GIDAN YAN KARYA

Pg14

by @zahrawriter12

Suna fita daga station din,Ummul ta ce"kaga yaya ba gida zamu koma ba asibiti zamu je a kaiwa Alhaji motarsa tun kafin waccan yar balaja'un tasa a kama Ubanmu"karya kan motar yayi yana cewa ai dama can muka nufa,amma wai ke Ummul a ina kike koyo wannan samfur samfur din karyar,dan yau ji nayi gaba daya kin gama tashin kaina sai naji ma ni ba komai na iya ba, sannan su wannan kudin a ina kika samo su, Allah yasa dai ba wata rigimar kika saka mu ciki ba?"dan tura baki tayi kafin ta ce"lallai ma yaya kai baka ga irin rigimar da ka samu ba sai ni ce kake tsoron kar na saka ka rigima,to kudin da baffa ya kwace ne na fanso ka da su"dukan sitiyarin yayi yana wata shegiyar dafiyar keta,cikin mamaki suke kallonsa,basu tanka masa ba har sai da ya gama dariyarsa dan kansa, sannan dubi Ummul dake gefensa ya ce "kin san me na tuna nake wannan dariyar?"

girgiza kai ta yi tana Allah Allah ta ji dalilin wannan shegiyar dariyar da yake yi,har yanzu da murmushi akan fuskarsa ya ce"wallahi Alhaji dan gaske na tuna yadda goshinsa yayi luhuni ga yadda jikinsa duk ya ɓaci da kasa kana ganinsa kasan cewa lallai an yi karon batta"take suka suka fara dariyar duk da cewa A'isha bata ga abinda ya faru ba,aiko take Ummul ta shiga bata labarin abinda ya faru amma bata gaya musu cewa shirinta ba ne,har suka je asibitin zancan suke suna dariya har A'isha na cewa hakkin gentle me gyaran takalmi ne.

Ali yana tsaida motar a harabar asibitin ya mikawa Ummul key din motar tare da wayoyin Alhaji da suke cikin motar, sannan ya ce"Ni zan shiga Masallaci na yi sallar la'asar idan kuka fito sai mu wuce gida"karba Ummul ta yi tana cewa "idan mun fito lafiya ba,dan wallahi in dai wannan yar masifar tana nan ba za a wanye lafiya ba"daga haka suka shige reception din,take nouses din da suka dinga kula da ita a kwanakin da ta yi jinya suka dinga girmamata da bata kulawa kamar su hadiyeta,su suka nuna mata bangaren da Alhaji dan gaske yake,A'isha dai bude baki ta yi tana bin Ummul din da kallo cike da mamakinta,a hankali suka tura kofar dakin suka shiga bakunansu ɗauke da sallama,momy ce ta amsa fuskarta cike da fara a tare da cewa wa zan gani haka? Ummul ke da kanki duka duka yaushe kika bar asibitin amma har kin kuma fitowa"murmushi Ummul ta yi tana cewa "kai momy ai naji sauki yaya me jikin ta ɗora maganar tana dan satar kallon Abba da ya canja kamanni"da sauki Ummul yaya ummin ta ki?",suna lafiya tana gaida me jiki"Ummul ta fada daga nan ta juya ta kalli zezee da ko kallon inda suke ba ta yi ba,girgiza kawai take tana cika tana batsewa kiris take jira ta fashe,"aunty zezee ina wuni ya me jiki"?wani uban tsaki zezee ta yi tana watsa wa Ummul din kallon banza ,a maimakon ta amsa gaisuwarta sai cewa ta yi "dalla Malama ina kuka kai mana mota tun dazu ubanki ya fita kawo key amma har yanzu babu shi babu alamunsa"da sauri Ummul ta mika mata key da wayoyin Alhaji tana cewa"Allah sarki aunty zezee ai yaya Ali yana ajiye su baffa tafiya yayi ya mayar masa da motar can gida saboda yasan komya barta sai an maida ita gida tunda me ita ba lafiya, sannan kuma idan zaku zo dole da mota zaku zo,shi yasa.ya dai kai muku key din ya sanar da ku abinda ke faruwa, to kuma a hanyarsa ta zuwa ciwon ciki ya turnukeshi, ya kasa karasawa,sai wani abokinsa yayiwa waya yazo ya tafi dashi gidansu, sai da ya sha magaji ya ɗan ji dad'i sannan ya kirani ya sanar dani shine fa muka je nisa A'isha muka sameshi, to da naga jikin nasa da sauki je yasa nace kawai ya zo mu kawo motar da wayoyin saboda suna da muhimmanci tare da Abba"wani banzan kallo zezee ta yi mata bayan ta kare maganarta sannan ta fizge key din tare da wayiyin ba tare da ta ce komai ba,dan a hakan daurawa take tana kai zuciyarta nesa akan Ummul din duk a cikin shirinta na canzawa,momy kuwa duban A'isha da ke gaidata ta yi tare da amsawa, sannan ta maida kallonta kan Ummul da ta wani cuno baki kamar zata fashe saboda haushin zezee ta ce"Allah sarki yana ina alin ai da ya zo likita ya duba shi shima kar ya zauna da ciwo"cikin sauri Ummul ta ce"a'a momy ai tuni ya ware yanzu ma sallah ya tafi yi muma bari muyi sallah sai mu wuce"to babu laifi cewar momy tana watsawa zezee harara cikin yi kaga gargadi da ido ta hanyar nuna mata Alhaji dan gaske da yake ta baccin wahala.

