Pg10
Cikin wani irin zafin nama ta ƙarasa gabansu ta tankwaɓe shayin tana wani irin huci,kamar bakar zakanyar da ta kwana bata ci komai ba.
Wani irin ihu ikram ta saka saboda zafin ruwan shayin da ya sauka a wuyanta ya sauka har zuwa ƙirjinta ,da ace ma bai dan fifita shi ba da tabbas sai gurin ya tashi,amma abinka da fari duk da haka sai da wuyanta zuwa ƙirjinta su kayi wani irin ja har zuwa cikinta da shayin ya gangara har zuwa kan cibinta,kuka ikram ɗin take sosai tana ɗage rigar uniform ɗin da ake sanyawa patient,dan kuwa sosai take jin zafi a guraren da shayin ya zuba,shi kuwa oga kwata kwata idanunsa ya dora akan zezee da sai yanzu ya ma ganeta,babu wanda zai iya fahimtar yanayin ɓacin ransa, sai wanda yayi matuƙar saninsa,to ita da bata sanshi ba bata gane komai ba kuma bata fahimci komai akan fuskar ba,sai haɗewarta da wani irin kwarjini me razana fitsararre,wani irin ja da baya tayi saboda abinda taci karo da shi a cikin idanun da bata taba ganin me kalarsu ba a duniya,samun kanta ta yi da tsugunawa tana kokarin tsince kwalaban cup din da ya fadi ya tarwatse , kafin ta ce"sorry but bai kamata a ce kai kake wannan aikin ba,i can help you?"ta fada tana kokarin sake hada wani shayin,"get out"ta ji muryarsa dake firgita lissafinta a tsakiyar kanta, bata iya yin musu ba ta yi saurin dire cup din da ta dauka tare da ficewa, tana fitowa ta yi ƙoƙarin dai-daita kanta,sai dai yadda ta yi wani wuri wuri yasa kowa ya fahimci cewa tana cikin dimuwa, Abban ta kuwa kama hannunta yayi suka bar falon yana ji kamar ya kwada mata mari,suna fita waje ya rufeta da masifa yana cewa"wallahi wallahi wallahi zezee muddin kika yi abinda murɗaɗɗan mutumin nan ya fasa aurenki ba zan yafe miki ba,kuma wallahi sai kin biyani asarar da kike shirin jawo min,wai ke zezee wace irin daƙiƙiya ce da ƙwaƙwalwar ki bata ja?kina nufin dan ban haifi da namiji ba ba zan mori haihuwa ba?to wallahi baki isa ba kuma ki kama hanya ki tafi gida tun kafin ki kuma yin abinda zai kara jagula komai,keda nazo dake dan ki kwantar da kai aci arziki dake amma kinzo kinawa mutane sakarci"daga haka ya koma falon ya barta tsaye tana kuka kamar zata hadiye ranta.
A can cikin dakin kuwa, sabuwar jinya ce ta tashi dan kuwa sosai ikram ta rikice masa da kuka,hannu ya kai zai duba wuyanta da ya ga kamar yana ƙoƙarin tashi,hakan yasa ikram ta yi wata irin zabura ta sauko daga saman gadon ƙafarta bata sauka a ko ina ba sai kan fasassun cup din tangaran din da zezee ta zube su anan wajen,wata karar ta saki,wadda ta sanya Dr BiLAL daga ta cak zuwa saman gadon tare da kama kafar yana kallon yadda jini ya fara zuba, runtse idanunsa yayi saboda tsananin yadda zuciyarsa take wani irin bugu kamar zata faso kirjinsa ta fito,yanzu irin wannan matar babansa yake son ya aura?ya tambayi kansa yana janyo kayan aiki irin su auduga da bandeji,yana fara wanke wajen,kwace kafar ikram ta yi tana kara sautin kukanta,ganin zata bashi wahala sai kawai ya mike ya zauna gefen ta ya riketa kamar jaririya ya wanke ya nade kafar sannan ya saketa yana watsa mata harara dan duk ta birkita masa jiki kayansa duk sun yamutse,hada wani shayin yayi ya tsareta da kaifafan idanunsa sai da ta shanye sannan ya bata magungunan tasha,daga nan ya ya danna wani abu ya ijikin kofa, ko minti ɗaya ba ayi ba sai ga su ummi gaba dayansu sun shigo dakin,ikram na ganin ummi taɓararta ta ƙaru,duban nos ɗin da ta canji waccan yayi kana ya ce "ki mata abinda ya kamata ta ƙone kar wajen ya tashi"daga haka ya fice ta hanyar da ya saba shiga,sai da suka tsaya nos din ta duba ikram tare da gyara mata jikinta, sannan ta fice ta bar musu dakin wanda hakan ya basu damar sakewa da ikram ɗin.
