Page 1&2
Wata kyakkyawan budurwa ce wacce a k'alla zata kai shekaru ashirin da d'aya zuwa ashirin da biyu, sanye cikin wando palazzo kalar fari fat, sai wata riga armless ita ma fara tass ta kuma kwanta a kan fatar jikinta, irin kyawawan yaran nan ne wanda za ku gan su kamar su suka halicci kan su don tsabar kyawu. Sosai take da k'irar jiki irin figure 8 d'in nan, kyakkyawan gaske ce mai d'an duhun fata wato irin chocolate colour d'in nan, sai dai skin d'in ta wani irin shining da glowing yake yi, kana kallon fatanta kasan ba k'aramin gyara da kula yake samu ba. Tana da gashi sosai a kanta, kuma ba k'aramin ji da gashin take yi ba saboda duk bayan 2weeks tana shagon saloon domin gyara. Wani irin dogon takalmin kalar silver ne a k'afarta, sai kuma wani farin siririn gyale da ta yi a cuci da shi yayin da uban tulin gashinta ya fito ta k'arshe. Wani d'an ubansu fashion bag ne a hannunta d'an k'arami kalar silver, bak'in tinted glases d'in dake kan fuskanta kuma ta d'an sauko dashi kad'an kan dogon hancinta tana taunar cingam k'as-k'as-k'as. Babu abunda kake ji sai k'arar takalmin ta yayin saukowarta daga stairs. Daddy, momma, Shuraim, Suhail da Sauban dake kan dinning suna yin dinner gaba d'aya suka zubawa stairs d'in idanu. Sai da ta gama saukowa gaba d'aya ta nufo wajen sannan momma ta d'auke kanta tana mai jujjuya spoon, ta kuma kasa k'ara kai loman abinci a bakinta. Su Shuraim da Daddy kuwa, gaba d'aya suka had'a baki wajen fad'in, "Wow!" Shuraim mai bi mata ya ce, "Wow! Akeela kin gan ki kuwa, looking beautiful. Ina za kije ne?" Sai da Akeela ta yamutsa fuska sannan ta ce, "Party muka had'a na kammala degree d'in mu. We guys are going to have fun!" Ta fad'a tana wani irin faarr da idanu. Gaba d'aya kallon momma suka yi wacce ta ajiye cokalin hannunta da k'arfi tare da folding hannunta tana kallon Akeela tun daga sama har k'asa, irin kallon you're out of your sense. Zarowa momma idanuwa Akeela ta yi tare da fad'in, "What again momma? Are going to stop me? I'm glad daddy is here to stop you from what you're trying to do!" Ta fad'a a tsiwace, cike kuma da rashin kunya tare da rashin tarbiya. Ita ma momma a fusace ta ce, "Akeela! You're not going anywhere, and that's final. Idan kuma ke kika haife ni, za mu gani yau. Kina hauka ne? Kalle ki fa kamar ba d'iyar musulmai ba. Na riga na gama magana, you are not going anywhere!" A zafafe ya mik'e har ya na buga glass d'in dinning d'in da k'arfi tare da fad'in, "Ke Fauza ki kiyaye ni a kan y'ay'ana! Wai mai yasa idan har na miki warning a kan y'ay'a na bai shiga kunnuwan ki? Wallahi, tallahi zan iya miki abunda baki tab'a tunani ba a kan y'ay'a na Fauzah! Akeela will go to the party, and that's final, sai in ga ni dake waye ya isa, kuma wanene shugaba a cikin gidan nan!" Akeela kuwa kukan k'arya ta soma yi tana bubbuga k'afa a k'asa tare da fad'in, "Daddy ban san mai yasa momma ta tsane ni ba, bata sona kamar ba ita ta haife ni ba, and kuma fa I'm _THE FIRST BORN_, abubuwan da ta ke min zai iya saka su Shuraim su raina ni fa. Kuma wai ba zan je party da na kashe kud'i wajen had'awa ba, ni wallahi sai naje ko ta barni ko bata barni ba". Ta k'arisa maganar tana murgud'a baki har da d'an harara k'asa-k'asa. Jawo ta jikinsa yayi tare da fad'in, "Come on don't cry Akeela! Ta isa ma ta hana ki, ke za kiyi driving ko kuma kai ki kike so ayi?" D'an turo baki Akeela tayi tare da fad'in, "Ni zan yi driving da kai na". Shafa kanta daddy ya yi tare da fad'in, "Ki na buk'atar wani abu ne?" Girgiza kai Akeela ta yi tare da fad'in, "I have money dad. Ni dai ka ce momma ta bar ni in tafi, my friends are their waiting for me, I have to go". Hanya Daddy ya nuna mata