GIDAN YAN KARYA

Pg29

by @zahrawriter12

Tana kusan shiga gidan ta fara sanɗa tare da leƙe leƙen ta inda zata ga mufty,ji ta yi an cafkota ta baya, da gudu ta fada dakin Ummi ta na cewa"wayyo Ummi kin gani ko,dama na gaya miki aljanune munafuntarki kawai suke son yi,Kum....hada idon da ta yi da mufty yasa ta yi shiru tana zazzare ido,sai kuma ga Safwan ya shigo yana dariya,tare da cewa "matsoraciyar kawai,wai daga na dan tsunguleta shine ta shigo tana yiwa mutane karadi"tura baki ta yi tana kunkuni kafin ta ce"ummi wai me yasa yaya mufty yayi kwalliyar aljanu?"ba a sani ba" mufty ya fada a dan fusace dan har yanzu bai gama hucewa ba,gum Ummul ta yi bata kuma cewa komai ba,sum sum ta wuce ta koma dakin gadonsu ta yi kwanciyarta,dan ta sa a ranta baza ta koma gidan Alhaji dan gaske ba har sai su ya Safwan sun tafi.

Mufty kuwa duk yadda Ummi ta so ya fita kasuwa ƙi yayi ko yayi kamar zai fita sai kuma ya dawo yana yatsina fuska kamar zai yi kuka,dole haka ta rabu da shi ya yi zaman gida,amma fa yini ummi ta yi tana raba fada shi da Ummul,duk da cewa akwai tazarar shekara har shida a tsakaninsu amma hakan bai hana su yin fadan sako da sakuwa ba,

*******

Sam bely bata ji a ranta zata hakura da mufty ba ,abinda take ji a ranta game dashi ya wuce so ya zama masifa wadda ta ɗorawa kanta,yini guda ta yi tana kiransa a waya amma yaki dagawa daga ƙarshe ma kashe wayar yayi,tunanin aika masa da saƙo ne ya zo a ranta, hakan yasa ta yi saurin tura masa sakon tare da fatan ya gani kuma ya amince da bukatarta a karo na biyu,

Yamma sakaliya Ummul ta shiga dakin samarin yayunnata dan ta share musu,sai da ta kalle dakin tsaf ko zata ga abin neman magana, sannan da bata samu komai ba ta fara sharar,bayan ta gama sharar tana cikin goge drowar kayansu,ta ci karo da wayar mufty a kashe, dauka ta yi ta kunna tana cewa,"Ni ban san yau me yake samun ya mufty ba duk ya wani susuce duk kaunarsa da waya yau amma ya kashe ya ajiye,har zata ajiye wayar sai ta ga sakkoni na shigowa,fasa ajiye wa ta yi tana cewa"bari na duba yanzu haka budurwarsa ce ta ji wayar a kashe ta turo masa sako, Ummul da karanbani take ta bude sakon ta shiga karantawa kamar haka(mufty dan soyayyar ka da ma aiki ka dawo mu yi magana ta fahimta, wallahi na canja kudirina akan ka,tun da har na fahimci cewa ba zan samu binda nake nema a wajenka ba,amma ka daure ka zo mu sake haduwa saboda ina da magana me muhimmanci, dan yanzu magana ce ta aure tsakanina da kai)ji tayi an wafce wayar daga hannunta,tana juyawa taga mufty tsaye yana kallonta bayan ya maida wayar ya kashe,ɗan sosa lallausan gashin da ya kwanta ta keyarta ta yi tare da kokarin ficewa daga dakin,sai dai zuciyarta cike take da son fahimtar inda wannan sakon da aka turowa mufty ya dosa,tana fita mufyahu ya kunna wayar tare da karanta sakon,wani zazzafan tsaki ya ja kamar wanda yake shirin tsinka harshensa,ji yake a ransa kamar ya kashe bely kowa ya huta,"dole ma na sauya layin nan dama bank ɗina ba uwar komai a ciki dan haka na bude wani",ya fada yana zare katin daga kan wayar ,yana fito dashi ya sa shi a bakinsa ya tauneshi, ji yake a ransa kamar bely yake taunewa shi yasa ya dage iya karfinsa yake taune layin.

