Page4
Tsawar da baffanta ya daka mata ne ya dakatar da ita daga yunkurin dukan zezee wadda ta ware idanunta tana kallon Ummul din,cikin mamaki da fargabar dukan da take shirin kai mata,"baffa dan Allah ka rabu da ni yau daya dai na nuwa wannan matar cewa ba taoronta nake ji ba kuma ba tsoron su Kore ni nake ba"ba za a bari ba din idan ke bakya tsoron a koreki ai ni ina tsoro da me na dogara idan ba wannan aikin ba?shekara da shekaru tun kafin ki fara tafiya nake aikina ban taba samun matsala ba,dan haka duk abinda za su yi miki na haneki da yin ramako"wani makirin murmushi zezee ta yi tare da cewa "ai da ka bari ta dake ni ta gani yau idan bata kwana a cell ba,kai kuma ka ga dai abinda ya faru bayan tsiya da suke dauke da ita har da tantiranci"cewar zezee tana duban saurayin da tuni yayi mutuwar tsaye a gun da yake,cikin fusata Ummul ta ce"wallahi mu ba matsiyata ba ne dan na tabbata wata rana sai kin zubda hawayen bakin ciki akan ni imar da Allah zai yi mana, kuma yanzu ma nasan kina cikin bakin ciki saboda ina da abinda Allah bai baki ba,ai gara ma ni ina da damar yin karyar kudin ke kuwa fa baki isa yin karyar kyau ba,ko da kuwa zaki koma ciki a sake haifoki yadda kike haka zaki dawo domin Allah ya gama halittarki, Ni kuma Allah zai iya yi min arziki ya haɗa min gaba daya ga kyan ga kudin idan yaso sai ki hadiyi zuciya ki mutu"wani uban ihu zezee ta fasa har da dora hannu aka, saboda yadda kalaman Ummul ikram suka shigeta shigar da ita kanta Ummul bata san zasu yiwa zezeen ba,tabbas bahaushe yayi gaskiya da ya ce idan baki yasan me zai fada bai san me za a mayar masa ba,sosai kalaman suka yi mata ciwo wanda suka yi sanadin kara ruruwar wutar tsana da hassadar Ummul ikram din a zuciyarta.
Da gudu momy ta fito tana tambayar ba a sin abinda yake faruwa, zezee ta kasa bata amsa, Ummul kuwa kanta ta kaɗa zata fita daga gidan, baffanta ya dakatar da ita da cewa "gidan ubanwa zaki je?"cikin kuka ta ce "dan Allah baffa ka barni na tafi wallahi na hakura da zaman gidan nan koda kuwa za a bani yanke talauci duk da yadda na tsani talauci kuwa"momy bata ce komai ba dan tasan tsiyar daga yarta ne,dan haka janta kawai ta yi su ka yi ciki,yayin da aka bar saurayin nan tsaye yana kallon Film din da bai taba ganin irinsa ba,sai yanzu ya fahimci komai akan Ummul ɗin sai dai bai ji zai iya fasa ƙudurinsa akanta ba, dan shi kam tuni ya kamu, wannan tunanin da yayi yasa shi nufar baffa yana bashi hakuri cikin ladabi da kwantar da kai,harara Ummul ta zabga masa da manyan idanunta da suke cike taf da kwalla tana cewa kawai malam ka yi tafiyarka ai duk kai ka jawo mana, da ba ka biyo ni ganin kwakwaf ba da haka bata faru ba,to hankalinka ya kwanta kazo ka tabbatar da ni wacece duk abinda na yi ko na fada karya nake ni yar aiki ce baffa na me gadi sai ka ƙara gaba abi wani sarkin amma ba Ummul ba"daƙuwa baffa ya yi mata tare da yi mata nuni da cikin gidan,sai da ta ballawa saurayin harara sannan ta juya ta kalli cikin gidan shima ta watsa masa banzan kallo kana ta yi ƙwafa ta wuce zuwa falon a ranta tana fatan su koreta a gidan gaba daya ko ta samu salama da yanci.
