Ɗan fari

Page 3&4

by @matarsayyadee3

Ko da Safara'u ta fito daga d'akin Inna Laadi, suf-suf ta fice daga gidan har da d'an had'awa da gudu. Kicib'is suka ci karo da Inna Abu ita kuma dawowar ta kenan daga kasuwar Laraba, sai da ta bangajeta kasancewar bata ga zuwan ta ba.

"Ke wannan wani irin iskanci da rashin hankali ne haka? Bakya gani ne? Wannan ai iskanci ne! Wallahi da kin min b'arna kin wa billahil sai kin biya ni kaya na, na fiki hauka wallahi". Dad'in Inna Abu tana hararar ta kamar idanunta zai fad'o k'asa. "Yi hak'uri Abu, wallahi wani bala'in da gujewa daga cikin gidan ku, d'an kishiyar ki ne ya karye ko kuma in ce miki uwarsa ta karya sa, kuma ko kallon inda yake bata yi ba, kuma ko da na shigo na iske Murja a tsakar gida tana yankar farce amma ko kallon in da Ahmadu yake bata yi ba. Shine fa na d'auki d'an na yi d'akin Laadi domin in ganewa idanuwana shin tana gidan ko kuma bata nan, sai kawai na iske ta kan gado tana ninkin kaya, da na fara yi mata k'orafi kuma, sai kawai gani na yi ta fice daga d'akin ta barni rik'e da yaro yana ihu a hannuna, to shine ni ma na ajiye sa a nan d'akin na yi fitowa ta gudun yaro yazo ya mutu a hannuna a ce ni na kashe sa, hukuma ta kama ni, shiyasa kika ga na yi irin wannan fitowar har ina k'ok'arin yi maki b'arna". "Inna lillahi wa'inna ilaihir raju'un! Shi Ahmad d'in ne ya karye a hannu? Na shiga uku!" Fad'in Inna Abu tare da shiga cikin gidan da sauri, a tsakar gida ta ajiye kayan tare da fad'awa d'akin Inna Abu in da take jiyo kukan Ahmad d'in har muryarsa ta dishe. D'ago sa ta yi, tare da kuma sakin salati ganin hannunsa na lilo. Cikin sauri ta fito daga d'akin ta yi hanyar waje ko bi ta kan kayan da ta shigo dasu bata yi ba. Inna Laadi kuwa tana ganin fitarsu, sai ta yi saurin shigewa d'akin ta, ta cigaba da ninkin kayan yara da take yi, kuma k'arya ne ka kalli fuskarta kace ka ga wani alamu na tashin hankali ko tausayi a idanunta, ko a jikinta ta cigaba da abunda take yi.

Inna Murja kuwa, tana ganin fitar Inna Abu ta yi saurin fitowa daga d'akinta gaba d'aya tayo wajen kayan Inna Abun tare da soma bubbud'e ledojin, ledan magi star ta d'auka guda d'aya, farin magi ma leda d'aya ta d'auka tare da lokan garin kuka da kuma barkono da kuma fulawa loka uku da Inna Abun ta sayo don yin taliya y'ar murji, ta yi d'aki da sauri har da turo kyaure tana murmushi.

