BARRISTER SUHAIL

49&49

by @officialkhadeey

🐾 BARRISTER SUHAIL 🐾

Mallakar

KHADIJA WRITES

YOUNG TALENTED WRITERS ASSOCIATION
(YOTA)


💖 Dedicated To My Mom 💖


بِسْمِ اللهِ الرَّحْمٰنِ الرَّحِيْمِ

masu addu'a da fatan Alkairi ina godiya Allah ya bani ikon faranta maku kamar yadda kuke min 

masu taƙurawa ayi page biyu ga shinan a hade🥺😩uzurruka ne kemin yawa dayan ma da kyar nake samu na kawo maku shi 

🅿️-----48&49

Suhail ne zaune a office din sa     secretary ta shigo hannun riƙe da files ta miƙa masa ta ce"sir muna da client tun safe take jiranka"

"let her in"

cikin girmamawa ta ce"thank sir"

reception ta koma wajen dattijuwar matar dake zaune ta ce"
hajiya yace ki shiga"

cikin sauri ta isa office din 

a hankali ta tura kofar ta shiga suhail ya nuna mara wajen zama

"Yallabai ina kwana"

suhail ya amsa da "lafiya qlau,baba mike tafe dake"

"Yallabai nazo akan yarinyata ne"

suhail ya gyara zaman sa yana sauraren ta 

"meya faru da ita?"

Wani nannauyan ajiyar zuciya matar ta sauke kafin ta ce" Sunanta Amina ita ce wacce ake zargi da kashe mijinta a kauyen tsauni"

suhail ya jinjina kansa tabbas yaji Labarin a watan daya wuce wata mata yar shekara sha takwas ta kashe mijin dan kimanin shekaru saba'in da uku 

Gaban Suhail ya ɗan faɗi 

ya ce"baba kinzo na kare ƴar ki ne ko mi"

kuka ta fashe dashi ta ce"Yallabai wallahi ba amina bace tayi kisan ka nan,nasan yarinyata ni na reneta da hannuna Amina mutun ce mai tausayi wanda ko ƙiyashi bazata iya kashewa ba bare dan adam kuma mijin ta duk da nasan a lokacin bikin Amina bata sonshi hakan baya nuna cewa zata kashe shi"

suhail ya ce"kikace bata sanshi"

hawaye kan fuskar ta share ta ce"kwarai kuwa Yallabai Amina bata san shi Mahaifin ne yayi mata auran dole dalilin kuwa shine duk kauyen mu babu attajiri sama da Shi barau yana sana'ar saida gero dawa masara wake da sauransu mu biyu ne a wajen mijin mu nice ƙarama Uwar gidan tana da yara biyar ukku maza sai biyu mata hadda wanda akayi wa aure a cikin su 

babban sani shine yaje ya ci bashi na naira million biyu ranar biya yazo babu kudi aka kamashi aka rufe 

ganin haka yasa ita uwargida ta matsawa mijin mu akan dole sai na nemo kudin ya biya su ganin ba ya dasu ya nemi bashi a wajen Alhaji barau ya bashi rancen million biyu tare da kudin ruwa na naira millon daya a haka ya amince zai biya akayi yarjejeniya zai biya a wata shidda 

lokacin biya yazo babu kudi sai Alhaji barau ya nemi shi mijin namu ya bashi yarinya daya cikin yaransa ya aura 

yaranta biyu akwai mai shekara ashirin sai kuma mai shekaru sha bakwai da yaje mata da maganar ta ce babu wanda ya isa ya daukar mara yara ya aurawa wanchan tsohon 

haka mijin namu ya bashi Amina ba tare da sanin mu ba nayi kuka nayi kuka ganin ba wanda zan kaiwa ƙara yasa na hakura naba Amina hakuri daya ke yarinya ce mai ladabi da biyyaya haka ta amince da auren Alhaji barau a don ranta yaso ba duk da a lokacin akwai wanda take so haka suka haƙura da juna 

tun Ranar da aka kai Amina gidan Alhaji barau komai ya chanza 

Ta ɗan dakata kafin ta ci gaba

Alhaji Barau mutum ne mai tsananin kishi Bai son ta fita ko ina Hatta zuwa gidan iyayenta sai da izinin sa

duk da a gidansa bata rasa ci bata rasa sha ba sai dai barazanar salisu wato baban ɗan sa kullum cikin yi mata baranaza yake akan lalle sai ta yarda sun hada shimfiɗa dashi 

ƙin Amincewa bukatar sa yasa kullum sai ya musguna mata tare da mahaifiyar sa Amina ko tsakar gida bata isa ta fito ba 

haka aka cigaba da tafiya har Amina ta samu juna biyu cikin ta na wata Bakwai ta roki alfarma Alhaji barau ya barta taje asibiti a duba lafiyar ta amman fur yaƙi a cewar gidan ba'a zuwa asibiti a gidan sa kuma hakan bai hana matan sa haihuwa ba

