GIDAN YAN KARYA

Pg11

by @zahrawriter12

Takun da yake yi yana tunkarota jinsa take har tsakiyar kirjinta,rashin abun yi yasa ta zamowa daga saman gadon ta shige karkashin gadon tare da rufe idanunta,dan yau kam tasan karshenta ya zo tunda wannan mugun ya kamata tana masa karya.

Shi kam Dr BILAL tsayawa yayi dai dai jikin gadon ya zubawa kafafunta da suka leko ido,fuskar nan a hade wanda hakan yasa baka gane bacin ransa tunda kullum a haka take a babu sauki,bare murmushi, farin glasses din da yake sanye a idanunsa ya ɗan gyarawa zama sannan a hankali ya tsugunna a bakin gadon yadda zai iya ganinta sosai, ido daya ta ɗan bude saboda jin alamun sa daf da ita,aiko caraf suka hade ido dashi,cikin rawar baki ta fara jan ayatulkursiyu wanda hakan yasa Dr cire glass din idanunsa yana mai ware matsakaitan idanunsa masu kwarjini akanta,"Ni shaidan ne da kike ja min ayatulkursiyu?"ya fada cikin ginshirarriyar muryarsa da take fita a dake,zare ido Ummul ta kuma yi dan kuwa yau ta kai kanta bata da fita gurin wannan me fuskar shanun, kai ita fa tun da take bata taba ganin irin mutane biyun nan ba a dabi a wato gentle da wannan Dr, dan sam basa murmushi sai dai kuma har gwara Dr akan gentle Dan shi jafar gentle ko magana ma ba yayi shi kuma wannan yanayi idan ta kama"bata gama tunanin zucinta ba taga ya zuro dogoyen hannunsa duka biyu ya daukota cak kamar wata yar baby,zata yi ihu ya sanya tafin hannunsa saman bakinta yayi masa rumfa,dole ta hadiye kukan rashin gaskiyarta ta kuma zare idanunta da suka kuma yin wani irin haske da maiƙo saboda tsoronta da ya bayyana sosai,kwantar da ita yayi kan gadon tare da kai bakinsa saitin kunnenta kana cikin radar da sautin da ya tada duk wata tsiga dake jikin ikram ya ce"yanayin tsoro yafi Kowane yanayi yin kyau a fuskarki,idan kika kuma yi min hira da wata nos sai na cire bakin ƙaryar, kuma kina nan zaki ga mace ta sha daya da me fuskar shanu zai sake aura, a wannan karon shi yake da sa a"daga haka ya dago daga rumfar da yayi mata tare da dalle karamar lips dinta,daga haka ya fice daga dakin ya bar Ummul hangeme da baki.

Kunnenta ta taɓa inda har yanzu take jin sautinsa da hucin numfashinsa dake bugun fatar kunnenta,kafin ta ce"to ke nan abinda na fada da gaske ne?kuma wace macece ta sha daya?ok kenan zezee ita ce ta sha daya kuma sabida yasan ita tana sonsa shi yasa yake ganin zai yi sa a a wannan karon,to idan haka ne kuwa ita din yar baiwa ce dan haka yanzu capacitynta zai karu.

Ita kuwa nos wasan buya ta shiga yi da Dr duk da tasan cewa ba zai ce mata komai ba,sai dai tasan zai matukar daure mata fiye da baya,

Tun daga wannan lokacin har zuwa safiyar da za'a sallemeta take ganin girmamawa daga wajen ragowar nos din nan, saboda labari ya je musu cewa ita kanwar Dr ce,abinda ya faru da safen baisa ta yi hankali ba, wannan girman da ake bata shi yake mata dadi,har hotunu take sawa suna yi mata da wayarta da ta ce musu,saboda Dr ya hanata rike waya ne yasa momynsu ta bata wannan dan ta ɗan dinga debe kewa,tsaf suke yarda da karyar Ummul ikram,wadda kaf asibitin suke ji da ita saboda shiga ranta, kallonta suke kamar wata yar baby,Dan har kyaututtuka suka dinga kawo mata, Musamman nos rabi a da aka lasa mata zumar auren Dr.

