Pg13
Mikewa Ummul ta yi kamar zata koma daki, amma sai ta yi wuf ta bi bayan Alhaji dan gaske dan ba za bari shagalin nan ya wuce ta ba, daidai lokacin, Alhaji dan gaske ya na kokarin bude motarsa,bai ankara ba ya ji saukar dutse a goshinsa a zabure ya daga kansa dan ganin abinda ke shirin faruwa hannunsa akan goshisa da yake jin alamun kamar ya fashe,sai dai kafin ya samu damar ganin wanda yayi masa wannan jifan tuni ya kuma jin saukar ruwan kasa a idanunsa take ya daina ganin komai ,gashi motar ta ki budewa, cikin kankanin lokaci ya fara jin ruwan dutsuna ta ko ina, kasar da ta cika bakinsa kuwa ta hanashi magana bare yayi ihu neman taimako,dakyar kokarin bude motar kawai yake ba tare da ya sanya key ba dan gaba daya a rude yake, sai da ya kuma jin saukar wani karin dutsen a keyarsa ne ya saki kara a kuma lokacin ya tuna bai sawa motar key ba dan haka ya sanya hannunsa a ljihun rigarsa yana laluben key din da ya ce daukar Ni in ka ganni,gashi idanunsa duk sun rufe bai ma san ta inda zai fara neman key din motar ba,zuciyarsa in da ta yi dubu ta ɓaci hankalinsa yayi masifar tashi,cikin kankanin lokaci jikinsa da kansa syoa ɓaci da jini ga farar shaddarsa duka sun ɓaci da jini da ƙasa,sai da ga can kunennsa suka fara jiyo masa ihun yara suna cewa "mahaukaci mahaukaci jama a taimakawa alhaji"da sauri Ummul dake labe jikin kofar gidansu ta koma gida da gudu tana cewa "baffa baffa kuzo kuga wani sabon mahaukaci dan ban taba ganinsa ba ya zo unguwar nan yana ta jifan mutane shine Alhaji na fita ya sameshi yake ta jifa gaba daya ya bata masa jiki da kasa gashi kansa duk ya fash"....ai baffa bai saurari karashen maganar Ummul ba ya fice wajen ba tare da ko takalmi ya sa ba,ai ko yana fita yaga yara sun kama mahaukacin dakyar sun janyesa,alhaji kuwa jinin da yake zuba akansa yasa ya fara ganin jiri, ganin haka yasa baffa ya rikesa yana cewa Ummul ta bude motarsa ya saka shi su tafi asibiti,babu bata lokaci Ummul ta zura hannunta cikin aljihun doguwar rigar ta ta dauko key din tare da buɗe motar, sosai baffa ya shiga mamakin abinda ya kai key din wajenta to amma sai yayi tunanin ko yar dashi alhajin yayi ta dauke masa, wannan tunanin da yayi ne yasa ya bar zarginta,dakyar ya samu ya saka Alhaji dan gaske a bayan motar,sai kuma ya shiga laluben wanda zai tuka motar, ana cikin haka Aliyu ya zo,dan haka sai kawai ya danka masa key din yana cewa "yi sauri ka kaimu asibitin da aka kai Ummul"Ali da take jikinsa ya dau barin ganin zai tuka hadaddiyar mota kamar wannan yasa bai tambayi ko ba a sin abinda ke faruwa ba ya shige motar yana cewa ai yau babu me gaya min naji dan wallahi sai na ji yadda masu kudin nan suke ji",daga haka ya ja motar suka bar layin.
Ummul kuwa cizon yatsa ta yi, dan bata taɓa takaicin rashin iya mota ba sai yau, amma dai babu komai tunda yaya Ali ne ya tuka tasan duk abinda zata yi shima zai iya fiye da haka,sai da ta tabbatar sun yi nisa sosai sannan ta janye yaran suka shige zauren wani gida inda saurayin da aka kira mahaukaci yake can yana jiranta tun bayan da yaran suka janyesa,tafawa suka shi ga yi da yaran wanda basu wuce shekara goma zuwa sha daya ba,daga nan kuma ta dauko yan dubu dubu ta shiga raba musu wajen su goma, sannan ta ce"wallahi in dai na ji labarin nan a wani waje to ku ne kuma duk sai kun biyani kudina da na baku dan haka bakinku kanin kafarku"basu fita daga wajen ba sai da suka yi alkawarin baza su fadawa kowa ba kamar yadda suka yi mata kafin ta basu aiki,daga nan kuma ta koma kan saurayin tana dariya tare da cewa"to yaya muftahu sai kasan inda zaka je ka gyara fuskarka da ka ɓata Allah yasa duk yaran nan basu san kai ba ne wallahi da babu tantama idan asiri ya tonu sai ka je cell"hannunsa yasa ya zame hular awilo me kitso dake kansa yana shirin goge fuskarsa, Ummul ta yi saurin dakatar da shi tana cewa "a'a yaya ka bari na fara fita sannan ka gyara ka sanya kayanka ta fada tana janyo rigarsa da suka boye a bayan kofa,"to wuce maza kije tun kafin baffa ya dawo ki zaro min dalar guda uku idan ba haka ba wallahi sai na fadawa baffa"kai yaya mufty dala guda biyu mu kayi da kai zan zaro maka amma ba uku ba,so kake yi baffa ya gane an taɓa?"harara ya watsa mata tare da cewa dalla Malama ki je ki dauko mana ta yaya zai gane bayan ba sanin kansu yayi ba, sannan kudin nan da idan kisn dauko ba sata kika yi ba tunda naki ne"tura baki ta yi tana kunkuni tare da ficewa, Allah ya sa babu kowa a wajen dan har lokacin gentle bai zo ba,suruf ta shige gida tana share kwallar karya, a tsaye ta samu ummi tana kakkabin abinda ya faru tare da sa idon ta inda Ummul zata ɓullo.