Inna Abu kuwa tun da ta d'auki Ahmad bata tsaya ko ina ba, sai gidan Murtala wanzan dake can k'asan layinsu, ko da taje bata sa me shi ba, sai da aka tura d'an sa yaje yayi kiran sa sannan suka dawo tare da d'an nasa. Kallo d'aya ya yi wa hannun Ahmad ya ce, "Subuhanallah! Ya aka yi wannan yaron ya samu karaya haka har guda biyu a hannu?" Inna Abu na sharar hawaye ta soma magana, "Dawowa ta kenan na jiyo ihunsa daga cikin gidan, ban san mai ya same shi ba, dan Allah a duba masa hannun sai a d'aura sa". Karb'an Ahmad yayi daga hannunsa tare da fad'in, "Kud'in ki dubu takwas, a haka ma wallahi Abu dan ma kece da kuma tausayin k'aramin yaron nan". Inna Abu ta ce, "Babu komai duba masa hannun dan Allah! Allah sarki Ahmad, kai dai Allah ya had'aka da sakaryar uwa wallahi". Fad'in Inna Abun tana sharen kwalla. Kai hannu kawai wanzamin nan yayi kan hannun Ahmad ya saki wani k'aran da sai da Inna Abbu ta yi maza ta bar wajen ta shige d'akin d'aya daga cikin matan Wanzan. Ahmad kuwa har da kashi sai da ya yi tsabar azaba. Bayan an gama d'orin, wanzan ya fad'a mata abubuwan da za'a kiyaye don ya yi saurin warkewa. K'irgo dubu hud'u da d'ari biyu ta yi tare da mik'a masa tana fad'in, "Dan Allah ka yi hak'uri da wannan, shi kad'ai ne ya rage min a jikina, dawowa ta kenan daga kasuwa na taras da wannan abu, in sha Allah nan da kwana biyu ko uku zan kawo maka cikon kud'in ka". Ba tare da damuwa ba ya ce mata babu komai ita kuma ta sab'a Ahmad da ke ta ajiyar zuciya a kafad'a suka yo gida.

Da butan da ke tsakar gida ya fara ball sai da ta daki jikin bangon ginin k'asa sannan ta watse a k'asa a fashe saboda dama ta kanta butar ta mugun jin jiki, kuma da ita y'aran gidan suke uzuri. "Wata shegiyar mata ce a cikin ku ta lalube min wando ta d'auki naira dubu da hansin d'in da ita kenan ta rage min cikin jikina? Na ce wata shegiyar ce?". Fad'in mal Bawa yana kallon ko wani d'akunan matansa. Inna Murja ce ta soma fitowa tana sakin hamma, domin ba k'aramin yunwa take ji ba, kuma ba ta da ko sisi kuma tsoran girki abunda ta sata take yi, don ta san dole Inna Abu ta gane ita ta d'auka idan har ta yi girki, gashi kud'in mal Bawan da ta kwashe da safe, zibin dashi tayi. Fuska a washe ta soma magana, "Ah malam ka dawo! Sannu da zuwa daman kuwa kaman ka san kai nake jira". Mal Bawa kamar zai watsa mata harara, sai kuma ya fasa do ya san kaf gidan wajen ta be kawai zai iya samun kud'i. Sai ya ce, "Murja ki koma d'aka, don ba dake nake yi ba, da Zainabu da Laadi nake yi, ko su fito min da kud'i na, ko kuma wallahi kin ji na rantse, kun yi wa kud'in cefanen su na sati guda". Mal Bawa na ida zancen sa, Inna Abu na kunno kai cikin gidan kuma komai a kunnanta ya sauka. Wani kallo mal Bawa ya bi Inna Abu dashi dama duk cikin gidan ita ce abokiyar fad'an sa, Inna Laadi ko bi ta kansa ba ta yi bare ta kula sa, ko yanzu haka tana d'aka tana jiyo shi amma ko motsi bata yi ba daga inda take balle kuma ta fito har tayi sa'in sa dashi. "Yauwa! Ke kuma daga gidan uban wa kike da d'a sab'e a kafad'a? Ko da yake ni minene damuwa ta, abunda na sani shine kawai a cikin ke da Laadi tabbas wata ta caje jiki na ta d'auke min dubu da naira hamsin kuma ko a biya ni, ko kuma kun yi wa kud'in cefanen ku na sati guda, ehe!" Jikin Inna Abu har tsuma yake yi, tabarman dake shimfid'e a kusa da k'ofar d'akin Inna Laadi ta shimfid'e Ahmad sannan ta dawo ta tsaya gaban mal Bawa tare da tsira masa hannu a goshi sannan ta soma magana, "Ka ci uwar rainin hankali da wayo Mal! Kalle ni da kyau, na yi maka kama da wacce zata d'auki kud'in ka? Ka dai koma kayi tunanin in da ka shiga har aka caje aljihun naka aka kwashe kud'in ka. Har kana wani bud'e baki kana fad'in mun yi wa kud'in cefanen mu na sati sai kace dama kud'in cefanen kirki kake bamu, bayan idan Allah yayi mu ka d'an samu d'ari biyu a hannun ka wanda a sati biyu bai wuce sau d'aya ba, to ba k'aramin sa'a muka yi ba. Allah ma ya k'ara da aka sace kud'in, alhakin mu ne mu da yara, kuma wallahi kar ka k'ara sa mana sata, da ka fita yau daga wani d'aki ka fita? Ni dai na san ba ni ce da girki ba, kuma Laadi ma haka".