Kwanaki ukun da Ummul ikram ta yi a asibiti yasa ta fara fahimtar wani abu a tare da Alhaji dan gaske,sulaiman dama tuni tasan inda ya dosa,gashi ya samu karɓuwa wajen baffa fiye da yadda take zato,Dr kuwa tun jiya da ta suburbuda masa karya bata kara ganin fuskarsa ba,bata damu da hakan ba dan ita dama tsoro yake bata,mutum daya ne rashin zuwansa ya tsaye mata a rai,dan haka take Allah Allah wannan murdadden Dr ya dawo ya sallame su kamar yadda nos ta fada mata cewa yau din za yi discharge dinta,Dan haka tuni sun hada kaya jira kawai suke yi ya zo ya sallame su, dan hatta da magungunanta da Inhela duka an basu, wanda kuma duk zaton su Alhaji dan gaske ne yake biyan komai, To shima dan gasken bincike yake dan son gano daga inda wannan hidimar take amma sam hakan ya gagara,saboda cashier da pamercy duk sun sanar da shi cewa suma basu sani ba saboda mutumin bai basu wata dama da zasu sani ba kudi cash aka biya bare su duba details din a kan bank dinsu, wannan abu ba karamin saka alhaji dan gaske yayi cikin taraddadi ba,har sulaiman ya vincika ko shine sai yaga shima sulaiman din ya shiga mamaki saboda shima yayi zaton alhaji dan gasken ne,saboda shima yayi kokarin biya amma aka ce masa an biya komai da komai,hakan yasa shima ya bi layin Alhaji dan gaske suka saka kansu a cikin wahalar binciken abinda ba zasu taba samu ba.

Sai bayan magriba Dr Bilal ya zo ya basu sallama tare da kafa musu dokokin lalurar ikram,daga haka bai sake cewa komai ba ya yi musu sallama ya fice,da harara ikram ta bisa tana murguda bakinta,A'isha ce ta zo zata dagota ta buge hannunta tana cewa"nifa na warke kike neman mai dani makauniya",harara ummi ta bita dashi tana cewa "kefa sam baki canja halinki duk halin da zaki shiga"fita su kayi gaba dayansu, sai kuma duk suka yi cirko cirko ganin motar sulaiman da ta Alhaji dan gaske duka a bude kowanne najiran Ummul ta shiga,yayin da muftahu yake bangaren driver na motar sulaiman a tsaye ya rike muddin motar yana ta girgiza key din da sulaiman ya bashi zai ja su,duk budurwa ko nos din da ta zo wucewa sai ya kashe mata ido,saboda kawai ya jawo hankalinsu su ganshi da mota,dan haka hankalin Ummul kansa ya koma abin na bata dariya ganin yan mata na yi masa kwarkwasa dan kuwa ko ba a soshi dan kudin ba tabbas za a so shi dan kyawunsa,baffa da ya fahimci abinda muftahu yake yi ne yasa shi ya nufesa tare da sanya hannu ya talle bayan kansa yana cewa"ku dai wadan nan yaran baku ji dadin halinku ba,duk halin da aoe ciki sai kun zubda hali?to kaza bashi mukullin motarsa tun kafin na sassaba maka"cikin sauri muftahu ya shige motar saboda kar baffa ya bada shi tunda da karfi yake fadan,juyawa yayi kan Ummul yana cewa ku kuma me kuka tsaya yi ku shiga motar sulen idan yaso mu sai mu shiga ta Alhaji"Alhaji dan gaske na shirin yin magana Ummul ikram ta yi wuf ta shige motar sulaiman din da ya ci darajar dan uwanta da zai tukasu, wannan abin da baffa yayi ba karamin dadi yayiwa sulaiman ba dan har wani doro yake sakarwa Alhaji dan gaske da yayi kokarin boye bacin ransa akan hukuncin da baffa ya yanke.

