Chapter 9
Tafiya Dada take yi kaman wacce zata tashi sama nisan da tagani dazu zuwan ta ko kadan bata ganshi yanzu ba burin ta kawai ta isa gida tasa Waheedah ta hada kayan ta.
Tana isa ko sallama batayi ba ta banka kanta cikin gidan tana kwala kiran Waheedah da duka muryan ta.
Waheedah da ta gama wanki tana gaban igiyan shanya tana shanya kayan taji kiran Dada a firgice ta juya tana kallon Dada da ta shigo gidan kaman an jefo ta sai haki take yi.
Dan uban ki baza ki zoba kika tsaya kina kallon na.
Da sauri Waheedah ta isa gaban Dada tace gani nan, kama hannun ta Dada tayi tashiga janta zuwa dakin ta, a bakin kofan dakin Dada ta kalle ta tace tsaya anan ina zuwa tana gama fadin haka ta shiga dakin cikin sauri ko kula Waseelah dake tambayan ta ina taje tun dazu batayi ba ta hau dube dube a cikin dakin, sai da ta wargaza dakin gaba daya kafin ta samu abun da take nema wani karamin buhu ne ta zazzage abubuwan dake ciki sannan ta sake fita a dakin da buhun a hannun ta.
Kallon Waheeda dake tsaye a inda tace ta tsaya tayi ta wurga mata buhun a jikin ta tana cewa maza ki dauki buhun nan kije ki hada duk wani kayan ki a cikin sa gobe da sassafe Karime zata zo ta dauke ki ku tafi birni lokacin barin ki gidan nan yayi dama banga amfanin da kike min a gidan ba dan haka gara kije can birnin ki nemo min kudi.
Tsaye Waheedah tayi a gurin ta kasa motsa kafan ta bawai bata ji abun da Dada tace bane A'a taji amma kuma ko kadan bata fahimci me take fadi ba, birni fa tace to ita wa take dashi a birni, waye ta sani a birni da Dada zata turata can da sunan neman kudi.
Wani tsawan da Dada ta daga mata ne yasa ta dawo daga cikin duniyan tunanin data shiga.
Baza ki wuce kije kiyi abun da na saki ba kin tsaya kina bata min lokaci Dada ta fada tana maka mata harara.
Cikin sanyin jiki ta fara taka kafafuwanta da suka mata matukar nauyi ta nufi hanyan dakin nata.
Tana shiga dakin ta zube a kasa tana jin yadda zuciyanta yake bugawa da karfi, ita kam ta shiga uku me tayi wa Dada ne da ta tsane ta har haka?
me yasa zata tura ta birni bayan tasan bata da kowa a can?
Gashi bata da wani wanda zata fadawa damuwan ta a duniyan sai Baba amma kuma a duk lokacin da taje da niyyan fada masa damuwan ta sai taji kaman an dinke mata baki ta kasa fada masa.
Ajiyan zuciya ta sauke kuka take sonyi amma idanuwan ta sun bushe ba alaman hawaye hakan yasa ta tashi daga inda take ta nufi gaban ganan ta dan yi abun da Dada tace tasan idan batayi bama ba zagi ba har dukan ta Dada zatayi.
Karfe shida da wasu yan mintina Dada ne tsaye a dakin ta tana rike da mayafi da alama fita zatayi.
Waseela dake kwance ne ta mike tsaye tana kallon Dada tace nifa Dada ki fadamin me kike kullawa a gidan nan yau tunda garin Allah ya waye baki zauna ba gashi yanzu ma dare na shirin yi amma kina shirin fita.
To kuma sai aka ce duk inda zanje saina sanar miki kenan saboda kece Malam yo ai ko malam dinne ma bai isa na sanar masa inda zanje ba bare ke Dada ta fada tana maka mata harara.
Girgiza kai Waseelah tayi tace to naji yanzu dai fadamin inda zaki je.
Gyara tsayuwa Dada tayi tace tunda kika ce kin daina bani kudin da Alhaji yake baki to nima na yanke shawaran ta yadda zanyi nake samun kudi fiye da yadda kike bani, dama ai ba wani abun arziki kike bani ba yar dubu goma ce dan haka nima bazan zauna kina raina min wayo ba ina matsayin uwar ki.
Murmushi Waseelah tayi tace ai ni Dada duk wannan maganan da kike yi din ban gane komai ba kuma baki fadamin ina zaki je din ba.
Gurin Malam nakan dutse zanje ya rufe min bakin Baban ku saboda gobe zan dauki yar son sa na turata birni neman kudi.
Dafe kirji Waseelah tayi tana gwalo idanuwan ta waje tace Dada birni kuma?
Wani kalan neman kudi zaki tura yarinya karama taje tayi a birni inda ba wanda ta sani, haba Dada me yasa bakya tsoron Allah ne nifa wllh duk da tana bani haushi kuma na tsane ta amma wani lokacin tana bani tausayi wllh.
