GIDAN YAN KARYA

Pg23

by @zahrawriter12

Alhaji dan gaske cikin farin ciki ya karasa wajen daurin auren, wanda nan take ya shiga gaisawa da mutane yana washe baki yawa gonar auduga,ya Ali da yaya mufty kuwa kallonsa kawai suke suna kunshe dariya,a gefe daya kuma gentle ne zaune kusa da baffa yasha farar shaddarsa kana ganinsa kaga ango duk da cewa shi ba fari ba ne amma bashi da muni, yana kuma da kwarjini da cikakken zati,namiji a tsaye irin mazan da mata suke so,yaya Ali dai yayi farin ciki da wannan sauyin,shi kuwa yaya mufty ya karbi auren ne dan yana jin hakan tamkar kubutar da Ummul ne daga auren Alhaji dan gaske,kuma ya tabbatar da cewa duk lokacin da kura ta lafa zasu nemi da ya sakar musu Ummul din ya je yayi rayuwarsa irin ta matsiyata Ummul kuma ta samu daidai ita, wannan dalilin nasa ne yasa bai tashi hankalinsa da auren ba.

Yaya Ali ne ya zunguri mufty yana cewa"dan Allah mufty kalli garan nan sai wani murna yake bayan bai san dawan garin ba, wallahi ba dan baffa ya hana ba da nine mutum na farko da zan fara yi masa albashir din cewa ba da shi aka daura ba"dariya mufty yayi yana cewa"ai ko,ko ban fada ba zan so wanda zai fada ya fada a gabana ko dan na more rayuwata da dariyar farin ciki",suna cikin maganar ne Alhaji dan gaske yazo kansu yana mika musu hannu"da sauri har rige rige suke yi wajen mika masa hannun karshe dai sai hade hannun nasu yayi tare su kayi misabihar,mufty ya ce"Allah y sanya alkhairi suruki ya bada kazantar daki ta shara,lallai muna taya ka murna da samun damar lashe zaban zama mijin Ummul a mafarki,"ganin yadda alhajin ya kalleshi yasa shi Austin gyara maganarsa da cewa"wato mijin Ummul autar gidan yan karya"Ali ne ya amshe yana cewa"Barka Barka Alhaji kafin zuwan wata rana,ey ina nufin ranar da Ummul zata haifa mana yan biyu wayyoo ALLAH ya kaga debo shoki" gaula duk bai fahimci gugar zanar da su ke masa ba, sai ma ci gaba da yayi da bin mutane suna gaisawa har hannunsa ya zo kan wanda ko a mafarkinsa bai taɓa zaton ganinsa a wajen ba, cikin wani irin firgici da bugun zuciyar da bai taɓa jin irinsa ba a rayuwarsa,kamar wanda ya kama wuta haka ya yi saurin zare hannunsa daga na gentle da yake masa wani irin muskilin murmushi me tsayawa wanda aka yiwa a rai.

Bai iya cewa komai ba ya nufi inda Alhaji Ahmed yake su ka gaisa,yana ta jira ya ji Alhaji Ahmed yayi masa barka da Allah ya sanya alkhairi amma shiru, har ya tashi tafiya shida zugarsa, karshe ma saboda al ummar da yake tare da su kare shi a ka yi ya dena ganin Alhaji Ahmed ɗin,tsayawa yayi sake da baki yana mamakin yawan mutanen da suka zo daurin auren Kuma duk yawansu jama ar Alhaji Ahmed ne,wata zuciyar ta ce da shi ,ka san fa matsayinka a wajen Alhaji Ahmed kuma yaji dadi da ka bashi waliccin a hannunsa kaga dole ya yi gayya, wannan tunanin ne ya cire masa kokonto duk da cewa har yanzu bai dawo daga shock din ganin gentle a wajen ba,bai samu ganin baffa ba dan kafin yazo kansa tuni ya sulale ya bar wajen zuciyarsa cike da fargabar binda zai je ya dawo duk da cewa an bashi kwarin gwiwa da kwantar masa da hankali akan cewa babu abinda zai sameshi daga shi har iyalansa suna cikin tsaro.

