GIDAN YAN KARYA

Pg28

by @zahrawriter12

Mamaki da al'ajabin wannan masifa da mufty yake gani kiri kiri shi yake kashe masa jiki har ya kasa kwatar kansa a wajen bely da yake ganinta kamar namiji Saboda karfinta,tsananin tsoron Allah yasa shi sakin kuka kamar karamin yaro, fadi yake "astagfurullah Allah astgafurullah Allah, Allah ka ci gaba da kare Ni da kariyarka Allah ka kubutar dani daga sharrin shaidaniya, Allah na san cewa ni mai laifi ne a gareka laifukan da ba zasu kidayu ba,wanda na sani da wanda ban sani ba, Allah ina rokonka da ka yafe min, ka kuma kare Ni daga yin babban sabo a gare ka, kananun ma gafara nake nema a gurinka"wannan addu'a da yayi ce ta bashi wani irin karfin da lokaci daya ya hankade bely, kana yabi ta da duka yana boll da ita kamar ya samu tamaula,tun tana ihu har ta koma fidda numfashi sama sama, bakinta sai fidda jini yake fuskarta kuwa duk ta fashe ta kumbura babu kyan gani,haka ya tsallake ta ya fice bayan ya dauki key din,zuciyarsa babu komai sai tsananin nadama.

****

A tsakar gida ya tarar da ummi ta zabga uban tagumi, tana ganinsa ta saki ajiyar zuciya kafin ta ɗan watsa masa harara,tana cewa daga ina kake har karfe sha daya da kwata baka shigo gida ba?"sunkuyar da kansa yayi ba tare da ya iya cewa komai ba,dan bai san me zai ce mata ba ,tunda basu ginu a kan yiwa iyayensu karya ba, wannan alama da yayi mata yasa ta ta fahimci cewa akwai damuwa wadda ba zai iya fada mata ba,kuma baya son yayi mata karya,"wuce ka je ka kwanta Allah ya kyauta"ummi ta fada tana kallon yadda duk ya yi wani wujiga wijiga kamar wanda yayi dambe,ummi bata takurawa yaranta akan lallai sai sun fada mata halin da suke ciki alokacin saboda shine babban abinda yake fara sawa yaranka su fara yi maka karya,barinsu take yi sai sun samu nutsuwa a hankali sai ta bincikesu wani lokacin ma kafin ta bincika din su sun kasa yin shiru sun fada mata,to yanzu ma ta san ko bata binciki muftahu ba zai fada mata ko mai dadewar lokaci kuwa,ile kuwa tana shirin mikewa daga kan kujerar tsungunnon da take kai taga muftahun ya fito daga dakinsu bayan ya cire kayan jikinsa,komawa ta yi ta zauna har ya karaso gabanta ya zauna dirshan tare da dora kansa a kan cinyarta,kawai sai ya fashe mata da kuka,hannunta ta ɗora akansa tana shafa sumarsa me laushi ba tare da ta dakatar dashi daga kukansa ba,har sai dai yayi shiru dan kansa,a daidai nan su Ali suka biyo bayansa saboda jin kukansa da suka yi ,kuma dama tun da ya shiga suke tambayarsa ko lafiya suma ya kasa ce musu komai,zama suka yi suma suna sauraron labarin da muftahu ya fara bawa Ummi.