Momy dai bata jima ba ta ce zasu tafi"dubanta Abban zezee yayi tare da cewa "to kuje Isa driver ya maidaki ni daga Nan zan wuce office"kallonsa ta yi kamar zata ce wani abu amma sai ta fasa tare da duban ikram da ta wani kanainaye ummi ta ce"to ikram Allah ya kara sauki ni zan wuce"momy an gode"ummi da baffa ma godiyar suka yi mata sannan ta fita ba tare da ta kuma kallon inda Alhaji Salisu dan gaske(afuwan sunan abban zezee shine Alhaji Salisu dan gaske ba Alhaji Musa ba kuskure na yi na canja)yake ba,shi din ma bai kalleta ba saboda gaba daya hankalinsa yana kan ikram wadda yaga ta kuma wani kyau kamar ba jinya take ba,tunda ikram ta gane kallon da yake mata ta hade fuska, duk sai ta ji dama basu zo ba,dan har ga Allah ta tsani mutumin nan,ana cikin haka sulaiman ma ya kara so da nashi kayan niki niki,sannu Ummu da baffa su kayi masa,tsugunnawa yayi har kasa ya gaidasu sannan ya gaishe da abban zezee da yake ta kallonsa yana son fahimtar matsayinsa a wajen su Ummi,amsawa yayi babu yabo ba fallasa,daga nan ya karasa gurin Imran da shigowarsa ya kuma.hada nata zafi akan wanda take kai,sannu da jiki yayi mata, dan babu yadda ta iya ne yasa ta amsa masa dakyar tana mai rufe idanunta domin kaucewa kallon mutane biyun da bata kaunar ganinsu,shiru dakin yayi na dan lokaci kafin Abba ya kalli baffa ya ce"shi kuma wannan fa ban shaida shi ba ko daga can agadex din yazo?"baffa ya ɗan kalli sulaiman da murmushi akan fuskarsa sannan ya maida dubansa kan abban zeze yana cewa"ai wannan suruki ne shine me son yartaka ikram"take Alhaji dan gaske ya kuma hade fuska kafin ya ce"yanzu kai Ibrahim tun kafin kasan halin mutum har ka bashi fuskar shiga cikin ahlinka,kasan halin samarin yanzu fa ba abin yadda ba ne"take kunya ta kama baffa da ummi Ita kuwa ikram dama ba wanda take spoting a cikinsu bare ta ji haushi hasali ma idanunta a rufe suke,sulaiman kuwa ko a jikinsa dan yaga gamsuwa akan karbar da baffa yayi masa,sai dai kawai yaji fargabar kalaman dan gaske saboda kar su sanya baffan cikin wasi wasi.
Sallamar su muftahu ce ta janyo hankalinsu,da sauri Ummul ta bude idanunta,fuskarta cike da shagwaba ta ce "yaya Ali sai yanzu?"dariya muftahu yayi yana cewa "Allah ya sa dai baki cinye kayan dadin ba?"kafin ta yi magana sun hada ido da wanda yake shigowa a bayan su muftahu,wani irin faduwar gaba ta ji yayin da take kokarin tashi zaune idanunta na akansa tana don kallon bakar fuskar tasa da yake boyewa kullum cikin p cap, gentle ke nan wanda yana shigowa ya wuce gaban su baffa yana gaida su da yi musu ya me jiki,kafin ya karasa kusa da ita yana dan kawar da fuskarsa daga kanta sannan,a hankali ya ce"ya karfin jikin?"samun kanta ta yi da sakar masa wani lafiyayyan murmushin da har kumatunta sai da suka loɓa,kafin cikin alamun fushi ta ce"uh mutum yayi sanadin jwanciyarka a don asibiti kuma ya ki zuwa dubaka?"shi ka dai ya iya jin abinda ta fada din, bai ce mata komai ba sai dan hararar gefen ido da ya sakar mata kana ya ce "waye ya janyo kwanciyar?"duk maganar da yake cikin sanyi yake yinta kuma fuskarshi na kallon gefe guda ba ita ba,"ba zan amsa maka tambayarka ba sai ranar da ka tsaya ka kalleni ka maimaita ta sannan zan baka amsa"maganar dan gaske ce ta sanya shi barin wajen,"ya kamata mu fita bawa mara lafiya wake ta huta kun san su nan basa son yawan zirga zirga akan patient dinsu,yanzu ma nasan sanayya ce tasa suka bari"yana maganar ne idanunsa na kai kawo tsakanin sulaiman da gentle da ya samu waje ya coge hannayensa zube cikin aljihunan wandonsa ko kallo dan gasken bai ishe shi ba bare a kai ga batun gaisuwa,wanda hakan ba karamin konawa Alhaji dan gaske zuciya yayi ba,musamman ganin yadda Ummul ta fi bashi a attention dinta fiye da kowa na dakin.