Amina kullin cikin ciwo take koda tazo ta faɗamin nace dole zamuje Asibiti ita kadai ce diya da Allah ya barni bazan zuba ido zalunci barau ya kashe min ita ba 

haka na saka rana nace ta fito mu tafi asibiti da kyar ta iya sato hanya muka kama hanyar Asibitin gari

wunin mu guda kafin muka ga likita ya sheda mana bazata iya haihuwa da kanta ba ya zama dole idan cikin ta ya kai watan tara tazo ayi mata aiki 

haka muka kama hanya muna shiga garin muka tarar da Kofar gidan Alhaji barau cike da mutane

salisu na hango mu ya rugo da gudu ya shake Amina wai gatan itace ta kashe mahaifin su ta gudu


cikin dan ƙankanin lokacin gari ya dauka amina ta kashe barau kan kace mi yan sanda suka zo suka kamata 

nayi kokarin binsu amman suka ture ni a kasa haka na fadi ina kururuwa babu wanda ya kulani

koda na koma gidan mahaifinta haka ya koreni wai bazan zauna dashi ba gudun shima wata rana kar na kashe shi 

Muka cigaba da shari'a a police station daga karshe aka Kai kaimu kotu yanzu haka Amina tana chan a tsare a gidan yari 

shine mutane suke bani Shawara na nemi lawyer da zai tsare min da taimakon makwabiciyar mu wanda ta bani wajen zama a gidan ta nazo nan 

Shiru ya mamaye office ɗin na wasu sakanni

Suhail ya jingina da kujerarsa yana nazarin duk abin da matar ta faɗa.

“Yanzu kina nufin lokacin da aka kashe Alhaji Barau, Amina tana tare dake a asibiti"

Da sauri matar ta ce"wallahi muna tare Yallabai"

“Kin gaya wa ’yan sanda haka?”

Ta yi dariyar takaici

“Na gaya musu Amma babu wanda ya saurare ni tamkar da hadin baki ita kanta Aminar babu wanda ya saurareta gata da tsohon ciki ina tsoron wani abu ya sameta dan allah Yallabai ka taimaka mana"

Suhail ya jingina da kujerarsa yana nazarin duk abin da matar ta faɗa

"zan taimaka maku amman akwai sharadi kwara ɗaya"

Ta share hawaye

“Wane sharadi?”

"inaso ya zamana duk abinda kika faɗa anan ya zama gaskiya dan da wannan hujjar zan kare ƴar ki a gaban Alkali"

"wallahi gaskiya na fada maka"

"yanzu yaushe ne zaman kotun"

"ranar labara ne"

suhail ya ce"ba matsala kafin nan ya kamata naje naga ita Aminar"

nan ta faɗa masa gidan yarin da aka kaita 

suhail ya kira    secretary dinsa ta kai ta kaita daki hutu ta kuma bata abinci 

a hankali ya soma binciken files din hotan Amina yake kallo 

yarinya ce karama da nutsuwar ta nuna har akan fuskar ta 

tabbas akwai wani babban al'amari dake tare da wannan case ya zama dole ya kare Amina matukar ba hannun ta awannan kisan luma ya zama Dole ya binciko duk wasu masu hannun a Wannan ƙisan

   secretary ta  kaita dakin hutu ta ajiyr mata abinci masu rai da lafiya  yadda Suhail ya ce 

kusan awa ukku tana chan bata san ma Lokacin da bacci ya dauke ta ba wanda rabon ta da irin wannan baccin a rayuwar har ta manta matsaloli duniya suk sakota a gaba 

sai wajen la'asar ya sa a kira ta ya ce"tana da masauki anan Abuja"

ta ce"a'a bata dashi kuma bazata koma kauyen tsauni ba har sai rabar da aka gama Shari'ah zata cigaba da zama a Abuja"

suhail ya ce"baba in ba damuwa zan a sama maki masauki"

rage tsayinta tayi ta ce"Nagode sosai Yallabai Allah ya biya maka bukatun allah ya saka maka sa Alkhairi" 