Shima Alhaji dan gasken ganin bai ga baffa ba sai kawai ya shige motarsa ya tafi gida a ransa yana cewa"wannan mutum akwai kunya da kara,na san abinda ya hana shi tsayawa mu gaisa kenan".kasancewar yau da gobe duk ba aikinsa ba ne shi yasa Alhaji dan gaske bai damu da rashin ganinsa ba,kawai dai ya sa a ransa komai dare sai ya je yaga fuskar masoyiyarsa Ummul, duk da cewa yana sane da alkawarinsu na cewa ba zai fadawa Ummul din maganar auren yanzu ba.

Tunda ya shigo mommy take binsa da kallo har ya gama duk abinda zai yi ya fito falon ya zauna, shi kansa zaman da yayi kana ganinsa kasan yana cikin farin ciki,duban mommy yayi tare da yin gyaran murya yana cewa"dama ina son magana daku,ina ita zezee kirata tazo?"yana rufe bakinsa sai ga ta ta fito idanunta sun yi jawur saboda kuka da damuwar Dr Bilal da ta sawa ranta,zama ta yi ba tare da ta ce da su komi ba,yar gajeriyar dariya yayi yana cewa"zezee ke nan har yanzu baki san waye ubanki ba,to maza share hawayen ki kisha labari"duban mommy da tayi kamar bata wajen yayi yana cewa"to uwar yan nunkufurci kin shirya jin abinda zan fada ko kuwa na kyaleki?"mommy ta ce"idan har kaga fadar zata amfaneka zaka iya fada idan kuma bata da amfani a wajenka to ka yi shiru"murmushi yayi irin na tura haushinnan,kana ya ce"mommyn zeeze ki bi a hankali dani domin Ni din nan da kike gani nafi karfin tunaninki,to idan ma wani abu ne a ranki gwara tun wuri ki ciresa saboda ke dai kece a wahala Ni ba damuwata ba ne,dan yanzu ma an riga an yi an gama sai dai haushi ya kasheki"bata iya ce masa komai ba saboda bata son yin kalamin da zai sa ya gane cewa tasan komai akan abinda yayi mata, domin shirun da ta yi tsayin shekaru shine yake rike da rayuwata har yau da kuma ƙaddarar Ubangiji da ya riga ya rubutu mata ita tun kan ahaifeta,shi yasa ta rabu da shi akan nasa tunanin,katse mata tunani da muryarsa da take cike da nishadi,ya ce"yau dai an daura min aure,dan haka sai ki dauki hakuri"a dan mamakance mommy ta kallesa tare da cewa"wace me tsai tsayin ce ta daukarwa kanta kara da kiyashi bata sani ba"ba tare da ya damu da kalaman da tajefeshi da shi ba ya makale kafada irin ko a jikinsa din nan, sannan ya dubi zezee da ta yi sunan zaune saboda yadda maganar ta zo mata a bazata ta kuma shigeta har sai da ta ji ciwo a zuciyarta.

Dariya yayi ya ce"kar ki damu zezeen Abba ke wannan aure gaba ya kai ki nasan zaki yi murna idan kika ji wadda na aura"girgiza kai ta yi idanunta na cika kwalla ta ce"Abba ba wata mace da zaka aura a gidan nan na yi murna"har da Ummul ikram da ta tare miki duk wani farin ciki da kike nema a wajen Dr Bilal mutumin da kike son ya so ki ke kadai ba tare da wata ta rabeshi ba"?tashi ta yi zaune tana zare ido saboda tsananin mamakin maganarsa,harda mommy ma sai da ta maida hankalinta kansa,tana son Karin bayani dan tabbatar da abinda kunnuwanta suke ji mata.

Cikin kwarin gwiwa da tabbatar musu da abinda yake fada ya ce"tabbas Ummul ce amaryata yau aka daura mana aure da ita,kuma na yi haka ne duk saboda farincikinmu ni da ɗiyata,na farko dai na hana Ummul ci gaba da kasancewa barazana ga tabbatuwar aurenki, sannan na samu Abinda nake so nake da burin samu a rayuwata dan haka dole mu yi Shagali"wani uban tsalle zezee ta daka ta rungume Abbanta tana hawayen farin ciki,kafin ta ta shi da gudu ta wuce dakinta dan kiran bely ta bata albishir din da yake neman dauke mumfashinta saboda farin ciki,mommy kuwa binsu kawai take da kallo,zuciyarta cike da bakin ciki, bakin cikin shigowar Ummul hannun azzalumi wanda zai iya yin komai saboda kudi wanda son kansa yasa ya maida rayuwar mutane ba , abakin komai ba,kwallar tausayin rayuwar ahlin huxu ta share domin ta tabbatar da cewa wannan auren na tursasawa ne,duk da zata iya cewa Gara Ummul tunda iyayenta basu da kudin da zasu tsolewa Alhaji dan gaske ido bare ya dauke rayuwarsu,ya hade dukiyar da yar ya rike,tashi ta yi ta bar masa falon yana kallonta da murmushi akan fuskarsa,zuciyarsa fes an jima kawai yake jira ya je yaga Ummul ko ya ji sanyi a ransa.

