THE ENCHANTED KINGDOM

CHAPTER 1

by @queenmahirah14

🧚THE ENCHANTED KINGDOM🧚
Story and writing by Queen Mahirah
Marubuciyar...
THE TWO LIGHTS (RIKICIN GIDAN SARAUTA)
KITABUL HUB
LABARIN DR NEELAH
LABARIN BINT ABDULAZIZ

Chapter One: Ƙofar Sirrin Nurayn





Madinatul Alam – Garin Al’ajabi
Madinatul Alam ba kawai gari ba ne, amma wata duniyar mafarki ce da ke cike da hikima da ban mamaki. Duk wanda ya taka Æ™afarsa a cikin wannan gari, yana jin kamar ya shiga wani littafin tatsuniya.  

A Æ™ofar garin, fitilu na zinariya suna kyalli kamar taurari, suna maraba da baÆ™i da annuri. A cikin gari, rafin hikima yana gudana da ruwan azurfa mai haske, wanda ake cewa duk wanda ya sha daga gare shi, zuciyarsa tana cike da natsuwa da basira.  

Kasuwar al’ajabi ta cika da kayan tarihi da abubuwan ban mamaki: kayan ado da ke canza launi da kansu, littattafai da ke magana idan aka buÉ—e su, da kuma kayan abinci da ke É—anÉ—ano daban-daban bisa ga yanayin mai ci.  

Dare a Madinatul Alam ba ya da duhu sosai; taurari suna kyalli fiye da yadda ake gani a ko’ina, suna haskaka hanya kamar fitilun birni. A cikin dajin kyandirori, bishiyoyi suna fitar da haske mai laushi, suna jagorantar masu tafiya cikin aminci.  

Wannan gari na iya zama mafarki ga mai neman hikima, natsuwa, da haɗin kai. Duk wanda ya shiga Madinatul Alam, yana fita da sabon hangen nesa na rayuwa – kamar ya gano wani ɓangare na kansa da bai taɓa sani ba.

 wani Æ™aramin Æ™auye mai nisa daga hasken MADINATUL ALAM, akwai wata yarinya mai suna Maryam Zahrah.
 A idanun mutane, ita kawai wata marainiya ce mai rayuwa cikin Æ™unci da wahala.
Amma abin da mutane ba su sani ba shi ne...
A bayan wannan fuskar mai sauƙi akwai zuciyar jaruma.
Maryam Zahrah
Maryam yarinya ce mai shekaru kusan ashirin, mai kyakkyawar fuska wadda take ɗauke da nutsuwa da kamun kai. Idanunta suna da wani irin haske mai nuna taɓa zuciya da zurfin tunani.
Ba ta da kayan alfarma, ba ta da kayan ado masu tsada, amma akwai wani abu a tare da ita da ya fi kowane ado daraja...