*****

Alhaji dan gaske kuwa tuni ya dagawa baffa hankali akan lallai sai Ummul ta dawo,wanda hakan yasa a washegarin ranar da aka cika kwana uku da faruwar al'amarin mufty da bely ya sanya Ummul a gaba suka tafi gidan Alhaji dan gaske, Ummul har da hawayenta, amma baffa ko dubanta bai yi ba bare ta sa ran zai ji tausayinta,lokacin da suka isa gidan, baffa ya tsaya a wajen aikinsa Ummul kuma ta shige cikin gidan,sosai mommy ta yi murna da dawowar Ummul din wanda har hakan sai da ya so bawa zezee da bely da suke tare a falon mamaki,bely kallon Ummul ta dinga yi tana raya abubuwa da yawa akanta, Ummul bata kalli ko daya daga cikinsu ba barantana su sa ran samun gaisuwa daga gare ta,binta su kayi da ido har ta kulewa ganinsu,zungurar zezee bely ta yi tare da yi mata alamar da su shiga ciki da ido,tashi su kayi suka bar falon,yayin da mommy ta bi su da kallon tausayi.

Suna shiga dakin bely ta dubi zezee ta ce"zezee ya zan yi ki bani shawara Yaron nan fa ya ki saurarata jiya da na hadu dashi a wajen zooroad baki ga cin mutuncin da yayi min ba"numfashi zezee ta ja kana ta ce"bely ba zaki taba samun kan yaron nan ba in dai har baki bi ta kan wannan mayyar kanwar tasu ba,suna ji da ita yawa tsoka daya amiya dan haka idan kina son cika burinki ki bi ta kanta,"wani mugun murmushi bely ta saki kafin ta yi solut din zezee tana cewa"wallahi mutuniyata wani lokaci kanki yana kawo wuta, wannan shawarar taki ta yi, kuma yanzu take har na gama shirya ta yadda zan yi komai na har na kai ga cimma burina"me za ki yi"?zezee ta tambayeta tana kokarin kwanciya saman makadeden gadonta,"idan na aikata koma meye zaki sani daga baya"cikin rashin damuwa zezee ta rufe idanunta tare da dora filo saman kanta tana cewa "bani da damuwa da koma meye zaki yi"ƙarar tsayuwar motar da suka ji ne yasa bely saurin bankaɗa labulen window dan ganin wanda ya shigo gidan,zaro ido ta yi ,kafin cikin murna da sauri ta dawo ta ɗauke fulon da zeze ta yiwa kanta rumfa da shi,tana cewa "tashi tashi zezee baki ga ta bacci ba,dan ga oga Dr Bilal can ya kara so"cikin hanzarin itama zezee ta tashi zaune tana yiwa bely kallon mamaki kafin cikin mamakin ta ce"bely kin san kuwa tun yaushe rabona da Dr Bilal?"girgiza kai bely ta yi jiki a sanyaye saboda yadda zezee ta yi maganar a sanyaye kuma cikin yanayin tausayin kai,tashi ta yi ta karasa jikin window tana kallon motar Dr Bilal din yana zaune a ciki bai fito ba, sannan ta ce"bely wannan zuwan ba nawa ba ne na Ummul ne"kamar yaya ba zuwanki ba ne,ita Ummul din ba tana a matsayin matar abbanki ba ne yanzu?"cikin kukan da yake son kwarewa zezee ta ce"abinda kika fada nima shi na sani,sai dai a wajen Dr Bilal ba haka ba ne,domin na kula duk sanda kika ganshi a gidan nan to Ummul ta zo,a yanzu na fara tunanin anya kuwa babu wata alaƙa dake tsakanin Ummul da Dr wadda suke yi a bayan fage?"dafa kafadar zezee bely ta yi kafin cikin gaskata hasashenta ta ce"zezee komai da kika fada zai iya tabbata sai yanzu kika farkar dani na hangi a binda kika hanga,idan hasasehnmu yayi daidai ke nan dr cin amanar surukinsa yake kenan?"shiru su kayi baki daya, kafin daga bisani bely ta ɗan bubbuga kafadar zezee tana cewa"kar ki damu zamu yi maganin abin amma yanzu ki shirya kije ki ji ko da wani bazatar yazo mana"bely ba zan iya zuwa ba, domin zuwana ba zai amfaneni da komai ba face ciwon zuciya,"tana gama fadar haka ta koma kan gadon ta kwanta tana tsiyayar hawaye.bely ta ce"wannan abin da kuke shirin yi ba mafita ba ce,ina jiye miki da na sani a wannan gabar, dan haka ki tashi kije ki danne zuciyarki akan duk abinda zaki gani idan ba haka ba, ba zaki taba cinnasara akan abinda kike nema ba"hudubar bely ce ta sa ta mukewa ba tare da ko mayafi ta sanya ta rufe jikinta ba.