Baffa kuwa waje ya samu ya zauna tare da kiran saurayin,sun jima suna magana, domin sulaiman kamar yadda ya fadawa baffa sunansa ya tabbatar da cewa son ikram yake kuma aurenta zai yi,hakan yayiwa baffa dadi a ransa yana jin cewa ƙarshen rikicinne yazo dan haka gwara yayi mata aure ya huta itama ta huta da yawon jaye jayen magana,baffa ya sanar da shi ya je bayan kwana biyu lokacin gimbiyar ta huce yaje can gidansu ya sameta,baffa da kansa ya bashi adireshin gidansa dake kofar ruwa,daga nan sulaiman yayi godiya ya tafi.
A can bangaren zezee kuwa kuka take kamar zata karar da hawayenta,momy dai nasiha kawai take mata da nuna mata abinda take ko tasawa ranta da ba daidai ba ne,momy ni dai a kori hari yar nan idan ba haka ba zata sa min ciwon zuciya ta kashe ni a banza a wofi"AA fa zezee babu wanda zai kashe ki sai dai idan ke kika sawa kanki abinda zai kashe kin, kuma wallahi kika dake kika fadawa abbanki wannan maganar sai na saba miki,dan idan aka kori ikram ba za mu taba samun masu aiki masu amana kamar su ba,ga tsafta da iya girki, ke kanki ba zaki samu nutswa ba dan babu me aikin da zata juri wahalar ki kamar ikram ɗin"momy ikram dince take da hakuri wannan fitsararriyar yarinyar duk abinda na gaya mata fa ko a ciki ne sai ta min gunguni,dan yau baki ji maganganun da ta fada min ba har duka na ta so yi, wallahi momy ikram bata da wani mutumci ko hakuri"murmushi momy ta yi tare da cewa "ai kuwa tana da hakuri ni a guna tunda ta iya zama da shalelena"ganin momyn ba zata fahimceta ba yasa ta hakura ta yi shiru amma ba dan zata sassautawa ikram din daga gallazawarta da ukubarta ba.
Ummul ikram kuwa tana shigowa, ta tsaya a tsakiyar falon tana hararar ko ina kamar shi yayi mata laifin,dakinta ta nufa ta cire kayanta ta saka na aiki,kana ta fito ta shiga kitchen, zuciyarta na son kiran ummi ta kuma tambayar ta ko gentle ya zo,sai dai kuma bata da dalilin yin hakan,tsaki ta yi tana jin haushinsa na karuwa a ranta,dan duk abinda ta yi yau din har da haushin rashin zuwansa da ya kuma tunzurata,girki ta fara ɗorawa kafin ta wuce dakin zezeen dan gyara mata.
Cikin ƙanƙanin lokaci ta gama ayyukanta, ƙarfe huɗu daidai tuni ta gama musu girikin dare ta jera komai a dinning room, wucewa ɗaki ta yi ta yi wanka ta sanya kayanta ta ɗauki 'yar jakarta ta fito dan tafiya gida,dan duk abinda take yi hankalinta na can,kicibus suka yi da momy, ɗan tsayawa ta yi tare da yiwa momyn sannu da gida,"tafiya zaki yi ne yauma da wuri?"momyn ta tambayeta tana tsareta da idanu,jinjina kanta ta yi tare da cewa "ey momy na gama komai sai dai kuma idan kuna bukatar wani abun sai na tsaya na yi?"dan jim momyn ta yi kafin ta ce"babu wani abu dan itama mutuniyar ta ki tana bangarena kanta ne yake ciwo"Ummul ta ce ai dole ta yi ciwon kai tunda ta ɗorawa kanta masifa"momy ta katse mata zancan zucinta da cewa "kije kawai sai Allah ya kaimu gobe amma dan Allah ikram ki ci gaba da hakuri da mutuniyar ta ki kin dai san halinta,kuma kizo da wuri goben saboda ina kyautata zaton zamu yi bako ko na ce zezee zata yi bako, kinga dole muna bukatarki da wuri ko?karbi wannan kudin idan kin fito ki biya wellcare ki yo mana soyayyar abinda ya kamata dan mutumin dntsurfa ne ga fi ili shi yasa nake so a yi abinda zai burgeshi ko dan mahaifinsa da yake son hada zuri'a damu"karbar rafar yan dubu dubun ta yi tana cewa "in sha Allah momy zanzo da wuri"Ummul ta fada tana ɗorawa da yi mata sallama.