Sai tayi ta baki tausayin ai yarinyar da uwar ta taso ta fitar da naki uwar a gidan mijinta ita zaki ji tausayi, kuma kema dan ubanki tsoron Allahn ne ai yasa kike bin wancan shegen Alhaji yunusa me katon tumbi.
Kinga tafiyata ni bazan cigaba da sauraran kiba kina batamin lokaci birni ne dai sai na turata kuma ko uban ta bai isa ya hana ba Dada na fadin haka ta nufi hanyan fita daga dakin abunta tana jan tsaki.
Ajiyan zuciya Waseelah ta sauke tana girgiza kai ta koma bakin katifa ta zauna itakam harga Allah tana jin tausayin Waheedah wani lokacin duba da irin aikin wahalan da take yi a gidan amma ko kadan bata taba korafi ko kaiwa Baba kara ba amma kuma ta rasa wani kalan tsana ne Dada tayi wa yarinyar haka.
Dada na fita daga dakin nata sai da ta duba dakin da Waheedah take ta ganta zaune ta buga tagumi tana tunani.
Tabe baki Dada tayi tace to da kika zauna kikayi tagumi ina fatan dai kin hada kayan naki kaman yadda nace.
A hankali Waheedah ta dago kai ta kalli Dada dake tsaye a bakin kofa ta amsa mata da eh kawai.
To yafi miki Dada ta fada tana juyawa ta fita daga gidan a bakin kofa suka kusa cin karo da Malam Musa dake kokarin shigowa gidan da sauri ya bata hanya ta wuce ko kallon sa batayi ba.
Shigowa Malam Musa yayi cikin gidan da sallama bakin a ransa yana mamakin ina Dada zata je dab da ana shirin kiran sallahn magriba sanin bashi da me amsa masa tambayan nasa yasa ya kawar da tunanin a ransa.
Waheedah najin sallaman Baba tayi sauri ta tashi tare da fitowa daga dakin tana kirkiro murmushi akan fuskan ta kallon Baba tayi da shima yake kallon ta tace Baba sannu da zuwa, ta fada tana karasawa gaban sa inda yake tsaye.
Murmushi Baba yayi ya daura hannun sa a kanta yace yauwa Waheedah ya gidan?
"Lpia qlau Baba"
To Masha Allah jeki samin ruwa a buta naji an fara kiran sallah Baba ya fada yana nufan kan wani dutse ya zauna a tsakar gidan.
Ruwan Waheedah ta kawo masa yayi alwala ya tafi masallaci.
Sai bayan sallahn isha Baba ya dawo gidan kuma har zuwa time din Dada bata dawo ba abincin sa Waheedah ta kai masa dakin sa ta ajiye masa tare da zama a gefen sa.
Jawo kwanon abincin Baba yayi shikafa da mai da yaji ne dabe wuce loma shida ba a ciki yasan kuma saboda shi ya kawo shinkafan ne ma aka tsakura masa wannan din dagowa yayi yana kallon Waheedah yace ke kinci abincin ne.
"Eh naci Baba"
Hannu Baba yasa a aljihun sa ya ciro ledar gurasa ya mika mata dan ko kadan be yarda tacin ba hannu biyu tasa ta karba tare damai godiya so take ta budi baki ta fada masa maganan Dada na tura ta birni amma kuma ta kasa dan haka ta bude ledar gurasan ta fara ci a hankali yayin da Baba shima ya fara cin abincin sa.
Bayan sun gama cin abincin shiru ne ya ratsa dakin Baba yana kallon Waheedah tunda ya dawo ya fahimci kaman tana cikin damuwa duk da dama kullum cikin damuwan take amma na yau din ya kasa boyuwa akan fuskan ta.
Gyara zama yayi yace Mamana lpia kuwa naga kaman kina cikin damuwa.
Girgiza kai Waheedah tayi tace ba komai Baba kaina ne yake ciwo kuma ina jin bacci zanje na kwanta ta fada tana mikewa daga zaunen da take.
Girgiza kai Baba yayi yace to shikenan sai da safe karki manta kiyi alwala sannan kiyi addu'a kafin ki kwanta.
Da toh ta amsa, har taje bakin kofa Baba ya kira ta.
"Waheedah"
Juyawa tayi tana kallon shi daga bakin kofan murmushi Baba ya mata kafin yace Ina so ki kasance me juriya da daukan kaddara a duk yadda tazo miki sannan a duk inda kika samu kanki ki rike mutuncin ki Waheedah kar kiyi watsi da tarbiyan da na baki ki zama me hakuri da juriya akan komai Insha Allah zaki ga riban yin hakan kinji ko?
Gyada masa kai Waheedah tayi dan ji tayi baza ta iya bude bakin ta ba kafin a hankali ta juya ta fita daga dakin.
Ajiyan zuciya Baba ya sauke bai san meya sa yake ji a jikin sa kaman wani abu zai faru akan Waheedah ba tunda ya dawo ya daura idon sa akan ta yaji nauyi da bugun da zuciyan sa yake masa ya karu fiye da kika kima yana kuma fata koma mene zai farun ya kasance Alkhairy ne a rayuwanta dama su gaba daya.
#Waheedah
#***