****

Har yanzu yana cikin motar a zaune ga dukkan alamu akwai abinda yake yi wanda ya dauke masa hankalin da yasa har bai san lokacin da zezee ta kara so ba,bely dama bata yi gangncin biyo ta ba, dan suna fitowa ta shige motar ta ta bar gidan.

"Hello Dr baka gaya min zaka zo ba"ba tare da ya kalleta ba,ya ce"ina kika ajiye sallamar?"dan dibibicewa ta yi sai kuma ta ta ce "Salamu alaikum" idanunta akan computersa da take saman cinyarsa yana ta latsawa,cikin yanayinsa na kullum ya amsa,daga haka bai kuma cewa da ita komai ba,gajiya ta yi da tsayuwar da kuma shurun ta ce"Dr mu karasa falo mana"no nan ma is ok"ya fada tare da daga idanunsa ya jefa su ta can wani sashe wanda hakan yasa itama zezee ta juya dan ganin abinda yake kallo wanda ita bata san da zuwansa ko zamansa a wajen ba,wani irin bugun zuciya ne ya sameta har sai da ta kai ga dafe saitin zuciyarta, kai tsaye ta fara tunkarar inda Ummul take tana aikin gabanta, dan a yanayinta ba zaka taɓa cewa ta san da zamansu a wajenba sai dai ina daga can karkashin zuciyarta tana jin yadda idanun Dr yake yawo a jikinta zuwa jininta,"karki sake ki je inda take muddin kika je kuwa"umh ya karasa maganar da sakin wani dan malalacin murmushin da ya kusa sumar da zezee a tsaye,daga haka ya maida ƙafarsa cikin motar ya rufe tare da yi mata key, ba dan zezee ta yi saurin matsawa ba to da tabbas sai ya taka mata koda yatsu ne,zezee kasa motsa wa ta yi daga wajen ,kenan Abinda nake zargi ya tabba?ke nan Dr Ummul ya zo gani ba ni ba?kallonta na sakon hamsin kadai ya gamsar dashi akan ita da tayi tsayuwar mintuna fiye goma goma a gabansa?wai kuma har gargadinta yake akan Ummul ɗin?kai anya kuwa zata iya rike alkawarin da ta daukarwa abbanta na bazata sanar da Ummul Matsayinta a wajensa ba,?tabbas dole ne sai ta sanar da Ummul abinda bata sani ba,wanda take ganin shine mafaitarta ta farko da zata samu ta rabu da Dr cikin sauki, wannan tunanin da ta yi ne yasa ta tun karar Ummul din gadan gadan,sai dai kuma kamar wadda aka dakatar haka ta tsaya cak,Tata tuna gargadin Dr me zafi akan kusantar Ummul din a dai-dai wannan lokacin"canja hanya ta yi tana jin shakkar tsallake maganarsa dan kar hakan ya kuma jawo mata wani mummunan asarar.

Duk abinda take Ummul na kallon ta sai dai bata nuna hakan ba,harara ta bita dashi lokacin da taga ta fasa zuwa inda take,kafin ta maida hararar tata kan hanyar da Dr ya bi ya fice daga gidan tana jin wani irin zafin dr Bilal na babu gaira babu dalili.