Bayan sun idar da sallah ne momy ta ce su tsaya su ci abinci kafin su tafi,amma sai Ummul ta ce mata ai sun ci abinci kafin su fito,nan kuwa Ummul cikin ta babu abinda yake sai juyin yunwa ta ki ci ne kawai saboda gudun wulakancin zezee, itama A'ishah dama bata yi niyar cin ba saboda abinda Ummul din ke gudu,suna gab da ficewa daga dakin Abba ya farka, cikin samun sassaucin azabar da yake ji,yana yin arba da aminatu kuwa ya kuma jin wani irin kwari a tare dashi har da kokarin tashi zaune,momy ce ta taimaka masa ya zauna tare da jingina masa fulo a bayansa,idanunsa akan Ummul da suke gaidashi da yi masa sannu da fatan Allah ya kiyaye, cikin sakin fuska da fara a yake amsawa wanda hakan ya dinga kona zuciyar zezee dan ji take kamar ta kamo makogoron Ummul ta cizge ko ta huta da abinda yake damun zuciyarta akan Ummul ɗin,rasa yadda zata yi ta huce takaicin da Ummul ke dasa mata yasa ta faki idonsu ta jefa ɓawon ayabar da ta ɓarewa Abba wajen da ta tabbatar dole sai Ummul tabi ta hanyar Sannan zata fita,sai a sannan zuciyarta ta yi haske,dan tasan yau dakyar idan ba a kuma bawa Ummul gado ba.

Duk yadda Abba ya so tsaida Ummul da surutu amma hakan bai samu ba, kallon A'isha ta yi tana cewa mu tafi ko",ransa bai so ba hakan yasa kawai ya bita da kallo yana ji kamar ya janyota gareshi dan tsananin so,zezee kuwa tuni fuskarta ta washe da murmushi ganin ƙafar Ummul na daf da taka ɓawon ayabar, ɗauke kanta ta yi tana jiran jin ƙarar ikram a kunnenta, Ummul kuwa hankali kwance ba tare da ta lura ba ta fara takunta wanda yayi daidai da ɓullowarsa cikin ɗakin tare da sallama a can ƙasan maƙoshinsa.

ƙamshinsa tare da takunsa ne ya sa ta dauke kanta daga kallon hanya wanda hakan ya jawo ta sanya kafarta kan ɓawon ayabar da kafin ta kai dubanta kan inda ta yi niyyar kalla taji ta zame,tare da tafiya suuuu zata kai ƙasa, ƙara ta saka tare da runtse idanunta tana shirin jinta a ƙasa,amma a maimakon hakan sai kawai ji ta yi ta tsinci kanta cikin wani irin ni im taccen jikin da yake wani irin sanyayyan ƙamshin da ta kasa gane wane irine saboda tsananin daɗinsa,zezee kuwa da ta gama shirya yadda zata kuma karawa Ummul azabar faduwar da ta yi tuni ta miƙe tsaye tana raba ido akan Ummul da kuma Dr Bilal da take kwance male_male saman faffadan ƙirjinsa,ɗif dakin yayi,tamkar an dauke nefa,yayin da Abba ya dinga jin wani irin zafi a ransa, tabbas da ya san cewa Ummul zata fadi har Dr ya sanya ta a jikinsa to da shi ne wanda zai yi wannan aikin,zezee kuwa wani irin miyau ta dinga hadiyewa ƙut ƙut ƙutt wuyanta kamar ya tsage saboda yadda miyan yake wucewa kamar reza a maƙoshinta, Ummul kuwa jin bata fadi ba yasa ta bude idonta a hankali wanda kai tsaye basu tsaya a ko ina ba sai cikin fararen idanun Dr Bilal da suke sakaye cikin farin gilashin da yake kara masa matukar kyau,da wani irin gudu ta maida nata ta rufe saboda yadda bugun zuciyarta ya sauya yake tafiya da wani irin sauri kamar zai bayyana kansa a fili,a nutse ba tare da wani yanayi ya sauka a akan kimtsatstsiyar fuskarsa me cike da kwarjini ba ya dagota tare da tdauar da ita kan kafafunta sannan a hankali ya durkusa ya sanya hannunsa da yake sanye cikin Safar su ta likitoci ya dauke ɓawon ayabar ya jefa cikin dusving, kana ya taka a nutse fuskar nan a hade zuwa gaban gadon Abba.

