Pg21
Tsaye yake gaban mirror yana sharce kansa da yake wani irin kyalli baki sidik da shi,gefe daya kuma yana duba tsararren agogon da yake sakale a fatar hannunsa da gashi suka kwanta gwanin sha'awa,cikin dan gaggawa ya karasa shiryawa,saboda yasan baba Yana can yana jiransa,cikin kankanin lokaci dakin ya cika da ƙamshin Dr Bilal,Yana fitowa daga dakin kasa ya nufa bangaren babansa,yanayi yana kallon agogon hannunsa saboda yana da fasinja zuwa katar karfe uku na rana,daidai lokacin ya karaso bangaren bakin na mahaifinsa, tare da yin sallama cikin nutsuwa da fuskewa irin tasa,duk da cewa bai san da zuwan Abban zezee baa ,Amma hakan bai sa ya nuna wani mamaki ko alamar wani abu a ransa ba,zama yayi kasan kafafun baban nasa yana kama ƙafarsa yana dan matsa masa ita,kafin ya mika gaisuwarsa cikin soyayya da biyayya,shi din ma Alhaji Ahmed cikin kulawa da kauna ya amsawa dan nasa,kafin nan ya juya ya gaida abban zezee,cikin yar diriricewa abban zezee ya amsa, saboda tun shigowar Dr Bilal din ya fada tunani da fargaban abinda zai kasance a wannan zaman.
Alhaji Ahmed ne ya katse tunaninsa ta hanyar yin gyaran murya kafin ya fara magana da cewa,bilalu tun dasu nan zaman jiran ka muke kamar yadda ka sani,amma ban sanar da kai dalilin jiran da kuma wanda ya zo ba,to gashi nan mahaifin yarinyar da zaka aura ne yake son a tsaida lokaci, Ni kuma ta bangarena bani da wata damuwa hasalima na fi kowa son wannan lokaci ya kara so,to amma dan fita hakki shi yasa nace kaima kazo ko kana da wani lokaci naka da ka shirya",shiru na kusan sakon goma kafin ya dago Kai ya kalli abban zezee da kirjinsa yake dukan tara tara, Sannan ya kawar da kansa yana magana cikin yanayin maganarsa ta kamar baya son yi fuskarsa babu wani annuri,ya ce"baba a Dan dakata ba yanzu ba sai mun gama fahimtar juna,baba yaushe muka fara zama duka fa zama biyu mu kayi da har za a fara maganar aure Ni a ganina yayi gaggawa kasan kuma aiki ne na shedan".
Shuru falon ya dauka baba yana dan nazarin maganar Dr ,kafin ya san saki numfashi yana cewa"to Alhaji Salisu kaji batun da dan naka yake,ina ga kuma ya kamata mu basu lokaci su gama fahimtar juna,kadan shi aure zaman lafiyarsa fahimtar juna ne,dan haka ku basu wata daya daga nan ba zan kuma sauraron wani jinkiri daga gareshi ba,sai kawai mu yi abinda ya dace"to to to shike nan ranka ya dade ai kamar yau ne Allah ya nuna mana ya kaiku lokacin"alhaji dan gaske ya fada yana jin kamar ya rusa ihu da wannan hukunci na Dr Bilal,to amma ba damuwa yasan duk akan me yake don jinkirta auren,dan haka sai ɓullo masa ta inda bai zata ba,tashi yayi ya musu sallama ya tafi yana ci gaba da saka hanyar da zai bi ya raba Ummul da Dr, dan a yanzu baya ta gentle dan bai daukesa wata tsiya ko abin barazana ga cikar burinsa ba.
Dr Bilal kuwa sun jima suna tattaunawa ta tsakanin da da mahaifi kafin ya tashi ya nufi cikin gidan wajen Mahaifiyarsa,a inda ya samu kausar kanwarsa ta biyu ta zo gidan tare da yaranta guda biyu,suna ganinsa suka rungumeshi,ɗaga su yayi ɗaya bayan ɗaya ya cillasu sama ya ajiye tare da shafa kansu fuskarsa da tattausan murmushin da su kadai suke ganin irinsa, dan hakika Dr yana da son yara matuka shi yasa yake ji da ƴaƴan kannennsa kamar ya'yan da ya haifa,daga nan ya je ya durkusa a gaban hajiyarsa tare da dora kansa akan cinyarta,shafa kansa ta yi tana amsa gaisuwarsa cikin kauna, kausar ma gaishesa ta yi tana cewa"yaya hala jirgi zaka shiga na ganka da kayan tuƙi a maimakon kayan asibiti?"harara ya ɗan watsa mata kafin ya ce ke ba zaki daina min tambayar rainin hankali ba ko?"dariya ta yi tana cewa"wallahi yaya ina son na ga kana magana ne shi yasa"Hajiya ta ce "kina so dai ki sashi ciwon kai"tashi yayi yana cewa "rabu da ita Hajiya,Ni zan wuce amma sai karfe shida na safiyar gobe zamu juyo"to Allah ya bada Sa'a ya kai ku lafiya ya dawo da ku lafiya Allah Ya tsare ku daga sharrin karfe ya baku nasara akan dukkan abin da kuka sa a gaba na alkhairi"shafa kansa yayi yana dan fesar da huci ta bakinsa kafin ya ce"Amin hajiyata Allah ya saka da lkhairi ya kara girma me amfani"Amin suka amsa ita da kausar,har bakin mota suka rakoshi ita da kausar da yaran kausar,suna masa addu'ar dawowa lafiya, Sweet ya dauko a cikin motar ya bawa yaran kausar, take suka juya suna tsallan murna,basu koma ciki ba har sai da suka ga fitarsa a farfajiyar gidan Sannan suka koma ciki Hajiya na ci gaba da yi musu addu'ar nasara a rayuwar duniya da lahira.
