GIDAN YAN KARYA

Pg22

by @zahrawriter12

Ba zan iya misalta muku irin tashin hankalin da baffa ya shiga ba,dubansa baffa ya yi fuskarsa dauke da murmushin mugunta ya ce"yardar ka ita ce fansar rayuwar ahlinka,dan haka zabi ya rage naka"durkushewa baffa yayi a gabansa tare da hade hannunsa guda biyu, kana cikin rawar Muryar da take daf da fashewa da kuka ya ce"dan Allah Alhaji ka yi min rai karka kashe min iyalina sannan karka gurbata min rayuwar yata daya mace da nake matukar so a rayuwata, wallahi idan Ummul ta ji kai zata aura zan iya rasata saboda yarinya ce bata kai munzalin fara Fuskantar irin wannan rayuwar ba"cikin tsawa baffa ya ce"dakata malam har ni zaka duba kace min kana son 'yarka bata kai munzali ba,to me ye a cikin auren nawa da har zaka ce bata kai munzalin rayuwar ba,kar ka damu baffa ina son ikram dan haka ba zan taɓa bari ta shiga matsala ba,idan kuma har kana ganin ba zaka amince ba,to wallahi in dai ina numfashi babu wanda ya isa ya auri Ummul dan haka gwara na kashe ta kowa ya rasa"da sauri baffa ya rike kafar Alhaji dan gaske cikin kuka yake cewa"na amince Alhaji amma dan Allah ka yi min alfarma ba yau ba, ka bani sati daya dan fuskantar Ummul ta karbi auren cikin dadin rai"wata mahaukaciyar dariya Alhaji dan gaske yayi,kafin ya sa hannu ya dago baffa da ga durkushen da yayi, sannan ya ce"idan kuma ta ki yarda fa?"cikin rawar baki baffa ya ce "shi kenan sai a daura haka ko da bata so"yauwa yanzu na ji batu,amma gaskiya sati daya yayi yawa sai dai kwana uku,saboda nima akwai ƙurar da ta taso nake son kwantar da ita tun kafin ta lullube min idanuwa"baffa ya ce"shike nan amma dole zuwa jibi Alhamis ke nan zanje can gida agadex domin sanarwa da yan uwa"wannan kuma ruwanka"Alhaji dan gaske ya fada yana kara wayarsa a kunne,"ku matsa daga kofar gidan amma ku dinga kasancewa a kusa da zarar ya sauya ta a yi umarni kawai zan baku"daga haka ya kashe wayar, hakan yasa baffa ya ɗan saki ajiyar zuciya tare da ficewa daga wajen yana jin wata irin muguwar tsanar Alhaji dan gaske.

Tunda baffa ya dawo bakin aiki yake sakawa da warwarewa gaba daya ya kasa samun natsuwa ,gani yake kamar zai koma gida ya tarar da iyalansa sun babbake,sai magriba sannan dayan me gadin yazo ya karbi aikin dan dama yau ya cika kwana ukunsa na aiki,cikin sauri ya tattara abinda zai tattara ya tafi gida.

Ajiyar zuciya ya sauke saboda samunsu da yayi gaba daya sun vaje a tsakar gida suna cin danbun shinkafar da Ummul ta yi musu da kanta,ko da suka yi masa sannu da zuwa amsawa ya dinga yi cikin kokarin boye damuwarsa,sai dai tuni Ummi ta gano shi wanda hakan yasa ta kai kasa abincinsa daki dan kaucewa tuhumar yaran idan har damuwarsa ta kasa boyuwa a garesu,ko da ta kai masa abincin tasa shi yayi a gaba yana kallo ya kasa kai ko koma daya bakinsa,ganin haka yasa Ummi ta shiga lallabashi da bashi baki ta hanyar nasiha me ratsa zuciya wanda hakan yayi sanadin dawowarsa cikin hankalinsa,sai da ya ɗan ci abincin sannan ya fara bata labarin duk abinda ya faru bayan ya tabbatar da cewa duka yaran basa kusa bare wani ya iya jinsu.