Daidai kofar gate din da zasu fita Ummul ikram taji gabanta ya fadi hakan yasa ta ɗago kanta tana duban hanyar shigowa asibitin ta ɓangaren ƙaramar ƙofar shiga,sai ko idanunta suka sauka kan gentle Yana ƙoƙarin shiga ciki,cikin sauri ya shiga dakatar da muftahu,"dan Allah yaya ɗan tsaya kaga gentle can kuma nasan wajen mu zai zo gashi mu kuma an sallame mu"muftahu ya ce "an ƙi a tsaya ɗin, me yasa baizo tun lokacin da muke asibitin ba?idan ya je yaga an sallame mu ya dawo, kuma idan mun tsaya ya kike so muyi dashi tunda dai zai same mu ki rabu dashi kawai"yaya dan Allah ka tsaya wallahi zai sha wahala tunda akwai nisa tafiyar, kuma ma ina ga a kafa ya taho daga gida"to sai me?"muftahu ya fada a ɗan fusace,basu ankara ba sai kawai gani su kayi ikram na ƙoƙarin buɗe ƙofar zata fice wanda hakan yasa muftahu ya tsaya ba da shiri ba yana balbaleta da ruwan masifa amma ko a jikinta, kai tsaye ta fice daga motar ta nufi hanyar da gentle ya bi duk da cewa ya ɗan yi mata nisa amma haka ta shiga kwala masa kira,ganin ya ki jinta gashi yana kuma yi mata nisa yasa ta takawa da gudu,ganin haka yasa gaba daya suka dafe kai,A'isha ta ce"dan Allah ya muftahu mu juya mu bita kar ciwonnan ya tasan mata kasan fa gudu yana daga cikin dokar da aka sa mata gashi bata gama warkewa ba"cikin takaici abinda ke faruwa sulaiman ya ce"dan Allah A'isha waye wannan gentle din yake kowa?"A'isha ta ce gyaran takalmi kawai yake yi a kofar gidansu bayan haka nasu da wata alaƙa"cikin kokonto sulamian ya kuma cewa "anya kuwa kuna ganin ba soyayya suke ba?"muftahu bai san sanda ya zabgawa sulaiman harara ba kafin cikin takaici ya ce"Allah ya sawwaka ka ma tofar da baƙin yawu dan wannan zance naka mugun fata ne,mu da kullum burinmu Ummul ikram ta auri me mugun kudi dan mu samu mu warke daga bakin talauci amma sai mu buge da aura mata matsiyaci, to ai ita kanta Ummul din da zata ji ka da ka barar da dan mutuncin da ta fara ganinka da shi a wajen ta"dadi kalaman muftahu su kayiwa sulaiman wanda hakan yasa suka maida hankalinsu wajen Ummul din da suka daina hangota.

Gudun da ta yi yasa numfashinta ya fara kai kawo akirjinta yana ƙin ƙarasowa hancinta,tana kokari durkushewa wajen ne ta yi masa wani irin kira me karfi da amo,wanda kai tsaye ya wuce cikin kansa zuwa kirjinsa ya bada wani irin sauti a tsakiyar kirjinsa,a nutsensa ya waigo Yana jin mamakin Muryar da yaji na kiransa, daidai lokacin take dirkushewa a wajen tana fidda numfashinta a wahale,cikin wani irin taku me hade da zafin nama ya karaso inda take tare da tarota yana cewa "ke baki jin magana me yasa ki yin gudu?me ya fito dake nan ina su Ummi?"yana mata tambayar tana lalubar Aljihun wandonsa tare da ciro sabuwar inhela ya ɓalle kanta yana mai shaƙa mata,numfashinta na tsayawa itama sai kawai ta tsaya tana yi masa wani irin kallon mamaki,basarwa yayi yana dagota suka mike tsaye,kokarin yin magana take ya dakatar da ita ta hanyar watsa mata tambayar da tasa ta watsa masa harara kamar idanunta zasu fado, saboda haushin tambayar dalilin ganinta a nan din da kuma hanata tambayarsa abinda yake cin ranta na ganin inhela a tare dashi,daidai nan su muftahu suka karaso cikin mota, ganinta lafiya yasa mufathun ya balbaleta da fada akan abinda ta yi wanda sai anan gentle yake samun amsarsa, muftahu ko kallon gentle da yake mika masa hannu bai yi ba ya finciki hannun ikram din ba tare da yasan cewa ita kuma tana rike da hannun gentle ba,sai da suka zo bakin motar ya ga gentle din a bayan ikram hankalinsa kwance sai dai ba wani abu da ake fahimta a bakar fuskarsa,duban ikram din yayi ya ce"sai na taho ko?"yana kokarin zame hannunsa daga nata, cikin sauri ta girgiza kanta tare da cewa "ai gidan zamu je dan haka tare zamu tafi"takaicin Ummul din yasa muftahu sakinta tare da komawa bangaren driver ya shige yana jin zuciyarsa kamar ya kifa mata mari.