Ita kuwa momy da sannu ta bi Ummul cikin tausayawa ba tare da zuciyarta ta kawo Mata zargin komai ba akan kokarin faduwar Ummul din.

Da sauri Ummul ta janyo hannun A'isha suka fice daga dakin dan tuni ta ga alamun waccan jahilar zata fara zubda hali kamar yar karya,ita ko irin ajin nan na masu kudi bata da shi kullum bakinta cikin masifa da manyan zagi kamar yar maguzawa,basu samu Ali ba dan haka sai kawai suka tare me dan sahu suka shige,tunda suka tafi bakin Ummul ya mutu wanda hakan yasa A'isha ta ɗan zungureta tare da ce mata,to ke kuwa Uwar tsoro tunda Allah ya sa baki fadin ba ai sai ki fita daga cikin firgicin haka ko?"yatsina fuska Ummul ta yi tare da shafa fuskarta kana ta ce"A'isha ba zaki ga ne ba wallahi al al'amarin zezee shi yake damuna dan na tabbata ita ce ta samun ɓawon ayaba dan na fadi, wanda hakan ya nuna min cewa zata iya kasheni tunda yanzu ma bata san iya inda tsautsayin zai tsaya ba amma ta yi"numfashi A'isha ta sauke tare da kama hannun Ummul din tana cewa, "ikram ke ba me damuwa ba ce dan haka kar ki sa damuwar zezee a ranki kin san dai baki da ishashshiyar lafiya dan haka dan Allah ki bar maganar nan kar ya dame ki"jinjina kai Ummul ta yi tare da dan sakin murmushi dan tunawa da moment dinsu na jiya ita da gentle, hakan yasa hirarsu ta koma kan gentle din, duk da cewa aisha amsa mata kawai take tare da karantarta da kuma mamakinta akan al amarin gentle din, ahaka suka karasa gida,suna sallamar me nafef din daga idon da zata yi ta ga sulaiman suna fitowa shi da yaya mufty daga cikin gidansu suna hira da dariya har da tafawa,take ta hade rai tare da fara yin muzuran da zasu sa sulaiman ya kiyaye ta.

A can wajen su Dr kuwa, jikin Abba ya shiga dubawa fuskar nan babu alamun rahma bare zezee taga wajen yin tabara,to sai ma wani tsoronsa da ya dinga shigarta wanda har yasa ta kasa yin katabus a wajen, tana ji tana gani ya gama aikinsa ya fice ba tare da ya kalleta ba, yana fita ta sanya kuka tare da kwanciya jikin momy tana cewa momy ya zan yi da soyayyar da nake yiwa Dr? wallahi momy ina sonshi kuma zan iya komai akansa ki bani shawara me zan yi ya so ni ya daina wulakantani?"tsaki kawai Abba ya ja tare da yatsune molalliyar fuskarsa, kafin ya ce "kinga zezee ki rufe mana baki dan duk abinda yake faruwa ke ce sanadinsa dan haka sai ki yi hakuri soyayya dai ba zaki taba samun ta daga Dr ba amma aure na yi alkawarin ko zan yi yawo tsirara sai an yi shi, dan haka ki bar kuka zaki samu Dr a matsayin miji amma ba zaki samu siyayyarsa ba"dagowa ta yi fuskarta gaja gaja da hawaye, sai da ta ja majina sannan ta ce "Abba duka nake so aurensa da kuma soyayyarsa dan haka nima ko zan yi yawo tsirara sai na nemo soyayyarsa"tana gama fadin haka ta mike ta suri jakarta ta fice daga dakin,Binta da kallo su kayi daga shi har momy,kafin daga bisani su janye suna sakin ajiyar zuciya a tare,sai kuma a ka koma kallon kallo tsakaninsa da momy kowa da abinda yake tunani akan dan uwansa, shi yana tunani akan yadda take nuna halin ko in kula akan samgarsu da shi da zezee, a bangaren momy kuwa tana tunani ne akan lallai lokaci ya yi da ya kamata ta cika nata burin da ya kasance daukar fansa ne,sun jima suna kallon kallo kafin daga baya momy ta mike ta bar dakin tana ci gaba da kullawa da kuncewa.

