Pg17
Hannu Ummul ta ɗora aka idanunta a waje kamar zasu fado,kafin ta kalli gentle da ya koma ya zauna tamkar wanda ya karya kara,ita Ummul ma abin mamaki ya bata dan a yadda gentle ya kama hannun ba zaka taba cewa zai samu wata illa ba,sulaiman kuwa rike hannunsa da dayan hannun yayi yana faɗin "wayyo hannuna ya karya ni jama a ku kawo dauki mahauci ya karyani"juyawa Ummul ta yi da gudu ta shige gida jikinta na karkarwa kamar ana kada mazari, Allah ne ya taimaki sulaiman yaya Ali da yake can nesa kadan dasu yana hango abinda ke faruwa ya karaso wajen da hanzari,bai tsaya bin ba a sin ta yadda abin ya faru ba ya kama sulaiman din suka tafi zuwa gidan baba me dori,sunyi sa a kuwa babu layi dan haka shiga kawai su kayi,lokacin da baba me dori ya taba hannun sulaiman kara ya saka,har sai da yaya Ali ya ce"kai wai ashe haka kake rago? to wallahi Ummul bata son ragon miji me kuka,dan haka kar ka sake ka bari Ummul ta ga kukanka"wannan kalamai na yaya Ali su ne suka sa shi yin shiru amma fa gumi ne yake karyo masa ta ko ina kamar wanda ake watsawa ruwa,baba me dori ya kalli Ali ya ce"ai ba ma karaya ba ce kashinne ya goce"tsaki Ali yayi haushin sulaiman na kamashi ya ce"ashe ba karaya ba ce amma kake wannan rakin kamar mace"sulaiman ya janye hannunsa da aka gama gyarawa yana cewa"Ali ba za ka gane ba wannan abin da nake yi har da na takaicin wanda yayi min illah a zuciya da gangar jikina,kuma wallahi ba zan barshi ba sai na sashi kuka da idanunsa kuma yanzu ma 'yan sanda zan kira su tafi dashi"kana hauka ne?"yaya ali ya fada dai-dai lokaci da suke fitowa daga cikin gidan me dorin,ya ci gaba da cewa "wallahi idan har kasa a ka kama gentle to ka tabbatar da cewa ka kashe kanka har da binnewa a wajen Ummul,don Alhaji dan gaske ma da ya mareshi bata kyale ba bare kuma kai,dan haka kabi a hankali ka nemi soyayyar Ummul ta hanyar da ya dace kar kuma garin neman gira kaje ka rasa ido",shiru kawai yayi har suka karasa kofar gidan inda ya ajiye motarsa,ga mamakinsa gentle baya nan dan har kayan sa babu da alama dai tsoron abinda ya aikata yaji ya gudu, wannan shine tunanin da sulaiman yayi,
Ali yana kokarin shiga gida sulaiman ya dakatar da shi ta hanyar cewa"dan Allah ka taimaka ka kaini gida saboda yanzu ba zan iya driving ba, dan gaskiya ina tunanin sai na je asibiti an duba hannun sosai, bana tunanin gocewace"abin dariya ya bawa Ali, dan haka ya kasa rikewa sai da ya dara kana cikin dariyar yake cewa,"gaskiya sulaiman kaji hannun maza irin wannan fita hayyaci haka,to yanzu da karya kan yayi ya ke nan,gaskiya gentle jarumi ne daga dan ture hannu sai karyewa sai kace hannun jariri"harara sulaiman ya watsawa Ali kafin ya ce "malam bana son wulakanci idan zaka kaini ka kaini idan kuma ba zai samu ba na wuce na nemi taimakon wani",cikin dariyar keta Ali ya ce "a'a muje me zai hana na kai ka kodan na zuba capacity a hanya,amma dan Allah ka daure ka zama yarona na awa daya kawai ka fin mu isa gidanku "saboda takaicin Ali sukaiman kasa magana yayi, sai shigewa kuejrar me zaman vanza da yayi yana hura hanci da rufe ido lokaci lokaci saboda azabar radadin da yake ji,yana daurawa ne kawai saboda kar Ali yayi masa dariya daga karshe ma yake ya bawa Ummul labari,shi.kuwa Ali cikin nishadi ya yiwa motar key ya fizgeta da gudu suka bar layin.