tare da fad'in, "You can take your leave my dear, no one can stop you, I mean no one!" Gaba d'aya sauran yara suka shiga ihu suna fad'in, "Daddy's girl! Oh you can go to the party sis, dad means it. You no, when he said yes, he mean yes and nobody on the earth can change it, just take you leave babe". Momma kuwa zuciyar ta har wani tafasa yake yi tsabar b'acin rai, bata san lokacin da ta isa gaban Akeela ba tare da fad'in, "Wallahi Akeela if you take step za ki ga abunda zan miki cikin gidan nan!" Sai kuma ta juya ta kalli daddy tare da fad'in, "Wai mai yasa kake min hakane daddyn Akeela? Ya kullum ina tufka kai kuma kana warwarewa? Kasan yanda ake zagin mu a gari kuwa akan tarbiyan y'ay'an mu? Must especially Akeela! Kar ka manta ita macece, kuma gidan wani za taje, idan har bata da tarbiya, ta ina zata iya baiwa y'ay'an da zata haifa nan gaba tarbiya. Na gaji, I'm tired Ahmad Sulaiman Bawa! I'm tiredof yanda nake k'ok'arin baiwa y'ay'a na tarbiya kai kuma kana rushewa ba. Kalla fa, kamar Akeela, a cikin wannan shiga, at this hours ta bud'e baki ta kalle mu, mu iyayen ta, ta ce mana wai zata party sabida kawai ta kammala degree! Mutane nawa ne kamar ta a titi suna nai man masu tallafa masu domin samun ilimin da ta samu, amma ita ta samu kuma shine zata godewa ubangiji ta wannan hanya? Har kuma kake bata go-ahead ta je party suna raye-raye da shaye-shaye da maza da mata ko? To ni ba zan amince ba, Akeela will not go anywhere!" Ta k'arisa maganar da k'arfi tana kallon y'ay'an nata dai-dai. Sai da daddy ya matso har gabanta suna jin k'amshin juna sannan ya saka idanuwansa a cikin na ta tare da fad'in, "Who are you da har zan yanke hukuncin a kan y'ay'a kice ke bai miki ba?". Zuciyar Momma a dake ta kalli cikin idanunsa tare da fad'in, "Mother! Ina nufin mahaifiyar su, wacce take ganin hanyar da ka b'ullo ba mai b'ullewa bace!". D'an yatsa ya d'aga ya nuna Akeela dashi tare da fad'in, "Wannan y'ar yarinyar ce kike wa fatan shaye-shaye kuma har kike kiran kan ki da her mother? Mother ce za ta yi wa y'arta wanna fatan? Wai anya Fauzah kina k'aunar Akeela kuwa? Wallahi I will never let what happened to me, to happen to my own daughter, never! Tarihi ba zai tab'a maimaita kansa a kan y'a ta ba. Kuma na gama magana, Akeela will go to the party!" Yana gama fad'in haka ya finciki hannun Akeelan tare da nufar k'ofa. Da gudu momma ta sha gabansu ta na kuka tare da fad'in, "Akeela baza ta fita ba, babu inda za ta je". K'ugu daddy ya kama, sai kuma ya kalli gefe da gefe tare da d'aga hannu ya wanke fuskan momma dashi sai da ta zube a k'asa tare da dafe kuncin ta. Da sauri Akeela ta d'aura hannu a bakinta tana waro idanuwa. Su Shuraim kuma bayan mamaki sai kuma suka fashe da dariya suna nuna momma da hannu. Akeela kuwa sai taji duk jikinta yayi sanyi, sai tayi wani irin tana kallon mahaifin nata. Momma kuwa wani irin kuka ta fashe dashi tare da fad'in, "Ni ka mara? Ni ka mara don ina k'ok'arin yi wa y'ay'a na tarbiya?" "Na mare ki Fauziyya Abubakar Turaki! Ko zaki rama ne? Kin san Allah, zan iya sakin ki a kan y'ay'a na, na gwammaci in k'ara aure ko kuma in nai mo masu reno! Tafiyar ki Akeela". Sai da Akeela ta kalli momma sannan ta kalli daddy jikinta duk a sake, sai kuma ta juya da sauri ta fice daga d'akin. Momma kuwa da k'arfi ta soma kiran sunanta tana fad'in, "Akeela nooo! Ki dawo gida, kin san fa ba ki iya driving sosai ba, don Allah ki dawo gida". Amma Akeela ko juyowa bata yi ba. Daddy kuwa ko kallo d'aya bai k'ara yi mata ba ya wucewar sa, yayin da su Shuraim suka gama dariyar su suma suka haura sama. Momma kuwa da kyar da ja jikinta tana kuka ta wuce d'akinta ta kullo k'ofa tare da rushewa da kuka.
