GIDAN YAN KARYA

Pg42

by @zahrawriter12

Saboda tsananin fargaba da son ganin gari ya waye Alhaji dan gaske bai samu yin isasshen bacci ba,abinda bai taba yi ba yau har sallar asuba,ba dan komai ba sai dan ya rage lokaci.

***

Ummul kuwa duk da cewa an yi mata yadda take so amma ta kasa samun nutsuwar zuciya,duk juyin da zata yi moment dinsu na jiyan shi yake dawo mata,a bangare daya kuma tsananin kauna da karamcin iyayen dr gen din ya kuma haifar mata da mutuwar jiki,dan a ganinta daga kan wadan nan bayin Allah bata jin za a kuma samun mutane irinsu,tun zuwansu gidan hajiyar ta kaita bangaren baba, dattijon da ya karbeta cikin wata irin soyayya da kauna kamar 'yar da suka haifa a cikinsu,gashi ba su nuna mata wani alamun rashin sani ba,saboda hatta da br sara da sauran yan uwansa mata sai da suka kirata a waya suka gaisheta, ita abin har kunya ya fara bata saboda yadda suke bata girma kamar ita ce Dr ,wai duk dan tana matsayin matar yayansu,duk motsin da zata ji sai ta dubi hanya amma a maimakon taga wanda take tsammanin gani sai dai taga wani daban,tsakanin yan uwan Dr Gen da suke ta kaiwa da kawowar da ta rasa na meye,ga dukkan alamu dai shirin biki gagarumi suke yi,dan taga har da uban kayan lefe da aka yi tafiyayya aka hado a ƙasashen duniya.

****

Gida ne me matsakaicin girma sai dai yana da tsari da kuma wadata,dan duk iyayin mufty sai da ya so gidan musamman da aka nuna masa katon daki da makeken gado aka ce nasu ne shida Ali ga kuma wani can daban kamar nasu wanda idan su Hamza sun dawo zasu sauka a ciki,dakunan nasu a farfajiyar gidan yake ,nasu Ummi da baffa kuma daga can cikin falon inda har kitchen anan yake,kowane daki akwai banɗaki a cikinsa ga fankoki da kayan kallo,kai abin dai masha Allah haihuwa ta yi rana,akwai me gadi a gidan da kuma securitys din da Dr Ya zuba musu saboda Alhaji dan gaske,sai kuma wata dattijuwar mata da zata dinga taya Ummi aikace aikace,takanas Ummi ta kira A'isha kawar Ummul ta sanar da ita suna lafiya, sannan ta ce ta shirya zata sa a zo a ɗauke ta akawota gidan da suka koma.

*****

A cikin kwana uku da Ummul ta yi a gidansu Dr gen taga tsananin gata da soyayya mara misaltawa taga karanci taga abinda ake kira ilmi, bata taɓa zuwa wajen baba ta tashi ba tare da ta samu karin karatu ba,daga karshe ma zaman kadaici yasa ta fara daukar karatu a wajensa na sauran littafan addinin da hadissan da bata karasa ba da ,sai dai duk da karatun da ta ƙirƙirarwa kanta taka sa sabawa da rashin Dr Gen,wanda ya kauracewa gidan ,amma bata sani ba ko yana zuwa ita ce bata ganinsa,ta rasa me yake damunta gashi dai har yanzu tana jin haushinsa,sai dai kuma wani bangare na zuciyarta yana jaddada mata cewa gentle yake kewa ba Dr ba,kuma gentle yana tare da Dr shi yasa take jin kewar akan Dr, a cikin kwana uku idan ka kalli Ummul sai ka kara kallo dan kana ganinta kaga inda hutu da gyara ya zauna,dan tun dawowarta gidan cikinta bai huta da cin ya'yan itatuwa da ganyayyaki ba, sai kuma wasu hade haden kayan dadi da Hajiya take yi mata,hatta da fruet din da Ummul take sha hadinsa na musamman ne,ga magungunan sanyi da Hajiya ta rike wuta take bata, duk da cewa sun yi magana da Ummi ta sanar mata cewa Ummul bata bukatar gyara sai dai kwaskwarima,saboda su tun yaransu suna fara al'ada suke fara gyarasu daga kan maganin sanyi har gyaran jiki basu da matsala ko auren bagatatan ne ya tasowa yaransu , shi yasa ko a bay idan Ummul ta fita ta xabga ƙaryarta ake yarda saboda kalarta ta ya'yan hutu da kuma dirarren jikin da Allah ya bata,shi yasa yanzu da ta kuma samun gyara ya yi wani luwai luwai da ita.