Suhail ya miƙar da ita ya ce"bakomai baba"

    secretary dinsa ya kira ya fada mata ta samawa baba waje kwana tare da abincin da zata ci


yana barin office ya kama hanyar prison da aka kai amina I'd card ya kaisa har baban office din da ake ganawa da masu laifi inda ya bukaci a kawo masa Amina yarinyar da ake zargi da kisan mijin ta 

ba bata lokaci masu aikin suka kawo ta sanye da ke da rigar gidan yari mai lamba dari da hudu da kyar take tafiyar sakamakon girman da cikin ta yayi har ya soma rinjayar ta 

a gaban suhail ta tsaya sai ya bata izini ta zauna a hankali ta buɗe baki ta gaishe shi 

ya ce"nasan baki san ni ba sunana Barrister suhail ni ne lawyer da zai tsaya akan cases dinki"

kai kawai ta daga 

ya ce"Mahaifiyar ki tayi min bayanin komai kema inaso naji daga bakin ki"

cikin abinda mahaifiyar ta,ta fada ba Abinda ya chanza sai dai gan ta gama masa bayanin kuka yaci karfin ta kuka take tamkar ranta zai bar gangan jikin ta 

Suhail ya tausaya mata tun fitowar ya lura da yadda idanunta suka kumbura sakamakon kukan da take ba dare ba rana 

suhail ya ce"Amina"

dago idanunta tayi ta kallesa "baso ki na Kukan baki tunanin zai iya shafar Abinda ke cikin ki kiyi haƙuri ki ida min bayani nayi maki Alƙawarin matukar ba hannun a wannan kisan zan tsaya maki sai na tabbatar na wanke ki daga dukkanin zargin da ake maki amman da taimakon ki"

kai kawai ta jinjina masa 

"kinga gawar Alhaji barau a ranar"

"a'a ko gidan ma ban shiga ba "

"To wa ya fara cewa kin kashe shi?"

“Salisu ne Babban ɗansa“

Idanun Suhail suka ɗan lumshe kafin ya ce “Me yasa zai zarge ki?”

Amina ta sunkuyar da kai Hawaye suka zubo mata
“Saboda ya daɗe yana son na yarda da shi"

Gaban Suhail ya faɗi ya ce“Ki yi min bayani"

Amina ta share hawaye
“Kullum sai ya ce min idan ban yarda da shi ba wata rana zan yi dana sani"

Suhail ya yi shiru

A karo na farko ya fara jin cewa wannan case ɗin ya fi yadda yake zato rikitarwa

a nutse ya kalli Amina ya ce"waye shedarki na cewa kinje Asibiti ranar banda mahaifiyar ki"

Amina ta ce"babu kowa saboda ba wanda yasan inda muka tafi ko shi Alhaji barau din ban faɗa masa kar ya hanani"

Wani zazzafan tunani ya ratsa zuciyarsa, ya miƙe tsaye

Amina ta ce"Barrister zata taimakeni in fito"
murmushi yayi " i will try mai best matukar babu hannun ki"

tana kallon sa ya fita aka maida ta ciki

yana fita ya doshi hanyar gida

duk tsawon hanyar tunanin case ɗin Amina ne ya mamaye zuciyarsa Tambayoyi da yawa suke yawo a kansa

Idan Amina tana asibiti tare da mahaifiyarta, wa ya kashe Alhaji Barau?

Me yasa Salisu ya yi saurin jingina mata laifin?

Da wannan tunanin ya ƙarasa gida

Motarsa na tsayawa a parking space ya fito ya nufi sashensa

Tun kafin ya isa ƙofar ɗakin nasa wani sassanyan ƙamshi ya bugi hancinsa

a hankali ya tura kofar dakin komai an gyara yayi fess hatta bedsheet din ma a chanza masa 

tun bayan fitowarsa daga gidan yari ya ji zuciyarsa ta ɗan samu nutsuwa 

murmushi yayi a hankali ya zauna a kan gadon ko ba'a fada masa ba yasan  aikin  iman ne 

a hankali ya soma cire kayyasan iya fuskar sa kadai ta isa ta nuna gajiyar da yayi 

iman ce ta Turo kofar dakin sanye take da wata atamfar green colour anyi mata ɗinkin doguwar riga ta yafa mayafin hannun ta riƙe da tray mai dauke da drinks da kuma ruwa 

a hankali ta kara sa kusa da Suhail ta ajiye masa 

"Welcome yaya Suhail"

"yawwa iman ya gida"

"Alhamdullilah"

"duk ke kikayi gyaran nan"

murmushi kawai tayi
ya ce"ina Zeenah"

ƙasa tayi da kai tun fitar sa zeenah ta saka kai ta fita har yanzu bata dawo ba 

sai ya tambaya a karo na biyu ta ce"ta fita"

da mamakin ya kalli iman "ta fita,ina taje"

"nima ban sani ba"

kansa ya dafe yanzu abin zeenah har yasa ta fara fita ba tare da izinin sa ba sai yanzu ya lura da babu mota guda a parking space 

iman ta juya ta fita ganin baccin rai kwance a fuskar sa


SHARE 
LIKE AND COMMENT

DA KYAR NA KAWO MAKU WANNAN BANDA LAFIYA KO DA ZAKU JINI SHIRU NAGODE