*****

Acan bangaren Alhaji dan gaske kuwa ,hanzari yake ya tashi office da wuri saboda ya tarar da Ummul a gidan tun kafin ta gama aikinta ta kara gaba,hakan yasa ya gama ayyukansa da wuri, sai dai yana shirin fita daga office din wani yaronsa ya zo,da bai yi niyar tsayawa ba,amma sai yaron me suna killer ya nuna masa cewa maganar da ya zo masa da ita tana da matukar muhimmanci, komawa Alhaji dan gaske yayi ya zauna yana cewa "ina sauraronka killer"numfashi ya dan fara ja kafin ya ce"ya haj aikin da ka sani a kan binciken aurenka da yarinyar nan shi na kawo maka"gyara zama Alhaji dan gaske yayi yana cewa"yauwa to me sakamakon ya nuna an samu wani abu ne bayan tabbacin da na samu na cewa nine mijin?"Yes Alhaji an samu,bincike na ya nuna min cewa tabbas ba da kai aka daura auren nan ba kuma da hadin bakin uban yarinyar,sai dai na yi iya yina dan gano wanda aka daura dashi amma hakan ya faskara,shi yasa na ce bara to na fara kawo maka wannan rahoton kafin na binciko ainihin wanda aka yi wannan musayar dashi"killer killer killer"Alhaji dan gaske ya fada har sau uku yana mai share zufar da take keto masa ta cikin hularsa,amsawa killer yayi, kafin Alhaji dan gaske ya dora da cewa"me ye tabbacin ka akan binciken da ka yi?"killer ya ce"ya haj ka san bana kawo maka abinda ba haka ba,dan haka ina so ka yi abinda za ka yi dan ka tabbatar da maganar nan"tashi Alhaji dan gaske yayi yana cewa "aiko zan yi,tabbas zan yi bincike a yau dan tabbatar da abinda ka zo min da shi, wallahi wallahi wallahi idan har na tabbatar da maganar nan sai na sanya rayuwar huzu da yarsa a cikin bala in da basu taba mafarkin shiga ba,zan sauya musu rayuwa ta hanyar sa su gudun neman ceton rai,Ni buzu zai yaudara ya wulakanta,Ni Alhaji Ahmed zai ciwa mutunci ta hanyar boye min abinda yake faruwa,tabbas kai ma lokaci yayi da zan yi fata fata da rayuwarka , a wannan karon zaku gane ainihin waye Salisu dan gaske"tamkar kububuwa haka ya fice daga office din yana kokarin danne zuciyarsa da boye tashin hankalinsa duk akan kudirin da yake cikin ransa.

Da sauri raliya sakateriyarsa da ke leɓe jikin ƙofar ta matsa baya saboda karon da su kayi da Alhaji dan gaske, cikin mamaki yake kallon ta kafin ya kai hannunsa ya shaƙe wuyanta yana cewa "dan ubanki fada min wanda ya turo ki dinga yi masa leken asirina?"raliya kuwa magana ta kasa saboda tsananin yadda Alhaji dan gaske ya shakure mata wuya gaba daya idanunta sun firfito waje gab take da shekawa lahira,zubar da ita yayi a wajen yana kwalawa killer kira kamar wani tsohon mafarauci, da sauri killer ya ƙarasa fitowa daga office din yana cewa"ya haj"nuna masa raliya dake sheme tana kakarin mutuwa yayi yana cewa"maza ka kwashe ta kar ka bari ta mutu har sai ta sanar da kai wanda take wa aikin leken asirina"daga haka ya fice daga office din kansa na kuma ɗaukar zafi akan abinda ya kama raliya da shi,lallai yana bukatar jin wanda ya sa raliya wannan aikin da kuma irin bayanansa da ta dauka ta fitar,to wai ma shi me ya kaishi sakin jiki da raliya tun farko ba tare da ya binciketa ba,kamar yadda ya saba ga duk wani ma aikacin da zai zauna akarkashinsa,da wannan tunanin ya je gida, dai-dai ana ta kiran Sallah magriba,amma Alhaji dan gaske baya tunanin salla a ransa sai hanyar da zai bi ya magance damuwarsa wato Ummul da Alhaji Ahmed dan utopia da kuma gwarzon dansa BILAL AHMED ƊAN ITOPIA,wanda a yanzu duk duniya bashi da damuwar da ta wuce su.

Kai tsaye dakin Ummul ya nufa,yana lekawa ya sameta tana sallah dan haka sai kawai ya rufe ta3ta waje, kana ya wuce zuwa dakinsa har zai shige sai kuma ya dawo da baya tare da bude dakin mommy ya sa kai,Mommy da waya ke hannunta tana ta kaiwa da kawowa kamar tana neman wani a waya ta kasa samu, ta ɗan zabura saboda ganinsa da bata yi tsammani ba,kallo daya yayi mata ya koma ya fice daga dakin,ajiyar zuciya ta sauke tare da saurin cire layin da ta sanya tana kiran dashi,banɗaki ta shiga ta yi floshin dinsa, Sannan ya dawo dakin tana kokarin daidaita mutuwarta.