******
A wani kayataccen wajen cin abinci dake cikin anguwar Nassarawa kuwa zezee ce tare da bely suna magana akan yadda za su yi, Ummul ta shiga hannun bely ba tare da ta san alakarsu da zeze ba,dan bely bata zuwa gidansu zezee sosai saboda Mommy bata sonta dan kiri kiri ta fito ta nuna mata bata son tana zuwa gidanta ko hulda da yarta, wannan dalilin ne yasa bata zuwa gidan shi yasa Ummul bata san bely ba,zamansu da kusan awa daya sai ga mufty shi da wani abokinsa sun zo yin kwari da burgar da ba a Isa ba,tunda suka shigo hankalin bely yake kansa saboda yadda ya tafi da tunaninta,zungurarta zezee ta yi ,tana cewa "ya dai ina hankalinki ya tafi ne?"ajiyar zuciya bely ta sauke kana ta maida dubanta kan zezee tana cewa"wallahi zezee wancan gayen ne ya tafi da tunanina"kallon wajen zezee ta yi Sannan ta dubi belyn tana sakin tsaki da cewa,"wancan dan uwan Ummul ne gayyar YAN KARYA kina zaune a gurin nan zaki ga yadda zasu kare da masu gurin"tashi bely ta yi zata je inda su mufty suke zaune,da sauri zezee ta rike hannunta tana cewa "ke wace irin sakarya ce wannan ai zubda mutunci ne"zezee wannan ba zubda mutunci ba ne indai wannan zubda mutunci ne a wajenki,to ke sai a ce kin rako mata ne akan zubar da darajarki da kike a wajen Dr Bilal,dan haka ki barni na tunkaresa kai tsaye, kuma ke banda abinki ai wannan dama ce a garemu ta yadda za mu janyo Ummul jikinmu, ina ce yanzu maganar da muke yi ke nan?"zezee da yi matukar shaka akan maganganun da bely ta gaya mata ta dake ta hadiye tunda ita take nema,ta ce"ta yaya hakan zata faru?"tabe baki bely ta yi kafin ta ce"bari na hakura a yanzu kafin na yi tunanin da irin suffar da ya kamata na je musu dan ya aminta dani ta hakanne zan samu shiga wajen yan uwansa,kinga kenan zamu jefi tsuntsu biyu da dutse daya,ni zan samu Abinda nake so a wajensa ke kuma zaki samu abin da kike so ta bangaren Ummul".
Dan jim zezee ta yi kafin ta ce"to ai in dai wannan ne ba zai yi wuya ba,ba sai kun wani canja masa ba,kudi kawai zaki sakar masa yayi facakarsa shi kenan kin kama zuciyarsa"girgiza kai bely ta yi Sannan ta ce"ba iya wannan ka dai ba zezee idan baka iya kama barawo ba to shi zai kamaka,dole na fara bibiyarsa dan sanin wasu abubuwan da ya ke so a wajen mace dan ya so ni da zuciya daya, saboda idan na biyo masa ta hanyar kudina to su zai so kawai kuma ba zai taba aminta sani ba saboda bai so ni dan halina ba,kin san duk iskancin da namiji yana so ya auri mace ta gari, shi yasa dole sai na ari halin da ba nawa ba,kuma kema kin san haka tunda gashi, kina son lalata tarbiyyar Ummul saboda ki nesantata da Dr Bilal".
Jinjina Kai zezee ta yi cikin gamsuwa da bayanan bely,abinci suka fara ci sai dai gaba Daya hankalin bely Yana kan duk Wani motsi na mufty.