A yau din ne kuma Hajiya ta sa driver ya taro mata bakuwarta kuma aminiyarta daga filin girgi wadda tazo takanas tun daga Sudan saboda gayaran Ummul ɗin,ko da Ummul ta zo ta gaisheta masha Allah take ta fada tana binta da kallo, Ummul tana barin wajen,hajiyar Sudan ta kalli hajiyar Dr tana cewa"gaskiya na taya ki murna Hajiya kun dace dan wannan yarinyar da gani zata yi biyayya sannan akwai kuruciya a tare da ita sai abinda miji yace da ita,gata kyakkyawa kamar ka sace ka gudu"murmushi hajiya ta yi sannan ta ce"bama daga gani ba ne,dan duk inda kike zaton mutanen kirki iyayen yarinyar da ita kanta yarinyar sun kai ko na ce sun wuce saboda ba zaɓen take yanke muka yi ba kamar irin na baya, wannan karon sai da muka bi wasu hanyoyi domin neman irin macen da ta dace da tilon gwarzon namijin danmu, dan haka ki fada kai tsaye mun dace, sai dai fatan Allah ya zaunar da su lafiya ya basu zuri a dayyiba"Amin hajiyar Sudan ta fada tana ɗorawa da "Allah kuma yasa kar ta canja kin san wani lokacin kudi su suke budewa mutum ido ko ya gyara shi ko ya lalata shi"hannu Hajiya ta daga mata alamar dakatarwa,hakan yasa ta sa hannu ta ɓame bakin tana cewa ,"na tuba Aminiya ina mana fatan alheri gaba ɗaya"dariya suka yi a tare, sannan suka ci gaba da hirar yaushe gamo.

*****

A kwana ukun nan Alhaji dan gaske kullum cikin fargabar dasabuwar masifar da zai karya yake,duk da ta bangaren kamfanunwansa sun gama magana da Dr ya ce"ya kwantar da hankalinsa in sha Allah ko mai nasa zasu dawo ba sai ma sun je can Abujan ofishin EFCC din ba,baba tuni ya ruga da yayi waya da su akwai wanda suke jira ya dawo za a zo a bude masa kamfaninsa,ta wanna bangaren ya ɗan samu sauki, to amma duk da haka kudin da ake zuke masa ta account dinsa a kullum ta Allah suna kara bashi tsoro musamman idan ya tuna kamfanin da suke kawo masa kudaden suna rufe hasalima kokarin raba shi dasu ake yi.

Yana tsaka da tunani ya tashi ya tashi ya bude drower da yake ajiyar takardar dun kamfanin da sauran gida da filayen da duk ya handame, ya dauko ya duba su ya tabbatar suna nan sannan ya mayar,dan shi har dakin nasa ma yanzu bai yadda dashi ba, duk wannan abun da yake faruwa dashi bai sa ya manta da Ummul da ahlinta ba, kullum cikin bulayin nema su killer suke yi,ga kuma uwa uba gentle da yafi son gani ido a rufe dan yasha alwashin duk sanda ya shigo hannunsa sai ya gaya masa inda su Ummul suke Sannan zai kashe shi kisa ta hanyar azabar da sai yayi dana sanin duk abinda ya aikata masa,daga nan ya koma kan wannan dan shegiyar da ya ke neman addabarsa a cikin gidansa.wayarsa ce ta fara babureshan, ganin killer ne yasa ya daga,kafin ya bude baki yayi magana killer ya riga shi da cewa"ya haj albishir zan yi maka amma dan ka tabbatar yi min kiran gani da ido"cikin sauri dan gaske ya sauya kiran ta hanyar maida shi video call,yana zaune sai gashi a tsaye saboda ganin gentle rike a jigace a hannun killer da yaransa a cikin wani tsohon gidan Alhaji dan gasken da ba a gama gina shi ba,saboda murna bai san lokacin da ya sheƙe da mahaukaciyar dariya irin tasa ta azzalumai ba,yana yi yana nuna gentle da kansa yake layi saboda tsananin bugun da yasha a hannun su killer,kafin cikin dariyar mugunta ya ce"Kai killer Kai bala I ne,bayan moses ban taɓa yin yaro me kwazonka ba, sai dai bana fata ka zamar min masifa kamar yadda moses ya zame min,dan haka komai yana kammala zan turaka wata kasar ka je can ka karaci iskancinka idan yaso duk lokacin aiki ya taso ka dinga zuwa"ya fada yana tashi tsaye tare da cewa"ku jira ni yanzu zanzo a yi ta ta ƙare, Ummul kin kusa zuwa hannu wallahi son da nake miki ne kawai zai sa na sausauta miki amma ba dan haka ba sai na baki mamaki"