******

A bangaren GIDAN YAN ƘARYA kuwa har yanzu babu wata alama da su ka nuna cewa wai ana aure a gidan,su mufty ma tuni suka shiga gari,baffa ne kawai da Ummi sai Ummul din a gida,shima getle din yana waje yana ci gaba da aikinsa ne,amma a ransa da zuciyarsa yana jin cewa ba zai iya barin wannan rana ta wuce a haka ba, yana son yin wani abu da zai kara tabbatar masa da cewa Ummul ta zama tasa,hakan yasa ya mike ya shiga gidan yana sallama, baffa ne ya amsa masa da cewa ya shiga"shigar yayi tare da taugunnawa gaban baffa yayi masa maganar da shi da ka dai ya jita,murmushi baffa yayi yana jinjina kai,tare da cewa Allah ya kaimu anjiman da rai da lafiya"daga nan gentle ya mike ya fita,baffa ya bisa da kallo dan har yanzu ganin komai yake kamar a farki har yanzu bai gama fita da shock din abinda ya faru kuma yake kan faruwa ba,a ransa ya ce"babu ta yadda Ubangiji baya lamarinsa,duk lokacin da yaso kanka ya kulle ka kasa gane komai dan yayi al'amarinsa ko shakka sai hakan ta faru saboda hakan yaso,dan haka babu kokonto ko mamaki ga ikon Ubangiji.

*******

A yammacin ranar ne kuma sulaiman ya dawo daga tafiyar da suka yi shi da mahaifinsa ya dawo cike da dokin ganin Ummul da kuma tunkarar baffa da maganar aurenta,dan yanzu yasan an samu ci gaba duba da yadda ya bata iska, dole yasan za ta yi kewarsa, wannan tunanin da yake yi shi yake kara masa karfin gwiwar son tunkarar ta a yau din.

Ummi ce ta sanar da Ummul cewar ta shirya an jima bayan sallar Magriba zasu je gidansu jafaru ta gaida kakarsa, sosai abin ya bawa Ummul mamaki dan tasan wannan ba dabi ar baffa ba ne,duk da cewa ita ka dai ce diyarsu mace,amma tasan ka'idojin gidansu da irin tarbiyyar da mahaifiyarta suka dora ta akai,kallon mamakin da Ummi taga tana yi mata ne yasa ta, dan waskewa da cewa,ba wani abu ba ne dubiya ce kawai kuma ko ke kinsan cewa jafaru ba zai cutar da ke ba ,shi yasa muka bashi amana,ki sauri ki shirya kar ya zo yana jiranki"Ummi ta fada tana ficewa daga dakin,ajiyar zuciya Ummul ta sauke tana dan jin kwarin gwiwa,tashi ta yi ta shirya tunda dama a tsaf dinta take, sai dai dan Abinda ba a rasa ba,kun san dai Ummul ba sai zata fita take yin ado da tsafta ba,ita din me tsafta ce ,kamar yadda ta tashi taga mahaifiyarta na yi, hatta da kamshi ya riga ya kama jikinta tunda dama sune gidan kamshi,dan haka ko bata turara jikinta ba sai kaji wani sanyayyan kamshi na fita daga jikinta,tsaf ta fito cikin sabuwar baka me fatan din ja na atamfar gold chiganvi,a cikin Dinkin da ta fi so wato bubu,ko dan ta san yana matukar yi mata kyauta ne oho,tana gama shiryawa ana tayar da Sallah magriba,kasancewar ita tana cikin hutu sai kawai ta zauna tana ci gaba da danna tasbin hannunta,har aka idar da Sallah.