*AFTER FOUR HOURS* Wayar daddy ce tayi k'ara, har bacci ya soma d'aukarsa, ya kai hannu ya lalubi wayar, ganin wacce ke kira yayi saurin picking tare da fad'in, "Akeela my love!" Shasshek'ar kukan Akeelan ya saka ya duro daga kan gadon tare da fad'in, "What's happening Akeela? Why are you crying?" A firgice yake tambayan ta kamar yanda ita ma take kuka da iya kacin k'arfin ta tana fad'in, "Daddy help me! Police sun kama ni, na bige wani mutum kuma ya mutu! Ga su nan za su tafi dashi police station". Da ihu yake magana yana fad'in, "Kina ina? Kuna ina yanzu? Ki ba d'aya daga cikin su in yi magana dashi, ina za su kai min ke? Calm down Akeela, I won't let anything to happen to you, stop crying, right. Your daddy will be there soon". Duk yana maganar ne yana tafiya dif-dif-dif har ya isa k'ofar d'akin momma da tayi fushi ta tafi d'akin ta, ta rufe k'ofa. Irin bugun da yake wa k'ofar ya saka hankalin Momma ya tashi sosai, don ta san tabbas babu lafiya, don ta riga ta sani, idan su kai fad'a in har a kan y'ay'a ne, ba shi yake nai man ta ba, ita ce da kanta idan ta sauko ta ke nai man sa. Dama kuma ba ta yi bacci ba tana jiran dawowar Akeela. Da sauri ta bud'e k'ofar, ganin shi da waya a hannu yana magana da ihu-ihu kuma ga dukkan alamu da jami'an tsaro yake maganar, sai taji duk hankalin ta ya tashi. Yana katse wayar ta shiga fad'in, "Dear mai ya faru, Akeela ce ko? Na shiga uku what happen to her?" "Ki d'auko hijjab d'in ki, Akeela tana hannun police, wai ta bige wani da mota kuma wanda ta bige d'in ya mutu!". Hannu momma ta d'aura a kai tare da rushewa da kuka. Da wani irin tsawa dad ya ce, "Come on ki wuce ki d'auko mayafin ki mu wuce, nothing will happen to my daughter, kin wani d'aura hannu kina wa mutane ihu tare da pretending kamar kina wani son ta ne". Da sauri momma ta koma ciki ta d'auko hijjab d'in ta suka fita tare da dad d'in a motarsa....
*_TUSHEN LABARI_*
Gida ne irin na kasa wanda ko arzikin penti babu, kana hango tsurar bulo d'in k'asan a zahiri. Gidan ba wani babba bane sosai, duk da kasancewar filin gidan rabin filoti ne, amma d'akuna hud'u ne kawai a gidan ciki d'ai-d'ai. Malam Bawa shine mai gidan, matansa na aure uku, sai mahaifiyar sa dake zaune a gidan tare dasu kasancewar mijinta mahaifin sa ya jima da rasuwa. Mama Ladi ita ce matarsa ta farko, tana da y'ay'a hud'u kacal, Ahmad shine *D'AN FAARI*, sai Abubakar, Lawal da kuma Umar. Bayan Mama Ladi, sai Inna Murja, ita kuma y'ay'an ta biyu, Sa'adatu da Sakina. Sai ta ukun Mama Abu, ita kuma bata tab'a haihuwa ba. Gaba d'aya gidan Ahmad shine babba, mahaifin su ba wani mai k'arfi bane, irin mutanan ne da basa iya ciyar da gidan su sau uku a rana sabida lalurar babu. Haka yake tun fil azal, gidan da yake ciki ma gadonsa yayi wajen mahaifinsa kasancewar shine d'ansa tilo. Malam Bawa yana da fad'a sosai, sam baya overlooking akan al'amuran gidan sa, mafad'aci ne irin na bugawa a jarida, da Allah ya bashi matar farko, sai ya sab'a masu hali, domin kuwa Mama Ladi irin way'ennan matan ne masu masifar hak'uri, kau da kai da kuma sanyin hali, ko magana bata cika yi ba, shiyasa a gidan ake cuta mata idan aka cire Mama Abu wacce ta kasance mafad'aciya sosai amma sai an tab'o ta. Bata fad'a for no reason. Kullum idan kaji muryoyi biyu na tashi a gidan, to mama Abu ce da mal Bawa, baya raga mata, haka ita ma bata ragar masa, cewa take _NI BA JAKAR MAGINIYA BACE, CI BAI ISHE NI BA, TSIKARI YA ISHE NI!