GIDAN YAN KARYA

Pg19

by @zahrawriter12

Tsananin karar marin ne ya firgita Ummul har bata san lokacin da ta kankame dr Bilal ba, fuskarta a cikin gadon bayansa,jikinta har wani bari yake yi,Zezee kuwa tsaye ta yi dafe da kuncinta tana kallon Dr Bilal da yake watsa mata kallon gargadi ba tare da taga wani sauyi akan fuskarsa ba,sai baffa da yale ta fadin"ashsha ashsha ashsha abun be yi dadi ba, su.yara ne dole sai ana kai zuciya nesa,Ni kaina ban ina kai zuciya nesa ba da waccan yarinyar ta bayanka da tuni na babballata,ita da yayunta,to amma idan na duba cewa akwai kuruciya sai na danne zuciyata na yi ta bi sunsu da addu'a "a a nutse kuma a mutunce Dr Bilal ya kalli baffa kafin cikin fuskarsa da bata cika walwala ba ya ce"baffa akwai irin mutanen da ake yiwa uzuri idan sun yi laifi, amma banda irin wannan,saboda ita ta wuce matakin Kuruciya ita ya kamata ta gyarawa wani,kar ka damu baffa wannan ba dabia ta ba ce,kawai na yi hakan ne dan naga shine kawai yaren da zata fahimta tasan cewa bata kyauta ba,shi kuma wannan maganar kamar kome a hannuna za a yi bincike me kyau"daga haka ya yi shiru tare da ɗan motsawa dan Ummul ta bashi damar tafiya, sai a lokacin ta tuna a jikin waye take, da sauri ta sake shi tana murtsika idonta,a ranta tana jin zafin Dr bayan kuma ba shi ya kar zomon ba.

Zezee kuwa da har yanzu ta ke faskari a wajen zuciyarta na kuka kuka irin wanda baya tsayawa,ta kasa gaba da baya sai idanunta da suka yi wani ja suka kankance,ji ta yi an ja hannunta,ba tare da ta musa ba ta bi me jan nata kamar wata raƙumi da akala, Ummul ma barin wajen ta yi ta, dan a ranta ta dau aniyar ba zata bar gidan ba har sai Abba ya dawo ta ji inda ya kai mata gentle ya boye.

Momy bata tsaya da zezee ba har sai da suka dangana ga dakinta, sannan ta dangwarar da ita bakin gadonta, Sannan ta bita da wani irin kallon takaici da bakin ciki,ita kuwa zezee sai a lokacin wani irin kuka me cin rai ya kwace mata ta fara ba tare da tsagaitawa ba,"wallahi in dai hanyar da kuka dauka kenan keda ubanki to baki fara kuka ba,zezee ni uwarki ce da ta yi renon cikinki wata tara ta haife ki dan haka duk duniya ba wanda zai fi ni sonki,zezee ki sani cewa ubanki bashi da hali dan haka kar ki biyewa son zuciyarsa kikai taki zuciyar ga halaka,ki sani cewa ubanki babu ruwansa da son da kikewa Dr domin ba don farin cikinki yake son kulla wannan aure ba,don nasa biyan buƙatar ne kawai yake son auren da zarar kuma yayi amfani dake ya cika burinsa shike nan ke ya barki da ciwon so tunda ba zai bari ki dauwama da abinda kike so ba,dan haka a shawarance,a matsayinsa na mahaifiyarki kija mutuncinki da kimarki ta ya mace ki fita da ga sabgar Dr da mahaifinki,tunda gashi har abin ya fara kaiwa ga mari gaban ma aikatanki"momy wallahi ina yiwa Dr son da ba zan taba iya rabuwa da shi ba,,ko da a ce kullum naman jikina zai dinga yanka yana rabawa mutane wallahi ba zan fasa aurensa ba,domin bani na dasawa kaina son sa ba Allah ne ya dasa min"cikin mamaki mommy take kallon bakin zezee kafin ta jinjina kai tare da cewa "ey lallai ikon Allah ya fi gaban mamaki,ba shakka Allah zai yi sakayya akan wanda aka zalunta ta hanyar jinin jikinka,duk abinda ka shuka shi zaka girba yanzu gashi Salisu zai girbi abinda ya shuka ta hanyar diyarsa domin na tabbata sanadin wannan soyayyar Allah zai kawo karshen zaluncinsa da cin amana da yaudararsa, wata kila nima ta hanyar ɗiyar da muka haifa Allah zai yi min tawa sakayyar"ta karasa maganar idanunta cike da kwallar da take hade da wani irin kuna da zugin tunawa da wani mummunan al'amari,zeze kuwa jahilar kwakwalwar ta bata sanya ta ta yi nazari akan kalaman mommy ba hasalima tunanin ta yana ga yadda zata samo kan Dr, hakan da mommy ta gani ya sa ta fice daga dakin tare da barwa Allah komai a cikin ranta dan tasan sakayyarsa ta fi ta ta.