"Ke! Wallahi kar ki fara! Don naga kina k'ok'arin k'ala min satan, ko da yake an ce dama tabarmar kunya da bori ake nad'e ta. Kuje can ku fiddo masa da kud'in sa tun kan dare ya muku". D'aga hannu malam Bawa yayi tare da fad'in, "Haba Murja, haba! Ke har sai kin tsaya kina sa'in sa da ita, ai ina kallon kwayar idanunta na tabbatar ita ta saci kud'in nan, don na shiga d'akin ta har take tamabayata zata fita zuwa kasuwar Laraba, don haka tabbas ita ta d'auki kud'in nan, kuma sai kin biya ni". "Bawa, na d'auka! Na ce na d'auka kuyi duk abunda za kuyi kai da b'arauniya matar taka wacce b'atar basira ya saka ka kasa gane ita d'in wacece tun tuni. Mun mun riga da mun san halinta, tantiriyar munafuka kuma b'arauniya ce". A fusace Inna Murja ta ce, "Ubanki na sata? Na ce wannan shagid'ad'd'an tsohon mai kama da wanda cutar sida (AIDS) ta cinye sa!". Ta fad'i tana hararar Inna Abu tare da rik'e k'ugu.. "Uban nawa ne mai kama da wanda cutar sida ta cinye sa? Wallahi sai na kakkarya ki cikin gidan nan!" Fad'in Inna Abu tare da yin kan Inna Murja suka kaure da dambe, kuma Inna Abu irin matan nan ne masu k'aramin jiki amma akwai k'arfi kamar doki, duk da Inna Abu ta yi biyunta, sai da ta kai ta k'asa ta hau kilarta. Mal Bawa kuwa, wani tsohon bokitin k'arfe dake gindin rijiya ya d'auko dare da zama a kai ya soma bugun k'asan bokitin yana fad'in, "Ku casu ku casu ba mai raba ku! Hooo ni Sulaimanu Bawa, sai ni na Laadi da Abu angon Murja! Yanzu duk cikin fad'in unguwar nan wanene ake fad'a a kansa idan ba ni ba". Haka ya dun ga kuranta kansa, su Inna Murja kuwa sai faman dambe suke yi. Inna Murja da taga fa tabbas Inna Abu za ta iya yi mata illa, sai ta shiga ihu tana kiran Jama'a. Duk abun nan da suke yi, Inna Laadi tana d'aka tana ji, amma ko lek'e. Mak'ota ne suka fara shigowa, sai dai duk wanda yayi arba da mal Bawa yana kid'i da bokitin k'arfe, sai ya saki baki yana salati. Dakyar aka janye Inna Abu a kan Inna Murja wacce sai kuka take yi wiwi tana fad'in, "Ku bar ta ta kashe ni a kai wa iyaye na gawa ta, dama na jima da sanin kina mugun bak'in cikin gani na a raye, don haka ku bar ta ta kashe ni kawai". Mal Bawa kuwa dariya yake har yana rik'e ciki yana fad'in, "Ki bar su, abinci suka ci suka k'oshi, ni ai ina son irin wannan wasan ina kallo ina jin nishad'i". Nan jama'a da dama suka shiga tur da halin sa, wasu kuma suna fad'in Allah ya shirya. "Lahaula wala'quwata! Dama na fad'i wannan yaro karyewa yayi a hannu, Allah sarki har an gyaro hannu. Sannu kaji Ahmadu!" Fad'in Safara'u har da k'ok'arin matso hawaye. Sai a lokacin Mal Bawa ya lura da hannun Ahmad d'in, sai kuma ya mai da kallonsa izuwa wajen Inna Abu dake cika tana kumbura, don taso sai daki Inna Murja sosai ko za'a cece ta. "Abu, ke na gani d'auke da Ahmadu, mi ya same sa? Garin yaya ya karye a hannu?" Ya fad'i hakane yana mai k'arisawa kusa da Ahmadu wanda har ya farka daga baccin azabar da ya soma d'aukarsa sakamakon uban damben da Inna suka ci da junan su. Harara ta maka masa tare da fad'in, "Sai ka tambayi mahaukaciyar mahaifiyar ta sa kaji ta yanda akai yaji ciwo". Mik'ewa yayi a zafafe tare da nuna ta da hannu yana fad'in, "Ke iskanci ki ya tsaya iya mata na kar ki sake kice za ki min shi don sai in kad'a ki gidanku, ya zan tambaye ki, ki tsaya kina harara na tare da fad'a min bak'ar magana. Iskancin banza da wofi!". "Idan har aka zo wajen ka an zo basto (bustop), don duk garin zariya ban ga irin ka ba, abinci bai ishe mu, tsikari duk ya bi ya ishe mu, wannan wani irin bala'i ne haka, a'ah!" Fad'in Inna Abu. "Bala'i! Ni ne bala'in Zainabu? Zainabu! Zainabu!! Zainabu!!! Sau nawa na kira sunan ki? To wallahi ki kiyaye ni, tom!" Ya fad'i hakane tare da hankad'a labulan Inna Laadi wacce ke zaune a k'asa tana