Duk da cewa hankalin Ummi ya tashi amma sai ta dake ta shiga kwantar masa da hankali, da tuna masa cewa Allah da yana nan,kuma ba wani abu da ya isa samun bawa face da yardar Ubangiji,dan haka ya sa a ransa cewa duk abinda ya samesu daga Allah ne ,babu tsumi babu dabara dole abin da ya ƙaddara musu shi ne zai faru,kawai su dukufa wajen kai masa kukansu cikin ikonsa zai kawo musu mafita ta inda basu taba zato ba,da kalaman Ummi baffa ya samu natsuwa har ya yi walwala.

Aiko a cikin wannan dare ko dan baccin da suke yi su tashi yau din ba su yi ba gaba dayansa raya shi su kayi wajen mikawa Allah kokensu.

Washe gari misalin ƙarfe hudu na yamma, baffa ya damu Alhaji dan gaske ya sanar masa da cewa,yana rokon alfarma kar Ummul ta san da wannan auren, saboda yayi shawara yaga cewa idan har ya sanar da ita to ba zata taba amincewa ba,karshe ma zata iya guduwa ta bar gidan, shi yasa ya yanke hukuncin nan"sosai Alhaji dan gaske ya gamsu da wannan shawara ta baffa dan haka ya ce ya je kawai kar ya damu da wannan shima hakan yafi masa idan ya so nan da dan wani lokaci sai a sanar da ita".

Saboda addu'a da mikawa Allah assamadu dukkan lamura yasa hankalin baffa da ummi ya kwanta tare da jiran yin Allah.

A bangaren bely kuwa a cikin kwana ɗaya duk ta bi ta sukurkuce, neman hanyar haduwa da mufty kawai take,dan sam ta ji ba zata iya daukar wani dogon lokaci ba tare da ta ganta tare dashi ba,duk da cewa har yanzu ta kasa tantance irin son da take masa,na sha'awa ne koko na aure ne?to ko ma dai wane iri ne a yanzu babu abinda take bukata da ya wuce kusanci da shi,shiryawa tayi ta fice daga gidan ko tana da rabon ganinsa.

Duk abinda ya ke faruwa Ummul bata san komai ba,hasalima ta ci gaba da zuwa aikin ta gidan Alhaji dan gaske ,duk da cewa bata so komawar ba, ta koma ne saboda umarnin baffanta.

Yau tana dawowa ta samu gentle a cikin gidansu zaune kan taburma yana cin burabuskon tsakin da Ummi ta yi,turus ta yi tana kallonsa saboda yadda yayi din ya bata mamaki,kafin kuma a hankali ta shige dakinsu tana waiwayensa,tana ajiye jakarta Ummi tana biyo bayanta,"ummi me ya kawo wannan Sarkin shurun yau har da wani zama?"wajenki ya zo sai ki fita ki sameshi"amsar da Ummi ta bata kenan ta samu waje ta zauna,gunguni ta shiga yi kafin ta fice daga dakin,samunsa ta yi har ya gama cin abincin yana zaune shiru kamar wani dan kurma,kujera taja ta zauna tana cewa"ina kwana"fasasshen agogon hannunsa ya kalla sai kuma ya dago kansa ya kalleta,yana mai nuna mata lokaci,kawar da kanta ta yi tana cewa"au ina yini"bai tanka mata ba,wanda hakan ya bata haushi ta dubesa tana cewa "baka da abin cewa ne?"babu" ya fada yana mikewa ya zura wasu kodaddun takalmansa,tashi ta yi tare da binsa tana cewa"ummi ce fa ta ce min kana nemana kuma nazo ka yi min shiru"daidai nan suka karaso zauren gidan tana biye dashi a baya,bata san cewa ya juyo ba wanda hakan yayi sanadin buguwar kanta a kirjinsa,da sauri ta dafe goshinta shi kuma ya dora tafin hannunsa akan kirjinsa idanunsa suna wani lumshewa da budewa a lokaci guda,juyawa ta yi zata koma amma sai taji ya riko hannunta,hakan yasa ta tsaya amma bata juyo ba basoba yadda take jin haushinsa akan wannan wulakancin nasa,a hankali ya shiga janyo hannunta har ya matso da ita daf da shi,har suna iya jin hucin numfashin juna,kafin cikin wani irin yanayi da murya me dan sanyi da kauri ya ce"kina son sanin abinda ya kawo ni?"kawar da kanta ta yi tana gunguni zuciyarta babu abinda take sai bugu saboda tsananin kusancinta da shi,bakinta kuwa ya kasa furta komai sai mis miss da take yi dashi,uhm amsa "ya fada yana matse hannunta da dan karfi cikin nasa,aiko abinka da me jiran kiris take ta fara hawaye, dan dama dakiya kawai take yi,saboda Sam bata iya jure shariyarsa jin zuciyarta take ta mata nauyi,shi yasa duk lokacin da yayi mata hakan bata samun kanta har sai ta zubda hawayenta,ganin hawayenta yasa shi ɗan fesar da huci me dumi wanda ya sauka akan fuskarta,rufe idanunta ta yi tana kokarin kwace hannunta, kamar daga sama ta ji saukar muryarsa a tsakiyar dodon kunneta har labbansa na taba fatar kunnenta,"zaki iya auren talaka me gyaran takalmi?"da wani irin sauri ta bude idanunta,wanda basu tashi sauka a ko ina ba sai tsakiyar nasa idanun da suke kallonta direct babu ko kiftawa,rashin abin yi yasa ta kwace hannunta tare da artawa da gudu zuwa cikin gida,binta yayi da ido kafin ya saki wani shegen malalacin murmushin da da a gaban wata yayi shi babu abinda zai hanata sumewa saboda tsananin kyawun da yayi masa duk da irin bakin fuskarsa kuwa.