A bangaren gentle kuwa shima yayi shirinsa tsaf cikin ash din shadda me sauƙin kuɗi,ana idarwa da Sallah bai yi zaman da ya saba yi ba ya fito daga masallacin,kai tsaye sallama yayi daga zauren gidan, ummi ce ta amsa saboda baffa bai dawo daga Masallaci ba,daki ta shiga ta kalli Ummul tana cewa"tashi kije yana jiranki Allah ya kiyaye ya dawo da ku lafiya"Amin Ummul ta fada tana jin wani irin nauyi a kirjinta kamar wadda aka dorawa gammo,mayafinta ta yana saman kanta tare da zura takalminta kana ta fito, bata san cewa yana zauren ba sai ji tayi kawai ta yi karo da mutum tsananin tsoron da ta ji yasa ta bude baki zata yi salati me hade da ihu,amma sai taji ya sanya tattausan hannunsa ya rufe bakinta inda ta shiga shaƙar wani irin kamshi da ta ka sa tantance wane iri ne, kai sai ma tunanin da ya shiga kanta na kamar ta san me irin kamshin,dauke hannunsa yayi daga kan bakinta yana cewa a hankali,"matsoraciya"ajiyar zuciya ta saki tana dan yi masa hararar kasan ido ba tare da ta iya cewa komai ba,kama hannunta yayi suka fita, suna fita taga a daidaita yana jiransu,zata yi magana ya girgiza mata kai,wanda hakan yasa ta yi shiru tana mai shiga, sai da ta shiga Sannan shima ya shiga,Kai tsaye wani hadaddiyar wajen cin abinci suka tsaya,ko ita Ummul din duk shige shigenta da son ƙaryarta bata taɓa zuwa gurin ba,kai ko zezee bata jin ta taba zuwa irin wannan waje dan daga ganin wajen nan ba wajen kananun masu kuɗi ba ne,dan gaba dayansa ma vip ne, ko da ya fita yaga tsaya tana yiwa wajen kallon kai yaci da kuma mamakin zuwannasu,sai kawai yasa hannu ya daukota cak daga cikin daidaitan,wanda sai a lokacin ta dawo hankalinta,da sauri ta zame daga jikinsa tana hararar gefensa tana magana ciki ciki.

"Nifa ba yar iska ba ce, da haka nan zaka dinga tabani ehe",tsaf abinda ta faɗa ya shiga kunnensa amma sai ya shareta,yayi gaba abinsa hakan yasa ta bisa da ɗan hanzari dan saura kiris ya shige kofar da ko kudi aka saka mata ba zata iya bude taba ya barta,sai gashi ita ce da kokawar kama hannunsa,suna shiga ta kasa boye kauyancinta dan sai da ta hangame baki tana kallon duniyar da sai a tv idan ana haska irin hadaddun wajen cin abinci na kasashen turawa take gani,wajen da aka basu shi kansa abin kallo ne saboda wajene aka zagaye shi da wasu irin labulaye masu kyau ga kuma wata kujera me kana3da gado sai dan teburin cin abinci a gabanta da kuma wajen wanke hannu,kai tsaye ya nufi kujerar ya zauna ya bar Ummul da sakin baki tana kallon haduwar wajen,"gashi a killace muke bare na baza ƙaryata yadda raina yake so"ta fada a fili tana yin kamar ta yi kuka,karasawa ta yi itama ta zauna bakinta cike da tarin tambayoyi,sai dai ba zata ce komai ba har sai ta cika cikinta da kayan yan gayun da aka fara jere musu a wajen,sai da ta ci ta koshi sannan ta fara jero masa tambayoyin da suke dankare a bakinta,tambayar farko da ta fara fitowa daga bakinta ita ce"yaya gentle wai dama ka san irin wannan wajajen a Kano Amma baka taba kawo Ni ba?to wai ma wa ya gayyaceka irin wajen nan ne?ko dama kana da abokai masu kuɗi?dan Allah waye zai biya kudin duk abinda muka ci?",shiru kamar bazai tanka mata ba dan har ta fara shaka zata fara halin,sai kuma ta tsinci kamilalliyar muryarsa me zurfi da amo yana cewa"Dr Bilal DAN ITOPIA mana, ke ba kanwarsa ba ce?".