Yau dai Ummul ikram bata cikin mood din da zata taba halin, dan haka kai tsaye nafef ta tara ta nufi gida.tun daga nesa tazubawa kofar gidansu, lumshe fararen idanunta ta yi tare da jan dan karamin tsaki,duk da ta gansa zaune yana ta aikinsa cikin kamewarsa da kowa ya sanshi da ita,hakan bai hana jin haushinsa ci gaba da nukurkusarta ba,suna karasowa kofar gidan ta fito tare da mikawa me nafef kudinsa, har ta juya sai ta ji me nafef din yana cewa "haba ashwariya kudin ki fa yafi dari huɗu"duk da yadda ta yi niyyar kin kula kowa a waje yau din amma sai da ta ji zuciyarta ta harzuka da abinda me dan sahun ya fada,jinjina kai kawai ta yi ta kuma juyawa zata shige gida idanunta nahasko mata gaban p cap din gentle da ita kawai ake iya gani duk da cewa kuwa a zaune yake,"ke wai ya na ga kina kokarin shigewa gida ne baki biya Ni hakkina ba,dan sahun ya kuma fada yana cire key din mashin din tare da fitowa, juyawa ta yi tana kare masa kallo, wani bakikirin da shi kana ganinsa kaga irin yan jagaliyar nan da rokon Allah ya sa suka fara nutsuwa suka kama sana'a,ya dai kike kallo na haka kawai ki sallameni na wuce"idan kuma naki fa"Ummul ta fada cikin dakiyar zuciyarta da take a kusa,wata banziyar dariya yayi tare da cewa kin san sauran dan dai kin san daga gani na ba zan yi wani mutunci ba dan babu ruwana da kyan mace kudi yafi min,idan na same su ko wace irin mace nake so zan aura dan haka ki cika min dari shida na na fece"kan bura U....sai kuma ta yi shiru saboda jin alamun ido akanta, juyawa ta yi saitin da yake, ga mamakinta bata ga wata alama da take nuna cewa yana kallonta ba, sannan ita kuma ta yi yakinin cewa yanayin da ta ji a jikinta ba na idanun kowa ba ne sai na sa, amma dubi yadda ya fuske tsabar iya nunkufurci kamar ba shi ya dora mata ido ba.
Juyawa ta yi ga me dan sahun tare da watsa masa kallon banza kamar idanunta zasu fado kasa,kana ta ce"kai kasan ko Ni wacece da har zaka zo ka dinga fada ina faɗa?"oho ko ma wacece Ni kudina kawai na sani"ya fada yana wani hura hanci kamar zai kaiwa Ummul ikram duka,wani hadaddaden murmushi ta yi saboda tunawa da kudin da momy ta aiketa da su, dan juyawa ta yi hagunta da dama kana ta dawo da kallon ta kansa tana cewa, idan ka ganka a cikin cell zaka fahimci ko Ni wacece,da fari dai ni ba talaka kuma matsiyaciya ba ce irinka,kuma kudina ba na yan shaye shaye ba ne shi yasa tun farko ban nuna maka asalin ko Ni wacece ba "bude jakarta ta yi ta dauko wannan rafar kudin ta nuna masa tana cewa kaga misali na farko,aby na biyu kuma zan sanar da kai waye mahaifina kafin kaga matakin da zan dauka kanka,me don sahu da jikinsa ya fara yin sanyi ya ce "to Hajiya da kin san da kudin amma kika tsaya raina min hankali"au Ni nake raina maka hankalin ma?"wallahi wannan mutumin da kasan arzikin da ka hana kanka da ka yi kuka dan ko yanzu kafin na shigo nafef dinka sai da na yiwa mutum uku kyautar irinsu sabbi duk fil daga companin mahaifina wato DAN ITOPIA MOTO'S,dama ina gwada ku ne saboda na san irin mutanen da zan taimakawa, saboda na fison na yi wa wanda nasan shi ma zai taimakawa wasu"daga haka ta dauko bogin iPhone dinta ta shiga latsawa fuskar nan babu sauki kai ka ce gaske ne,me dan sahu tuni ya fara share gumi yana kai kawo a tsakanin wajen,bai ida rikicewa ba sai da ya ji Ummul ta na cewa"yauwa cp dan Allah ina son ka turo min mota guda ta yaranka", dan jim ta yi kafin ta ce" a'a ina wannan gidan marayun dake kofar ruwa kasan yau basaja nayi na fito ni kadai babu gerd bare driver"kafin Ummul ta kai karshen zancanta tuni me nafef ya zube a kasa yana magiya da roko kamar ba shi ne ya gama fadar abinda ya gadama ba yanzu.