Da gudu ta fada dakin ummin tare da fadawa saman gadonta ,ta dauki fulo ta shigar da fuskarta ciki idanunta a runtse,suna ci gaba da haska mata gentle da maimaita mata furucinsa a cikin kunenta,ummi kuwa sake da baki ta bi Ummul din da kallo,kafin ta ɗan tabe baki tana ci gaba da aikinta.

Ranar Ummul tamkar wata zautacciya haka ta koma, itaka dai zaka ga tana murmushi daga karshe kuma ta sa hannu ta rufe fuskarta tana mai jin kunyar kanta da abinda gentle ya fada mata, duk da cewa bata san me take ji akansa ba,ba tasan wane irin yanayi ne yanayin da take ji ba,abinda kawai ta sani shine ta kasance cikin farin ciki ta kuma kwana cikin farin ciki,tana kuma tunanin in dai zata rayu da gentle to za ta kasance cikin farin ciki muddin rayuwarta.

Washe gari ana ya gobe daurin auren da ba wanda ya san dashi,Alhaji dan gaske ya fito cikin shirinsa na office ya samu tuni Ummul ta gama hada musu break fast,yau duk sonsa da girkin Ummul kasa zama yayi saboda dokin zai je ya sanar da Alhaji Ahmed dan itopia maganar auren, kuma yana fata ya samu Dr Bilal a wajensa, saboda sakon nasa ne,kuma yana da tabbacin irin wannan lokacin Dr ya fi zuwa wajen babannasa wato lokacin da yake fita aiki,ko wajen da mommy take bai kalla ba dan itama ya ga take takenta kwana biyu kamar da wani abu a ranta,kawowa dai ya rabu da ita ne saboda yanzu ba ta tata yake ba,yana da abinda yafi ta muhimmanci,itama mommyn bata damu ba saboda a yan kwanakin komai dawo mata sabo yake ji take kamar yanzu komai yake faruwa shi yasa ko ido bata son ta bude ta ganshi a gabanta,hakan yasa itama tabi bayansa da hararar da bata rage mata komai daga irin radadin da take ji.