Sulaiman ma dai hakan ba karamin jan hankalinsa ya yi ba,sai dai kuma yasan yadda gentle din yake da muhimmanci a wajensu kuma yana da yakinin cewa Ummul ikram a yadda take yar karyar nan ba zata taba auren talaka ba, takakan ma me gyaran takalmi, sannan mara kyawun gani me bakar fuska,wannan tunanin da yayi ne yasa shi jin sanyi sanyi a ransa,baffa ne ya fara fita tare da ummi,su kuwa muftahu kayan abinci suka dauka suka yi waje dan tunda suka ga tana magana sun san cewa ta warke shi yasa suke son kare mutuncin cikinsu,ganin gentle yaki fita yasa sulaiman ma kin motsawa,hakan ne ya kuma harzuka Dan gaske ya magantu ta hanyar ce musu su tafi kawai an gode da ziyara,sulaiman dai ya tashi ya fice dan ya fuskanci kamar mutumin nan so yake ya tunzurashi, Ummul kuwa kallon abban take ciki da mamakin karfin halinsa ko meye dalilinsa na yin hakan oh?".
Dawo da dubansa yayi kan gently cikin tsare shi da idanu tare da cewa"kai har yanzu baka gama taka dubiyar ba ne?"a nutse gently Wanda ke amsa sunan jafar ya dubi wani kodadden agogonsa sannan ya ɗan kalli dan gasken ya gyada masa kai! alamun dai bai gama ba ɗin "cikin fusatar da Abban zezee ya fara yi dashi ya ce "kai baka da kunya ko?wai me yasa ku almajiran nan kuke da fadin rai ne kamar ya'yan wasu?"a'a fa Abba ba almajiri ba ne"Ummul ta fada tana kallon gentle da har yanzu bai nuna yasan Alhaji dan gasken yana wajen ba ma,"tayaya zaki ce ba almajiri ba ne ai duba da sutturar jikinsa duba agogon dake hannunsa kinga da fatarsa kamar wanda ya fito daga babbaka saboda datti da bakin talauci"cikin jin haushin maganarsa Ummul ta ce"dan Allah Abba ka ta fi ka barsa wannan ba girmanka ba ne idan ya so ma ya shekara a gurin"wannan furuci nata na karshe shi yasa sanyaya zuciyar abban har yana dan sakin murmushi tare da cewa to shike nan yar kyakkyawa bari na wuce office, Amma ki fada min abinda kike so na kawo miki an jima?"saboda tana son ya tafi ta ce abba kome ka kawo min ina so"to to shike nan ki kwanta ki yi bacci ki huta kinji"jingina kanta kawai take tare da gyara kwanciyarta har da rufe ido kamar zata yi bacci"dariya sosai Alhaji dan gaske yq fita yana yi bayan ya watsawa gentle kallon banza kamar wani sa'ansa,dan yanzu ji yake ba ya shi kuma in dai har ya samu kan Ummul ikram ba shi da wata matsala, burinsa biyu zasu cika a daidai lokacin da ya fi buƙatar hakan.
Da sauri Ummul ta mike zaune tana yatsine fuska tare da raka bayansa da harara tana fadin wannan dai an yi dattijon banza me budurwar zuciya kawai"kallon gentle ta yi kamar zata ce wani abu sai kuma ta fasa ta zuba masa ido kawai tana son gano illolinsa da Alhaji dan gaske ya lissafo,"idan har zaka dinga boye halittar da Allah yayi maka dan kawai bai yika kyakkyawa ba to tamkar ka yi masa butulci ne domin yayi maka kyautar da ba kowa yayiwa ba dan haka ka yiwa kanka fada ka daina gudun mutane saboda muninka ko bakinka"daga haka ta koma ta kwanta, "Allah ya baki lafiya ya fada yana barin dakin,wani irin haushi kanta ne ya kamata,ko me ya Kaita yi masa nasiha akan rayuwarsa oho?"
