GIDAN YAN KARYA

Page1

by @zahrawriter12

......"ke ke ke dalla matsa daga jikin motar nan, "kufa ya'yan talakawar nan matsalata da ku bakin ciki, idan ba bakin ciki ba,me yasa za ku rasa inda za ku dauki hoto sai a jikin motata?"matashiyar budurwar dake ta wannan babatun ta karaso gaban motar da yan matan suke tsaye cirko cirko suna kallonta.

"Me ye kuke kallona banga kuna shirin barin wajen ba?"ta kuma fada cikin dan tsawa bayan ta karaso daf da su,duk cikin yan matan babu wadda ta iya tankawa sai sulalewa da su ka yi suka bar jikin motar jiki a sanyaye tare da tsananin kunya,saboda yadda mutane suka zubo musu na mujiya,hannu tasa kamar zata bude motar sai kuma ta fasa ta koma ta jingina da motar tare da harde kafa da hannu tana kallon mutanen wajen a dage,ganin haka yasa kowa ya shiga watsewa na wajen kuma suka dauke ido daga kanta,duk da cewa ba wai dan sun gaji da kallonnata ba ne,saboda ita din macece irin wadda ta kai a kalleta a kuma kalla saboda baiwar kyawun jiki da na fuska da Ubangiji ya bata,hakan da ta sani ne yasa ta kuma tamke fuska tare da cuno dan karamin bakinta kamar zata yi kuka,wayarta ce ta bada Wani dan daddan sauti, a yangance ta daga tare da sawa a kunnenta,cikin fada me hade da kufula ta fara cewa "wannan wane irin wulakancine za ka ajiye mota ka yi tafiyarka,ba ce maka na yi ka tsaya a gama min wankin kan ba amma saboda raini ka yi tafiyarka,to wallahi idan ba ka yi da.gaske ba karshen aikinka ya zo a gidanmu,dan zan gayawa dadyna a canja min driver,ai kasan dady ya hanani driving bare na ja motar na tafi shi yasa ka yi min wannan wulakancin, na baka mintuna biyar duk inda kake kazo ka maida min da mota gida Ni kuma zan tafi a nafef tun dama haka kake so kuma kasan in dai dady ya ganni a dan sahu abin ba zai taba yi maka kyauba",ba ta saurari kome ba ta kashe wayar tare da barin jikin motar tana ci gaba da mita murya a sama dan duk wanda yake wajen sai da ya ji wannan tattaunawar.

A dedeta ta tare sai dai ganin wani a ciki yasa ta coge tare da cewa "gaskiya malam sai dai wanda ya ke ciki ya fito dan ba zan zauna da wani ba,ba cin ma driver ya min shirme me zai sa Ni hawa nafef"jin haka da me nafef yayi ne yasa shi saurin juyawa ya kalli na ciki yana cewa "dan Allah malam yi hakuri ka sauka tunda kaga dama ban jima da daukarka ba ka samu wani kawai kasan irin hajiyoyin nan yaran masu kuɗi basa son raini, Ni daukar wannan yanzu sai kaga ya yi sanadin canja nafef din nawa ma"cikin haushi da takaici matashin ya fito yana bankawa me nafef da budurwar harara,kafin yayi kwafa ya ce "wallahi kinci darajar kyanki amma da sai na miki rashin mutunci ko da ubanki zai daure Ni"ko kallonsa bata yi ba ta shige nafef din,shi ko me nafef yaja ta da gudu yana yashe bakin yau kakarsa ta yanke saka.

