GIDAN YAN KARYA

Pg40

by @zahrawriter12

Bude baki ta yi zata fasa kuka ya toshe bakinnata ta hanyar hade shi da nasa,ga hannunsa saman fararen cinyoyinta da suke bude kamar zaka ga fuskar ka a ciki,yanayin yadda yake tafiyar da itace yasa ta ji kamar kanta zai yi tsawa,kamar kuma zata shide, saboda bangare biyu da suke aiki a zuciyarta, bangare daya yana kokarin cusa mata tsanarsa da abinda yake mata a ranta,bangare daya kuma yana son yi masa yafiya akan abinda ya aikata mata,bata da ikon yin kokawa da shi tunda ko ta yin ba riba zata ci ba,karar wayarsa shine abinda ya kwace ta daga gareshi,shima din sai da ta yi karfin halin zare jikinta ta yi kasa tana kukan da bata san na menene ba a cikin Abu biyun da take ji a kansa.

A kasanlance ya daga wayar, sai taga ya tashi ya fice daga dakin, binsa ta yi da kallo kan harara tana ci gaba da sheshshekar kukanta.

Yana fita bai wuce ko ina ba sai bangaren da su baffa suke,yana zuwa ya samesu har sun mike tsaye cikin shirin tafiya,kallon mufty da yake ta hade rai yayi Sannan ya kalli ummi yana cewa"me aka yiwa babban yaya ne?"da sauri mufty ya ɗan sosa keyarsa tare da sunkuyar da kansa saboda har yanzu kunyar kallon Dr gentle din yake,duk da cewa ya roke shi yafiya akan abinda yayi masa kuma ya nuna masa shi hakan bai dauke shi a komai ba,to amma duk da haka ya kasa sakewa da shi kamar yadda Ali yayi,Ummi ta ce"wai fushi yake za a cire shi daga cikin ac za a maida shi ruga"murmushi me dan sauti dr gentle yayi abinda ba kowa ne yake ganin hakan ba,kana ya ce "kai kam babban yaya akwai gajen hakuri"shima muftyn yar dariyar jin kunyar tonon sililin da Ummi ta yi masa yayi, Sannan suka dauki jakar kayansu suka bi bayan baffa da Dr gentle,Sai da suka je har wajen mota,da kansa ya budewa baffa motar ya shiga Sannan Ummi ta shiga ,sai mufty,Ali kuma ya shiga wajen me zaman banza,magana su kayi da baffa Sannan ya koma bangaren driver shima su ka ɗan yi magana daga nan ya ja baya, driver ya ja mota, dama tuni security sun bude gate din gidan,suna gab da ficewa suka hango Ummul ta taho da gudu tana dago musu hannu idanunta face face da hawaye tana kuka kamar ranta zai fice,cikin wani irin zafin nama Dr ya sunkuceta yayi ciki da ita yana jin zuciyarsa kamar ta yaga kirjinsa ta fito saboda yadda Ummul ta fito dan ma Allah yasa hankalin ma aikatan gidan babu wanda ya zo kanta,a kan kujera ya zubar da ita,cikin fada fada ya shiga cewa"baki da hankali zaki fito a yadda kiken nan ba tare da kin saka hijab ba"ina Ummul bata fahimtar komai sai yanayin fuskarsa da take a miskile babu wasa bare sassauci,wanda hakan ya kuma gigitata ta shiga kuka sosai har da birgima,zama yayi tare da rufe idanunsa kansa yana wani irin sarawa, Ummul ta zame masa wata yar karamar yarinya yar yaye Sam sam taki karbar rarrashi hatta tsawar ma idan yayi mata sai dai shi ta kara masa ciwon kai amma bata tasiri a wajen Ummul.

********

Sassafe Alhaji dan gaske ya shirya ko karyawa bai tsaya yi ba, tunda dama yanzu baba adama CE take yin kwabarta idan mommy bata ga damar yin girkin ba,yau din kuma bata nan a asibiti ta kwana wajen zezee,yana fitowa ya shige daya daga cikin motocinsa guda biyar da suke jere reras kamar wajen wankin mota,da gudu ya fice daga gidan yana ci gaba da lissafin dokin rano.