****

Abba dan gaske bai dawo gidan ba sai karfe tara na dare,kuma har lokacin Ummul bata tafi gida ba,duk da cewa a ranta tana tsoron fitar daren dan tunda ta fara aiki a gidan baffanta bai taba bari ta wuce takwas bata tafi gida ba,shi yasa anasa bangaren ya ke ta sake saken ko lafiya Ummul din bata fito ta tafi gida ba,ko da ummi ta kira shi ya sanar da ita cewa Ummul din tana cikin gidan bata fito ba,ummi ta ce da shi to Allah ya sa lafiya amma dai kar ya barta ta taho a wannan daren kawai ta kwanta sai goben, dan ita Ummi ta san bayan alhinin rashin sanin inda gentle yake, har da son bincike akan inda gentle din yake, tabbas tasan cewa Ummul tsayawa ta yi dan ta yi magana da dan gaske akan sanin inda gentle yake,kuma ko ita ummin ta gamsu da hakan,shi yasa bata tashi hankalinta da tunanin ko lafiya Ummul din take ba,haka kuma bata nemeta a waya ba.

Lokacin da Ummul ta ji dawowar dan gaske cikin sauri ta mike ta dauki mayafinta da karamar jakarta yar amana,dama tuni ya shirya tsaf jiransa kawai take ya dawo,lokacin da ta fito falon tuni shi kuma ya sauko sanye da jallabiya yana zaune a kan dinning yayi shirin cin abinci, mommy na zaune a gefe tana zuba masa lafiyayyar miyar egusin da ta ji naman rago kamar yayi magana,sai sakwarar da ta bare masa ita a leda tayi wani kyau kamar tuwon madara,Ganin haka yasa Ummul ta koma daki ta bashi lokaci ya gama dibar garar girkinta da kullum sai yayi santinsa kamar a ranar ya fara ci,yau din ma yana fara ci ya dubi mommy da ta ke cin nata a nutse ba tare da wani hayaniya ba domin cin abinci ana magana ba ya daga cikin ladabi ko sunnar Annabi,"wato Hajiya yarinyar nan ta yi masifar iya girki idan ta yi girki kamar a aljanna, saboda dad'i, kullum kuma ta yi sai ka ji shi kamar ranar ka fara cin girkinta"mommy na ji yana ta zubarsa Amma ko daga kai bata yi ba bare yasan tana sauraren sa,harara ya zuba mata tare da yin kwafa, daga nan dole yaja bakinsa yayi shiru bai kuma cewa komai ba har sai da ya gama yayi gyatsa ba tare da yayi wa Allah godiya ba,tashi yayi ya koma falo ya zauna yana cewa"ina zezee take bata fito ta bani labarin yadda su kayi da Dr Bilal ba?"ya yiwa Mommy tambayar yana canja tasha zuwa tashar da yake son kallonsa, kafin mommy ta yi magana sai ga Ummul ta fito, hakan yasa mommy ta fasa bashi amsa saboda ba me dadi zata fada ba a wajensa amma.

