GIDAN YAN KARYA

Pg34

by @zahrawriter12

Tunda Ummul ta tashi a rayuwarta bata taba ganin bindiga ba,shi yasa yau din take ganin abin kamar a mafarki,"tambaya daya zuwa uku nake so ki amsa min sai ka rabu da ke na maida ki gida abinki,me ye hadinki da dr Bilal?"da sauri ta girgiza kanta bakinta har rawa yake wajen amsa masa da cewa "babu komai tsakaninmu ban taba sanin sa ba ka sai ranar da ya fara zuwa wajen aunty zeeze wlh Abba da gaske nake na daina karya wlh gaskiya nake fada maka"shi kuma wancan matsiyacin na kofar gidan ku fa meye alakarki da shi?"ya fada yana kara cusa mata bakin bindigar a goshinta,shiru ta ɗan yi wuyanta na sama da kasa saboda miyan da take hadiya da kyar,tsawa ya daka mata wanda yasa ta matukar firgita,"ba magana nake miki ba"cikin saurin baki ta ce"wallahi ban sani ba,ban san komai ba"ba za dai ki fada min gaskiyar da na nema ba ko?"girgiza kanta tayi idanunta na zubar da hawaye, Sannan ta ce"wallahi gaskiya nake fada maka Abba ban San komai ba"janye bindigar yayi Sannan ya zuba mata ido yana cewa"ikram baki san cewa ina sonki ba"?da wani irin razana ta dubesa idanunta dauke da kallon mamakinsa duk da cewa dama tasan cewa abinda yake yi akanta akwai manufa, amma ba ta yi tunanin wannan babbar kalmar ce lamarin ba.

bai damu da yanayin ta baya ci gaba da cewa"idan baki sani ba to yau ki sani,zan iya yin komai saboda ke,karamin abun da zan yi saboda ke shine kisan kai"cikin kiɗima ta sanya hannunta akan bakinta ta toshe saboda kukan da yake shirin subce mata,bindigar dake hannunsa ya shiga jujjuyawa yana ci gaba da cewa.

"Zan baki aiki guda daya zan kuma baki zabi guda biyu, sannan akwai kashadi ,duk wanda baki aikata ko kin yi daidai ba, to daidai yake da mutuwar rayuwa masu muhimmanci a cikin rayuwarki, aikin da zan baki shine,yanzu idan kin koma gida ki sanya mahaifin ki a gaba ya sanar dake mijin da ya aura miki idan har bai fada miki ba to a bakin ransa,idan kuma ya fada miki to kin fansheshi,zabin da zan baki kuma shine, idan har kika tabbatar da mijin da ya aura miki to zaki rabu da mijin ki dawo gareni,idan kuma kika ƙi to a bakin ran wanda aka aura mikin,zabi na biyu shine duk abinda kika ji zan aikata akan dr Bilal dole ki sanya hannunki a ciki ma'ana zaki taya ni yaƙin cimma burikana saboda naga alamun cewa shima ya fada dake kuma zan iya yaudararsa dake kamar yadda babanki tsohon najadu yayi min,idan ba haka ba a bakin ran yan uwanki duka maza,kashedi kuma da zan miki duk wanda kika sake kika fadawa abinda kunenki suka ji to abakin ran kaf ahlinki".

tsananin razana da abinda kunnuwanta suke ji suke gani yasa ta fashewa da wani irin kuka har da ihu tana bige bige kamar wadda ta zare,da sauri ya riketa yana cewa"Ni ban yi miki dole ba zaɓi kawai na baki idan kin bi shike nan kin cececi rayuwar mutanen da suke a karkashinki,idan kuma baki amince ba wannan ma bani da matsala dan ni bana daukar alkawarin da nasan ba zan sauke ba, dan haka ki ƙaddara cewa zan aikata fiye da abinda na lissafa miki,kuma daga ƙarshe dai dole nine da nasara tunda xan daukeki mu yi nesa da duniyar nan gaba daya muje can inda zamu yi rayuwa daga ni sai ke".