k'ulla manja a farar santana. "Munahika almura! Sai ki rik'a yin abu kamar mutuniyar kirki nan kuwa ta banza da wofi ce! Yo to ta banza da wofi mana. Yau kuma uban mi ki kai masa har ya yi sanadiyar karyewarsa a hannu?". Ya fad'i yana kallonta duk da kuwa ya san ko da zai shekara a tsaye a wajen ba za ta yi ko da tari mai k'arfi fa in dai akan Ahmad yake mata magana, ba shi ba, ko wanene idan zai yi mata maganar Ahmad baza ta tab'a bashi amsa ba, domin akwai wani lokaci da duka shekarun Ahmad d'aya da wata bakwai, yana wasa gindin rijiya, kuma saura kad'an ya fad'a sai Allah ya turo da wata mata ta zo d'iban ruwa a gidan ta yi saurin k'arisawa ta rik'o sa, ya kuwa tsandara ihu sabida ya tsorata, matan ta shiga kwad'a sallama a gidan tana tambayan d'an waye, Inna Laadi kuwa tana kallon komai a window, tun kamin matar ta shigo, amma kunyar *D'AN FAARI* ya saka tak'i fitowa gudun kada wani ya shigo yaga taje ceton *D'AN FAARI* zai fad'a rijiya, matar ta hankad'a labule su kai ido biyu da Inna Laadi, sai matar ta saki salati don a tunanin ta Ahmad ba d'an ta bane d'an kishiya ne shiyasa tak'i fitowa, nan kuwa ta shiga surfa bala'i da masifa har wasu suka shigo gidan way'en da suka san Inna Laadi ita ce mahaifiyar yaron kuma suka shaida mata. Baki sake matar take kallon Inna Laadi, daga k'arshe tsabar takaici matar ta fashe da kuka tare da dangwarar da yaron a nan k'asa ta fice daga d'akin, don ji take zata iya rufe Inna Laadi da duka idan ta cigaba da tsayuwa a cikin d'akin, ruwan da bata d'iba ba kenan ta fice daga gidan. Kwafa mal Bawa yayi tare da sakin labulan ya juya tare da ficewa daga gidan ko kallon Ahmad d'in bai sake yi ba, gudun kada a tambaye shi kud'in gyaran hannun Ahmad d'in. Inna Abu ce ta fito daga d'aki da sauri tana zuba salati tare da fad'in, "Wallahi ba haka na ajiye kaya na ba, an min sata cikin gidan nan, loka uku na fulawa da zan yi taliya y'ar murji, ledan magi star da kuma fari babu, har da kukan da na sayo zan k'ulla, wallahi da sake a gidan nan, dole a fito min da kaya na, tun da babu shegiyar da ta bani jari lokacin da na fara sana'a ta." Tana gama fad'in haka ta fad'a d'akin Inna Abu tare da mik'a mata hannu tare da fad'in, "Fiddo duka kaya na da kika d'auka ki bani tun muna shaida juna ko kuma in canza maki kamanni yanzu, ni ba Laadi bace da za ki yi wa abu ta kyale ki, Zainabu Abu nake!" Duk da Inna Murja a tsorace take da Inna Abu, amma sai ta daure ta soma magana da tsawa da kuma ihu, "Bam gane in fiddo maki kayan da na d'auka ba! Yaushe na d'auki kayan naki? Kin ganni ne ko kuma wani ne ya gan ni ha fad'a miki? Allah ya isa tsakani na da ku da kullum kuke bi na da sharrin sata, wallahi ba zan yafe maku ba kuma sai Allah ya mana shari'a ranar gobe". Hararar ta Inna Abu tayi tare da fad'in, "Ko kin fad'a, ko baki fad'a ba, tabbas sai Allah ya mana hisabi, ba ma ni kad'ai ba, har da sauran mutane da kike wa sata, ehe! Fito min da kaya na kawai tun muna shaida juna". Tsabar k'arfin hali irin na Inna Murja, tak'i fito da kayan, kuma Inna Abu ta caje ko ina amma bata ga kayan ba, babu in da bata hargitsa ba a d'akin, amma bata gani ba, hakane ya saka ta kalli Inna Murja tare da fad'in, "In Allah ya yarda, sai an kama ki dai dai kin kai hannu a kan kayan mutane zaki d'auka, kuma a cikin dubban mutane ta yanda kowa zai gane asalin koke wacece, kuma bazan tab'a yafe miki kaya na da kika d'auka ba". Tana gama fad'in haka ta fice daga d'akin. Inna Murja kuwa ta d'aga murya tare da fad'in, "Ni ma sai Allah ya mana hisabi na k'azafin da kika min!" Amma kuma k'asa-k'asa sai cewa tayi, "Ke kin isa in yi ajiya ki gani, to cikin kayan wanki na k'ulle! Kuma wallahi sayar dashi zan je in yi yanzu, in samu kud'in da zan saya abinci muci ni da y'ay'a na".