Cikin Nassarawa gra suka shiga, a daidai bakin wani tafkeken gida tasa ya direta, tana fitowa ta sanya hannunta cikin karamar hand bag dinta ta zaro dari biyu ta mika masa,sakin baki yayi yana kallonta saboda kudin da ta bashi ko kudinsa basu kai ba,ganin tana shirin tafiya yasa shi saurin magantuwa da cewa "hajjaju ko dai kina da matsalar ido ne kin dauka dala kika ba Ni ne?"a fusace ta juyo tana cewa "ina sane da abinda na baka iya kudin ka na baka,uban son banza da ka dauka zan baka kudin sabuwar nafef ne?"wani kakkauran miyau ya hadiye sannan ya iya cewa "to amma ko baki bani kudin nafef ba ai kya biya Ni kudin aikina ko"?bata kulashi ba ta ci gaba da tunkarar gidan, sai kawai me nafe ya saki baki ya bige da kallon halittar Ubangiji, duk da cewa kuwa ba wai shigar banza ce a jikinta ba a'a kawai halittar ta ce me matukar jan hankali ko da kuwa a cikin hijabi take, wannan dalili yasa ya hakura da maganar kudinsa ya juya yana cewa ga kyau iya kyau amma da ga Ni wannan zata yi girman kai ko na ce rashin mutunci yanzu haka ma yar aiki ce a gidan ta fito tana hura hanci da karya".

Cikin sanda ta bude karamin gate zata shige, amma tsawar da aka daka mata yasa ta dabarbarcewa tare da kokarin zubawa da gudu,"kar ki sake ki bar wajen nan idan ba haka ba kuwa sai na miki dan banzan duka"buzun mutumin da ya fito daga wani dan daki ya fada, wanda farin fatarsa da rawanin da yasha suka tabbatar da cewa shi din cikakken buzu ne.tsayawa ta yi tana kifi kifi da ido kana ganinta kaga mara gaskiya,"yau kuma wane magana ku ka dauko ke da yayunnaki dan nasan ku din nan baku taba fitar banza ba musamman ma ke da kike karamar su kuma mace kanwar maza"wallahi baffa babu kome Hajiya ce ta aike ni kawai"ungo nan taki ya fada yana ware yatsun hannunsa akanta tare da cewa "tun daga cikin banɗaki nake jiyo hayaniyarki kuma sannan kice babu kome ke Ummul ikram ki kiyaye Ni fa,duk abinda kuke keda yan uwanki na sani kawai dai ina kawar da kai ne in ga iya gudun ruwanku to amma naga abun naku kullum gaba yake yi,dan haka zan yi maganinku wuce ki bani waje"ya fada yana kai mata bugu da sandar dake hannunsa,aiko da gudu ta sheka zuwa cikin gidan, dan kuwa Ummul ikram na matukar tsoron abinda zai taba lafiyar jikinta.

Binta yayi da kallo daga bisani kuma ya girgiza kansa yana zama bisa dan bencin dake bakin kofar dakinsa dake daf da gate din gidan,yana cewa "yarinya sai shegen rashin ji da karambani kin dauki dabi'u na banza da wofi ke da yan uwanki kun mai da su sana a,zan je gidan ne an jima duk sai na ci kaniyarku daga ke har zuwa kan masu daure miki kugu "haka ya ci gaba da kananun mita kamar ikram din na gabansa.

Lokacin da Ummu ikram ta shiga tankamemen falon, saurin nutsar da kanta ta yi ta koma kalarta na masu aiki tana wani sunne kai kamar ba za a sa mata hannu a baki ta ciza ba.

"Ke daga ina kike?"ta ji an fada daga bayanta bayan da take kokarin shigewa bangaren da dakinta na wuccin gadi yake,diri diri ta shiga yi kafin ta ce"um Hajiya na ga ke din kika aikeni"eh Ni na aike ki shi yasa nake tambayarki ina kika je tunda naga baki da shirin zuwa ki sanar da ni sakon bayan jimawar da kika yi"sai da ta fara tura karamin bakinta kana ta matso kusa da hajiyar tare da mika mata farar ledar dake hannunta tana cewa "gashi dama zan kai miki kitching ne"karba ta yi tana watsa mata harara ba ta ce kome ba ta yi kwafa tana hayewa upstairs.yatsina fuska ita ma Ummu ikram ta yi tana mele karamin bakinta kana ta juya tana wani taku irin na kasaitattun mata tare da cewa "in sha Allah mu ma dai za mu yi arzikin nan har ma muyi taku irin na masu dashi"sai kuma ta kyalkyale da dariya daidai lokacin da ta karasa dakinta tana mai fadawa saman katifar dake malale kasan dakin wadda ake kira da gado huta,tana cewa wayyo Allah ya kuka Ummul ikram a g l k ta ke ko me oho tana juya kan sitiyari bisa kwalta, Allah dai yakai damo ga harawa, baffana sai ka daina gadi ummi na da yaya Safwan da ya Hamza da ya Ali da ya muftahu duk sai kun daina kwadago".

