Pg38
Fakan_fakan haka dan gaske yake tafiya yana baza babbar riga, Mommy kam sai ta haɗa da gudu take tadda shi shi,yana tafe yana tambayar emagency,can ya hango wasu mutane cincirindo guda kawai sai ya ratsa ta cikinsu yana kiran,wata mata da ta juya baya da sunan raliya,yana cewa"ki tsaya kar ki tafi dan wallahi ko kin tafi sai na sa su killer sun nemo min ke dole ki dawo ki amsa min tambayoyin da suke cikin kwakwalwata suna ruguza min lissafi"da sauri mommy ta kamo hannunsa tana cewa"haba abban zezee me ya sa kake yin abinda zaka sa mutane suna yi maka kallon mahaukaci cikin riga,ka duba fa ka ga yadda ka janyo hankalin mutane kanmu,ita wacece raliyar da kake nema"?bai bata amsa ba sai da ya hanga ya leka ko ina ya tabbatar da cewa ba raliyar ba ce Sannan ya juyo suka ci gaba da tafiya yana cewa"to a yi min kallon mahaukacin mana,in dai har zan samu biyan bukatata ai ba abun kunya ba ne idan an nuna ni an kira ni da mahaukaci,ke dan ba ki san ya nake ji a cikin jinina da ƙwaƙwalwata da zuciya ta ba ne shi yasa har kike jin kunyar a kira Ni da mahaukaci".
Ita dai Mommy shuru ta yi masa yana ci gaba da bin bayansa,a zuciyarta tana yi masa fatan shiriya idan har yana da rabo.
Suna zuwa emagency suka tarar an canja mata daki saboda ta fita daga crtical condition, kai tsaye wata nouse da ita ce aka bawa kwangilar kula da zezee ta kai su har dakin da aka maida zezeen,suna shiga mommy ta yi kanta a rude saboda ganin yadda ta koma a cikin yini guda, girgizata ta shiga yi tana kiran sunanta,cikin Muryar kuka,a hankali zezee da take jinta kamar ba a duniya ba ta bude idanunta tana kallon abbanta da mommynta kafin ta bude bakinta dakyar tana cewa "Abba ka san waye mijina?"sai a lokacin Alhaji dan gaske ya tuna da wani batun auren da aka daura mata, tsaki ya ɗan saki yana cewa "haba zezee ya za a yi kina cikin wannan halin ki dinga tunawa da wani shirmen Abu da ba zai taba yiwuwa ba,dan Allah ki bar batun nan ki fada mana dalilin rashin lafiyarki da har ya kawo ki wannan asibitin da ba shi muke zuwa ba"?.
Sai da ta saki wani irin numfashi me ciwo Sannan ta ce"Abba wancan maganar auren da kake cewa a barshi ba shi da muhimmanci to shine dalilin da ya kawo Ni ga kwanciya gadon asibiti har ina neman rasa raina"mommy ta ce bangane me kike nufi ba ki yi mana bayanin da zamu fahimta mana"shi kansa Alhaji dan gasken cikin zakuwar jin me yake faruwa ya matsa kusa da mommyn tare da cewa,"zezee maza ki yi mana bayani tun kafin kisa na rasa yar ragowar nutsuwar da ta rage min".
Kuka ta fashe da shi mai tsananin ciwo da cin zuciya,sai da ta yi mai isarta ba tare da sun dakatar da ita ba, Sannan ta bude baki ta basu labarin abinda ya faru kaf ba tare da ta boye musu komai ba, daga karshe ta kuma rufe bakinta da kukan da har sarke mata numfashi yake yi,wani irin zufa ne ya shiga yiwa Alhaji dan gaske wanka a duk sassan jikinsa,kafin cikin hayagaga ya lailayo wani uban ashar ya saki yana ɗorawa da cewa "Ni za'a kawowa iskacin banza,to wallahi duk.yadda kuke ji da iskancinku Ni Na fi ku, saboda Ni guda ne ba rabi ba,ina ne dakin shi ɗan Iskan da aka ce shine mijinnaki?"ya.tambaya yana kallon zezee da har yanzu kukanta ya ki tsayawa,wanda hakan yasa ta kasa yin magana,ganin haka yasa shi ficewa a fusace yana jin kamar ya tashi wuta a garin kowa ya mutu ya huta da wannan bakin cikin da itopias suke kulla masa.