Aiko zumbur sai ga Ummul a tsaye tana zare ido yawa mage a gaban kura,kafin ta ce"wallahi wallahi babu ruwana,,shike nan yau zaka samu kwanan cell,innalillahi wallahi yaya gentle kana sane kasan cewa karya nake babu abinda ya hadani da wannan mugun me idon magen,.kaima mugunta kawai ka shiryawa kanka dan wallahi ba ni ka shiryawa ba ,dan kai ne ka san ya kwanan cell yake"duk maganar da take bai ko daga kai ya kalleta ba,sai yar a kurkin wayarsa da duk tasha mannin saletif ya ke dannawa,kafin jim kadan ya karata a kunnensa yana magana a hankali,kasancewar Ummul mace me ji yasa taji abinda yake fada,"kuzo ta biya ku kudin zamu wuce"daga haka ya kashe wayar yana maida kansa bayan kujerar yana kwanciya har da lumshe ido,jin abinda ya fada yasa hankalin Ummul ya kuma tashi dan wannan wajen ba irin wajen da suka saba zuwa ta yi musu burgar banza su yarda ba ne,da alama nan wajen ta kawo musu wasa da sojoji zasu hadata,tsugunawa ta yi a gabansa tana cewa"dan Allah ka rufa mun asiri ka boye ni wallahi tsoro nake ji"ba tare da ya bude idonsa ko ya motsa daga yadda yake ba ya ce"karki damu nan wajen wajen yayanki Dr Bilal ne shi yasa na kawoki ki bude ido, nasan a abinda kuka sani nasa baki san da wannan wajen ba ko?"ya fada yana bude idanunsa da zuba su a kanta,kuka kawai ta sanya masa wanda dama hakan yake so, ganinta cikin yanayin tsoro yana sashi jin wani iri akanta da komai nata,so yau ranar farin ciki ce a gareshi hakan yasa yake neman duk wani abu da yake sashi farin ciki ya kasance a kusa dashi,dagowa yayi daga kashingiden da yake yana zuba mata idanunsa da suke boye cikin bakin gilashi, kafin a hankali cikin mutuwa da wani irin shaukin da ya saukar masa da gajiya a dukkan gabbansa ya kamo hannunta duka biyu ya dagota,bai yi kasa a gwiwa ba wajen yi mata kyakkyawan masauki a ni imtaccen jikinsa.

A can bangaren Alhaji dan gaske kuwa tuni yayiwa kofar gidan su Ummul tsinke,yana ta kiran wayar baffa dan ya fito masa da Ummul din sai dai wayar a kashe take dan bata shiga,yana cikin haka ne kuma sai ga motar sulaiman ya danno kai inda ya samu waje kusa da inda Alhaji dan gaske ya faka tasa shima ya faka tare da fitowa daga ciki,

Kallon kallo suka shiga yi kamar wanda basu taba ganin juna ba,daga karshe dai Alhaji dan gaske ya saki murmushin nan irin na yaro fa bai san wuta ba sai ya taka,a ransa yana cewa na gama da ku yara dole ku san cewa Ni ba sa an ku ba ne,saura wancan fitsararren shima yazo a gabanku zan rungume Ummul na sumbaceta naga karyar iskanci".

Shima sulaiman nasa sake saken yake, yana samun kwarin gwiwa idan ya tuna tsanar da Ummul ta yiwa Alhaji dan gaske,dan haka a yanzu yake ganin shi kadai ne yake da qualitys din da za a bashi Ummul kai tsaye ko da ta hanyar tursasawa ne,sai kawai shima ya shiga watsawa Alhaji dan gaske murmushin mu zuba Ni da kai aga me nasara,

**""

Kukanta kara ƙarfi yayi a lokacin da gangar jikinta ta samu matsuguni a nasa gangar jikin,da dan sauri ya dora bakinsa a kan fatar kunnenta yana hurawa tare da bubbuga bayanta,yana son ta yi shiru ta daina yi masa kukan da yake jinsa tamkar waka ko kuma wata sarewa me sanyi da dadin sauti,.....

Ya ne ya ne,ko ya fada so ne?😂😂😂

Zahra✍️

***

💕GIDAN

💕GIDAN ƳAN ƘARYA💕

By

FATIMA Y ADAM......

Littattafan marubuciyar.

KUDIRAR ALLAH

KADDARATA SANADIN HASKE

ƁOYAYYIYAR RAIHAN

ƳAR GIDAN YARBAWA

MATAR ƊAN BIRNI

And

GIDAN ƳAN ƘARYA....