Kiran da ake kwalla mata kamar na mafarauta yasa ta saurin mikewa tare da ficewa a dakin, saboda sauri har dan kwalin kanta na zamewa,daidai tana fitowa cikin main falon,harara wadda ke kwala mata kiran ta zabga Mata kana ta ce "ke mahaukaciyar ina ce ina ta zuba miki kira amma kin yi kunnen uwar shegu da ni?oh saboda kin san yadda na tsani wannan tsinannan gashin naki shine kike bude min shi wato na hadiye zuciya na mutu ko?"ke kika so idan kin hadiye zuciyar"Ummu Ikram ta fada cikin kunkuni,"me kike cewa?"zezeee ta fada tana danko dogon gashin Ummu ikram din me tsayi da laushi kamar auduga,runtse ido ta yi tana ƙoƙarin kwatar kanta, sai da zezee ta tabbatar ta azabtar da ita sannan ta saketa tare da tunkudata baya tana cewa "kije maza ki hada min salad yanzu"daga haka ta samu waje cikin manyan luxury kujerun da suka yiwa falon kawanya tana wani sakin numfashi tare da lumshe kananan idanunta tana wani kalar hura hanci irin na isassun da suke ji da kudi.

Da sauri Ummul ikram ta goge hawayenta bayan ta shiga kitching din tare da cewa"sorry ikram kar ki yi kuka ki adana hawayenki zuwa ranar da zaki bawa zezeee aronsa saboda na tabbata duk ranar da kika yi arziki hawayen zeezee sun yi kadan dole sai an bata aron wasu dan haka zama jaruma kafin zuwan wannan ranar"tana gama fadin haka ta saki wani kayatacecen murmushi wanda har sai da kumatunta suka loba hagu da dama take wani boyayyan kyau ya kuma bayyana saman fuskarta,cikin nutsuwa da kwarewa ta shiga sarrafa kayan aikinta domin kokarin yin abinda aka saka ta yi.

A wannan yanayin da zezeee take ciki mom dinta ta sauko daga upstairs,har ta zauna zezeen bata san ta shigo ba, saboda yadda ta yi zurfi cikin tunaninta,har sai da mom din ta taɓa ta sannan ta ɗan zabura daga bisani kuma ta ja ajiyar zuciya tana cewa "mom kin sauko?"ba tare da mom din ta amsa ta ba ta watsa mata tambaya da cewa" ke kuwa me ke damunki zezee da irin wannan zuzzurfan tunani haka?"numfashi zezee taja kana ta kama hannun mom dinta tana cewa"wallahi mom duk lokacin da na kalli yarinyar nan ji nake kamar na kwace kyanta,saboda gani nake bai dace da ita ba dani ya da ce tunda Ni ina da kudin sarrafashi ta hanyar da ya da ce ita kuma talaka ce a karkashina take bai da ce ace ita take da wannan baiwar Kyan ba Ni ba, wallahi mom ina bakin ciki da haka, ke kuma nayi nayi ki ce ta koma gidansu ta bar aikin, ko kuma mamanta ta dawo ta ci gaba duk kin ki na rasa me yasa haka?"tunda ta fara maganar mom dinta take kallonta kamar taga wata sabuwar halitta ba ta cire idonta akan zeze ba har sai da ta dire zancan ta,kana mom ta numfasa tare da kawar da fuskarta daga kan zezen tana cewa,"gaskiya zezee kin bani mamaki yanzu kina so ki ce min duk irin ni'imar da Ubangiji yayi miki ba ki gode masa ba,duk irin matsayin da kike kai hakan bai sa kin ji cewa ke me sa a ba ce?to gaskiya idan har wannan ciwon zaki sakawa zuciyarki, to ba zaki taba samun sauki ba domin kuwa Ubangiji ya gama halittarsa ya rabawa bayinsa da suke takawa a doron duniya,dan haka ba ki isa canja abinda Allah ya ƙaddara ba,Ni wallahi na dauka wani mummunan abinne ya sameki shi yasa har na tsaya sauraren ki,da nasan wannan jahilcin zaki kawo min sam ba zan saurareki ba"daga haka ta mike ta bar zezeee tana faman kumbura baki da kuma mamakin mom din da ta kasa goya mata baya,duk kuwa da irin dinbin son da suke mata a matsayinta Na ya tilo daya da Allah ya basu.fitowar Ummu ne ya katse mata mamakinta a kan mahaifiyartata,a hankali ummu ikram ta ajiye dan bolw dake hannunta da salad ke ciki kana ta juya ta bar wajen ba tare da ta bi ta kan hararar da zeze take mata ba tun bayan karasowarta.