Yana fita Mommy ta sa hannu tana sharewa zezee hawaye tare da dan bata baki,sai da taga kukan zezee ya fara tsayawa Sannan ta mike daga zaman da ta yi daga gefen gadon ta janyo kujera ta zauna tare da kama hannun zezee, Sannan ta kira sunanta har sau uku,ba ta damu da sai ta amsa ba tunda tasan condition din da take ciki,dan haka ta ci gaba da cewa "a yau zan baki labarin da baki taba sani ba,Amma idan na sanar da ke wannan labarin ina so ki yi min alkawarin cewa gaba daya rayuwarki da abinda labarin ya kunsa zai zama darasi da izna gareki"dan shiru ta yi tana jiran amsar zezee,jin jina kai zezee kawai ta yi ba tare da ta dauki abinda mommy zata fada da wani muhimmancin da zai sa har ta yi wani alkawari ba,hannun zezee ta kuma dankewa cikin nata ba tare da ta ce komai ba,zezee kuwa tsam ta yi da ranta tana jiran jin labarin da mummyn zata bata.
*****
Zubawa fuskarsa ido ta yi zuciyarta cike da tambayoyi da kuma mamakin abinda ya kawo Dr Bilal dakin gentle tunda matsayinsa ya wuce ya kwanta a makwancin da ya bawa gentle din na wuccin gadi,dawowa ta yi cikin dakin tare da maida kofar ta rufe,karrar kofar ne ya farkar da Dr Bilal daga baccin da bai san ya dauke shi ba,a nutse ya bude idanunsa da suka dan yi masa nauyi yana kallonta kamar a cikin mafarki,yunkurawa yayi ya tashi yana salati kafin ya zura kafafunsa kasa yana barin saman gadon baki daya,kawar da fuskarta ta yi daga kallonsa saboda yadda ya tunkaro ta a hakansa gadan gadan ja da baya ta fara yi har sai da ta kure bango, shi kuma bai daina binta ba,har sai da suka dangane da bangon a tare,Ita kuwa babu inda take kallo sai cikinsa wajen shatin yankansa kwakwalwar ta ta tafi nazari har bata san lokacin da ya dago da fuskarta yana mata tambayar da ta ji ta a rainin hankali ba"me kike nema anan?"a maimakon ta amsa masa tambayar da yayi mata sai ita ma ta jefa masa tambaya,da cewa"ina wanda ka kawo dakin nan?"dan dum yayi wanda yake nuna kamar ya so ya sha a fa da wani abu, juyawa yayi yana cewa"ina tambayarki kina tambayata to cikinmu wa zai bawa wani amsa?"yaya Dr Kai zaka fara bani amsa sannan na san irin amsar da zan baka"gaban mirror ya tafi yana shiru bai ce mata komai ba,wanda hakan ya kuma harzukata,abinda take zargi ya fara tasiri a cikin kwakwalwar ta da tunaninta, matsowa ta yi bayansa tana kallon fuskarsa ta cikin madubi, Sannan ta kuma cewa "yaya Dr ina yaya gentle yake"sosai ya kara hade fuska ya koma mata asalin Dr Bilal dinsa Sannan ya ce"ki je ki kwanta ki huta an jima zaki ganshi ya dawo,saboda ya je gida zai duba parent dinsa"zata kuma yin magana ya dakatar da ita cikin dakakkiiyar muryarsa wadda take dauke dan tsawa tsawa yana cewa"Ummul tutsiyeni kike yi kamar wani danki"?girgiza kanta ta yi idanunta na cika da hawaye, Sannan cikin rawar murya ta ce"a'a ba haka ba ne, amma dai ni nasan cewa da akwai abinda kake boye min daga kai har su baffa"daga haka ta juya ta fice daga dakin tana sakin kukan da ya ke cin ranta.
Binta yayi da kallo har ta fice daga dakin,ajiyar numfashi yayi tare da dan duba agogon dakin, Sannan ya shige toilet ya dauro alwalar al'asar Sannan ya zura ash din jallabiya ya dauki carbi ya fice daga dakin, ba tare da fuskar shi ta nuna alamun damuwa ko akasin haka ba.