Yayi mamaki sosai lokacin da ya isa main house din na Alhaji Ahmed dan itopia ya ga kartin security's din gidan mara sa fara a da imani sun tare shi sun hana shi shiga, tun daga kofar farko ma bare ya kai ga ta biyu,"baku gane Ni ba ne"?ya tambaye su yana wani zazzare ido yawa tsohon maye,dayan da yake jin Hausa kadan kadan ya ce"mu gane ki mana,shegiya butulu me sin mutunsin ale jin kirki a wajen taro aure ɗanka"take Alhaji da gaske ya gano dalilin wannan murtuke masan da suka yi, dan haka sai ya shiga kwantar da kai yana basu hakuri da nuna musu cewa yazo bawa Alhaji hakuri ne,sai da suka kira p.a din Alhaji suka sanar dashi shi kuma ya sanar da Alhaji Ahmed,kai tsaye kuwa ya ce a barshi ya shigo,ba dan ransu ya so ba suka barshi amma daidai da wayoyinsa sai da suka kwace, ko tsinke basu barshi ya shiga gidan da shi ba,motar ma a wajen gate na farko suka ce ya ajiye ta,sosai ya shiga tashin hankali saboda ba karamar tafiya ba ce tsakanin gate din farko da na biyu ba,bare kuma akai ga ainahin cikin gidan,zai fara musu magiya suka dakatar dashi da cewa idan bai yadda ba ya koma inda ya fito,ai yana jin haka ya tattare kafar wando tare da kulle babbar rigarsa ya taka da gudu,wai dan ya ragewa kansa tafiya,amma a maimakon hakan sai karawa kansa gajiya yayi,daga karshe ma sai ga Alhaji dan gaske yana kan kafa daga nan kuma.ya koma rarrafe,duk inda ya gifta ma aikatan gidan nan sai dai kaji ana kyalkyala dariya ana nunashi,da rarrafe Alhaji dan gaske ya karasa har falon Alhaji Ahmed dan itopia, yana shiga ya zube a gabansa yana maida numfashin wahala fuskarsa da jikinsa babu abin da yake sai uban gumi kamar tsohon kuturun da yayi kwanaki a rana.

"Yallabai a yi min aikin gafara wallahi sharrin shaidan ne na tuba na bi Allah na bika ayi min hakuri, tsananin kidima ce ta sa ni yin abinda nayi"Alhaji dan gaske ya fada yana fashewa da kukan makirci,shiru Alhaji Ahmed bai tanka masa ba,har sai da ya gaji da kukan munafurcin nasa ya yi shiru yana kame kame, Sannan daga can Alhaji Ahmed ya nunfasa tare da duban dan gaske kana cikin muryarsa ta dattijon arziki da suka san kansu wadan da ilmin addini ya cika su,wadanda duniya bata da sun manta da Allah da ma'aikinsa Sallallahu alaihi Wasallama ba,ya ce"dan gaske ne ya faru ne kake wannan kukan tare da neman yafiya?"wani irin kunya da mamaki su suka cika Alhaji dan gaske har ya kai ga kasa cewa komai,murmushin manya Alhaji Ahmed yayi Sannan ya kuma cewa"to idan kana tunanin ka yi min laifi ka je na yafe maka,saboda Ni zuciya ba ta taba rike wani abu mara muhimmanci a cikin rayuwata da addinina ba"ba karamin dadi dan gaske ya ji ba musamman da ya ga bai ce ya bashi keys din stores din da suke hannunsa ba, Sannan bai karbi na office dinsa ba,shi fa Alhaji dan gaske saboda tsananin hadama bai tsaya yayi aiki a Company's da kuma dukiyar da yayi rufda ciki da ita ba,a cewarsa zama a yaron wani yafi karbarsa,shi yasa tunda ya kammale dukiyar Alhaji matawalle ya dora wasu mutanen akan Companys din,dake shi sai da ya tsaya ya duba ya tace ya dauki ma aikata shi yasa bai samu matsala ba,daidai gwargwado ya samu masu amana,dan gaba daya sai da ya kori duk wasu ma aikata da suke karkashin Alhaji matawalle daidai da masu gadi bai bari ba,duk wanda ka gani nasa ne shi ya kawo shi,baya aikin fari ba re na baki sai dai ya yi ta jin shigowar kudade account dinsa idan lokacin biya yayi ya bada albashi, wannan dalilin ne yasa Company din basu dukrkushe ba,saboda yana bawa ma aikatansa hakkinsu bai taba bari ya cinye musu kudi ba,shi yasa suka suke tsaye wajen ganin an samu ci gaba a duka ma aikatun.