Tana shiga daki ta yi saurin ɗaukar gyalenta tana cewa "bari na bar muku gidan da wuri tun kafin ku cinyeni ban ida cika burina ba"ta baya ta yi ficewarta dan tasan in dai ta fita suka ganta ba zasu barta ta tafi a wannan lokacin ba,zuba mata ido babanta yayi har sai da ta karaso gabansa kana yayi gyaran murya yana cewa, "se kuma ina da yammar nan?"baffa gida zan tafi"ta fada tana yin ƙasa da kanta a ranta tana addu'ar Allah yasa karya ce ta koma ba yanzu ba,"to wuce Allah yasa dai ba wani lefin kika yiwa mutanen gidan ba, saura kuma ki tsaya a hanya neman magana irin taki kamar yadda kika Saba"bata ce komai ba ta wuce sum sum a ranta tana cewa yo Abba ai kai ma kasan dole sai nayi rahazal dan kuwa arzikina yana tafe aha".daga fitar ta sai da ta bari ta dan yi nisa da gidan sannan ta canja takunta har da karkata dankwali,nafef ta tsayar, wanda sai bayan da ta tsayar dashi taga ashe da mutum biyu a ciki dattijuwa da kuma saurayin da kallo ɗaya zaka yi masa ka tabbatar shi din ɗan boko ne kuma ɗan masu kuɗi wata kila wani dalili ne yasa shi hawa nafef,to fa su Ummu abin nema ya samu nan fa daga shigar ta aka zaro fankon iPhone pro Max 13 din zezee da ta lalace aka shiga dannawa a wani yangance,kafin daga bisani ta karata a kunnenta,cikin daddar muryarta da turancin da take koya a bakin zezee , ta ce"hello Nancy i m hearing you"bayan dan jim da ta yi alamar sauraro sai ta kuma yatsine fuska tare da cewa, "ok kinga yanzu ina kan hanyar zuwa bank din amma ina nafef ne,becous of my car tana wajen driver bai dawo daga aiken da na yi masa shopping moll ba,if you can wait come back from the bank ,I dan yaso sai na na sameki a restored din,ok ai ba masu yawa zan cire ba just ane milion Naira only,by"ta fada tana kashe hasken wayar da shi kawai yake amfani akan wayar,gaba daya nafef din ita suke saurare, yayin da dan bokon nan yake dan murmushi a ta gefe guda idan yaji kuskure a Turancin nata da kuma kudin da ta ambata zata ciro a bank,dattijuwarce ta fara sauka dan haka sai ya rage daga wannan saurayin sai Ummul ikram,hakan yasa ta kuma dagewa da wajen kiraye kirayen wayar karya,tana shirya karya kamar babu gobe,wayar da ta yi ta karshe shi ya kure saurayin ya kasa dauriya har sai da ya saki dariya,saboda jin tana cewa wanda take wayar da shi ya je ya zabi motar da yake so a campanin abbanta me suna DAN ITOPIA MOTOS,bayan kuma duk cikin garin Kano da wajen Najeriya babu wanda bai san DAN ITOPIA MOTOS ba, gidajen mansa da sauran kamfanunuwa da abubuwan sarrafawa kamar su auduga shinkafa karafa da dai sauransu,babu inda utopia's basu zaga a fadin duniyar nan ba,hasali ma a garin Abuja yake zaune da iyalansa,amma wai yariyar nan take cewa babanta ne in a wani wajen ta fada fa tsaf za a kamata.