*****

Ita dai Ummul tana Sallah ta ji alamun shigowar mutum da komawa, amma dake hankalinta yana wajen Ubangiji shi yasa bata fahimci komai ba,tana idarwa bata yi wani dogon Zama ba ta shafa addu'a ta mike saboda bata son yin dare bare a ce ta kwana a gidan makiyinta,yau da hijabi da zo shi yasa ko ciresa bata yi daga cikinta ba,ta dauka yar jakarta ta ka'ida,tare da nufar hanyar fita,sai dai me zata ji? gam kofar a rufe wanda hakan yayi matukar bata mamaki,to waye ya rufe ta?ko dai zezee ce,tunda dama tasan tana cike da ita tun daxun,duk da cewa yau a saninta bata yi mata komai ba,bata taba tunanin baban zezee ba ne dan bata ga dalilinsa na yin hakan ba, wayarta ta dauka dan kiran mommy ta zo ta bude ta, amma sai dai kash wayar babu ko sisi,gashi kofar irin kofar nan ce da idan ba mutum yana kusa ba,ba zai taba jin maganar da kake yi ta ciki ba,komawa ta yi bakin katifar ta zauna tana jiran ganin ikon Allah.

****

Wanka yayi ya sanya jallabiya Sannan ya fito ya tunkari gate,baffa na hangoshi ya ji kirjinsa ya yanke ya fadi,dan kuwa sosai Alhaji dan gaske ya zamewa baffa abin tsoron ji da gani,cikin rawar jiki ya karaso gaban Alhaji dan gasken yana masa Barka da fitowa dan shi a tunaninsa ma ko Sallah zai shiga Masallaci yayi duk da yasan cewa hakan ba dabi'arsa ba ce,ganin dan gasken bai amsa shi ba, Sannan bai dauke kai daga kallon tsakiyar idon da yake masa ba,yasa jikin baffa ya kuma daukar rawa,dan da za'a duba shi a lokacin tsaf za a same shi da hawan jini.

****

Tunda zezee ta koma daki take sintiri da tunanin yadda zata fidda Ummul daga rayuwar Dr, cak ta tsaya da ga kaiwa da kawowar da take ,ta lokaci daya tana sakin wani shu umin murmushi,kafin bakinta ya furta "asid.

******

Ita ma bely Tana zuwa gida ta kira yaranta, ta shirya musu yadda take so a taso mata Ummul a daren yau a lokacin da take fitowa daga gidan su zezee dan tafiya gida.

******

Zumbur Ummul ta mike tsaye tare da daga kiran yaya gentle din da sunansa yake ta yawo akan fuskar yar karamar wayarta,"fito mu tafi ina waje"abinda ya fada kenan ya kashe wayar,gadan gadan ta tunkari kofar ba tare da ta tuna cewa har yanzu fa kofar a rufe take ba.

*****

Cike da isa da gadara Alhaji dan gaske ya bude baki ya ce da baffa"yau anan Ikram zata kwana saboda ina bukatar na kadaice da matata, kaga wannan ita hanya mafi sauki da zata san cewa ita din matata ce ba matar wani ba".....

Dumm ..dummm...dummm....dakan da kirjin baffa yayi kenan.

Cikin sauri gentle da ke jikin gate din gidan a tsaye yana jiran fitowar Ummul , ya rufe idanunsa tare da dora hannunsa akan kirjinsa,kafin cikin wani irin zafin nama ya bankada gate din da wani irin matsiyacin karfi,wanda tsananin karar da gate din yayi har Sai da ya sanya Alhaji dan gaske fara fitsari a wando dan a zatonsa 'yan fashi ne.....

Wash alkalamin ya karye✍️

NA san dai jiya na sha kira, to amma dai ina neman afuwa ba laifina bane laifin solar gidanmu da ta tsinke ne,bani da caji,

Sorry nima na dan taba irin na Ummul 😂😂

Wutar mu ce ta lalace kwana ɗaya ban samu caji ba shi yasa kuka ji Ni shiru jiya, wannan shine gaskiyar zance😂😂

Zahra✍️***

💕GIDAN ƳAN ƘARYA💕

By

FATIMA Y ADAM......

Littattafan marubuciyar.

KUDIRAR ALLAH

KADDARATA SANADIN HASKE

ƁOYAYYIYAR RAIHAN

ƳAR GIDAN YARBAWA

MATAR ƊAN BIRNI

And

GIDAN ƳAN ƘARYA....