Ga mamakinsu har ita ikram din basu zaji gentle zai iya binsu kai tsaye ba haka,don kuwa ikram tana shiga tsakiya shima ya shiga kusa da ita wanda haka yasa ta sauke ajiyar zuciya, ga hannunsa ƙam cikin nata kamar wanda za akwaceshi.

Sulaiman kuwa idan ransa yayi dubu to duk ya ɓaci wannan shi ake kira ramuwar gayya, shi ya gama yiwa ɗan gaske dariya shi kuma gashi an yi masa abinda yafi wanda aka yiwa ɗan gaske,takaici ne ya sa shi kwantar da kan sa jikin kujerar tare da kara tura kujerar baya dan kawai ya takurawa dogayen kafafun gentle,ita kuma Ummul da take hankalce da duk wani motsin gentle tuni ta ga lokacin da sulaiman ya matse kafafunsa dan haka kai tsaye ta shiga tura kujerar ta karfi ba tare da ta yi magana ba,dole dai sulaiman ya gyara kujerar yana jin kamar ya sanya bindiga ya fasa kan gentle,a cikin wannan halin Ummul ta bingire da bacci sai ga kanta saman kafadar gentle tana baccinta hankali kwance.

*****

A can wajen su baffa da Ummi da Alhaji dan gaske kuwa sun jima da zuwa gida, amma sun kasa shiga gidan saboda basuga su muftahu ba, wannan dalilin ne yasa dan gaske ya shiga fada, yana cewa "ai wallahi buzu naga wautarka da har ka bar yaranka har biyu tare da kawar yarka a cikin motar mutumin da baka san ko waye ba,ai irin abinda ake gudu kenan Allah yasa ba wani wajen cutarwar ya wuce da su ba"cikin tashin hankalin da ummi ta fara shiga ta ce"in Allah ya yarda zasu zo lafiya dan dai Ni nafi tunanin ko sharrin karfe ne,amma sulaima bashi da alamun cutar damu"tsaki dan gaske ya kuma yi yana cewa, ai shi mugu ba a yi masa tambari dan haka basu da kama ke dai kawai mu yi kyakkyawan fatan su dawo lafiya"ko rufe bakinsa bai gama yi ba motar sulaiman ta tsaya a kusa da tasa,gaba daya suka nufesu sai dai tuni don gaske yayi burki ganin mutumin da ya fito da Ummul a kafadarsa tana layin bacci, saida A'isha ta fito ne ta karɓe ta wanda hakan yasa tafarkawa, cikin mamaki Alhaji Salisu dan gaske yake kallon gentle kafin ya ce"kai kuma daga ina haka?me ya haɗaka da su kai da ba mu taho tare da kai ba?"muftahu ne ya basu labarin abinda ya faru yana hararar gentle din da yake matukar jin haushinsa musamman saboda fatan da sulaiman yayi musu,kuma shine har da rike ta saboda iskanci da sakarcin banza , wannan ai shirmene,kai kuma muftahu kana kallonsa ka kyalesa, yarinyar da bata gama warwarewa ba ka bari za a kuma sanya mata sabuwar cutar da zata buwayi kowa da kowa"haba Abba wace irin cuta kuma za a sa min gentle dinne zai sa min cuta?"kai tsaye don gaske ya bata amsa da cewa "kwarai kuwa dan wannan dattin da yake jikinsa da tsamin jikinsa tsaf zai kashe mutum"malam ya isheka haka?"cewar gentle idanunsa suna wani rin juyewa,"fass fass karar marin da Alhaji dan gaske ya shararawa gentle ya sanyasu daskarewa a wajen gaba ɗayansu cike da shock din bazatar da da gaske yayi musu .........✍️

***

💞GIDAN ƳAN ƘARYA💕

By

FATIMA Y ADAM......

Littattafan marubuciyar.

KUDIRAR ALLAH

KADDARATA SANADIN HASKE

ƁOYAYYIYAR RAIHAN

ƳAR GIDAN YARBAWA

MATAR ƊAN BIRNI

And

GIDAN ƳAN ƘARYA....