Daga haka ya juya ya adana bindigarsa Sannan ya tada motar suka fara tafiya,sai da suka fara shiga cikin gari ya ɗan waiwayo kana ya ce da ita "idan baki min shuru ba sai na fasa kokon kanki da bindigar nan".ya fada yana nuna ta da bindigar,

Take Ummul ta hadiye kukanta,sai dai bata daina na zuci ba, Sannan kanta ya cushe da tsananin mamakin batun auren da aka daura mata, wanda ta jishi daga sama,ta yaya za a ɗaura mata aure ba tare da sanin ta ba?idan an daura mata aure da waye aka ɗaura auren?"to ai koda abban zezee bai ce ta nemo masa ainihin wanda aka daura mata aure da shi ba,to tabbas ita kanta sai ta nema,iya sanar mata da yayi ma kaɗai ya isa ba sai ya haɗa mata da abinda ita ma dole take son sani ba.

Ji ta yi kawai yana ce mata"fita kije ki fara aikinki,kuma ki san da cewa duk wani motsinki yana kan idona".

A sanyaye ta fice daga motar idanunta sun yi jawur kana gani kasan cewa tasha kuka ba kadan ba,dan jijiyar kanta har wani motsi take yi,wani mugun kallo Alhaji dan gaske ya watsawa gentle da ke zaune a mazauninsa yana gyaran wani sosashshen takalmi kansa a sunkuye,cikin shigarsa ta ko yaushe.

Ummul kuwa da ganin gentle ya tada mata wata irin kewa da kukan da take jin cewa babu me iya rarrashinta idan bashi ba,yasa ta yi kamar zata tsaya amma sai Alhaji dan gaske ya daka mata wata irin gigitacciyar tsawa,yana cewa"ko da a ce shine mijinki ban baki umarnin kara kallon inda yake ba idan ba haka ba zaki nadama me tarin yawa a rayuwar kuruciyarki zuwa girmanki,wuce ki shiga gida ki fara lissafin karewar wanakin wasu rayayyu muddin baki abinda ya da ce ba"da sauri Ummul ta shige gida kamar zata kifa batare da ta kuma kallon inda gentle yake ba.

Sai da Alhaji dan gaske ya tabbatar da shigar ta gidan Sannan,ya dawo da dubansa kan gentle da har yanzu bai dago kansa ya kalli inda suke ba,yana cewa"kai kuma zaka gane cewa ni ba a yaudarata daga kai har munafukan da suka shirya komai ina nan biyowa ta.kansu suma bari na gama da kai ɗan karamin alhaki kawai".

Shiga motarsa yayi ya ja ta da karfi tare da bule gentle da ƙurar wajen.

****

Da sauri Ummi da baffa tare da Safwan da Ali suka mike tsaye saboda ganin yadda Ummul din ta shigo gidan kamar an watsota,tareta ummi ta yi tana dudduba jikinta ko zata ga wani ciwo,sai dai bata ga komai ba,hakan yasa ta ja ajiyar zuciya tare da yiwa Allah godiya, baffa ne ya ce"daga ina kike Ummul? tun dazu aka ce an kawo ki har kofar gida tare da kula, amma ko da muka fita bamu sameki ba sai kulolin da aka ce an sauke ki tare dasu,me ya sameki?"a maimakon ta bashi amsa sai kawai ta tsugunne a wajen tana wani irin kuka numfashinta har sarkewa yake,hankalinsu ne ya kuma tashi ,su mufty tuni suka zagaye ta idanunsu cike da kwallar tausayin Ummul din duk da cewa basu san me ya sa meta take irin wannan kuka ba, amma sun san duk abinda zai sauya Ummul a lokaci daya irin haka to ba karamin abu ba ne.

Dukansu an rasa wanda zai iya rarrashinta hakan yasa suka bari ta yi me isarta, sannan dan kanta ta bari ta dago kanta tare da zubawa baffa idanunta da suka rine kamar basu ne waɗannan fararen idanun masu kama da madara ba,kana cikin Muryarta da ta shaƙe ta ce"baffa da gaske ne ni ɗin matar aure ce?da gaske ne akwai igiyar wani a kaina ina yawo da ita ba tare da na sani ba?baffa idan da gaske ne waye mijin?kuma me yasa aka rufe min ba a gaya min ba?".

Ajiyar zuciya gaba daya suka sauke kafin daga bisani,baffa ya kama hannun Ummul din ya maida ita kan tabarma ya zaunar shima ya zauna, Sannan su duka yayi musu umarni da su zauna,ba tare da wani jan rai ko nuku nuku ba,baffa ya warwarewa Ummul kaf yadda su kayi da Alhaji dan gaske akan aurenta,da yadda ya maida auren kan gentle acewarsa saboda yaga kamar Ummul din shi take so.

kuka ta sanya sosai tare da cewa"baffa da ka sani ka daura da shi, tunda ka san ba ka tanadi makaman yaki dashi ba,wane irin tunani ka yi akan makomar rayuwarmu da har ka yanke hukuncin daura min aure da yaya gentle?"cikin sanyin murya wadda take cike da yaƙini akan furucin da zai yi ya ce.