Tuni ya fara washe baki kamar wani tababbe,"a'a ikrama ce har zuwa wannan lokaci baki tafi ba,to Allah yasa dai lafiya?"zama ta yi a kasa tare da cewa ba lafiya ba Abba"to me ya faru Allah yasa dai ba wani ne ya taba ki ba"wani irin haushinsa ne ya karu a aranta," hamagon banza wato shi ya ma manta da abinda yayi sai ka ce wanda ya kulle dabba, ko da yake ta fahimci yadda ya dauki gentle dabba ma tafi shi daraja a wajensa,maganarsa ce ta katse mata tunani inda yake cewa"ina jin ki Uwar karama me karamci me ya faru kike zaman jiran dawowata?"cikin jin haushinsa Ummul ta ce"Abba a ina a ka kulle Yaya gentle?"take ya hade fuskarsa kamar bashi ya ke dashare haƙora ba yanzu,ita ma Ummul din kwabe fuska ta yi kana kallon ta kasan cewa ta shiryawa duk abinda dan gaske zai zo mata dashi,gyara zamansa yayi tare da yin gyaran murya kana ya ce "ikram ke yarinya ce shi yasa baki san ciwon kanki ba kuma ana son kwatar miki yanci kina ganin kamar ba a yi miki adalci ba"Abba Ni dai dan Allah ka fada mana inda yake kawai, Kai kanka kasan cewar babu abinda gentle yayi kawai sai dai in akwai wata manufa"wani mugun murmushi Abba yayi kafin ya shafo sankonsa,ya ce"shi ke nan gobe za mu je ki ganshi,na yi miki wannan alfarmar"ba ta ce komai ba,ta mike tare da nufar hanyar fita "Mommy ta yi saurin cewa "Ummul dawo dare yayi ki bari gobe idan Allah ya kaimu sai ki tafi ko?"bata musa ba ta juya ta koma dakinta,dan dama tasan ko ta fita baffa ba zai bari ta tafi ba.

Maida dubansa kan Mommy yayi,tare da cewa "me ya faru dazu ya a kayi tasan me yake faruwa"?kai tsaye Mommy ta gaya masa duk abinda ya faru ba tare da ta rage ko da ɗa ba,shiru yayi zuciyarsa cike da tunani akan abinda mazan nan guda biyu suke nufi da Ummul, dan kuwa Dr Bilal ma abin dubawa ne a cikin wannan sabgar,duba da yadda abubuwa suke ta faruwa tsakaninsa da Ummul din,dole ne ya bincika Dr dan samun karin haske akan abinda yake tunani,tun kafin kwabarsa ta yi ruwa,Mommy ganin yadda ya zurafafa tunani yasa ta sakin Dan murmushi tare da barin wajen.

Ya jima yana sakawa da kwancewa kafin ya saki murmushi saboda ya fara samowa kansa mafita,bashi ya tashi daga falon ba sai wajen karfe daya na dare.

Ummul kuwa duk da kasancewarta ita kadai hakan bai hanata tashi sallar dare ba,saboda abin ya riga ya shiga jikinta(ku koyar da 'ya'yayenku dabi U masu kyau da koyi da sunnar ma aiki Sallallahu alaihi Wasallama,koda suna ƙi a lokacin da kuke koyar da su ,to wata rana zasu yi alfahari da ku ,saboda a bayan idonku zasu kasance masu yin abinda kuka koyar da su me kyau ko akasinsa)sai da ta yi Sallah raka a goma, daga nan ta yi addu'a sosai akan al'amarin gentle Wanda a yanzu shine kawai damuwarta dan har yanzu Ummul bata fara shiga matsalar da take ganin zata roki Allah akansa ba,dama addu'ar ta ɗaya ce zuwa uku,iyayenta da kuma fatan cikawa da imani sai yan uwanta da Al ummar Musulmi,tana gamawa ta fara karatun alkur'ani, sai da gama karance bakara, Sannan ta shafa ta mike,tana jin cikinta na wani irin kukan yunwa, sai a lokacin ta tuna bata ci komai ba tun kafin tasan halin da gentle yake ciki,a hankali ya bude kofar ta fita,cikin sanda take tafiya kamar barauniya har ta isa ga kitchen ɗin,bude bude ta shiga yi har ta samu ragowar sakwarar da suka bari a kula,faranti ta dauko ta saka guda daya tana kokarin zuba miya ta ji kamar motsi da magana a ta bayan kitchen din, duk da cewa ta ji tsoro amma hakan bai sa ta kasa lallabawa zuwa bakin window kitchen din ba,a hankali ta ɗan janye kofar ta leka idonta guda ɗaya,ga mamakinta Abba ta gani da waya a kunnesa yana ta kuskus,barin jikin window ta yi ta nufi kofar kitchen wadda zata maida ita can bayan inda Abba yake,a bude ta sameta wanda hakan ya nuna mata cewa tanan ya fita,dan haka bata sha wahala ba wajen fita,cikin sanda ta ke tafiya har ta isa bayan kujerar duwatsun da ke girke a wajen,ta inda zata iya jin abinda yake fada,kirjinta dukan tara tara yake yi akan abinda take yin, to amma haka kawai take son jin abinda abban yake fada dan tasan ba alkhairi ne zai fito dashi cikin wannan daren dan kawai yayi waya ba.