Tunda ya fara ummi take jinjina kai,su Ali kuwa Sarkin yan zuciya har ya fara huci kamar zai daki iska,muftahu ya kai karshen maganarsa da cewa"ummi ba zan iya bari har sai bayan wani lokaci Sannan na fada miki wannan mummunan ƙaddara da ta kusa fada mun ba,saboda tun yau nake son Karin addu'ar ki wadda ita ce ke tare da mu a ko da yaushe"dago fuskarsa Ummi ta yi tana share masa hawaye tare da cewa"ya kamata ku yi hankali ku daina wannan karyace karyacen saboda shima babban laifi ne wajen Ubangiji,ko ba ku san cewa Allah yana jarrabar bawa da mummunan ƙaddara a sakamakon aiyukansa marasa kyau ba?"to wannan kadai ya ishe ku ishara,hatta ita Ummul din shigowar Alhaji dan gaske rayuwarta yana daga cikin jarrabawa da kuma sakamakonta na laifin karya,wadda kaf din ku ita ce kadai illar ku,Hamza ne kawai ya fita daban a cikinku,dan haka gani ga wane ya ishi wane tsoron Allah"ta fada tana kallon Ali da Safwan da su kayi tsuru tsuru,da sauri myftahu ya ce"wallahi Ummi tun a gidan na dinga neman gafarar Ubangiji in sha Allah ba zan kuma ba,amma fa Ummi har da kyau wanda shine yake rudar yan matan yanzu ga samari,, ko ita tsinanniyar kyauwun fuskata ne ya rudeta,dan duk magana daya da za mu yi da ita sai ta ce mun "mufty kana da kyau na asali shi yasa nake sonka kuma nasan haka kake ciki da bai",ya fada cikin kwaikwayon Muryar bely,sannan ya ci gaba da cewa,"Ni da ban kawo haske akan abinda take nufi da wannan kalmar ba, sai yau da naga zahiriyan za ta min fyade"dariya suka sheke da ita, ummi kuwa tashi ta yi tana cewa "kai dai ka sani maras kunyar banza"tana shigewa daki suka saka shewa gaba daya,Safwan ya ce"kowa sai ya kama kansa tunda mata sun koma yiwa maza fyade"dariya suka kuma sawa a yayin da suke shigewa dakinsu suna ci gaba da tsokanar muftahu,karfe uku daidai Ummi ta buga musu kofa saboda jin su shiru da tayi, tashi su kayi suna mirza ido dan basu kwanta da wuri ba saboda abinda ya faru da muftahu,to amma sun san wannan tsayuwar daren ta zama dole musamman yau da shedan ya biyo ta kan mufty.

*****

Bely kuwa tunda mufty ya shemar da ita a wajen ko dan yatsanta kasa motsawa ta yi,da kyar da jan jiki ta kai hannunta kan bedside drower ta lalubo wayar ta ,ta dannawa me gadinta kira, cikin mintina biyu ya kara so har cikin dakinnata,shine ya taimaka mata ya kira mata likitanta kuma kwartonta ya zo a daren ya duba ta ya bata magunguna da dressing ciwon da ta ji,duk da halin da take ciki amma tsananin masifar da ta ɗorawa kanta,sai da ta rike likitan ya biya mata bukatarta tunda bata samu yadda take so a wajen mufty ba.

******

Duk abinda ake ciki Ummul bata san komai ba,dan ko da garin Allah ya waye babu wanda yayi mata zancan,misalin ƙarfe goma tana zaune tana wanke kwanukan da suka gama karyawa,cikin nishadi take raira wakarta ta, ta auta mg boy wadda yake cewa kina bani dama sadaki na aiko,amma ita sai ta juya ta akanta tana cewa(ina baka dama sadaki ka turo aure za a Daura mu bar kai da kawo soyayyar ka baby ta sanyani kiwo ina jinka sosai so ne ya kawo a Hausar basakkwace ake furta awo ya Habibi da kai zan yi aure)"nima dake xan yi aure"ta ji dirar kalaman a cikin kunnenta kamar daga sama,da sauri ta waiwaya gefenta inda ta ga gentle tsugunne hannunsa cikin ruwan wanke wanken yana dauraye mata wanda ta tara bata dauraye ba,a dan firgice ta shiga waiwaye ko zata ga wani a tsakar gidan,ajiyar zuciya ta sauke ganin babu kowa a wajen, cikin dan zaro ido da Muryar rada ta ce "yaushe ka shigo?yaushe ka dawo daga tafiyar?"lokacin da kika yi nisa cikin kogin SOYAYYAr da baki san kina yi ba"nifa waka kawai nake"ta fada tana ture hannunsa da ya sanya cikin ruwan kumfar yana laluben dogayen yatsunta da suka sha jan lalle,bai ce komai ba sai rike hannun da yayi yana kallon kunshin kafin a hankali ya kai hannun bakinsa ya ambaci yatsun,take ta fibcike hannun tana cewa"sai ummi ta ganga?to ka tabbata Ummi ko yan gidan mu suna ganinka sunanka ya tashi daga gentle ya koma dan is.....Sai kuma ta kasa karasawa saboda yadda ta watsa mata lulu eyes din nan nasa masu haske kwarjini,"Uhm uhm dama cewa zan yi hakan babu kyau"bai tanka ba,sai hannunsa da ya cire cikin ruwan ya dora akan cinyarta ya goge ruwan sannan ya tashi daga tsugunon da yayi ya kama hanya ya fice,da karfi ta sauke numfashi tana cewa"na shiga uku me yake damun yaya gentle ne,a baya sai da lalura yake tabani amma yanzu bini bini?sai ta mele baki kamar zata yi kuka saboda rashin gane manufar canjin yaya gentle dinnata.