"Ummul Allah na tuna, saboda shine Ubangijin da ya halicci duniyar baki daya ya kuma halicci Mutum da zuciyarsa, Sannan shine ya ce a duk lokacin da muka shiga cikin tsanani mu tuna dashi, ma'ana mu koma gareshi dan neman ɗauki,shi kuma yayi mana alkawarin zai amsa mana, yana kuma tare da duk wanda yake tare dashi, yana kuma jibantar lamarin bayinsa masu roko a gareshi masu nema a gareshi, wanda suka yi tawassali da shi suka rike shi suka yadda cewa shi daya ne ba shi da abokin tarayya, suka kuma amince Annabi Muhammad Sallallahu alaihi Wasallam ma'aikinsa ne,ma'ana ɗan aiken sa ne,wanda ya aiko da shi da addinin gaskiya dan ya sanar damu, kuma ya shiryar damu, wanda ya sanar damu yadda zamu bautawa Ubangiji,wanda Ubangiji ya saukar masa da alkur ani me tsarki, Ummul wannan shine abinda na tuna wanda kuma a take Ubangiji ya kula dani ya amshi rokona ya kawo min mafita ta inda ban taba zato ko tsammani ba,wanda hakan yasa tsoron Allah ya kuma shigata na kuma jinjina kudurarsa da buwayarsa ,wato Ummul ikram duk wanda ya tsaya ga Allah to ya samu babban rabon duniya da lahira, wanda kuma bai ji tsoron Allah ba ya taɓe duniya da lahira,dan haka ta shi kije ki huta anjima ki tashi ki nemi zabin Allah".

Ko baffa bai bukaci ta tashi ba dama tashin ya zamar mata dole,duk da cewa ta wani ɓangaren ta samu nutsuwa da kalaman baffan,amma har yanzu tana cikin tsoro da wasu wasi kan hukuncin da dan gaske zai yi akan gentle dinta,Ummi ce ta kama ta ta miƙar Sannan ta riƙe ta suka shige daki,Ali da mufty ma tashi su kayi ba tare da sun iya cewa komai ba,sai dai suma sun ƙaddara a ransu sun dena ɗan baccin da suke yi cikin dare.

Ummi bata fita ta barta ba sai da taga ta yi bacci, sannan ta shafa kanta cikin tsananin kauna da tausayi tayi mata addu'a sannan ta fice daga dakin.

Ummi tana fita Ummul ta bude idanunta, dan dama ba bacci ta yi ba,ta yi hakan ne dan ta kwantarwa da Ummi din hankali,numfashi ta ɗan ja tare da maida idanun ta kuma lumshe su,tana rasa abin yi, shin farin cikin kasancewarta matar gentle za ta yi ko kuma kukan bakin cikin auren nasu ya zo da kalubale zata yi?sai yanzu abubuwa da yawa suke dawo mata dan gane da abinda ya faru tsakaninta da gentle,wato dan yasan ita din matarsa ce shi yasa yake mata irin wannan abubuwan,moment dinsu na wajen cin abinci ta tuna wanda har sai da murmushi ya subce mata,tare da sanya hannu ta rufe fuskanta kamar wadda take gabansa,da karfi ta dafe kirjinta tare da ambatar astagfurullah saboda tunawa da moment dinta na tsakanin jiya da yau ita da Dr, ta shi ta yi zaune tana buɗe dukkan idanunta a yayin da kalamansa suke dawo mata cikin kwakwalwar ta,(ina sane da duk abinda nake,Ummul ni me tsantseni ne bana taɓa kayan da ba nawa ba")Marin fuskarta ta shiga yi tana cewa"me yake faruwa da ni?me wannan kalaman nasa suke nufi?me yasa kalamansa suke kamanceceniya da na gentle?shin akwai wani dalili da yake sanyawa mutum ya sumbaci matar da ba muharramarsa ba bayan dalilin aure?ko akwai dalilin da yake sawa ka rungume matar da ba halal dinka ba bayan dalilin aure?"da karfi ta daki tsakiyar katifar gadon da take kai,daga nan ta shiga warware gashin kanta tana jin kamar yana kara mata nauyin ƙwaƙwalwa da na zuciya.