_. Inna Murja kuwa uwar husuma ce ita, idan kaga mata sun cika gida ana fito ki maimaita abunda kika ce, to ka tabbata da Inna Murja ake yi, sam bata zama ba tare da ta yi munafuncin wani ba, idan kuwa suna zaune su da yawa a waje, d'aya na tashi zata hau tsegumin ta, ko kuma a zauna ayi gulmar wata da ita, ana watsewa sai ta zari mayafi ta tafi har gidan mata ta zayyane mata k'arya da gaskiya sannan ta nuna ita bata ce komai ba, ga d'an hali, yanzu ka aje yanzu ta d'auke, kamar mai wankin ido, idan ta san akwai kud'i a jikin ka, to fa sunan ka sorry don sai ta san yanda tayi ta tatik'eka tass, sanan idan za ayi caje, ko ina za'a duba a jikinta baza a tab'a ganin kud'in nan ba kuma yana jikinta. Hakan ne ya saka wasu da dama basu gane tana sata ba sai y'an kad'an daga cikin su. Kuma a hakan ita ce matar so a wajen mal Bawa da mahaifiyar sa Daada sabida ita Abun hannunta a bud'e yake amma a wajen Daadan da kuma mal Bawa wannan dalilin ne ya saka yake ganin duk cikin matansa ba mai k'aunar sa kamarta, don idan yana son kud'i kai tsaye wajenta yake zuwa ya nok'e yana y'ar murya, ita kuma a cikin na jama'a da tayi wuuf dashi take tsungula masa wani abun shi da mahaifiyar tasa don ta k'ara fari a idanunsu........ Da gudu yaro d'an shekaru biyar ya shigo gidan yana kuka da ihu tare sa soshe-soshen jiki yana fad'in, "Inna ki taimaka min zan mutu, wani abu na cizo na a cikin riga, ki taimaka min Innar mu". Ahmad ya fad'i tare da rik'e hannun Inna da ko d'agowa bata yi ba ta cigaba da sharar ta, hannunta da ya rik'e ta fizge da k'arfi tare da hankad'a shi gefe tana fad'in, "Abun da yake cizon naka ya kashe ka! Ni na tura ka wajen da abun yake, ko kuwa ni na saka abunda yake cizon naka ya cije ka?" Duk maganar nan da take yi, ko kallo d'aya bata masa ba, balle taga halin da yake ciki, sai sakin tsintsiyar tayi tare da shigewa d'akinta ta sauke labule. Shi kuwa Ahmad d'akin ya fad'a yana kuka yana fad'in, "Innar mu dan girman Allah ki duba min taguwata, wasu abu cizona suke a ciki". Wuuull ta wulloshi tun daga cikin d'akin har waje, sai da kanshi ya k'umu da k'asa, hannunsa ya juya tare da bada sautin k'ass, ya saki wani irin gigitaccen k'ara sai da gidan ya d'auka tare da fad'in, "Wayyooo Innar mu hannuna ya karye!" Ko lek'owa bata yi balle taga halin da yaron yake ciki, Inna Murja kuwa tana zaune daga k'ofar d'akinta tana yankan farce tare da taunar cingam, Daad kuma na d'akin ta, Inna Abu kuma bata gidan ta tafi kasuwar Laraba kasancewar tana saide-saide a gidan dangin su barkono, kanwa, magi, gishiri, kub'ewa, kuka, ashana, farin magi da sauran su, kuma duk laraba take fita ta saro, dashi take d'aukewa kanta buk'atun ta, yayin Inna Ladi ke sai da manja da mangyad'a da wake. A cikinsu Inna Murja ce kawai mai zaman banza sai idan an kyallara ido an ga na wasu ayi wuff dashi, ko b'era baya nuna mata sata da jin k'amshin kud'i ba... "To ni mai zan maka, uwar da ta haife ka ma bata damu da kai ba, balle kuma Murja karere. Ta ma kashe ka wa yayi asara idan ba ita ba". Fad'in Murja dai-dai lokacin da wata mata ta shigo da bokati a hannu domin jan ruwa a rijiya kasancewar suna da rijiya kuma ruwan gidan irin mai kyau d'in nan ne, sam bai k'afewa, idan an kwashe shi tsaf, bashi minti talatin zai sake tsattsafowa. Da sauri ta nufi inda Ahmad d'in yake kwance tana rabga salati. D'ago shi tayi, wani salatin ta k'ara rafgawa ganin hannunsa na lilo alamar karaya, "Inna lillahi wa'inna ilaihir raju'un! Gaskiya Murja baki da imani, kina ganin yaro yayi wannan fad'uwar amma kina zaune kina kallon shi! D'an mijinki ne fa shi, ai ko ba kiyi dan Laadi ba, kyayi don shi mal Bawa ko!".