Bai taba bari Alhaji Ahmed ya san yana da wasu harkoki na dukiya ba,shi yasa kai tsaye Alhaji Ahmed din ya sakar masa dukiya yake yadda ya so da ita, saboda a tunaninsa a karkashin sa dan gaske ya doga, wannan shine tunanin Alhaji dan gaske.

Yadda ya shiga gidan a wahale haka ya fito a wahale, dakyar yake iya taka kafafunsa,tsinuwa kuwa ba irin wadda security's din Nan basu sha ba,ko da ya shiga motar sai da yayi kusan mintina ashirin yana hutawa tare da maida numfashi, Sannan ya ja motar a hankali kamar wanda bai da laka ya bar layin,sai dai tun da ya fara tafiya yake tunanin ta yadda zaisa su killer su shiga gidan su kashe Alhaji,duba da yadda ya cika gida da kartin maza wai su security's,to amma yana ganin zai iya hada baki da wasu daga cikin securitys din, tunda yasan a yanxu babu wanda yake ƙin kudi,yasan cewa amana ta yi ƙaranci dan haka baya jin zai samu wata babbar matsala da wannan,to amma dole sai ya fara kebewa da wanda zasu yi masa aikin ta yadda koda sun yi gardama zai aika su lahira ba tare da wani ya ji ya gani ba,da wannan tunanin ya karasa companin da yake aiki a cikinsa, yana kashe motar ya fita ya nufi officer dinsa yana faman hurawa sauran ma aikata hanci.

******

Bely bata tashi farkawa ba sai da ta ji rana tana dukan saman fuskarta, sannan cikin azaba ta yunkura amma sai ta ji ta kasa motsa kafafunta, hakan yasa ta koma ta kwanta cikin kazantar da ta bude ido ta ganta a kai,tana kuka me cin rai kukan nadama da kaicon rayuwa,sai yanzu ta fara tunawa da asalinta danginta da iyayenta wanda ta yi banza da su tayi kamar bata da kowa a duniya,kai ko haduwa ta yi da mutum ya tambayi ahlinta cewa take bata da kowa iyayenta duk sun mutu,kuka ta kuma fashewa da shi lokacin da ta tuna yadda suka rabu da iyayenta ,da kyar ta samu ta dinga rarrafawa har ta isa bakin titi,a inda ta dinga daga hannu tana neman me taimaka mata sai dai duk wanda ya zo daf da ita yayi kamar zai tsaya sai taga ya kara gudun abun hawansa,mutane na kasa kuwa da gudu suka dinga giftata don a xatonsu mahaukaciya ce,wani Dattijo ne irin masu tuka dan sahun nan shine ya tausaya mata ya tsaya,shima dakyar ya samu wata mata ta taimaka masa suka sa ta a cikin mafef din, Sannan ya ja suka fara tafiya, sai da suka.fara tafiya Sannan ya tambaye ta inda zai Kaita,gidanta ta kwatanta masa bai yi musu ba kuwa ya kaita har kofar gida,me gadi shine ya shigar da ita cikin falonta,dadin taimakon dae dan sahu yayi mata yasa ta sanya me gadi ya dauko mata jakarta ta bashi kudade masu yawan da ita kanta bata san yawansu ba,me dan sahu ya tafi yana godiya a binsa.

Likitanta ta kira dan yazo ya duba ta ya bata taimakon gaggawa dan gani take yi mutanen nan sun farka ta gaba dayanta.

*****

Sosai kukanta yake damunsa, ga kansa kamar zai fashe saboda ciwo,a hankali ya ɗan motsa yana saukowa daga kan kujerar, tana ganin haka kuwa ta kuma zabura tana wurgi da duk abinda yake kusa da ita,tare da cewa"bana so karkazo kusa dani, Ni sai ka maida Ni wajen baffa da Ummi,ba zan zauna a nan ba bana son zama anan"numfashi yaja yana komawa da baya fuskarsa duk a dame, dogon hancinsa har wani tsatstsafo da gumi yake, jijiyar kansa ta bayyana saboda ciwon da yake masa,Dr Bilal mutum ne da sam bai san hayaniya ko doguwar magana ba, ko da zai yi doguwar magana kuwa sai yana yi yana hutawa kalma bayan kalma,to yau kuma gashi ya hadu da bala in kukan Ummul da mita, shi ko rarrashin bai san ya ake yinsa ba, amma yau saboda Ummul ya na gani dole ya koya dama idan aka ce mutum bai iya a bu ba,to sai dai idan abun bai sameshi ba, wannan tunanin da yayi yasa shi kuma yunkurawa da dan zafin namansa ya mike,ja da baya ya shiga yi tana jifansa da kananun matashin kujerun da ta ke wurgi da su,bai damu ba ya nufeta gadan gadan, yana zuwa ya dauke ta cak ya nufi daki da ita,duk yadda take cilla kafa tana dukansa da fadin ya sauketa amma hakan bai sa ya sauke tan ba har sai da ya Kaita cikin bathroom ya daka ta a cikin bahon da ya ke cike da kumfar wanka me tsananin kamshi.