******
Ummul kuwa shigar ta gida ke da wuya ta samu Ummi har ta gaji da jiranta ta nemi bakaken leda ta kulle tuwonta ragowar kuwa da basu samu leda ba ta kyabawa Ummul a faranti saboda ta san halin Ummul din babu abinda ta tsana irin a saka mata tuwo haka kiri kiri a kwano ba tare da sutura ba,turus ta yi tana kallon ummin da take daura alwalar magriba ranta a ɓace kamar zata kaiwa iska duka,sumi sumi Ummul ta shige ta ajiye ledar kanta a kasa tana ta faman murde mayafin ta,"uban me kika tsaya yi a waje Ummul?"Muryar Ummi da ta sanya ta razana saboda yadda sautin ya fita cikin tsawa da kaushi,matsawa baya ta dinga yi tana yan kame kame dan duk karyar Ummul kasata take yi a gaban Ummi,ganin ta kasa cewa komai ne yasa ta barta a nan ta wuce kan shimfidarta ta sanya hijabi ta zauna tana ci gaba da laziminta da azkar kafin a kira sallar magriba,ita ma Ummul din wucewa ta yi kamar wata tsohuwar munafuka ta dauki buta ta daura alwala, itama ta zo ta zauna tana azkar zuwa kiran sallar, amma duk da banzar da Ummi ta yi mata ɗar ɗar take yi da ita, saboda tasan sarai ba kyale ta ta yi ba wata kila ma sai ta sakankance ta ji ruwan bulalai a gadon bayanta.
Ali dai ganin da gaske sulaiman yana cikin mawuyacin hali yasa ya hakura da zubar da galan galan din karyarsa ya kai sa gida kai tsaye, godiya sulaiman din yayi masa tare da karbar key din motar ya shige gida yana kara kwabe fuska saboda ya zo inda za a rarrasheshi a sakaltashi kamar jariri.
Da kallo Ali ya bisa yana tabe baki kafin ya ce "gaskiya ko ni ban goyi bayan Ummul ta auri wannan sangartaccen ba,sai kuma ya bi gidan da kallo yana cewa "babu laifi suma da nasu arzikin amma dai ba dai ba irin nasu ya ke so ba, wanda yafi nasu, gwara na roka da babban masaki ya fada yana fita daga gidan cikin kwanbo da takun fadi, dan kar ma wani ya ganshi ya rainashi.
Su zezee basu dawo Kano ba sai cikin dare dan ma kauyen da suka je farkon Niger ne ba can ciki ba,sai da ta ajiye bely a gida sannan ta wuce gida,tana shiga ta samu momy a zaune ta tafka tagumi hannu biyu, ganin zezeen yasa ta sakin ajiyar zuciya tare da binta da kallo,zama zezeen ta yi cikin kujera cike da gajiya tana cewa "tafiya yankin azaba,an sallamo Abba ne?"an sallamo Ni daga gidan ubansa kike tun da sassafe aka ce kin fita daga gidan nan amma baki shigo ba sai a irin wannan lokacin,zezee wai me kike so da Ni ne?anya ba kina sane kike son ki janyo min salalan tsiya da asara ba,saboda na fahimci take takenki duk hanyar da zaki janyowa kanki tsana a wajen Bilal da familynsa su kike nema,to idan ba ki sani ba ki sani dangin da zaki yi aure a cikinsu mutanene masu daraja da kima da kuma tarbiya duk ahlinsu basu da mummunan tabo, dan haka kuma dole ki zama me tarbiyya me mutunci me kamun kai idan ba haka ba kuwa wallahi ba zamu taba samun abin da kuke nema, ko Ni ubanki sai da na zama me waɗannan halayyar sannan na samu yarda da SOYAYYA a zuciyar uban gidana bare kuma wata ke karamar alhaki,dan haka tun wuri ki kama kanki da na ga alamar nema yake yanar jikin ki saboda rawa",cike da tsananin mamaki mommy take kallonsa dan haka yana sa aya a maganarsa ta tafa hannu tare da jan salati, kafin ta ɗora da abinda yake ranta,"yanzu dan Allah Alhaji kai ba abin kunya ba ne a wajenka ka dinga irin wannan maganar?ni na yi zaton zaka tambayeta daga ina take amma sai naga sam hankalinka ba anan yake ba, wannan abin da kake yi fa sam ba tarbiyya ba ce",hanyar dakinsa ya nufa yana cewa "Ni dama na ce miki tarbiyya nake mata ke dai da kika ga zaki iya sai ki yi amma Ni dai tattalin kudi da hanyar nemansu shine karshen tarbiyar da zan iya yiwa 'yata"daga hakan ya karasa shigewa daki ya bar mommy sake day baki,duk da cewa dama ta san halinsa akan kuɗi kuma babu abinda ba zai iya ba akan kudin to amma bata san cewa hatta da yar da ya haifa zai iya salwantar da tarbiyarta akan kuɗi ba,waiwayawar da za tayi dan yiwa zezee din fada sai taga ita ma ashe har ta gudu dakinta,jinjina kai kawai tayi tare da sakin wani dan takaitaccen murmushi a ranta tana cewa "fansa na nan take fansa irin wadda ke haukata ƙwaƙwalwar mara hakuri,dan haka zata ci gaba da hakuri da boye kanta har zuwa lokacin da ranar wanda take fata Allah ya a rana mata.