MARYAM ZAHRAH
Mutuncinta.
Tana da zuciya mai tausayi, tana taimakon duk wanda yake cikin buƙata ko da ita kanta tana cikin wahala. Ba ta son cin zarafi, amma kuma ba ta yarda a karya mata gaskiya ba.
Tana da haƙuri mai yawa, amma idan an taɓa wanda take ƙauna, tana iya nuna ƙarfin da babu wanda ya zata.
Asalin Rayuwarta
Maryam ta girma tana tunanin cewa ita marainiya ce.
Bayan rasuwar mahaifiyarta, an kai ta gidan wata mata mai suna Sayyadah Rukayya, wadda ta É—auki nauyin kula da ita.
Amma abin da Maryam ta samu a gidan ba kulawa ba ce...
Azaba ce.
Sayyadah Rukayya ba ta taɓa kallon Maryam a matsayin 'ya ba.
A gare ta, Maryam kawai wata yarinya ce da za ta yi mata aiki.
Daga wayewar gari har dare, Maryam ita ce ke share gida, wanke kaya, girki, da duk wasu ayyukan da suka fi ƙarfin mutum ɗaya.
Sau da yawa tana kwana cikin yunwa, tana ɓoye hawayenta domin kada a ga rauninta.
"Ke ai ba ki da amfani sai aiki."
Wannan ita ce kalmar da Hajiya Rukayya ta fi yawan gaya mata.
Amma duk lokacin da aka ci mata mutunci, Maryam tana tuna kalmar da Mahaifiyar ta ke mata...
"Ya Maryam, kada ki bari wahalar duniya ta canza kyakkyawar zuciyarki."
Wannan kalmar ce ta sa ta ci gaba da zama mai tausayi duk da azabar da take fuskanta.
--
Dare ya sauka a hankali a garin MADINATUL ALAM, ya lulluɓe gidaje da tituna da wani sanyi mai taushi. Hasken wata ya ratsa ta cikin rassan itatuwan da suka zagaye garin, yayin da iska take ɗauke da ƙamshin furanni daga lambunan da ke kusa. Mutanen garin sun kasance suna ganin wannan dare kamar sauran darare, amma ga Maryam Zahra, wannan daren ya kasance daban da kowanne lokaci.
Maryam ta zauna a gefen tagar ɗakinta tana kallon sararin sama cike da tunani. A hannunta akwai wani tsohon abin wuya da ta gada daga mahaifiyarta tun tana ƙarama. Abin wuyar yana ɗauke da wani dutse mai haske wanda ba ta taɓa ganin irinsa ba. Duk lokacin da ta riƙe shi, tana jin wani yanayi mai ban mamaki kamar akwai wani abu da yake ƙoƙarin tuna mata wani abu da ta manta.
Tun shekaru da dama, Maryam tana yawan yin mafarkai iri É—aya. Tana ganin wani babban fada mai haske, mutane sanye da tufafin sarauta suna tsaye suna kallonta, sannan wata murya mai zurfi tana cewa:
"Kin dawo inda haskenki ya fito."
Amma duk lokacin da ta farka, sai mafarkin ya ɓace kamar hayaƙi. Ta kan tambayi kanta ko me yasa zuciyarta take jin kamar tana da alaƙa da wani wuri da ba ta taɓa zuwa ba.
"Maryam..." wata murya ta katse tunaninta.
Ta juya sai ta ga mahaifiyarta ta shigo ɗakin a hankali. Matar mai suna Amina Rahmah ta kasance mai nutsuwa da fuska mai cike da hikima. Ta kalli abin wuyan da ke hannun Maryam, sannan idanunta suka sauka ƙasa kamar tana tuna wani tsohon lokaci.
"Har yanzu kina riƙe da wannan abin?" ta tambaya cikin sanyin murya.
Maryam ta ɗaga abin wuyan. "Ummu, me yasa kika bani wannan? Kuma me yasa duk lokacin da na kalle shi nake jin kamar akwai wani sirri da yake ɓoye?"
Amina ta yi shiru na ɗan lokaci. Ta zauna kusa da ita sannan ta riƙe hannunta.
"Maryam, akwai wasu tambayoyi da lokaci kaÉ—ai yake iya ba da amsarsu. Amma ki sani... akwai abubuwa da yawa game da asalin ki da ba ki sani ba."
Maryam ta kalli mahaifiyarta cikin mamaki.
"Me kike nufi, Ummu?"
Amma kafin Amina ta amsa, sai wani iska mai ƙarfi ya shigo ta tagar ɗakin. Fitilar ɗakin ta fara rawa, sannan abin wuyan Maryam ya fara haske da wani haske mai ban mamaki.
Dukansu suka tsaya cikin mamaki.
Amina ta kalli abin wuyan da tsoro ya bayyana a fuskarta.
"Ya fara..." ta furta a hankali.
"Me ya fara?" Maryam ta tambaya cikin firgici.
Amma Amina ba ta samu damar amsawa ba.
Cikin zallan firkici ta tashi daga baccin nata daya haddasa mata wannan mafarki É—aya zama ruwan dare a gareta...
HaÉ—e kanta tayi da guiwa tana mai kewar mahaifiyar ta hadi da tsoron abinda rayuwa zai gabatar mata dashi...
---
A wannan lokacin, daga nesa cikin dajin da ya wuce garin Madinatul Amal, wata tsohuwar ƙofa da ta daɗe a rufe ta fara bayyana. Duwatsun da suka rufe ta suka fara motsi, kamar wani abu da aka daɗe ana jira ya dawo.
A ƙofar akwai rubutu da tsoffin haruffa:

"Wanda yake dauke da zuciya mai tsarki, shi zai bude kofar ÆŠaular da aka manta dashi...''