Yana fita ya shiga Mota bai tsaya a ko ina ba,sai main house din DAN ITOPIA,ya taki sa a kuwa dan Dr Bilal bai dade da shiga ba, aka sanarwa da baba zuwan Alhaji dan gaske, kai tsaye ya bada umarni da cewa a barsa ya shigo,kamar yadda ya saba yana zuwa ya zube yana kwasar gaisuwa cikin girmamawa da kankan da kai,a shekare Dr ya gaida sa, daga nan Alhaji dan gaske ya fara magana kamar haka"yallabai dama zuwa na yi na sanar da kai maganar daurin aurena gobe in Allah ya kai mu bayan an yi sallar juma'a a masallacin sheik malam Ja'afar"to to masha Allah aure haka ba sanarwa"cewar Alhaji Ahmed kenan"Alhaji dan gaske ya wani kwantar da murya cikin neman afuwa ya ce"ayi min gafara yallabai nima abin bai zo min da wuri ba ne,yanzu ma kaine mutum na farko da na fara sanarwa, kuma idan ba damuwa ina so ka karbi waliccina"murmushin girma Alhaji Ahmed yayi sannan ya ce"wannan ai ba wani abu ba ne,tunda dama kai tamkar Kani kake a gareni,matar a ina take yar gidan waye?"dan sosa keya yayi kafin ya ɗan kallo inda Dr Bilal yake a sace sannan ya saki murmushin mugunta,ya ce"ai 'yar wajen me gadina ce buzu tana aiki a gidana, to yarinyar tana da hankali shi yasa kawai na ce ya bani aurenta",abinda yake nema ya samu domin sai da dr ya dago kansa daga kallon wayarsa da yake ya kalli Alhaji dan gasken,sai dai Alhaji dan gaske bai fahimci komai na sauyawa daga kan fuskarsa ba,wanda kuma hakan bai masa dadi ba,to amma ko hakan babu laifi tunda yasan ya riga yayi wining,fatan alkhairi Alhaji Ahmed yayi masa tare da fatan ganin gobe lafiya da rayuwa,daga nan ya tashi ya tafi yana jin kallon da Dr ya bisa dashi,.

A gaba daya wunin ranar Alhaji dan gaske yayi shi ne cikin farin ciki da dokin wayewar gari.

A yammacin ranar ne kuma zezee ta samu bakuntar Dr Bilal ,bakuntar da ta yi matukar bata mamaki,mamaki ba ɗan kaɗan ba ganin idan yayi zuwa ɗaya baya kuma yi sai sun nema ko an turo shi,kasancewar bata san da zuwansa ba yasa ,sai lokacin ta tsiri shiryawa,hakan yasa mommy tasa Ummul ta kai masa ruwa da lemo, Ummul kuwa baya san waye yazo ba, dan haka kai tsaye ta shige falon,ganin bata ga kowa ba yasa bayan ta ajiye lemo da ruwa akan karamin Centre table, sai kawai ta tsaya tana gwada tafiya da maganar zezee wai yadda take yiwa Dr idan yazo,can kuma sai ta fara gwada yadda Dr din yake magana a wani tsume yana daddaure fuska,duk abinda take bata kula dashi ba,ganin ba zata ankare da shi ba yasa shi mike ƙafarsa daidai ta inda zata wuce,aiko tana tafiya tana karya hannu sai ji tayi taci tuntube da abu kafin ta yi wani abu ta tafi kai tsaye ta fada sakan jikinsa,"ash ya fada a hankali tare da dan runtse ido na alamun yaji zafin fado masan da ta yi,Ita kuwa Ummul da kamshin turarensa kawai ta ganeshi,kokarin tashi take, sai dai kafin ta kai ga tashin zezee ta sako kai falon",wata uwar kara zezee ta kwada kafin ta fice da gudu tana kuka kamar wadda taga wani abin tsoro, da sauri Ummul ta mike tsaye tana watsa masa harara,kafin ta juya zata fice,amma sai ya riko hannunta da sauri ta kuma fuzgewa tana cewa "ganin ka ba alheri ba ne a wajensa saboda duk sanda kazo sai wani abu ya faru dani"sakin hannunta yayi yana bude idanunsa da suke a tun daxun,ita kuma sakin hannunta da yayi ne ya bata damar guduwa ba daga iya falon ba har gidan gaba daya,tana cewa wace Ni na koma gidan nan zezee ta tashi gidan da bala I ta ganni jikin sahibinta bisa tautsayi".

Shima Dr fitowa yayi fuskar nan a tamke ba zaka taba gane yanayinsa ba,mota ya shiga ya fice saboda ya samu abinda ya zo nema.

Zezee kuwa ɗakinta ta wuce,ko ta kan mommy bata bi ba dan tasan ba rarrashinta zata yi ba sai dai ta kara mata wani takaicin,sai da ta yi kuka me isarta sannan ta kira wayar bely Dan Jin inda aka kwana.

WASHEGARI.......