Inna Abu da zuciya tayi a kan ba za ta kuma kula Ahmad ba, ko hakan zai saka Inna Laadin ta yi hankali, amma da ta tuna ko wacece Laadi, sai kuma ta fito hannunta rike da robar abinci mai d'auke da fara da mai da yaji yaji man k'uli. Yana nan kwance a kan tabarma, amma kallo d'aya zaka masa ka san ba k'aramin jin jiki yake yi ba, kuma bini-bini yake durza bayansa a kan tabarma sabida rad'ad'in da bayan yake masa. Baccin ma a mugun wahale yake yin sa. K'arisawa Inna Abu tayi tana jin matsanaicin tausayin yaron a zuciyar ta. Ajiye kwanon tayi a gefe tare da d'an bubbuga k'afarsa, sai ya bud'e idanunsa. Mik'ar dashi zaune tayi tare da jingina shi da bango, amma sai ya fashe da kuka tare da shigewa jikinta yana kuma so ya kai hannusa mara ciwo zuwa bayansa. A hankali Inna Abu ta kware rigar, gabanta ne yayi wani irin mugun bugawa lokacin da tayi arba da bayan jazurr kasancewar sa fari, sannan ka kwarkwasa sama da ashirin sun manne a bayansa suna manna masa cizo..........

*MATAR SAYYADEE* [6/7, 6:34 AM] Rahamanatu: 🦜 *D'AN FAARI*🦜 ( _THE FIRST BORN_) *PAID BOOK*🤧 _TRUE LIFE STORY_

_Story and written_ *ZULFA'U SA'EED IBRAHIM* ( _MATAR SAYYADEE_)

☀️ *ZAFAFA WRITER'S ASSOCIATION*☀️ ( *Forum of intelligent and non-vulgar writer's of the nation*)💪🏻 _We aren't only writing for entertainment but rather we use our pen to highlight some of the challenges faced by women with a view to finding solutions to them._

*_D'AN FAARI ISN'T FREE, PAY #600 NAIRA THROUGH THIS ACCOUNT NUMBER 0592412800, ZULFAU SAID GTBANK AND SEND YOUR EVIDENCE OF PAYMENT THROUGH THIS NUMBER ***_*