Yana fita sallama yayi da su ummi ya wuce ya koma gun sana'arsa.
Su muftahu dai an ga waje domin basu da niyar tafiya gurin neman kudinsu,daga karshe dai sai da baffa ya korasu sannan suka tafi amma sun ce idan suka tashi nan zasu dawo.
Bacci sosai ikram ta yi tun bayan da ta yi sallar azhar, ba ita ta tashi ba sai la asar,tana idar da Sallah ne nos ta shigo ta sanar da su ummi zata duba ƙunar ikram ɗin,, su dan basu waje,bayan sun fita ne ta fara duba ikram din cikin kulawa ta musamman,tana yi tana dan yiwa ikram din hira har take cewa,"gaskiya na jima ban ga patien din da Dr yake kulawa da ita ba sai ke har mun fara tunanin ko ke ce wadda zai aura ko kuma yar uwarsa dan kuna kama sosai"ai jin haka yasa ikram ta gyara kwanciyarta ta fara rattaba zance,ai ni kanwarsa ce baya son a sani ne shi yasa yake yin kamar bai sanni ba"nos din ta ce haba ko da na ji dan gaskiya wannan kulawar sai da wata dangantaka saboda Dr ba irin mutanen nan ne masu faran faran ba,kullum haka yake fuskar nan a tamke"dariya Ummul ikram ta yi tare da wani yin wani fari da ido tana cewa, "uh ai kullum haka yake ci mana wannan maganin a gida shi yasa bamu da saboda dashi dan ma a hakan nice ta gaban goshinsa,gyaran murya nos ta shiga yiwa ikram saboda shigowar Dr room din ta hanyarsa, sai dai ina ikram ta yi nisa wanda ta kwana biyu ba tayi ba shi take ramawa,ta wani lumshe ido tana cewa ,ai in gaya miki wannan karon shine karo na goma da ake samowa yaya Dr mata suna guduwa biyar an yi auren, dan daya a cikinsu ita kwananta daya ta bar gidan sai aika mata yayi da takardarta,su kuma hudun sati Daya Daya suka yi suka gudu,wanda bai aure su ba kuma tafiyar bata yin nisa ake yin uwar watsi saboda ba zasu iya da murdadden halinsan nan ba,na rashin dariya gashi bai iya musu soyayya ba sai muzurai shi yasa,amma dai ke nos tun da naga kun iya da halinsa ko na fadawa babanmu a zo a nema masa aurenki wallahi zamansa haka yana damun abbanmu sosai"ta fada cikin damuwa da jimami,ita dai nos in banda rawa jikinta babu abinda yake yi,ganin surutun Ummul ba zai kare ba yasa shi takowa cikin dakin,take kamshinsa da da dama tsananin shagala ne ya hanata jinsa ya shiga kofofin hancinta.
Cikin sauri nos din ta fice daga dakin jikinta na rawa,a ranta tana cewa ke yar uwarsa ce hukuncinki zai iya zuwa da sauki"
Idan ka kalli idanun Ummul ikram a wannan lokaci basu da maraba da idanun mage.......✍️
Ya kuka ga salon
Amma fa gaskiya ana min kwairan comment daga wani bangaren,dan haka na tafi hutun sati🚴🚴🚴🚴
Sannan ina bukatar a yi min share a ƙalla ko wane mutum daya yayi zuwa groups 5 wadda bata yi ba 😒😒😒😒zan ji haushinta,dan nasan idan paid ne sai yafi wannan yaɗuwa....
[10/15, 10:08 PM] fatima y Adam(Zahra✍️): ***
***
***
💞GIDAN ƳAN ƘARYA💕
By
FATIMA Y ADAM......
Littattafan marubuciyar.
KUDIRAR ALLAH
KADDARATA SANADIN HASKE
ƁOYAYYIYAR RAIHAN
ƳAR GIDAN YARBAWA
MATAR ƊAN BIRNI
And
GIDAN ƳAN ƘARYA....