Wayarta ta fara lalube sai da ta duba ko ina bata ganta ba sannan ta tuna tana dakinta na gidan Alhaji dan gaske,A'isha take son kira,saboda a daidai wannan lokaci tana bukatar wanda zai taya ta tunani akan gentle da dr Bilal,rashin ganin wayar yasa ta zari hijabinta ta sanya Sannan ta debi takalmanta a hannu,cikin sanda ta leka tsakar gidan,ganin Ummi bata tsakar gidan yasa ta saurin fitowa ta fice cikin sanda ba tare da ta sanya takalmin ta a kafarta ba.

Karon da ta ci da mutum a daidai fita daga zaurensu yasa ta dafe goshinta tare da duban wanda suka ci karon da shi duk da cewa zuriyarta ta sanar mata da ko waye,yadda ya zuba mata ido ita ma haka ta sanya masa ido, zuciyarta na tsananin bugawa da tarin tunani akansa,ina zaki je?".

Ya tambayeta cikin tsare fuska kamar wanda aka yiwa albishir da mutuwa,kawar da fuskarta ta yi ba tare da ta amsa masa ba, tana kokarin yin jarumta wajen kawar da damuwarta da raunin ta,amma hakan ya faskara dan tuni raunin ya rinjayi dakiyar har bata san lokacin da ta kai masa wata hadamammiyar runguma ba,zuciyarta da gangar jikinta suna dauke da wani irin shauki da so da kuma rauni tare da tashin hankalin kalubalen da tsaka mai wuyar da take ciki.

Ba komai ne yake kuma ragargaza mata zuciya ba,sai tsananin tunanin,shin wa zata fansa gentle ko Dr,bayan dukkansu jinsu take kamar sun zama rayuwarta,a baya bata dauki Dr a matsayin komai ba sai na wanda yake wa rayuwarta shishshigi da yawan sanyata a cikin Matsala,amma daga ranar da okacin da ya fansheta a hannun Alhaji dan gaske da kuma rana da lokacin da ya fanshi rayuwarta ya sallama tasa rayuwar a hannun mugun mutumin da har yanzu bata san daga ina yazo ko wanda ya turo shi ya nakastata ba take jin wani abu na musamman a kansa,ga kuma gentle da ta tabbatar da cewa ko bai gwada ba zai iya yin makamancin hakan a gareta,idan haka ne ke nan ya zama dole ta fanshi rayuwar su duka biyun,idan tana son fansar rayuwar Dr dole sai ta yi Abu daya zuwa biyu wanda shima yana cikin wata babbar sadaukarwar, idan ta fadawa Dr sirrin Alhaji dan gaske,hakan na nufin Alhaji dan gaske zai kashe gaba daya ahlinta,shi kuma gentle idan tana son fansar rayuwarsa sai dai ta sa ya tsinke igiyar aurenta dake kansa,wanda shi kuma hakan zai iya sanadin salwantar nata fitar numfashin?shi dama baffanta ta fiddashi tunda ta riga ta sanya ya faɗa mata waye mijin kuma ya zama dole ta sanar da dan gasken ko dan ta ceci rayuwar mahaifinta.

Dago fuskarta da gentle yayi shi ya yanke mata tunanin mafitar rayuwarsu su duka da take yi,a hankali ya kai bakinsa daf da idanunta ya ɗan hura mata iska wanda hakan yasa ta ƙifta idanun ta da suke kafe kaf ba tare da suna motsawa ba,daga nan ya ɗage mata gira tare da yi mata alamun me yake damunta ta hanyar magana da idanunsa,da sauri ta girgiza masa kanta tana mai kara kwantar da kanta a kirjinsa,a hankali ta sanya hannunta zata zagaya dashi ta barin cikinsa, amma sai ta ji yana kokarin ture ta, ta hanyar ce mata,"naga baki cikin yanayi me dadi gashi kin fito ba tare da Ummi ta sani ba,ki koma gida kar na kuma ganinki kin yi satar hanya kin fito".

Sakin shi ta yi tana dan ja da baya, kafin ta watso masa tambayar da bai yi zato ba,"Yaya gentle zaka iya rabuwa da ni?ma ana zaka iya tsinka igiyoyin aurenka dake kaina?"

Yadda ya yo kanta hannuwa bude baki bude kamar zakin da ya kwana goma bai ci ba bai sha ba,hakan yasa ta tsugunne a gurin tare da kifa kanta a cikin gwiwoyinta tana jiran saukar dukansa,amma sai ta ji shiru tsawon sakonni hansin, hakan yasa ta fara ɗago kanta a hankali dan ganin abinda ya dakatar dashi daga kai mata dukan da ta tabbatar yana yi mata shi sai lahira.