******

Tunkarar gidan ta yi kai tsaye tana kuma murtuke fuska,sai dai hakan bai yi mata amfani ba,dan kuwa shan gabanta sulaiman yayi fuskarsa dauke da murmushin da tsananin jin dadin da yake ciki na ganinta,"malam lafiya bashi ko tara"ta tambayesa tana masa kallon sama da ƙasa,muftahu ne ya matso tare da watsa mata harara yana cewa, ke wai me yasa baki da hankali ne, wannan abin da kike yi shine tarbiyyar da su baffa suka bamu?to wallahi ki nutsu idan ba haka ba sai na gayawa baffa duk abinda ya faru yau din nan"gunguni ta shiga yi tare da komawa gefe ba dan ranta ya so ba sai dan gudun tonan sililin da ya mufty yake iƙirarin yi mata, duk da cewa idan ma ya tona har da shi a cikin lamarin,ba tare da A'isha ta shiga ciki ba ta yi mata sallama ta tafi a cewarta zata dawo da daddare, gyara tsayuwa yayi yana kallonta cike da kauna kafin ya ce"Ummul ina sonki wallahi dan Allah ki bani dama na nuna miki irin tsantsan son da nake miki"tun da ya fara zancansa idanunta suke tsaye kyam kan gentle da yake ta karkade kujerar da yake zaman yin aikin gyaransa,ko a fuska bai nuna ma ya santa ba bare yayi mata magana ko da ya jiki ne, wannan ne ya kuma tunzurata har yasa ta kalli sulaiman ta ce"sulaiman dan Allah ka rabu dani ka san dai bana da lafiya amma kake so dole sai ka karawa zuciya da gangar jikina wata lalurar, ka rabu da ni na shiga gida saboda a yanzu bana cikin yanayin da zan iya tsayuwa a gabanka"hanya kawai ya bata yana cewa"ina nan ina addu'a wata rana sai dai mu tuna wannan muyi dariya"wucewa ta yi a ranta tana cewa "ba dai da Ummul ba"kallon inda gentle Yake ta yi tana cewa "me Aljanu kawai"har da dan murguda masa karamin bakinta tare da yin fari da idon, sannan ta yi shigewarta gida tana jin zafin rashin kulatan da bai yi ba,mutum sai ka ce me alamutsutsai kamar ba shi ne ya gama zurara zance ba jiya,dama na sani ban rama maka marin da aka yi maka ba "ke kuma da wa kike magana Ummul,cewar ummi da take daura alwalar magriba,"ba kowa ta fada ita ma tana daukar buta dan yin tata alwalar.

A can waje kuma bayan shigar Ummul cikin gidansu ne ,sulaiman da tun dasu ya lura da cewa ganin gentle dinne yasa ta kasa tsayuwa da shi,saboda hankalinta gaba daya ya koma kansa,takawa yayi ya karasa gaban gentle din tare da dan yin tsuguno a gabansa yana karewa kayan gyaransa kallo cikin kyama da takaicinsa da ke ransa, kafin ya sanya hannu ya daga wani takalmi da gemtle din yake gyarawa fuskarsa cike da nuna kyankyami, ajiye takalmin yayi sannan ya maida dubansa kan gentle din yana cewa"idan ma wani suddabarun kayiwa yar mutane ka janyo hankalinta to tun wuri ka warware shi,dan wannan yarinyar ta fi karfinka ba kalar taku ba ce,ka barmu mu masu abinda zamu kawata kyanta da shi mu sameta,duk da cewa ban san me yake taka zuciyar ba amma alamu sun bayyana abinda yake cikin zuciyar Ummul dan haka ka kiyaye shiga hurumin da ba naka ba"yana gama fadar haka ya mike tare da dan ture takalman da suke gabansa ya shige motarsa ya bule gentle da ƙasa,wanda ko motsi bai yi ba bare ya daga kansa ya kalli sulaiman din.

Zahra✍️

***

💞GIDAN ƳAN ƘARYA💕

By

FATIMA Y ADAM......

Littattafan marubuciyar.

KUDIRAR ALLAH

KADDARATA SANADIN HASKE

ƁOYAYYIYAR RAIHAN

ƳAR GIDAN YARBAWA

MATAR ƊAN BIRNI

And

GIDAN ƳAN ƘARYA....