Kai tsaye ya shiga cire kayan jikinta yana wurgi da su tare da janyo soso masu taushi yana sakawa a hannunsa, da wannan damar Ummul ta yi amfani ta mike zata fito daga cikin ruwan,da sauri ya riketa tare da maida ita ciki yana fara cuɗa mata jikinta,hannusa ta shiga bugewa tana turesa amma ko gezau bai yi ba,ganin hakan yasa ta koma magana tana cewa "ka daina taɓa min jikina bana son wannan abin da kake min, ni ba yar iska ba ce, Ni bana so ka dai.....tuni ta hadiye sauran maganar ta saboda baxatar da yayi mata ta hanyar zame jallabiyar dake jikinsa ya bita cikin ruwan tare da manne bakinsa da nata wanda hakan yasa dole ta hadiye masifarta.

****

Tun sassafe aka yi discharged din zee Dan haka tana farkawa daga bacci ta azalzali Mommy da su tafi gida,bata son wannan dan uwan musan ya zo ya hana su tafiya,dake ba wani kaya ne da su ba,shi yasa su kayi saurin gamawa,suna shirin fita aka turo kofar aka shigo, wannan mutumin ne wanda ganinsa yasa zezee ta ji kamar zata kuma komawa gadon asibitin,sai dai ga tsananin mamakinsu bai ce komai ba sai hanya da ya basu yana cewa "ashe ma an sallame ku?bai saurari amsar su ba ya ci gaba da cewa "shike nan zaku iya wucewa"ai ko take zezee ta saki wata ajiyar zuciya tana saurin ficewa kamar wadda za a ce ket ta zura da gudu,suna fita ta kalli Mommy ta ce"wannan mutumin anya bashi da Aljanu,Mommy kinga abinda yayi min kuwa jiya Allah na zata zai hanamu tafiya saboda a jiya cewa yayi ni zan yi jinyar Musa idan naga na fita daga asibitin nan to tare da Musa ne"daidai lokacin suka karaso jikin motar su mommy tana cewa,"to dama wa zai iya ja da shu'umancin babanki ai kin ga kuwa dole su sallama"shiga motar suka yi driver yaja suka bar asibitin,sai zezee take ji kamar ta rabu da alaƙaƙai musa kenan.

***

Alhaji dan gaske yana shiga office din farko wanda sakatare ko sakatariya suke zama ya fara ganin canji,saboda tashin farko yaga wata sabuwar sakatariyar da bai sani ba kuma bai san an kawota ba,muzurai ya shiga yi a tunaninsa ko an kawo ta ne saboda rashin ganin raliya kwana biyu,dan haka cike da kasaita ya amsa gaisuwarta yana kokarin shigewa office din,"sir why are you going"a fusace ya kalleta har zai yi magana sai kuma ya fasa ya tura kofar office din tare da sa kai ,sai dai yana shiga yayi turus saboda ganin wani matashin saurayi akan kujerar da yake jinta kamar kujerar mulki yana ta juyi akanta, kan faffadan teburin da yake gabansa kuwa tarin takardu ne yana ta aikin dubawa,cikin mamaki dan gaske ya ce"kai kuma waye haka da zaka shigo office dina har ka zauna akan kujerar mulkina"?cikin kallon raini matashin saurayin ya dubi dan gaske na sakonni kafin daga bisani ya dauki wani fayal dake gabansa ya mikawa dan gasken ba tare da ya ce masa komai ba,karba dan gaske yayi hannunsa har rawa yake saboda tsoron abinda zai gani a cikin takardar, da sauri ya shiga farke fayal din har sai da farar takardar dake ciki ta bayyana yasa hannu ya zarota tare da bude ta gaba daya,"what "Ya fada yana kwalalo ido akan farar takardar da take dauke da rubutun korarsa daga aiki ga sa hannu da komai daga oga Alhaji Ahmed dan itopia,har zai yi magana sai kuma ya fasa saboda ko yayi magana wannan da yake zaune a gabansa babu abinda zai iya tsinana masa,dan haka sai kawai ya fice daga office din afusace yana tunanin irin matakin da zai dauka akan wannan mayaudarin mutumin.