Duban kayan wanke wanken ta yi duk ya gama daurayewa dan haka tashi ta yi kawai ta kwashe kayan ta sharce wajen tas, take tsakar gidan ya dau haske idan da zaka tsaya ka zubawa sumintin tsakar gidan ido tabbas zaka iya hango fuskarka a ciki saboda tsananin sharuwa da wankin da yake sha,rike kugu ta yi tana kallon tsakar gidan loko da sako ko zata hango abin da bai yi mata ba ta gyara,a haka Ummi ta fito daga daki ta sameta,murmushi Ummu ta yi tare da cewa "to ai sai ki wuce ki daura alwalar walhar idan yaso daga baya kyazo ki ci gaba da kallon gidan har ki gano tawayarsa"dan tura baki ta yi kafin cikin shagwaba ta ce"wallahi Ummi tsafta ta yi a rayuwa wanda bai da tsafta bai gama more jin dadin duniya ba"oh yanzu kin sauka da ga kan kalmar ki ta wanda bai da kudi bai more jin dadin duniya ba kenan?,shi ne yau kika maye gurbinta da tsafta?"Ummi ta fada tana rike habarta cike da mamaki,dan Ummul bata da wani zance sai na idan baka da kudi baka more jin dadin rayuwa ba,kafin Ummul ta ce wani abu ,an bude kofar banɗaki an fito,wani uban tsalle Ummul ta daka ta koma bayan Ummi tana cewa"la ila ha illallah kuke ganinmu bamu muke ganinku ba,dan Allah ku koma mazauninku kar ku fito ku cutar da bayin Allah da basu ji ba basu gani ba,mu ta fafutukar yadda za mu ci musha mu yi sutturar rufin asiri muke dan....."dallah Malama rufe mana baki duk kin cika mu da karadi ko hadiyar yawu bakyayi, dan wulakanci so kike kice baki ga lokacin da na zo na dibi ruwa na shiga bandakin yin wanka ba?"muftahu ya fada a kufule da karadin Ummul ɗin,

Salati ummi ta sa tana tafa hannunwanta kafin ta ce"yanzu muftahu kai ne ka koma haka?to ai ko Ni ta maza na yi da ban gudu ba,yanzu me ye hakan da ka yi?"duban kansa mufty yayi sannan ya dago ya kalli Ummul da har yanzu jikinta ke karkara dan fa ita sam bata yadda cewa wannan aljanin mutumin yaya muftyn ta ba ne"ya ce"Ummul ba mu guri zan yi magana da Ummi"tabdi wallahi ba ka isa ka yi min wayo ba,wato na barka da uwata ka shekata lahira ko?to ba da Ni ba,idan ma dan kaga ina jin tsoronka ne to na daina yanzun nan zan koneka da ayoyin Allah,yo ai idan ni kafi karfina yasin baka fi karfin Allah ba,dan haka bari ka gani,"kafin mufty ya ce komai Ummul ta fara karanto masa ayatusshifa tana yi tana tofawa gefen ta da na ummi,mufty kamar yayi kuka yace"Ummi kina kallonta ba zaki mata magana ba aljani fa ta maidani"to ni me zan ce ne ai ni kaina idan ba cire wannan kwalliyar ajanun da ka yiwa fuskarka ka yi ba to idan zamu shekara ba zan yadda kai muftahu ba ne"hannu muftahu ya sa a fuskarsa ya shiga goge farar kasa da bakin kwallin da ya haɗa ya murza a fuskarsa wanda ta maida shi ash calor kuma gaba daya jikinsa,ko da ya goge din bai fita ba saboda ya riga ya bushe dan haka ya kalli Ummi cikin maraicece fuska ya ce"wallahi Ummi na yi haka ne dan na kaucewa sharrin yan matan zamani tunda naga farar fatar da dogon hancin suke yiwa"da kuma kariyar kudi ba"Ummi ta karasa masa tana watsa masa harara.