Ummul kuwa direct dakin da ta farka ta ganta a ciki nan ta koma,ta ci sa'a kuwa babu kowa dan haka tana shiga ta maida kofa ta rufe tare da murda key,ta fada saman gadon tana fitar da hawayen damuwar da take ciki,me yasa take zargin Dr Bilal da kasancewa Abu daya shida gentle?take zuciyarta ta bata amsa da cewa"dole ne ki dinga ganin haka saboda komai nasu iri daya ne kama ce kawai ta banbanta,amma kuma dole ne ta gano abinda gentle yake boye mata, sai yanzu ma taga wautarta da ta tutsiye Dr bayan kuma gentle ya kamata ta yiwa tambayoyin da tayiwa Dr,tashi ta yi ta shiga ba yi ta daura alwala ta fito ta shimfida abin Sallah ta sanya hijab Sannan ta tada Sallahr la'asar.
****
Alhaji dan gaske yana fita ya ci karo da wannan nouse din, hakan yasa ya dakatar da ita yana tambayarta inda Musa yake,to dake ta san musan da kuma alakarsa da zezee shi yasa ba tare da wani dogon bayani ba ta gane shi,kai tsaye ta tafi raka Alhaji dan gaske dakin,suna zuwa bakin dakin ya dakatar da ita da cewa"yauwa na gode zaki iya tafiya"ya fada yana mika mata kudin da bai san yawansu ba,karba ta yi tana godiya tare da barin wajen,kai tsaye ya fada dakin yana cewa "ina dan Iskan yake"?yana yi yana kalle kallen inda zai ga Musa,dan bai taba tunanin yakunannen mutumin da ya gani kife akan gadon shine musan ba,sai da ya juya ko ina ya tabbatar da cewa wannan da ya gani fa shi kadai ne majinyaci a dakin Sannan ya dawo wajensa yana cewa"kai ba dai kai ne moses din da ake cewa an daurawa zezee aure da shi ba?"nine Alhaji"Moses ya amsa ba tare da wani jinkiri ba,numfashin Alhaji dan gaske ne ya nemi tsayawa saboda tashin hankali dan duk bai yi zaton abin ya kai munin haka ba,har lokacin kuma bai ga fuskar Moses din ba,sai da ya matsa sosai ta gefen da zai iya ganin fuskarsa yana cewa"ka fada min duk abinda kake so da irin farashin da kake so zan biyaka ka sakar min 'yata"a hankali Moses ya juyo da fuskarsa ta yadda dan gaske zai ganshi sosai yana cewa"ai baka da farashin da zaka iya biyana in saki zezee, ko an gaya maka dan na rabu da ita na saketa?"wani irin dumm Alhaji dan gaske yayi tare da ja da baya yana nuna mosess da shima yake yiwa Alhaji dan gaske kallon sani da mamaki,kafin ya yi dariya yana cewa.
"Sai yanzu na tabbatar da karin maganar nan da Hausawa suke cewa barewa ba ta yi gudu danta yayi rarrafe ba,Salisu dan gaske ashe zezee 'yar ka ce?lallai Allah buwayi ne gagara misali".
Har yanzu Alhaji dan gaske ya kasa magana sai rawa da bakinsa yake da uban gumi da yake haɗawa ya kasa furta abinda yake son furtawa,murmushi me ciwo Moses ya kuma yi, Sannan ya ce"nasan abinda kake son cewa,kana son ka tambayeni ya a kayi ban mutu ba ko?"hannu na rawa Alhaji dan gaske ya yarfe gumin da yake masa tsartuwa a kan goshinsa,kafin cikin roko da magiya ya ce da moses "dan Allah ka yi hakuri kar ka cutar min da zezee, wallahi ko me kake so zan baka na yi maka alkawari"moses yayi masa wani banzan kallo tare da cewa "wallahi Alhaji har abada ba zan kara yadda da kai ba, kai din nan fa ba karamin tsohon dan iska ba ne, ka jima kana ta ta iskanci a duniya sannan kuma yanzu ka ce Allah ba zai yi nasa ikon ba,kaga ka fita ka bani waje tun kafin na yi maka ihu dan nasan tsaf zaka iya karasa ni a dakin nan ba tare da kowa ya sani ba".kai tsaye Alhaji dan gaske ya fice daga dakin zuciyarsa na neman barin mazauninta,dariya moses ya fashe da ita yana cewa,"Alhaji dan gaske ka zo hannu mai fidda kai sai Allah ".