Mufty kuwa da Bai san da zaman su bely ba hankalinsa kwance yake baza capacity nsa,sai faman dage kafada yake,abokinnasa ne ya kallesa tare da cewa"mufty ya kamata mu yi Wani abu tun kafin mutuncinmu ya bare,kaga dai kowa ka kalli kan teburinsa za ka ga abinci da kaza a gabansa Amma mu tunda muka shigo ba abinda muka sa aka kawo mana sai baza ido muke kamar bera yaga mage"kifta masa ido mufty yayi wai ya dinga magana a hankali kar Wani yaji,sai kuma ya ce"yanzu nawa ne a jikinka mu samu mu kankarowa kanmu mutunci ka ga dai mun hayo motar babandi kuma kasan ba mutunci garesa ba,idan bamu cika masa kudinsa ba zai iya yaga mu"alkasim ya ce"ni dai akwai dubu biyar a jikina kuma suma na rigima ne idan kasan zaka hada ka biya na fito da su"dan Jim mufty yayi kafin ya ce"rigima ubanwa ta kashe dan haka ba ita ta dameni ba kankantar kudinne ya dameni,saboda ba zasu isa a kawo mana kowa faranti Daya da ruwa da lemo ba"alkasim ya ce mu cika ragowar da baki,bari ka gani"sai kawaii ya sa hannu ya yafito ma aikacin gurin ,cikin sauri kuwa ya karaso wajensu,dan kallon gefen ido mufty yayi masa kafin ya ce"ka kawo mana chips da chicken kowa Daya Daya"cikin rawar jiki yaron ya amsa tare da juyawa,sai da mufty y bari ya kusa karasawa wajen sannan ya daga mirya Yana cewa"ba ka ji ba"jiyowa yaron yayi yana sauraren mufty da y ci gaba da cewa,ka kawo plet Daya ya isa shi wannan ba zai ci komai ba kasan bakin turan nan wannan basu cika burgesu ba"ok sir yaron ya fada yana ci gaba da tafiya"
"You see" zezee ta fada tana kallon bely da take ta sakin murmushi,dan kaf a rayuwarta bata taba ganin saurayin da ya burgeta kamar mufty ba,yanayin karyarsa ya banbanta da na sauran yan karya,"wallahi gayen nan ya burgeni zan so ganin ire_iren wannan kalar wasan nasa abin burgewa"tsaki zezee ta yi tana mai share bakinta da tissue tare da mikewa tsaye,daukar bag dinta ta yi tana cewa"aikin banza banga abin burgewa a karya ba,idan zaki tashi mu tafiya ki tashi,idan kuma rakiyar asara zaki yi kinga tafiya ta sai kin taho"zezee ta fada tana nufar hanyar ficewa daga gurin,dole bely ta bi bayanta ba Dan ranta yaso ba sai dan bata zo da mota ba,tana tafiya tana waiwayen su mufty da sai a lokacin ya dan lura da ita,bai Wani maida hankalin a kanta ba,ya ci gaba da sauraren masifr da alkasim yake masa kasa kasa saboda ya ce baya cin abincin Wanda hakan yake nufin ko an kawo abincin zai zauna yasawa mufty ido ne kawai yana ci,dariya mufty yayi kasa kasa kana ya ce"to ko Banda abinka mutunci f na kankaro maka fa"bana bukatar mutuncin mutuncin yaci abun ubansa"alkasim ya fada a fusace,a daidai lokacin aka kawo lafiyayyan chips and chicken da ruwa aka ajiye musu,cikin yanga mufty ya fara ci Yana Wani kalar basaja dan kar ace babu a house,yayin da alkasim yake cike da bakin ciki da takaicin abinda mufty yayi masa,Dan kuwa ba karamar yunwa yake ji ba,har gara mufty din yasan idan ya koma gida zai samu an ajiye masa abinci shi kuwa da uwarsa bata gidan ba Wanda zai tuna da shi sai idan Yana zaune aka raba,shi yasa ya tanadi muguntar da zai yiwa mufty Dan muddin bai ci abincin nan ba to wallahi shima ba zai bada kudin ba.