"Ka gane ko kurege na yi magana da inspector lawan,da kun je zai bude muku cell din, da kun shiga ku yi masa dan banzan duka Sannan ku yi masa kashedi akan yarinyar nan idan har ya sake ya kara kusanta kansa da ita to wallahi zan ɓatar dashi a duniyar gaba daya ta yanda babu wanda zai kuma jin duriyarsa"bata ji me aka ce masa daga can bangaren ba,kawai dai taga ya kashe wayar Sannan ya kuma danna wani kiran,jim kadan aka daga,kai tsaye Abba ya fara maganarsa cikin kasa kasa da murya,"jangul maza maza ina so ka sa min ido akan Dr Bilal, na baka kwana biyu ka gano min idan yana son wata yarinya daban a gefe,saboda na fara ganin take takensa, in na cikin fargaba bana so ya fasa auren zezee saboda duk wani burina yana kan auren domin ta hanyar auren ne kawai zan samu na cika burina"dan shiri yayi kafin ya ce "yauwa ina sauraren ka"daga haka ya kashe wayar,har yayi gaba zai bar wajen sai kuma ya dakata saboda jin alamun motsi a bayansa,juyawa yayi yana yan dube dube kafin kuma ya shige ta hanyar da ya fito.

Zaro ido Ummul ta yi tare da dafe kirjinta saboda ganin Abba ya maida kofar kitchen din ya rufe ta ciki,"na shiga uku ya zan yi idan Abba ya ganni anan dole zai gane nice na shigo na ji abinda yake faɗa"ta fada kuka na shirin kwace mata,dama ga tashin hankalin abinda taji abban na fada a yiwa gentle din, wannan wane irin mugun mutum ne, in Allah ya yarda ALLAH ba zai bashi damar cutar da bawan Allah ba"tana gama fadin haka ta mike ta nufi kofar ta gani ko da dabarar da zata iya yi ta shiga,hamdala ta yi wa Ubangiji saboda ganin ashe bai ja jamlock din ya ahiga ba,dan haka cikin sanda ta bude kofar ta shige, ba tare da ta tsaya daukar abincin da ta zuba ba ta ta tafiyarta daki ta maida kofa ta kulle ta zube a wajen tana kukan dukan da za a yiwa gentle,har da runtse ido da sosai ta ke jin zafin dukan a cikin jikinta kamar ita ake yiwa.

