Page 3
Cikin takun isa take saukowa daga mata kalar benen dake cikin falon,kallo daya zaka yi mata kasan cewa akwai gayu da ji da kai, sannan kana kallonta zaka bata shekaru sama da talatin,tana da jiki sosai wanda shi yake nuna shekarunta ƙarara a fili. ba wata kyakkyawa ba ce amma ba zaka sa ta a layin munana ba domin yar gayu ce ta ajin ƙarshe,Hajiya zahida kenan mata gurin MUS'AB JAMIL babban da ga wannan ahli..
Tana saukowa wata mata dake dakon saukowarta ta yi saurin tashi tare da miƙa mata farar labcort ɗin da take hannunta cikin tsantsar biyayya da taka tsantsan ɗin yin kuskuren da zai sa tasha zagi ta uwa ta uba.ba tare da ta yiwa matar kallo ɗaya ba ta karɓa tana wani ƙara tsuke fuska wadda tasha sun glass baƙi,daga haka ta ci gaba da takun isa idanunta akan hadaddiyar wayarta, sai da taje bakin ƙatuwar kofar galass din da ta raba tsakanin valconin gidan da falon kana ta ɗan dakata, sannan cikin fuzgo maganar kamar ana mata dole ta ce "larai har yanzu ba a samu me ci gaba da kula da khalid ba?" Cikin ladabi larai ta ce"ki yi hakuri ranki shi daɗe ana nan muna cikitawa saboda har yanzu ba a samu wadda ta cike sharadanki ba" ci gaba ta yi da tafiya ba tare da ta tanka ba,sai da larai taga fitarta sannan taja ajiyar zuciya tare da hamdala sun rabu lafiya da uwar dakinta ba tare da anzagi iyayenta na kabari ba,wucewa ta yi dan ci gaba da haɗawa mutanen gidan karin kumallo kafin su fito.
Tana gamawa kuwa sai ga uwar gida sarautar mata Hajiya Nana,daga nan sai Khalid yaro dan shekara biyar cikin shigar makaranta shida auta suhaima wadda ita ce ta shiryasa,daga nan sai bukar me bin mijin Hajiya zahida sai karaminsu suleman,daga nan sai kan gidan wato kakarsu wadda suke kira da anne.
Tunda suka zauna babu me surutu har suka gama suka tashi da daddaya kowa na wucewa sabgarsa me makaranta me aiki duka kafin wani lokaci sun watse,sai iya anne da Hajiya Nana wanda sune kawai basa fita aiki.
Kai tsaye zahida JGK hospital ta wuce inda a nan ne take aiki a matsayin likitar mata, sannan kuma tasan sirrin fida dan haka ake ji da ita a asibitin duk da ta kasance ɗaya daga cikin ya'yan masu asibitin.
Duk yadda take da girman kai da raina talaka hakan baisa ta hana ko ta gaza wajen basu taimako ba a duk sanda hakan ta bullo, wanda hakan yake matuƙar bawa yawancin mutanen da suka santa mamaki da bincike da bin kokofin cewa lallai da wani abu a ƙasa dan abin da matuƙar mamaki ace zahida Garba da bata da tausayi da imani ace tana taimakon talaka da bada gudummawarta a duk sanda hakan ta taso,da yawan mutane suna zargin cewa akwai manufa akan hakan wasu kuma suna ganin ai dama ɗan adam tara yake a komai bai cika goma ba,to koma dai me ye zahida Garba na ɗaya daga cikin amintattun wannan asibitin wanda suke bada gudummawa ta temako akan talaka me ƙaramin ƙarfi wannan kenan.
******
Alhaji Garba da Alhaji Kabir da Alhaji Jamil, Aminan junane tun zamanin KURUCIYA tare suka taso babu wanda yasan sirrinsu daga su sai su,tare suka yi arziki suka yi aure suka kuma gina rayuwar ahlinsu a tare ba tare da wani yaji kansu ba,dukansu marayu ne babu me uwa ko uba a cikinsu sai Alhaji Jamil, banbancin su suna da yan uwa na jini amma shi shi kadai iyayensa suka haifa, shi yasa mahaifiyarsa anne ke ji dashi kamar tsoka daya amiya,tare su kayi aure suka fara haihuwa.
Alhaji Garba 'yarsa ɗaya zahida daga kanta bai kuma samun haihuwa ba,shi kuma Alh kabir yaransa biyu duka maza,sai Alh Jamil wanda yafi su yawan ya'ya, nasa guda hudu ne maza uku mace ɗaya,Dukansu sun fito daga daga asali daya wato Fulanin gombe.matansu duka yan Gombe ne komai nasu yana cikin gida arzikinsu ne kawai yayi shura ha fita kasashen duniya.
JGK hospital idan ka haɗa farkon sunansu zata bayar asibitinsu ce guminsu ce babu wanda yasan yadda suka yi suka samu tarin arzikinsu sai su tsakaninsu,basu yi karatu suna yara ba sai da suka fara samun duniya sannan suka yi yaƙi da jahilci wanda idan baka sani ba bazaka taba cewa basu yi karatun tun farkon kuruciyarsu ba,amma fa sun tsayawa yaransu sun yi ilmi na boko da Arabia sosai dan haka rayuwar ahlinsu ta ginu da wadataccen ilmin duniya da na lahira,sun yi kokari sun haɗa zahida da MUS'AB aure a matsayinsu na masu iko da ya'yansu ba wai dan shi mus ab yana so ba,sai dai ita zahida tana balain sonsa duk da cewa ba wani mugun girmanta ya yi ba dan shekara ɗaya tsakaninsu.
Abu na farko da addinin da suka basu ya fara tasiri kenan akan mus ab dan bai yi jayayya da cewa wani lokacin tsananin muskilanci ne yake sawa ya haƙura da son ransa, zahida dai a bayyane tayi makarantar addini amma a badini babu komai a kanta dan bata da basira ta fannin ilimin addini sai wajen boko a nan tafi kauri.
Zahida takasance mace me shegen son kudi ko nace son duniya, hakan ya sami asali ne daga yadda take da girman kai da son ace kowa tafi shi kuma kowa a kasanta yake wannan ne yasa ta dage ta yi ilmin boko dan cimma burint na zama sananniya a bangaren d maimatsala.hagamtaryƙan gari, tana ganin aminatu kuwa salon tsakano aminatu sai da ta yi yadda ta yi ta bangajeta garin g
[10/15, 10:08 PM] fatima y Adam(Zahra✍️): 💞GIDAN ƳAN ƘARYA💕
By
FATIMA Y ADAM......
Littattafan marubuciyar.
KUDIRAR ALLAH
KADDARATA SANADIN HASKE
ƁOYAYYIYAR RAIHAN
ƳAR GIDAN YARBAWA
MATAR ƊAN BIRNI
And
GIDAN ƳAN ƘARYA..