Kamar mufty yasan abinda alkasim yake shirya aransa sai kawai ya ajiye cinyar kazar da yake figa ya kira yaron,yana zuwa ya ce masa"nawa ne Bill dinmu?"yaron ya ce"dubu goma sha daya"what?"mufty ya fada yana zare ido dan shi kudin jikinsa ko dubu uku ba su kai ba, yana shirin yin magana sai ga daya daga cikin ma'aikatan gurin hannunsa rike da raset, yana zuwa wajen ya mikawa mufty resit din, yana cewa,"ga resit ɗinku yallabai an riga an biya kudin"duk da cewa mufty yana cikin mamakin lamarin sai da ya saki ajiyar zuciyar samun mafita,kafin nan ya kuma gyara zamansa ya ci gaba da cin banza,Sam bai nuna musu komai ba saboda kar su rainashi,ko alkasim ya ji dadi ko ba komai kudinsa sun tsira ko ya ce ya tsira daga shiga rigima,ma aikatan suna barin wajen alkasim ya shiga taka kafar mufty ta kasan teburin tare da yi masa magiya da ido akan ya rage masa ko da kazar ce ya dandana saboda an dade ba a hadu ba,amma mufty yayi kunnen uwar shegu dashi,to da farko ma da yake tunanin za a biya da kudin alkasim din bai yi niyyar rage masa ba,bare kuma yanzu da ya tabbatar gashin kansa yake ci,mufty bai rage komai ba sakamakon yasan hakan ba wata damuwa ba ce a irin wannan wajen,goge bakinsa yayi Sannan ya tashi yana cewa "to oga ta shi mu tafi kar ka rasa jirgi dan naga lokaci yana kurewa"wata banzar harara alkasim ya watsa masa tare da yin kwafa ya mike yana ji kamar ya shake wuyan mufty din duk abinda ya ci su dawo,mufty kuwa in banda dariyar keta babu abinda yakewa alkasim a ransa,da sauri wani ma 'aikacin daban ya biyo bayansu da lada a hannunsa wadda ke dauke da tambarin wajen,mika musu yayi kawai ya juya,mufty ya kalli ledar da ya tabbatar da cewa take away ne a ciki Sannan ya kalli alkasim yana cewa"gaskiya Yaron nan kai dan baiwa ne kaga har take away aka hada mana,hakan yana nufin zaka maida mugun yawu,dan haka yi sauri ka maida maganganun da ka rike kana jira mu fito ka fesar min"fuzge ledar alkasim yayi yana cewa"wallahi baka isa ba wannan dai hakkina ne dan haka sai yadda na yi"dariya mufty yayi yana cewa to ban da abinka ni da na ci na koshi me kuma zan yi da wannan,kawai dai shawarar da zan baka ka yi saurin cinyewa tun kafin cikina ya sarara,a haka suka fita suka hau motar opay dinsu suna ci gaba da yar canki cankin wanda ya biya musu kudin abinci.
*****
Tun da ya dawo office yake nazari da kaiwa da kawowa akan wannan babban lamarin da yake shirin tunkaro shi,lokaci daya wani tunani ya fado masa,take ya dibi komai nasa ya bar officer zuwa gida,baffa na bude masa kofa ko daidaita fakin bai yi ba ya kashe motar tare da fitowa yana cewa baffa ya idan ya gama rufe gidan ya biyo shi zuwa wajen hutawarsa za su yi magana,cikin sauri baffa ya rufe gidan kana ya bi bayan Alhaji dan gaske jikin sa na bari da fatan Allah yasa ba Ummul ce ta dauko masa magana ba,yana shiga Alhaji dan gaske ya yi masa umarnin da ya zauna a saman kujera a maimakon kasan da ya zauna,a darare baffa ya zauna yana fatan jin alheri daga bakin Alhaji dan gaske,sai da Alhaji dan gaske yayi gyaran murya Sannan ya dubi baffa na wasu yan dakiku kafin ya fara magana da cewa"baffa na kira ka ne dan na roke ka wata alfarma idan kuma baka yarda ba to kai tsaye zai iya zama barazana ga rayuwar ahlinka"a halin yanzu kuwa tsoron baffa ya gama bai yana saboda jin kalamin da Ubangidan nasa yake masa,Alhaji dan gaske ya dubi baffa da idanunsa da suka sauya kala saboda halin bakin ciki da takaicin da yake ciki ya ce"so nake ka bani auren yarka Ummul ikram,kuma a yau nake so a Daura auren"wata irin zabura baffa yayi sai gashi a tsaye dan har ga Allah bai taba tunanin abinda Alhaji dan gaske zai ce masa kenan ba,zufa ce ta fara hado masa yasa hannu yana sharewa, yayin da miyan bakinsa ya kafe gaba daya.
Muryar Alhaji dan gaske yaji a tsakiyar kansa yana cewa"buzu bafa dole na yi maka akan sai ka amince cikin lallama ba,idan baka amince ba to zaka rasa ahlinka gaba daya"ya fada yana kunna masa wayarsa da a lokaci daya aka nuno masa video da wasu matasa su biyu a kofar gidansa hannunsu dauke da galan din fetur da wata yar karamar lighter,da alama yan kunar bakin wake ne umarni kawai suke jira,take hankalin baffa ya nemi gushewa saboda tsananin firgita da wannan Al amarin da ko a mafarki bai taba kawo shi cikin rayuwarsa ba..........
Zahra .......✍️
***
💕GIDAN ƳAN ƘARYA💕
By
FATIMA Y ADAM......
Littattafan marubuciyar.
KUDIRAR ALLAH
KADDARATA SANADIN HASKE
ƁOYAYYIYAR RAIHAN
ƳAR GIDAN YARBAWA
MATAR ƊAN BIRNI
And
GIDAN ƳAN ƘARYA....