*****
A dai-dai lokacin kuma,ummi ta sakawa kowa tuwonsa cikin aminci da sutura amma banda ikram da nata yake a hangame, gashi ya wani sandare babu ko kyan gani in jita,Ali da mufty suka ja nasu aka zuba musu miya suka fara kaiwa baka cikin jin dadin yadda mahaifiyarsu ta iya girki me dadi da sanya nishadi, Ummul kuwa sai balala ido ta ke taga an miko mata nata amma sai taga har ita ummin ta kama cin nata bayan ta zameshi da ga leda fari tas gwanin sha awa sai tururi yake saboda an sanya shi a kula,kallon wanda yake gabanta ta yi dan tabbatar wa da shi ne fa ummi ta bata wai ta ci,kawar da ka ta ta yindsga kan tiwon dan wallahi ganinsa tashin zuciya yake sata,hannunta kai zata sa a na mufty yayi saurin janye tuwonsa yana cewa "wallahi ba ki isa ba ki ci naki sandararre kawai hajjaju ta gaban mota matar sulaiman"take ta tuna da abinda ya faru a dazun hakan yasa ta kama kanta tana rarraba ido gwanin tausayi,gashi ta kasa cin ko loma daya,janyewa ta yi ta koma can karshen tabarma ta zuba tagumi abin tausayi,ya Ali ne ya kalleta tare da cewa taho nan autar baffa kici nawa kinji shalele,ina Ni ina yiwa me sa ar gidanmu rowa,dan wallahi ji nake ajikina silar arzikina yana tare da Hajiya Ummul ikram dan haka zo ki ci towo "girgiza kai Ummul ta yi tana sakin hawayen da tun dazu suke makale a kwarmin idanunta,tashi yayi cikin sauri yana cewa "ina da ragowar wata dubu daya bari na je wajen kamalu me tsire na siyo miki,tun da yau kin yi fushi da tuwon ummi "cikin sauri ya mufty ya zaro wata dubun yana cewa ka siyo mata na dubu biyu kasan halin auta kura ce naman dubu daya ba zai ishe ta ba"tuni Ummul ta manta da damuwarta ta shiga dariyar abinda mufty ya faɗa,karba ali yayi yana murmushin ganin farin cikin autarsu wanda hakan yasa ummi da take jinsu share kwallar farinciki,tare da yiwa Allah godiya da ya shirya mata yaranta ya kuma hada kansu,saukar kan Ummul bisa cinyarta ne yasa ta dawowa daga tunaninta,murmushi ta yi tare da dora hannunta kan Ummul din tana shafawa,kafin a hankali ta fara yi musu nasiha tare da kawo musu misalai da tarihin annabawa ko wasu manyan bayin Allah,wanda hakan ba sabon abu ba ne a wajensu,a cikin haka Ali ya dawo,ya bawa Ummul namanta sai dai kuma memakon ta ci ita kadai duk sai ta janyo hannayensu ta sanya a cikin naman, sun san ko sunce ba zasu ci ba rigima za ayi dan haka har ummi sai suka biye mata su ka ci tsoka daya daya,daga haka suka dinga yi kamar suna ci, ummi kuma na ci gaba da basu tarihi wani lokacin kuma ta basu tatsuniya.
WASHE GARI.......
Da wuri yau ma Ummul ta tashi dan ta tashi ne da niyar komawa bakin aikinta, sai da ta taya Ummi suka gama aikin gidan suka karya sannan ta shirya tsaf dan tafiya gidan Alhaji dan gaske,kamar kullum sai da Ummi ta ja mata kunne da nasiha sannan ta sa tasa ta yi addu'ar fita daga gida,ita ma ta yi mata addu'a kamar yadda suka saba, sannan ta fice daga gidan,kasancewar bata fito da wuri sosai ba yasa ta samu har gentle ya zo ya fara aiki,har zata wuce sai kuma ta dakata tare da dawowa da baya,ta tsaya daga gefen gentle din, sai da ta dauki dan lokaci sannan ta tura baki tare da cewa Barka da safiya"Barka ya fada kamar wanda aka yiwa dole"harar gefen ido ta yi masa a ranta tana cewa"mutum sai mugun bakin hali kamar a zamanin su fir auna,tsugunnawa ta yi a gabansa tana cewa"me yasa jiya ka karyawa saurayina hannu?"sai a lokacin ya dago idanunsa da suke sakaye cikin bakin galss ya kalleta na sakon biyar sannan ya maida kansa ya ci gaba da abinda yake ba tare da ya bata amsa ba,ji ta yi kamar ta fasa masa baki, amma dai tunda ita take nema ba za ta yi fushi ba, dan haka ta ɗan leka bayansa inda take yawan ganin takalman da aka kawo masa gyara ba a zo an karba ba,taga suna nan har da wani takalmi me kyau na yan gayu dan da ganin takalmin me tsada ne,gyara Muryar ta ta yi tare da kariyar da kai kamar wata saliha sannan cikin kwantar da murya ta ce"yaya gentle dan Allah ba dan bi ba ka raimaka ka kawo min dauki,bana so na zama makaryaciya kaga dai a gabanka na yiwa likitar nan alkawarin takalmi, kuma dai kasan bani da takalmin nan sannan bana so mutunci na ya zube a idon likitocin nan,gashi kuma ni ba barauniya ba ce bare na sato na zezee na bata,shine nace ko zaka bani daya daga cikin wanda ake kawo maka gyara suna barinsa basu karba ba?"