Gyaran murya Ummul ta yi sannan ta ce"Ummi ki daina magana dashi yaudarar mu yake son yi kin san dai halin shedanun aljanun nan basu da tabb.....kafin ta rufe bakinta muftahu yayi kanta a harzuge,ai ko da gudu ta yi hanyar zaure tana cewa"eho jama ku kawo dauki aljani ya shigo mana gida"duk wannan muhawarar da ake tafkawa, Ali da Safwan da Hamza suna cikin daki suna tuntsura dariya har da birgima dan su a gaban su mufty ya gama hada kayan canja halittar da zai yi saboda yan mata masu fyade,jin gidan ya hargitse ne yasa su fitowa da gudu suna dariya,suna fitowa Ummi ta kallesu tare da cewa"au dama duk abinda ake kuna ciki shakiyan banza?Ali ne ya yi saurin taro mufty da yake shirin bin bayan Ummul waje cikin dariya yake cewa"kai yanzu sai ka fita haka?anya muftahu ka kalli kanka a madubi kuwa?"ummi ki musu magana "muftahu ya fada muryarsa kamar zai yi kuka,tausayi ya bawa Ummi saboda yadda yayi wani iri dashi kana ganinsa kasan yana cikin damuwa da dimuwar abinda ya faru jiyan,kamo hannunsa ta yi tana cewa "rabu da su muje ka wanke jikinka, Allah shi zai ci gaba da kare ku a duk inda kuke, wanda yake da Allah ai shi yake da abin fariya".

Sai dai tun kan ta karasa fitowa wajen ta ci karo da kaifafan idanun gentle akanta yana watsa mata kallon gargadin kar ta sake ta fito a haka,tsaf ta fahimci yarensa na magana da ido,wanda hakan yasa ta yi saurin kallon jikinta,sai a nan ta fahimci cewa ko mayafi babu a jikinta ,har zata koma sai kuma ta tsaya tana kallonsa bayan ya ci gaba da aikin gyaransa,a jikinsa ya ji alamun kallonta hakan yasa ya dago kansa tare da yi mata tambaya da ido ke ta tsaya yi bata tafi ba?"sai kawai ga samu kanta da mayar masa amsa da idon,kai ka tsayar da ni?"dan kare hade fuskarsa yayi sannan a fakaice yayi mata nuni da mutane da suke dan kaiwa sa kawowa,makale kafada ta yi, sannan ta shiga yi masa maganar bebaye da nuni da hannu,wai me yasa duk wani abu naka irin na dr Bilal ne har magana da idon da yake kaima ka iya?"sai kawai ya kawar da kansa yana ci gaba da aikinsa ba tare da ya kuma kallon inda take ba"mele baki ta yi sannan ta dinga ja da baya har ta shige gidan,sai dai fa ba zata taba gajiya da yi masa irin wannan tambayar ba a duk lokacin da yayi abinda yayi kamaceceniya da na Dr Bilal......

Zahra✍️***

💕GIDAN ƳAN ƘARYA💕

By

FATIMA Y ADAM......

Littattafan marubuciyar.

KUDIRAR ALLAH

KADDARATA SANADIN HASKE

ƁOYAYYIYAR RAIHAN

ƳAR GIDAN YARBAWA

MATAR ƊAN BIRNI

And

GIDAN ƳAN ƘARYA....