Harara Inna Murja ta watsa mata tare da mik'ewa tsaye tana tafi tare da fad'in, "Ahayyee, yau naga ikon Allah! To ita uwar tasa da ta tsuguna ta haife sa, ta kuma san zafinsa, ita ta wurgo sa wajen har ya samu rauni a hannu kuma tana ciki tana jin ki, sai ni y'ar karere ce zan kwashi jiki inzo in taimaka masa! Ba ki da hankali Safara'u. Idan zaki ajiye sa a wajen kizo ki d'auki bokitinki ki ja ruwa ki yi gaba to, idan kuma zaki tsaya a wajen kina b'ab'atu, to ni kin ga shigewa ta d'aka". Tana gama fad'in haka ta d'aga labule ta fad'a d'aki har da turo kyaure...
Safara'u kuwa, Ahmad d'auke a hannunta yana ihu ta d'aga labule ko sallama bata yi ba ta fad'a d'akin Inna Laadi tare da fad'in, "La haula walaquuwata! Dama da gaske Laadi kina cikin d'aka kina jiyo irin wannan ihun nai man taimako da d'an nan yake yi? Haba Laadi! Wannan wani irin mummunar al'ada ce haka? D'an ki ne fa! Dubi halin da yake ciki fa!" Ta fad'i tana mai yin nuni da lankwashasshen hannun Ahmad d'in. Inna Laadi dake zaune bakin gado tana ninke kayan su Abubakar da ta kwaso daga shanya kamin ta fara shara. Ko kallon inda Safara'u take bata yi ba, sai ma tsam da tayi ta tashi daga kan gadon tare da yin wuff ta fito daga d'akin ta bar Safara'u da sakakken baki rik'e da Ahmad a hannunta. "Na shiga uku ni Safara, wannan wacce irin uwa ce, ko zamanin kakanni anya akwai irin su kuwa? Ka jeho d'an ka da kanka har ya karye amma ko a jikin ka sabida kawai ya kasance *D'AN FAARI!* Idan kunya ce tuni kika zubar tunda har kika iya tub'ewa a gaban ubansa har ya d'ura miki ciki kika haife sa. Akwai wani rashin kunya ne da ya wuce wannan? Tun da duk wanda ya gan ki da d'a ya san abunda kika yi kika haife sa". Tana gama fad'in haka ta kwantar da Ahmad nan k'asa a d'akin ta fice tana fad'in, "Ba ruwana billahil kada in taka sawun b'arawo, yaro yazo ya mutu a hannuna daga zuwa d'iban ruwa ace ni na kashe sa hukuma ta d'aure ni, ni wallahi d'ibar ruwan ma na fasa....
Comments and share as much as you can please🤝
*MATAR SAYYADEE* ✍️ [6/7, 6:34 AM] Rahamanatu: 🦜 *D'AN FAARI*🦜 ( _THE FIRST BORN_) *PAID BOOK*🤧 _TRUE LIFE STORY_
_Story and written_ *ZULFA'U SA'EED IBRAHIM* ( _MATAR SAYYADEE_)
☀️ *ZAFAFA WRITER'S ASSOCIATION*☀️ ( *Forum of intelligent and non-vulgar writer's of the nation*)💪🏻 _We aren't only writing for entertainment but rather we use our pen to highlight some of the challenges faced by women with a view to finding solutions to them._
*_D'AN FAARI ISN'T FREE, PAY #600 NAIRA THROUGH THIS ACCOUNT NUMBER 0592412800, ZULFAU SAID GTBANK AND SEND YOUR EVIDENCE OF PAYMENT THROUGH THIS NUMBER ***_*