Dubansa ta yi cike da mamakin dariyar da yake yi,sai kuma ta dauke kanta tana mai ciro katon glass dinta da ya kusan mamaye fuskar gaba daya ,sai dai fa ba karamin kyau yayi mata ba kasancewarsa baki ya samu lafiyayyar farar fuska,duk da cewa ba za mu saka ikram cikin farare kal ba sai dai kalarta me haske ce dan tafi hasken calculate, sannan zamu iya kiranta da fara amma ba kal ba,yadda ta hade fuska yasa saurayin shiga taitayinsa dan gaskiya fa shi tuni ya fada,kuma salon yarinyar ya matukar burgesa duk da cewa ba komai a cikinsa sai zallar karya da actin din masu kuɗi,gyaran murya ya yi tare da cewa hello baby zan iya cewa wani abu?"no need"ta fada cikin kara hade girar sama da ta kasa,tare da cewa me nafef "malam wai ina zaka yi dropping din wannan uban shishshigin?"kafin me nafef ya bata amsa saurayin yayi tsalan ya ce"a'a sai an fara a jiye ki saboda Ni drop na daukesa kuma za mu yi nisa sosai so dan haka muje a fara kaiki bank ɗin "wani irin kakkauran miyau Ummul ta hadiya, wannan mutumin so yake kawai ya kureta,idan ba haka ba me ye zai ce a fara Kaita,to idan ya Kaita bank da wane kudin zata kuma shiga ta koma gida gashi ja iz bank ta ce a kaita ba union ko access ko gt ba bare idan an sauketa ta karasa gida a kasa tunda kofar ruwa ne,to me ma yasa ta ambaci ja iz ne?ya dai naji kin yi shiru ?saurayin ya fada yana leka fuskarta tare da nazarin halin d ta shiga,bata kula shi ba sai duban me nafef din da t kumayi tace,kaga ma muje kawai ka kaini Access na kofarruwa na fasa ja iz din dan sai yanzu n tuna ATM card din baya wannan bag din" ok baki da matsala hajjaju in dai zaki cika min nawa aljihun ai shike nan"dam kirjin Ummul Ikram ya buga ita fa ba tsoron ta dauki kudi ta bashi ya ce yayi kadan take yi ba,a'a wannan saurayin da ya tare gaba da baya shi take tsoron kunyata a gabansa dan wallahi bata da kudin da ya wuce dari biyar dan dama shine iya kudin da ake kaita gida kullum ke nan daga nan Nassarawa gra zuwa kofar ruwa.

Tun daga lokacin bakin Ummul ya mutu har suka karaso kofar ruwa bata kuma cewa komai ba duk da yadda saurayin nan yaso kulata d magana,lokacin da me nafef ya faka a daidai Access sai da gabanta ya fadi, amma sai kawai ta dake ta fito daga nefef ɗin, tsoron bashi kudin take, kai su kansu kudin kunyar fito da su take saboda yadda suke a yagagale, da wuya ma idan zai karba,yanzu ina zata kai wannan abin kunyar............😒✍️

Yanzu wa zai fidda Ummul daga kokarin shan kunya wajen gayen saurayi?😂

[10/15, 9:51 PM] fatima y Adam(Zahra✍️): 💞GIDAN ƳAN ƘARYA💕

By

FATIMA Y ADAM......

Littattafan marubuciyar.

KUDIRAR ALLAH

KADDARATA SANADIN HASKE

ƁOYAYYIYAR RAIHAN

ƳAR GIDAN YARBAWA

MATAR ƊAN BIRNI

And

GIDAN ƳAN ƘARYA..