Cikin damuwa Ummi ta kamo hannun Ummul tana cewa "ina kika tsaya ke da ba lafiya gareki ba,kin sa duk hankalina ya tashi kar kema mahaukacin ya yi miki wani abu"cikin marairaice fuska da yanayin alhini Ummul ta ce "wallahi ummi baki ga abin tausayi ba, yanzu haka fa ya sume baffa da yaya Ali sun tafi kaisa asibiti"to Allah ya kyauta shi kuma mahaukacin ya aka yi da shi?"Ummu ta fada tana jan hannunta zuwa kan shimfidar da Alhaji dan gaske ya tashi,"zama Ummul ta yi tana janyo kular doyar da ummi ta gama soyawa, sannan ta ce"to ummi ina za a ga mahaukaci ko an gansa ma ya za ayi da shi tunda kin san ba a yin shari a da mara lafiya,Ni baffa ma nake ji wallahi bai ci kome ba ya tafi asibitin nan"ta fada cikin Muryar tausayi, "Allah ya kyauta kawai ummi ta ce tana haɗa musu kunun da ya ji kayan kanshi gashi yayi lambau da shi kamar madara.
*********
A can bangaren su Alhaji kuwa suna zuwa aka ɗauko gadon da ake dora marasa lafiya aka saka shi akai,suka tura shi zuwa emagency, baffa ya bi bayan su da gudu,shi kuwa Ali juya kan motar yayi ya fice daga asibitin yana wani mugun murmushi tare da gyada kai,saboda yau akwai chilling.
Ummul tana gama karyawa ta dauki karamar aitel dinta ta dannawa momy kira,tana dagawa ta sanar da ita abinda ya faru,tare da asibitin da aka kaisa,momy tana kashe wayar zeze ta shigo dakin," momy lafiya na ga kamar kina cikin damuwa"?zezee ta tambaye ta tana zama kusa da ita,cikin damuwa momy ta sanar da ita halin da ake ciki,shuru su ka ɗan yi na wani lokaci kafin zezee ta kalli mom din tana cewa "momy wai me yake damun Abba ne naga duk ya canja saboda kulawar da yake bawa wannan matsiyatan tana damuna,ina ta son sanin dalili,dan duk abinda kika ga Abba ya zage yana zuba kudinsa akai to tabbas da manufarsa"daga kafadarda zezee momy ta yi tare da cewa ,nima abinda yake damuna kenan zezee sauyawar abbanki akan ma aikatansa dole akwai wani babban dalili,sai dai kuma na ta allaƙa abin da son hadin aurenki da BiLal da yake yi"cikin rashin aminta da hakan zezee ta ce gaskiya momy ba haka ba ne ,da a ce dan haka yake yi to a iya lokutan da muke tare da Dr zai dinga yi,to kuma kina ganin dai an sallame su daga asibitin gida fa ya bi su wannan abin ya sameshi,gaskiya ina da ja akan wannan hasashen naki,amma dai koma meye dole zamu sani ne,yanzu ki tashi muje asibitin Allah yasa Dr yana nan?"ta karasa maganar da murmushi akan fuskarta.
Cikin kankanin lokaci suka karasa asibitin, a lokacin Alhaji dan gaske har ya farfaɗo sai dai duk an yi masa faci a fuskarsa, goshinsa kuwa kamar me bisin kai saboda yadda ya kumbura sumtum ko idanunsa ba a gani sosai,baffa dai gaisawa kawai su kayi da momy yasa kai zai fice dan komawa gida,zezee ce ta dakatar da shi ta hanyar tambayarsa key din motar Abban da kuma wayoyinsa,"bari na karbo key din wajen Ali wayoyin kuma duka suna cikin motar"zezee ta ce to amma me yasa da muka zo bamu ga motar a waje ba?" Momy ce ta harareta sannan ta maida kallon ta kan baffan tana cewa "shike nan je ka karbo key din kai ma kaje gida ka huta ai ka zaunu"fita yayi kamar zai kifa saboda gudun rashin mutunci irin na zezee.