"Ni kike so na yi satar ke nan na baki,to Ni ba barawo ba ne kije saurayinnaki ya baki"ya karasa fada yana tsare ta da ido, take jikinta ya mutu bayan ya yi wani irin sanyi lakwas kamar an zuba mata ruwan kankara,kawai sai ta tsaya tana kallonsa kamar yadda shima yake kallonta ta cikin dakayayyun idanunsa,ita ce ta fara kawar da kanta tana mulmula bakinta, shi kuma ya kafe bakin nata da ido yana son fahimtar abinda take fada.
Daidai nan motar Alhaji dan gaske ta faka a saitin su,tun daga nesa ya hangosu wanda hakan yasa yaji kamar yabi takan gentle din da mota, bai fito daga motar ba kawai ya tsaya yana kallonsu ta cikin bakin glass din motar da ya kasance na waje baya ganin na ciki sai dai na ciki ya hangi na waje,a yadda suke sai yaga kamar wata irin hirar soyayya suke wadda har ta sa su basa ji basa ganin me shiga da fita,da karfi yasa hannu ya daki sitiyarin motar tare da cizon yatsarsa da har sai da ya ji zafin na shigarsa sannan ya janye ta,tabbas dole ya dauki matakin farko akan wannan yaron dan yaga alamar shine zai zame masa babbar matsala,me yasa ma wai bai tsaya sun yi magana da baba buzu ba tun kafin ya fito?"tsautsayin da yake shirin saukarwa wannan saurayinne ya sa hakan ta faru,ya tambayi kansa da bawa kansa amsa duk a lokaci daya,duk da cewa yasan bashi da matsala a wajen baffa amma yana jiyewa kansa tuburar yarinyar nan dan ya fahimci ba karamar fininanniya ba ce,dan haka zai yi kokari a cikin sati guda ya samu kanta daga nan magana ta kare bashi da wata sauran fargaba, yana kaiwa nan a lissafinsa ya bude motar ya fito tare da nufarsu kai tsaye yana sakin murmushin yaudara.
Ummul kuwa saboda haushin maganar da yayi mata da kuma halinsa na ko in kula, sai kawai ta shiga watsawa ƙafarsa da kayan aikinsa kasar wajen tana hawayen da basu da wani dalili, shi kuwa tamkar ba dashi take duk wannan ba ,yayi mata kunnen uwar shegu, wanda hakan ya kara harzukata, har bata san sanda ta mike ta fara fatali da kayan sana ar tasa ba, dai-dai nan Alhaji ya yi gyaran murya fuskarsa na washewa da annurin ganin wannan lamari,abinkamar a mafarki,"yaya dai ikram me ya yi miki kike watsa masa tattalin arzikin nasa?"ko kallon Alhaji bata yi ba ba kuma ta fasa abinda take yi ba ,sai ma ƙaruwar lamarin ta hanyar sakin kukanta me dan sauti da ya ke fita da wani irin kuncin damuwar zuciya akan abinda bata sani ba,hannu Alhaji ya kai dan dakatar da ita saboda yadda duk ta burkice kamar wata mahaukaciya,amma sai gentle ya riga shi ta hanyar yiwa Ummul din wata irin hadaddiyar rumfa da faffadan jikinsa inda ya tare ta daga ganin kowa da komai dake giftawa a sararin samaniya da kasar Allah ta ala,take Ummul ta dauke wuta daga haukar da take yi, zuciyarta tuni ta yi dif daga tashin hankalin rashin sanin inda ta dosa,tsayuwar numfashin Ummul wanda ya kasance na samun nutsuwa ne daga tunzurin zuciya da ruhi,yayi daidai da tsayawar numfashin Alhaji dan gaske wanda nasa ya kasance na tsananin rudewa da tashin hankali ne...
Zahra✍️
***
💕GIDAN ƳAN ƘARYA💕
By
FATIMA Y ADAM......
Littattafan marubuciyar.
KUDIRAR ALLAH
KADDARATA SANADIN HASKE
ƁOYAYYIYAR RAIHAN
ƳAR GIDAN YARBAWA
MATAR ƊAN BIRNI
And
GIDAN ƳAN ƘARYA....