*****
Tun sassafe bely take zagaye a anguwar su mufty, har zuwa yammacin nan da ake gab da kiran Sallah magriba,har yanzu tun jiya ko zeezee ta kasa nema, sai bulayin neman abinda bata da tabbacin samu, bata sani ba ashe mutanen anguwa tun jiya suna lure da ita,dan hatta da motar Alhaji dan gaske da ya tafi sun dauka ita ce ta sake dawowa,dan haka suka hada ganganko dan su kamata,saboda sun yi zaton me satar yara ce take neman hanya ta sace musu yara,dan haka sun riga sun gama shirya mata tarko,sai da suka bari ta fito daga motar tana kiran wani yaro dan ta tambayesa ko ya san inda su Ummul suka tafi,kafin yaron ya kara so ta ji saukar duka da sanduna har da masu jifa ,kan kace meye sun yi raga raga da motarta,.ita kuwa ko numfashi bata iya futarwa,da taya zasu saka mata sai da wasu suka hana suka bada shawarar akaita wajen yan sanda Sannan suka hakura,haka suka jata kamar kayan wanki aka tafi da ita ba tare da tana iya fidda numfashin arziki ba,jikinta ko'ina yayi jina jina kamar an yanka rago.
****
A hankali Mommy ta fara magana da cewa"
Asalin sunan yarinyar bilkisu kuma asalin iyayenta yan Kaduna ne,ita kadai tilo mahaifinta ya mallaka, wanda hakan yasa ya janyo wani yaron makwabtansu jikinsa,saboda yaron bashi da wani cikakken gata,gidan da yake zaune a hannun kanin babansa yake,wanda suka yo hijira daga kauyen baure suka dawo nan da zama,kawai talauci ne yake tawainiya da su, amma iyayen rukonsa suna iya bakin kokarin su akansa, wannan ne yasa ya kama hannun yaron ya zama kamar dan aikensu, tun kafin a haifi bikisu kenan,Alhaji matawalle yana da arzikinsa wanda za a iya sashi a masu kudin wannan lokacin, Sannan yana da don taimakon na kasa dashi dattijo ne me mutunci da sanin hakkokin Allah,l.
A lokacin da aka haifi birkisu tuni wannan yaron me suna Salisu ya zama saurayi , kuma babu inda baya shiga gidan Alhaji matawalle kai idan ba sani ka yi ba zaka iya yin zaton dansa ne na cikinsa,haka matar Alhaji matawalle macece me ilmin addini dan haka bata cutar da Salisu ba,ko da bilkisu ta taso bata taba tunanin cewa Salisu ba dan uwanta ne na jini ba, duk wani girma da soyayya irin ta ɗan uwa ta dauka ta bashi,hatta da karatu Alhaji matawalle ne ya dauki nauyinsa, a haka har iyayen rikonsa suka koma ga Allah, daga nan Salisu ya koma hannun Alhaji matawalle gaba daya ya zama shine komai nasa.
Kwanci tashi a sarar mai rai har bilikisu ta kawo munzalin aure, a lokacin samari da magidanta suka fara Kawo Mata cafka,sai dai ita kuma gama daya hankalinta yana kan wani bawan Allah me suna idris, dan haka ganin yadda samari suka takura mata,yasa ta kai idris ga babanta ,shi kuwa bai yi wata wata ba yasa a ka yi masa bincike akan idris, ko da ya tabbatar da ingancin idris sai kawai ya bashi dama ya turo manyansa aka sanya ranar Aure.
A bangare daya kuma basu san cewa ashe Salisu ya riga ya kwallafa ransa akan birkisu ba,wanda kuma a cikin ransa ba wai son nata yake tsakani da Allah ba yana sonta ne saboda ya mallaki dukiyar da idan babu ran mahaifinta ta zama tata, wannan dalili ne yasa shi shiga cikin kunci da tunanin hanyar da zai bi ya samu abin da yake so,tashin farko yayi tunanin ya jewa da mahaifin bilkisu da maganar ko zai amince musamman sanin matsayinsa a wajen mahaifin nata,amma sai dai kash abinda bai taba zato ba ne ya faru, dan kuwa Alhaji matawalle kai tsaye yabawa Salisu hakuri da nuna masa cewa baya son ya zama karamin mutum,tunda bai riga da yayi Magana da wuri ba yayi hakuri,, amma ya ce masa ya nemo duk 'yar da yake so zai shige masa gaba wajen ganin ya sameta, ashe Salisu ya kullaci ubangidansa da yake tamkar mahaifinsa.