********

Duk da cewa bata samu yin bacci ba, amma hakan bai sata fita da sanyin safiyar ba,cikin kankanin lokaci ta gama duk aiyukanta ta dawo ta yi wanka ta sanya kayanta na jiya,wanda dama tunasuba ta wanke su ya shanya,karfe takwas da rabi tuni ta gama komai sai zaman jiran fitowarsu,iya gakuwa Ummul ta kagu ta je ta ga halin da gentle yake ciki,duk ta yi wani irin kamar ba Ummul din da muka sani ba,shigowar Mommy yasa ta mikewa tare da gaisheta cikin ladabi,kaya mommy ta mika mata tana cewa"karbi ki cire na jikinki sai ki fito ku tafi kan Sannan alhajin ya gama karyawa"Godiya ta yiwa Mommy , Mommy tana fita ta sanya doguwar rigar leshin da dama tamkar dan ita aka dinka,ta san daya daga cikin kayan zezee ne ta dauko mata,"Allah Sarki mommy da a ce halinta zezee ta dauko da yanzu bata zo tana wahala akan soyayya ba...

Yadda Ummul ta yi matukar kyau a cikin kayan yasa Abba jin wani irin kishi kamar ya hanata zuwa wajen wancan dan iskan,to amma yasan uwar rigimar ba zata yadda ba,dan haka sai ya hadiye abinsa, amma bai tashi sun tafi ba har sai da ya tabbatar da cewa Ummul ta shaƙa har tana daf da fashewa,dan fuskarta kawai zaka kalla ka tabbatar da cewa a kan gwiwa take kiris take jira a taɓota.

Baffa ko da wasa bai nuna son zuwa ba,saboda kar ya batawa Abba rai, Ummul kamar zata fasa ihu lokacin da Abba ya umarceta da ta shiga baya su zauna tare,banza ta yi kamar bata ji abinda ya ce ba,ta yi shigewarta kujerar me zaman banza,saboda idanun driver da baffa yasa Abba hakura amma shi kam ba haka ya so ba,so yayi ace tana gefensa yana jin kashinta ko zai samu sassauci daga azabar radadin sonta da ALLAH ya saka masa,

Motar tana tsayawa a harabar devision din driver yayi saurin fita dan budewa Alhaji dan gaske mota, Ummul kuma na kokarin fita,amma sai ta ji Muryar Abba kamar daga sama yana cewa"duk abinda kika fada sabanin abinda na fada to tabbas zan aiwatar da abinda kunnuwanki suka jiye miki a daren jiya akan gentle,kuma na san daga jiya zuwa yau kin fahimci cewa zan aikata fiye da abinda kika klji na fada"daga haka ya fito daga motar yana baza babbar riga,kasa fita Ummul ta yi tana mai jin jina karfin shu'umanci ko ta ce zalunci irin na Alhaji dan gaske,ashe jiya ya san cewa ita ce ta kasa labe?Amma yayi shiru kamar bai fahimci komai ba,ashe yayi tanadi ne domin yayi mata barazana'ko ba zaki fito ba a maida shi ya ci gaba da zama a cell din?"ta ji Muryar Alhaji kanta,wanda hakan yasa ta fitowa jikinta a sanyaye kamar wadda kwai ya fashewa,bayansa ta bi tana tunanin ta yadda zata kufcewa tarkon Alhaji dan gaske,suna shiga kai tsaye office din dpo suka shiga, Ummul gaisuwa ma kasa yi masa ta yi saboda tsananin haushinsu da take ji, dan dukkansu bakin su daya,hakan yasa ta tsaya daga can gefe ta zubawa kofar shigowa ido,, saboda jin dpo ya ce a shigo da gentle.

Ana turo kofar ta ji kirjinta ya buga,ai bata san lokacin da ta tafi da wani irin gudu ba,kai tsaye ta hankade dan sandan da ya yi mata katanga da ganin gentle da ke bayansa,wata irin mahaukaciyar runguma ta kai masa ba tare da ta yi duba da dattin da yake jikinsa ba,

"Innalillahi wa inna ilaihi raji un"Alhaji dan gaske ya fada yana cire hularsa yana mai yin fifita da ita .........✍️

***

💕GIDAN ƳAN ƘARYA💕

By

FATIMA Y ADAM......

Littattafan marubuciyar.

KUDIRAR ALLAH

KADDARATA SANADIN HASKE

ƁOYAYYIYAR RAIHAN

ƳAR GIDAN YARBAWA

MATAR ƊAN BIRNI

And

GIDAN ƳAN ƘARYA....