Dan Allah ranki shi dade ki yi hakuri wallahi ban san ke yar gidan dan itopia ba ce,ki rufa min asiri wallahi fursuna babu dadi, ban jima da fitowa,na bi Allah na bi ma aiki n biki"kallonsa ta yi bayan ta shaki iska tana wani bude hanci da kanne manyan idanunta, "ta shi ta fada cikin alamun sassauci, yana tashi ta nuna masa nafef dinsa, ai ko da gudu ya nufeta ya shiga ya tayar, kan ka ce kif ya bar layin da matsiyacin gudu,ai ko Ummul bata san lokacin da ta sheke da dariya ba har da wahaye,sai da ta yi me isarta sannan ta juya zata shiga gida, sai da ta kallesa sama da kasa sannan ta tura karamin bakinta hadi da murgudashi tana mai harararsa kasa kasa hadi da gungunin da ita ka dai tasan me take fada.
Tana shiga gidan ana magriba dan haka jakarta da mayafinta kawai ta ajiye ta dauki buta ta shige bayi.
Bayan sun idar da sallar ne Ummul ta dubi Ummi ta ce"ummi wai yayuna duka basu dawo gida ba?"kafin ummi ta bata amsa suka tsinkayi sallama daga zaure, amsawa ummi ta yi tana fadin waye ne?"wanda yake sallamar ya amsa da cewa musa ne me guga"oh musa shigo mana ka tsaya daga zaure" cewar ummi tana gyara lullubinta, kasancewar zaune take akan sallaya tana ci gaba da lazimi,shigowa yayi ya ɗan yi tsuguno tare da gaidata,amsawa ta yi tare da tambayarsa ko lafiya?"fuskarsa da alamun damuwa ya fara kora mata bayani da cewa, "wallahi ummi karar Ali na kawo miki,wato tun shekaran jiya ya zo ya har wajen sana a ta ya haɗa Ni da Allah akan na bashi aron kayan fitar kunya a cikin kayan da ake kawo min wanki da guga,da farko na hanashi saboda gudun shiga rigima, amma sai ya dinga magiya akan cewa yana dawowa zai kawo min,to haka dai na hakura na bashi tare da alkawarin ba zasu kwana ba sannan za a kiyaye duk wani abu da zai taba lafiyarsu,amma ummi da Ali ya tashi dawo min da kayan nan sai ya dawo da su a wanke a goge kamar yadda na bashi,na karba na yi godiya dan naji dadin yadda ya cika alkawari,to ashe ban sani ba barna ya tabka dan ban tashi sani ba sai dazu da me kayan ya dawo ya tarfa ni akan lallai sai na biya shi kayansa saboda sun yi fata fata da ƙuna babu ta yadda za a yi su moru gashi kayan sabbi ne ko sanya su bai yi ba, a halin da ake ciki yanzu ya ce sai na biya shi kudin shaddar ya yafe na ɗinkin,saboda ya ce ban gaya masa ba sai da yazo sawa ya bude kaya yaga sun kone,shine kuma na tari alin na fada masa amma sai ce min yayi shifa dama a haka na bashi kaya ko sawa bai yi ba ya dawo min da su"tunda Musa ya fara magana ummi take tafi da salallami,har sai da ya kai karshen maganarsa sannan ta ce"innalillahi wa inna ilaihi raji'un, yanzu yaran nan ba zaku barni na huta da wannan mugun halin naku ba? ku dai idan ba ku debo min magana ba ranku baya fari babu babba babu yaro", Ummul ikram ta yi tsalam ta ce"a'a fa ummi ki yi bincike kafin ki bawa yaya Ali laifi kina ji fa ya ce a haka musan ya bashi"ke dalla rufe min baki sakaryar wofi, to maza tashi ki dauko wayarki ki kira min shi yazo a duk inda yake ya sam.....sallamar yaya alin ne ya katse ummi,binsa ta yi da harara kafin ta dauki takalmin gefenta ta wurga masa,dan tsalle yayi ya matsa gefe yana cewa Ummi ki fara yin bincike kafin ki yi hukunci ta bakin auta kar a zo ana nadama"nadamar ubanka za a yi"ummi ta fada cikin kufula,zai yi magana kenan suka jiyo sallamar mace da namiji suna shigowa gidan kai tsaye ba tare da sun jira an musu izini ta hanyar amsa sallamar ba.