Yadda aka san ko wane aure shine idan an tashi zaka ga ana ta shirye shirye da shiga da fita dan tabbatar da cewa komai yayi daidai,to wannan auren ya bambanta da irin wancan daurin auren da muka sani,dan wannan auren idan ba fada maka aka yi ba,ba zaka san cewa wai yau din ana shirin yin aure a gidan su Ummul ba,ko Ali da mufty kama kansu su kayi saboda gargadin da suka sha wajen iyayensu,to dake suma bason abin suke yi ba shi yasa shirun yayi yawa,to ita ma Ummul din yau bata tashi da niyar zuwa gidan su zezee ba, dan ta ce ba zata je ba har sai ta huce daga fushin kwanta mata ajikin sahibi da ta yi.

Karfe daya da rabi,tuni baffa yana masallaci, abin har yaso bawa Alhaji dan gaske mamaki,to amma da ya tuna yadda baffan ya tsorata da ganin rayuwar iyalansa zata salwanta yasa ya kauda mamakinsa,sai kawai shima ya maida hankali wajen yin shirinsa wanda ya kusan makara saboda aikin da ya karasawa wasu mutane da zasu bar kasar a yau,shi kuma dama baya wasa da duk wata harka ta Kuɗi l, Shi yasa ya tsaya ya fara kammala shi kafin ya taho gida yin shiri,cikin gaggawa yake yin komai har sai ya samu ya fito karfe biyu saura mintina goma.

A can bangaren Ummul kuwa haka nan ta dinga jin wani irin faduwar gaba da kasala,har sai da ya kai ta ga kwanciya saboda ciwon kai da zazzabin da ya rufeta,magani Ummi ta bata tasha, ta zauna tana mata fifita har bacci ya dauke ta.

Gentle kuwa tun haɗuwar su ta jiyan bai kara ganinta ba,sai ya shiga kokonto a ransa, anya kuwa bai yi gangancin furtawa Ummul abinda ya furta mata ba,wai ma ke ya shiga kansa ne?shi din jarumi ne ta ko wane bangare tuna hakan da yayi ne yasa shi karfafa kansa ta hanyar tuna waye Ummul?"""

*****

A wajen Alhaji dan gaske kuwa sauri ne ya haifi nawa dan wani uban cunkoso ya tarar a titin da zai kaisa Masallacin,gashi bayansa ma duka a rufe yake bare ya juya ya canja hanya,wata Uwar zufa ya shiga sharewa yana jin wata irin faduwar gaba,to amma idan ya tuna waliyinsa Alhaji Ahmed yana wajen sai ya dan ji sanyi,haka kuma idan ya tuna tsoron da ya dasawa baffa sai ya ji kwarin gwiwa,wayar Alhaji Ahmed ya kira bai daga ba sai kawai ya tura masa text akan cewa a Daura auren ko baya nan,saboda cunkuson ababen hawa ya rike shi,kafin ya ajiye wayar an dawo masa da reply da cewa,ai an ma daura auren"wata kakkarfar ajiyar zuciya ya sauke yana sakin wata shegiyar dariya har da buga Sitiyari.

A can masallaci kuwa,tun karfe biyu aka daura auren bayan an idar da sallar juma'a kasancewar ba wata gayya su ka yi ba yasa ba wanda ya fahimci abinda yake faruwa,sai mufty da ya Ali da tun da aka ambaci sunan angon suka shiga yin kallon kallo,su dai a ganinsu Alhaji dan gaske ne mijin kamar yadda baffa ya fada musu to amma me kawo wannan sauyin?"....

Kaka tsara kaka wai me yake shirin faruwa ne ko na ce ya ma faru?

Anya kuwa an yiwa Alhaji dan gaske adalci duk wannan zumudin amma ace ba dashi aka daura ba?

To idan ba dashi aka daura ba dawa aka daura,ko dai Sulaiman ne?""🏃🏃🏃🏃

Shin ya gentle zai ji idan aka ce an bawa wani Ummul dinsa😂😂😂😂

Ina Dr NE anya wannan shurun nasa baya nufin komai?"😂😂😂***

c💕GIDAN ƳAN ƘARYA💕

By

FATIMA Y ADAM......

Littattafan marubuciyar.

KUDIRAR ALLAH

KADDARATA SANADIN HASKE

ƁOYAYYIYAR RAIHAN

ƳAR GIDAN YARBAWA

MATAR ƊAN BIRNI

And

GIDAN ƳAN ƘARYA....