Sai dai kuma tunda ya fito yake neman Ali da mota suka ce daukar mu inka ganmu,babu inda bai shiga ba a farfajiyar asibitin nan, kai har inda mota ba zata shiga ba sai da ya shiga neman Ali da mota amma babu su babu me kama da su,take ya fara gumi saboda a yanzu ya gama tabbatar da cewa Ali ya fita yin karya da motar Alhaji kai har ma da wayoyinsa tunda suna cikin motar,bai koma ciki ba saboda gudun zafin zexee dan yasan tsaf zata tara musu jama a, zata iya cewa ma sace motar su kayi,dan haka sai kawai .ya tare dan sahu ya nufi gida yana fatan ya samu Ali a can,a.hakan kuma yana yi yana kiran wayarsa amma ta ki shiga.
****
Ummul kuwa bayan sun gama karyawa, gyara wajen su kayi, suka ajiye wa Ali da mufty da baffa kayan nasu karin,to shi dai mufty ya shigo ya karya nasa kumallon,daga nan yasa Ummul ta faki idon ummi ta fada dakin baffa ta zaro masa dala uku a cikin kudin da Dr Bilal ya bata,saboda lokacin da ta fita dan neman wanda zai yiwa Abba luhuni a matsayin mahaukaci,sai kawai ta ci karo da yaya muftyn, To anan ne fa ya ce zai yi mata amma da sharadin zata bashi dala biyu a cikin kudinta na wajen baffa,ba tare da wani dogon tunani ba Ummul ta amince,a anan ne ta koma gida shi kuma ya buya ya cire kayansa ya boye a zauren gidan nan, sannan ya yiwa kansa kwalliyar mahaukata babu wanda ya isa ganeshi idan ba sanin kayi shi din ba ne,ko ilya abokinsa da ya ari hular da rigar da ya sa bai san me zai aikata ba,dan shima yana cike da jin haushin alhajin shi yasa yayi abin ba tare da kowa ya fahimci wani abu ba,to shine daga baya ya dage akan sai dai ta dauko masa guda uku,tana bashi yayi wanka ya bar gidan.
Cikin tashin hankalin rashin ganin motar Alhaji a kofar gida baffa ya shiga gidan,ganin sa a birkice yasa Ummi ta rude tana masa tambaya,gumin da ya shiga tsatsafo masa ya goge, sannan ya gaya mata duk abinda ke faruwa,ummi ta ce"to ai sai dai ka ta fi nemansa dan kuwa ni tun da kuka tafi ban ga Ali ba,kaga can karin kumallonsa ma bai yi ba"juyawa kawai baffa yayi ya fita dan ya zamar masa dole ya fita neman Ali koda kuwa ba zai ganshi ba.
Ummul tana jin su amma bata fito ba bare ta jajanta lamarin, sai ma dariya da ta yi tana cewa"dama nasan dole sai wani abu ya faru"tana rufe bakinta wayarta ta shiga haske, dan ita sam Ummul bata sanya wayar ta a ringin kiran ta daga da sauri tana cewa"haba yaya Ali ina ka shiga zaka sa a kama baff.....ke ba shi ba ne" cewar wanda ya kira wayar,duban fuskar wayar ta kuma yi sai a sannan ta ga ashe ba nomber yaya alin ba ne, mayar da wayar ta yi kunnenta,inda ta fara sauraren mutumin yana cewa,"ya kade a kuyar wani bawan Allah ne garin tukin ganganci irin nasu na sangartattun yara kuma an ce ya biya shi ya ki, dan haka yana nan dala devition mun rike shi"subhanallahi gani nan zuwa yallabai yanzu dan Allah kar a sa shi a cell kaji" to ki yi sauri ya fada yana kashe wayar,bata gayawa ummi ba ta yi saurin shirya wa ta fito tana cewa"ummi bari na taya baffa neman yaya Ali saboda Ni nasan wasu daga cikin gidajen abokansa"Ummi ta ce"amma ikram jiya fa aka sallamoki daga asibiti ina kika karfin zuwa neman Ali?"karki damu ummi zan iya"to ki dauki inhelarki ki sa a haka dan yanzu dole duk inda zaki sai kin kasance tare da ita"to Ummi dauko min ta fada cikin hanzari,Ummi tana shiga daki ita kuma ta fada dakin baffa ta debo dala guda biyu ta fito ta tsaya a inda Ummi ta barta,ko sakan biyar bata yi da fitowa ba ita ma ummin ta fito rike da Inhela,tana bata ta fice tare da kuma kiran A'isha a karo na uku akan ta fito su tafi.