A wata rana da bilkisu ba zata taba mantawa da ita ba, a kuma ranar ne ake sanyata a lalle, a cikin wannan dare mai tsananin muni a gare ta ,suka samu bakuntar yan fashin da suka kwashe komai na babanta bayan sun sashi ya saka hannu akan duka dukiyarsa daga can dakinsa, sannan a take a wajen suka harbe shi tare da matarsa mahaifiyar bilkisu,a lokacin bilkisu tana labe ta windown dakin tana kallo, da farko bata san ko su waye ba,sai daga baya Allah ya nuna mata fuskar Salisu wanda ya kasance oga a cikin yaran,iya razana bilkisu ta razana har bata san ta sume ba,sai farkawa ta yi ta kuma tarar da wani tashin hankalin wai idris dinta mota ta buge shi ya mutu take a wajen ba tare da ya shura ba,ba zan iya misalta miki tsananin tashin hankalin da bilkisu ta shiga ba,dan sai da ta yi kusan wata biyu bata fahimtar komai,a ranar kuma da ta dawo hayyacinta aka daura mata aure da wannan salisun,a ranar kuma ya tare da ita a cikin gidansa dake garin Kano,.
Tun daga ranar zuciyar bilkisu ta soye kullum ba abinda take tunani sai hanyar daukar fansa, ba ta taɓa farin ciki ko na minti ɗaya ba a cikin ayuwarta da Salisu, duk wata rayuwa da zai yi da ita sai dai yayi ta karfi kamar yadda ya fara tun farkon kawo ta da yayi gidansa,har Allah ya sa ta samu ciki ta haife masa yarinyar da yake son maimaita tarihi akanta ta hanyar aura mata dan ubangidansa da yake son ya mamaye komai nasa kamar yadda yayi wa Ubangidansa na farko,kuma duk abinda yake takama da shi a yanzu ba na kowa ba ne sai na bilkisu"ta kare labarin da cewa
"Zeezee ke da kanki nake so ki karasa min wannan labarin idan har kin fahimci labarin waye"daga haka ta mike zata fice daga dakin,zezee ta yi saurin rike hannunta tana wani irin kuka me cin rai....
*****
Duk abinda Ummul take yi, yinsa kawai take a sanyaye ,saboda kanta har ya fara ciwo saboda tunanin da ta takurawa kanta da shi,ganin yanayin nata ne ma yasa ummi take ta lallabata duk dan saboda ta cirewa kanta damuwa.
Ummi bata bar Ummul ba har sai da ta tabbatar ta yi bacci Sannan ta fice daga dakin bayan ta tofa mata addu'a,Ummu tana fita daga dakin Ummul ta bude idanunta tare da tashi zaune,sai da ta dauki kusan mintuna goma a zaune Sannan ta tashi ta zura silifas dinta ta fice daga dakin,sai da ta tabbatar ba kowa a falon Sannan ta wuce dan corridor da zai sada ta da dakin da gentle din yake,a hankali ta yi sallama tana murda kofar sai dai kuma ta ji ta a rufe wanda hakan yasa ta ɗan kwankwasawa har sau biyu,sosai ta ji haushin yadda ya barta a wajen tsawon mintina biyar bayan kuma ya amsa mata ta hanyar yi mata gyaran murya,har ta juya zata koma sai ta ji ya bude kofar tare da bata hanya,kallonsa ta shiga yi har ta shige dakin,mai da kofar yayi ya rufe shima yana kallonta ba tare da yace komai ba,
Dakin ta koma tana kallo kafin ta kuma maida idanunta kansa, tana kokonton yanayin da ta ganshi aciki, duk da ya kasance mutum mai nutsuwa amma yanayinsa sai da ya nuna cewa akwai wani abu da yayi kafin ya bude mata kofar.
Abinda ya zo a tunaninta shi ta aikata duk da wani bangaren na gaya mata cewa hakan ba zai yiwu ba,shammatarsa ta yi ta rungume shi ta baya a yayin da ya juya zai shiga bathroom,kafin ya ce wani abu ta zura hannunta cikin rigarsa ta gefen cikinsa,wani irin dumm taji a yayin da hannunta ya kai kan tabon yankan nan da har yanzu bai gama warkewa sumul ba......
Zahra✍️
***
GIDAN ƳAN ƘARYA💕
By
FATIMA Y ADAM......
Littattafan marubuciyar.
KUDIRAR ALLAH
KADDARATA SANADIN HASKE
ƁOYAYYIYAR RAIHAN
ƳAR GIDAN YARBAWA
MATAR ƊAN BIRNI
And
GIDAN ƳAN ƘARYA....