Ganinsa ta yi a tsaye akanta yana watsa mata kallon da yake cike da haushi da takaici, cikin bayyanannen yanayin da bata taɓa ganinsa a ciki ba,da sauri ta mayar da kanta ta duƙunƙune a cikin gwiwoyinta saboda ta fara tantamar anya ko shi dinne,duba da yadda yake a matukar fussace,dakakkiyar muryarsa da take fita da dan wani kauri da sauti kamar sautin na'urar computer, ce ta fara magana a karon farko tun dukan da furucin Ummul din yayi masa a kahon zaciya.

"Saboda an ruguza miki mafarkinki na auren me arziki irin su Dr Bilal Ahmad Dan itopia ko?"da wani irin hanzari ta miƙe tsaye bakinta har rawa yake, gashi furucin bakinta ya kasa fitowa sai ruwan hawaye da suke zuba kamar famfo daga idanunta,juya mata baya yayi yana ci gaba da cewa "idan har auren me kudi shine burinki kuma saboda haka kike min wannan tambayar to ba zan tauyeki ba zan rabu da ke ki je ki yi auren kudi ta yadda mafarkanki za su cika cif cif".

Babu abinda Ummul take yi sai kuka da faman girgiza kanta ,ta ma rasa hanyar da zata bi yaya gentle din ya fahimceta, ita kanta ta yi furucinne dan ta gwada shi amma har abada bata jin zata iya nemar saki daga gentle din,duk da cewa tana tsoron Allah tana tsoron sharrin Alhaji dan gaske, bata son wani abu ya samu gentle din a dalilin aurenta.

Cikin rawar murya ta tare shi saboda ganin yana kokarin ficewa daga zauren,"ka yi hakuri ba zan kara ba, wallahi ni bana son wani kudi ,ni tsoro ma suke bani,na yadda tun kafin na san zaka aureni zan rayu da kai a duk yadda kake ,tun kafin na san meye Abinda nake ji a kanka na amince zan rayu da kai har karshen numfashi cikin arziki ko talauci,dan Allah yaya gentle kar ƙi fahimtata"

Cikin natsuwar da ya samu a lokaci daya ya juyo yana kallonta ba da irin kallon dazu ba ,ba da irin fuskar dazu ba,ba kuma da irin harzuƙar dazu ba,kafin ya kara takunsa dan hade tazarar da ya bari a tsakaninsu, sai da ya zo daf da ita sannan ya sunkuya bisa kanta yayi mata rumfa, duk da cewa a tsaye take, Sannan a nutse ya fara cewa"idan kuwa haka ne ki sa a ranki duk runtsi duk wuya gentle yana tare da Ummul ikram,babu wani karamin barazana da zai sa ya rabu da ita,haka babu wata hanyar mutuwa ko a zabar da zai gwammaci mutuwa da zai sanya gentle rabuwa da Ummul ukrammm,je ki kwanta ki bacci kafin anjima, idan kuma kika yi kuka ina kallonki,dan haka idan na zo cikin barcinki sai na cinye bakin kukan, xan kuma hukunta idanun da suke zubda hawaye masu tsada irin na sarauniyar mata Ummul ikrammm"daga haka ya sanya bakinsa ya sumbaci lips dinta Sannan yayi mata alama da gira da ta tafi.

Cikin kasalar da ya sanya mata ta zame ta karkashinsa daga rumfar da yayi mata sannan ta shige gidan tana mai waiwayensa,shima sai da ya tabbatar ta shiga gidan Sannan ya juya ya fice, idan har na kula daidai to murmushi ne akan fuskarsa wanda bai baiyana sosai ba.

Gentle na fitowa matashin saurayin da yake tsaye a jikin garun gidan,yayi saurin fadawa zauren, wani abu ya dauko me kamar na ura ya saka a gefen rigarsa sannan ya fice ya dau hanyar zuwa gidan Alhaji dan gaske.

***

GIDAN ƳAN ƘARYA💕

By

FATIMA Y ADAM......

Littattafan marubuciyar.

KUDIRAR ALLAH

KADDARATA SANADIN HASKE

ƁOYAYYIYAR RAIHAN

ƳAR GIDAN YARBAWA

MATAR ƊAN BIRNI

And

GIDAN ƳAN ƘARYA....