******

Yadda Dr gentle din naku ya kanainaye Ummul ikram cikin ruwan nan kai baka ce za a samu sauran wani abu a tare da ita ba,tun Ummul na kukan da hawaye har ta koma na zuci dan kuwa dan gidan dan itopia ya gama tashin karamar ƙwaƙwalwarta da zazzafan salonsa,da ace Ummul a nutse take tsaf zata bada kai bori ya hau, sai dai ina dake ba wannan ne a gabanta ba fitina da daru ta sa aranta bata fasa kiriniyar kwace kanta daga gare shi ba,wanda shi kuma hakan da take wani irin sabon yanayi take saukar masa, Saboda duk motsin da ta yi sai ta tabo masa wani waje me muhimmanci a gangar jikinsa,fitinarta ita tasa yayi mata filla filla a cikin ruwan nan daga karshe ya dauraye musu jiki da ruwa masu dumi ya daga ta cak suka fito daga cikin bahon.

"Na shiga uku"Ummul ta fada tana boye fuskarta a jikin da take tsoro da kunyar gani ba kaya,saboda tsananin tacewa irin ta Dr bai duba halin da Ummul take ciki ba ya janyo katon towel ya rufe su a ciki gaba dayansu ya zamana towel daya suka daura,tsananin takaici da kunya hana Ummul cewa komai su kayi sai kukan zuci da,idanunta kuwa sun fita daga kalarsu,da kansa ya kwantar da ita kamar jaririya Sannan ya dauko mayuka masu taushi ya zuba a hannunsa ya goge mata jiki da su, wanda suka sa jikin ya kara wani sulbi kamar jikin tarwada,shi yasa ya kasa dauke hannunsa daga jikinta har sai da ta gaji ta ture shi tana tura baki da yi masa hararar gefen ido,bata san ina ya samu kaya ba, kawai dai taga ya dauko wata karamar riga da bata wuce gwiwa ba itama bata da hannu sai uban santsi ya sanya mata ,duk irin kumburin da Ummul take yi bai kulata ba,sai ma fuskarsa da take a hade tsam kamar ba shi ya gama lalube yar mutane a bathroom ba,barin ta yayi tana bin jikinta da kallo kamar yau ta fara ganin kanta,kafin ta ce"shi ke nan kuma haka zan kare cikin shigar turawa saboda kawai na zo gidan turawa,to wallahi ba zata sabu ba tunda Ni ba kafura ba ce"amma a gidan aurenki kike"ta ji ya amsa mata muryarsa a dake, wanda hakan yasa ta kalli inda yake,samun kanta ta yi ta zuba masa ido saboda kyawun da yayi cikin farar shet da wando baki sumar kansa sai sheki take yi a kwance lambam,dage mata gira yayi tare da hura mata hannunsa da su da ya fara sumbatarsa, Sannan ya fice daga dakin 6a barta da takaicin kanta.

****

Cikin dan farin cikin da ta zezee ta far samu suka shige falon ita da mommy da take ta tarairayarta dan yanzu da zezeen ta fara jin maganarta yasa ta kara jin soyayyarsa da jin cewa basu da kowa sai Allah da kawunansu,zezee ce a gaba mommy a bayanta suna ta zance cikin kulawar da junan da basu taba yiwa junansu ba,kafin mommyn ta kai ga shiga ta ji zezeew ta kwalla kara tare da dawowa baya da gudu tana nunawa Mommy hanyar falon baki bude ta kasa yin magana.....

Zahra✍️

***

GIDAN ƳAN ƘARYA💕

By

FATIMA Y ADAM......

Littattafan marubuciyar.

KUDIRAR ALLAH

KADDARATA SANADIN HASKE

ƁOYAYYIYAR RAIHAN

ƳAR GIDAN YARBAWA

MATAR ƊAN BIRNI

And

GIDAN ƳAN ƘARYA....