Duhu ya fara sauka a kan ƙaramin ƙauyen Zan-zabir iska tana kadawa a hankali tana motsa rassan bishiyoyi. Mutane sun riga sun rufe ƙofofinsu saboda labarin da aka daɗe ana bayarwa game da wani wuri mai ban tsoro da ke bayan ƙauyen, DAJIN KAINUWA...

Wani daji ne da aka haramta shiga tun shekaru masu yawa. An ce duk wanda ya shiga ba tare da izini ba yana iya haÉ—uwa da abubuwan da ba za a iya bayyana su ba.

Amma ga Maryam Zahrah...
Ba ta da zaɓi...
---

6:00am

"Maryam!"

Muryar Sayyadah Rukayya ta cika gidan.

Maryam da take durƙushewa tana wanke kaya ta ɗaga kai da sauri.

"Na'am Ummi?"

Matar ta fito daga ɗakinta tana riƙe da wata ƙaramin kwalba.

"Na ga jikina ya fara ciwo, ga shi fatana ya sama tauyewa. Likita ya ce ina buƙatar ganyen kainuwa."

Maryam ta kalli kwalbar.

"Ganyen kainuwa?"

Ta san inda ake samun shi.

Amma zuciyarta ta firgita.

"Ummie a... kina nufin na je Dajin Kainuwa?"

Fuskar Sayyidah Rukayya ta canza.

"Eh."

"Amma... an ce ba a shiga can."

Sayyidah Rukayya ta yi dariya mai sanyi.

"Ke za ki gaya min abin da ake yi?"

Ta matsa kusa da ita.

"Ko kina so ki zauna a gida ki daina cin abincin da nake baki?
Burin zuwa MADINATUL ALAM...
Kin mance da wannan?''

Maryam ta sunkuyar da kai ta hadiya wani yawu mai daci, tana tuna abubuwa da dama gane da mafarkinta da kuma tambayar da tana da tabbacin a Madinatul alam ne kadai za'a amsa mata...
Kasancewar suna da littafai na fassarar mafarki da kuma masana tarihi...
Haƙiƙa tana son sanin tarihin wannan sarƙa nata da Asalinsa....
Ajiyar zuciya ta sauke ta ta ce:
"Zan je."

Wani mursmushin da baza ka iya fassara shi bane Sayyadah Rukayya data kasance Kawaliyah a wannan ƙauyen ta yi ta kuma miƙa mata kwanan tace da ita:
''ki tabbatar in kin gama aikin nan kin je kin samo mun''
Kai kawai Maryam Zahrah ha sadda bata iya tace komai ba...

Sayyadah Rukayya hamdala tayi tana mai ayyana abubuwa da yawa a ranta da suka shuÉ—e...
Tabbas da bata karbi Maryam Zahrah daga ganin mahaifiyarta shekaru 20 da suka wuce ba da tayi asara na fitar hankali...
Tana iya tuna yadda ta samu matsayi arziki da daukaka saboda wannan yarinyar...
A yau data ce da ita tana son GANYEN KAINUWAR shine wani shiri ne da Sahir ya umarce ta data yi game da yarinyar yana son gane asalin ta...
Yasan in har itace makullin tsohon Daular da aka manta dashi ba shakka zata dawo da rai da kuma GANYEN KAINUWAR...
Wani weird smile ta sake take '' yah Allah... Na kusa zaka Sultana mai cikakken iko, ba shakka in yarinyar ta dawo da rai zan zama Sultana da ba'a taba samun irinta ba a faɗin ƙasar MADINATUL ALAM...
Lumshe idinta tayi ta soma rawa irin nasu ka larabawa cikin salo na jin dadi da kwarewa...
💃💃💃💃💃💃💃💃


END OF CHAPTER 1
---