A bakin titi suka hadu da A'isha suka tare dan sahu,kai tsaye wafa Ummul ta ce ya kai su za ta yi canji,dubanta A'isha ta yi har zata yi magana sai kuma ta fasa,cikin kankanin lokaci suka karasa, ita kadai ta fita ta je ta yo canjin sannan ta dawo nafef din zuciyarta cike da mamakin yawan kuɗin da aka canja a dala guda biyu,wanda ya kama kusan dubu dari da hamsin.
Dubanta A'isha ta yi tare da cewa"wai ina kika samu kudi ne har da yin canji?"zan baki labari bari mu kashe wannan case ɗin", Ummul ta fada tana adana kudin gudun mugun ido ya sauka akansu,a haka suka karaso devition din, suka sallami me dan sahu ya tafi abinsa, yau dake sauri take yi babu rigima da me a daidaita,ma aikatan da suke a bakin gate suna ganin Ummul suka zuba mata ido, dan kam Ummul mace me daukar hankali ko ga mata yan uwanta,basu sha wuyar kaiwa ga ainihin wajen ba saboda jagorar daya daga cikin ma aikatan da suke zaune a bakin gate,sunw shiga da Ali dake wajen zaman masu laifi suka fara cin karo Sai wani hura hanci yake sai kace dan gidan wani ƙusa, babu wata alama ta nadama a tare dashi,yana ganin Ummul ya saki murmushi dan yasan zata baza capacity ta fadda ba za a raina shi ba shi yasa ma ya kirata.
Gaisawa suka fara yi da yan san dan dake kan kantar tare da sanar da su wajen wanda suka zo,nuna musu shi yan sandan suka yi,hakan yasa Ummul ta maida kallonta kansa kamar dama tunda ta shigo bata kula dashi ba,cikin hade fuska ta ce"haba yaya me yasa kake irin wannan,dama sai da Abba ya ce da kai motar nan ta fi karfinka amma ka dage da ka dauki daidai da kai ai da haka bata faru ba,to da ia ki biyansu kudin sha"awa zaman station din yayi maka dan nasan ba za a rasa kudi a jikinka ba?"a dan fusace Ali ya bata amsa da cewa "ban fito da kudi ba saboda ba dan na yi nisa na fito ba tsautsayi ne kawai,ke kuma kin tsaya kina Min fada sai kace uwata ko yayata,idan zaki biya ki biya mu tafi idan kuma ba zaki biya ba na kira Abba"dariya Ummul ta yi tare da cewa kai ka isa ka kira Abba da za ka kira shin ai da sai ka kira shi kafin Ni ɗin ko?"harara ya watsa mata a ransa yana cewa kaji yar banzar yarinya da wannan rashin kunyar zan biya farashin fidda ni zata yi ke nan,duban dan sandan ta yi tare da cewa"ina dpo yake?"cikin girmamawa wanda ya kirata a waya ya amsa da cewa yana ciki ranshi ki dade muke na rakaki"ok muje ina me akuyar yake kuma nawa ne kudin akuyar?"shima me akuyar cikin rawar jiki ya taso yana cewa nine madam"ok to duk ku muke3wajen dpo a yi a gama case din saboda tafiya zan yi yanzu jirgin karfe hudu zan hau zuwa Rasha"kallonta Ali yayi cikin takaicin bata sashi cikin tafiyar ba ya ce"amma dai kin san nima na ce zan je Australian ko?"to me ye hadina da tafiyarka kai da zaka tafi a jirgin Abba Ni kuma na duniya zan bi "take Ali ya washe fuska yana cewa kuma fa haka ne,duk da sun shiga office din dpo ne basu fasa maganar ba har sai da suka kai aya,take shima dpo ya shiga karramasu kamar zai kwanta musu,zama su kayi cikin kasaita, daga nan ta lissafa kudin me akuya da ya ce Naira dubu talatin ta bashi,ta kuma zaro dubu goma ta bawa dpo,har waje dpo ya rako su yana godiya,tana fitowa kan kanta ta mika musu dubu ashirin su raba,ai take wajen ya kare3da kirari da godiya, dpo bai dawo ba har sai da suka shiga motar Abba da Ali ya zo da ita suka fita sannan ya koma yana murna yau ranar rabo ce........😂😂😂
To team gidan yan karya sai ku fara hada kayan tafiya Saudiya tunda ga shi har jirgine daku🤭🤭🤭🤭
Zahra✍️
***
💞GIDAN ƳAN ƘARYA💕
By
FATIMA Y ADAM......
Littattafan marubuciyar.
KUDIRAR ALLAH
KADDARATA SANADIN HASKE
ƁOYAYYIYAR RAIHAN
ƳAR GIDAN YARBAWA
MATAR ƊAN BIRNI
And
GIDAN ƳAN ƘARYA....