Ummi ta ce "baba batula lafiya na ganki a haka kamar ba lafiya ba?"dole kice haka mana bayan kinzo mana da yara sun gallabe mu a gunwa saboda sun fariya da shegiyar karya, to idan ma karyar za ku yi ai ba da kayan aro ya kamata ku yi ba, ban da iskanci irin na muftahu ya rasa wular wa zai ara sai ta kanin kaninsa, sabuwar hula baban Anas ya aiko masa da ita me shegen tsada ko sawa bai yi ba ,amma yaron nan muftahu yazo ya yi masa wayo ya karbe dan kawai zai je yayi karya da karya ya burge mahaukata"tsaki Ummul ta yi tare da cewa "wai dan Allah ku bakwa sallah ne? To idan ba rashin sallah yanzu ya dace ku zo mana gida a daidai wannan lokacin da ake ibadar Allah"ummi ce ta buge bakinta, tura bakin ta yi tana gunguni tare da hararar Musa da baba batula da ta ke ta banbami akan sai an biya su hularsu,muftahun ne ya shigo gidan yana wani takun fadi da tuni ya riga ya bi jikinsa,sai kuma yayi turus ganin kallon da ummi take watsa masa, sosa keyarsa yayi yana cewa"sorry ummi wallahi akasi aka samu hular aka sace a shagon babaye,kuma ai na basu hakuri sun ki hakura"Ummi ta ce wallahi babu ruwana idan basu hakura ba dole ku biyasu kayansu"baba batula ta ce "Ni babu inda zanje daga nan sai an biya Ni, ko sai gobe ba zan bari ba"tunda kece da goben ba"cewar Ummul ikram tana shigewa bayan yaya Ali saboda dukan da ummi ta kawo mata,hakuri ummi ta shiga basu akan su tafi zuwa gobe za a san yadda za ayi,amma fur sunki yadda.
Babu wanda ya lura da barin Ummul ikram wajen, bare su ankara da abinda ta je yi,Ita kuwa Ummul cewa ta yi tunda kunki hakura ta girma da arziki zaku hakura ta tsiya tsiya da dole, ta na fadin haka a ranta ta zame ta shige karamin madafarsu ta dauki kaskon turaren wuta, a hankali ta sauke tuwon Ummi dake sulala akan garwashin kurfoti ta zuba akan kaskon, sannan ta mayar da tuwon,borkonon da ummi ta dauko zata daka daddawa dashi ta dauka ta kwance ta debo kusan guda goma, bata zuba ba sai da ta fito tsakar gidan,saboda tsananin masifar da baba batula take yasa duk basu ankara da zuwan Ummul tsakiyarsu ba,ajiye kaskon ta yi tare da watsa barkonon akai.......✍️
[10/15, 10:08 PM] fatima y Adam(Zahra✍️): ***
💞GIDAN ƳAN ƘARYA💕
By
FATIMA Y ADAM......
Littattafan marubuciyar.
KUDIRAR ALLAH
KADDARATA SANADIN HASKE
ƁOYAYYIYAR RAIHAN
ƳAR GIDAN YARBAWA
MATAR ƊAN BIRNI
And
GIDAN ƳAN ƘARYA..