Dariya Mom tayi tace oh don't cry my baby your mom will come home on this coming Saturday insha Allah.
Wani dan karamin ihu Hibbah tasa cike da farincikin tace Mom are for real? jikin Bro Rayyan din yayi sauki ne? tare zaku dawo dashi Mom?
Duka a jare ta jero mata tambayoyin cikin zakuwa da son jin amsan da Mom din zata bata.
Ajiyan zuciya Mom ta sauke tace Hibbah calm down ni kadai zan dawo Rayyan har yanzu yana kwance ba wani improvement so I just decided to come home nayi kwana biyu sai na koma.
Cikin sanyin murya saboda duk dan farin cikin nata ma da taji ya kau jin babu wani improvement akan ciwon dan uwanta da take tsananin kauna Hibba tace okay Mom Allah ya bashi lpia.
Da Ameen Mom ta masa kafin sukayi shiru na wasu dakika Mom ne ta breaking silence din ta hanyar cewa.
How is baby Zunairah? I hope she's eating well.
Murmushi Hibbah ta sake tace Yes, Mom, she's at school, buh I think she's almost back, Isah driver yaje daukota.
Okay Dear, I want to turn off my phone now. Please take very good care of yourself and baby Zunairah Okay?
Mom ta fada cikin kulawa.
Cikin sanyin murya Hibbah tace okay Mom sannan ta cire wayan a kunnen ta bayan taji Mom din ta kashe wayan nata.
Shiru tayi tana kallon wayan nata deep down tana jin tsananin kewan dan uwanta guda daya tilo da take dashi a duniya, she miss him so much tana fata kuma wata rana ya fara daga wannan dogon ciwon au cigaba da rayuwan su kaman da cikin farinci da kaunar juna.
#Waheedah
#***