A cikin mintinan da basu gaza sha biyar ba ya shirya, har zai fito ya tuna da wani abu dan haka ya koma ya dauka, Sannan ya shiga dakin zezee da duk ta sauya kamar ba zezee dan gaske ba, kullum tana kan sallaya gashi yanzu malami guda Mommy ta dauko mata yana koyar da ita karatun addini,shi yasa gaba daya hatta da kamanninta sun sauya,shi bai ma tsaya ya lura da sauyin zezee din ba saboda abinda yake gabansa ya gama rufe masa ido,ko yanzu ma da ya shigo ya ganta akan sallaya bai damu ko mamaki da ganin hakan ba,kai tsaye ya tsugunna a gabanta ya mika mata wata yar kwalba yana cewa"karbi wannan zezee idan har kina son rabuwa da alaƙaƙai to dole sai dai mu yi maganinsa ta wannan hanyar "juya kwalbar zezee ta shiga yi a hannunta tana kallo,kafin ta maida dubanta kan Abban tana masa tambaya da cewa "meye wannan din Abba?"ƙasa ƙasa yayi da murya sosai sannan ya ce"guba ce"wata irin zabura zezee ta yi tana mai yin cilli da kwalbar kamar ta taɓa kashi,"meye haka zezee?kin san wahalar da nasha kafin na samo wannan abun shine kike masa wannan cillin, inda ya zube fa?"cikin tsananin tsoro zezee ta ce"Abba kisa fa kenan kake cewa na yi?"to meye idan kin yi kisan,eh to lallai yanzu na fahimci cewa baki damu da kanki ba,zezee dole fa kisa masa gubar nan idan ba haka ba moses ba zai taba sakinki ba na san shi fiye da yadda kike zato"to amma Abba sai mu rasa ta hanyar da zamu yi maganinsa sai ta hanyar kasheshi,? To Ni dai gaskiya ba zan iya kashe dabba ba ma bare kuma rai haba Abba wallahi da na kashe Musa gwara na hakura na zauna dashi saboda yanzu na san abinda ake nufi da ƙaddara,don haka ba zan yadda ka kuma kaini ka baro ba,yanzu maganar mahaifiyata kawai nake dauka sai kuma ta ya sheik saboda sune suke fada mun gaskiya cikin kalaman ilmi da nusar dani gaskiya"tass dan gaske ya haske fuskar zezee da wani shegen marin da sai da taga taurari, Sannan ya mike ya dauki kwalbar ya fice daga dakin ba tare da ya kuma cewa komai ba.

*****

Lokacin da A'isha ta je gidan su Ummul taga yadda rayuwa ta juya musu a lokaci daya ,ba karamin farin ciki ta yi ba, burin ta kawai taga Ummul,sai dai kuma Ummi ta gaya mata iya abinda ya kamata ya sani a matsayin ta na aminiyar Ummul ɗin,dan yanzu duk yadda kake da mutum dole ne ka dinga kiyaye sirrinka domin bacin rana dan ita zuciya ba kashi ne da ita ba, wannan yasa A'isha ta yi hakuri da ganin Ummul din har zuwa lokacin da Ummin ta faɗa.

Ko da ta nemi ganin baffa Ummi ta sanar da ita cewa shima ya tafi can Niger domin sanar da su bikin Ummul din da ake shirin yi Sannan ya yi musu bayanin abinda zasu iya fahimta game da saurin daura auren ba tare da an gaya musu,daga nan zai wuce ya taho da su Hamza da Safwan saboda sun kammala karatun su gaba ɗaya,anan dai shuru A'isha tayi dan tuni ta san da dawowar su Hamzan saboda tsaftacciyar soyayyar da Ummul ta jima da haɗawa tsakanin kawarta da ya hamzanta sai dai bata bari Ummul din tasan cewa sun hada kansu sosai har haka ba.

****

A bangaren bely kuwa tuni kazamiyar dukiyarta ta fara dauko hanyar karewa a cikin kwanakin da basu gaza shida ba,saboda siyan magani masu tsada duk dan ta samu ta rabu da masifaffiyar cutar da ta sameta,sai dai kuma kamar wadda ake karawa azaba, duk maganin da take yi da allurai babu ko daya da yau zata bigi kirji ta ce yayi mata amfani,gashi duk samarinta da kawayen ta sun gujeta me gadin ta ne kawai yake tare da ita,shima daga karshe komawa yayi yana lalabata da ta sanar dashi adireshin garinsu ya je ya sanar da iyayenta abinda yake faruwa da ita,ita kuma ba wai bata son hakan ba ne,kawai tana tsoron gamuwarta da mahaifinta ne sannan ma tasan ba zasu taba karbarta ba,dan cewa zasu yi bata neme su dan Allah ba sai da ta ke kusa daƙabari,amma kuma da ta yi wani tunani dole sai taga zuwan nasa shine yafi akan zaman nata tun da dan sauran abinda zata iya tafiya dashi a nema mata magani ko na gargajiya ne,dan haka sai kawai ta bashi adireshin tare da kudin mota har da doguwar wasika duk dan ta samu iyayenta su yarda su karbeta.

****

Tunda Ummul ta shiga dakinta zaune take shiru, babu abinda yake damunta sai kewar yan gidansu, fadan su da yaya mufty bari barin Ummi, da yar tsumagiyar baffa da idan ta kureshi yake sabga mata a kafafunta, ga lallashin yaya alinta me sonta da rama mata duka idan yaya mufty ya daketa,sai kuma kewar da tafi komai taɓa mata zuciya duk da yadda take dannewa da son tursasawa kanta ba haka ba ne,A'isha ce ta fado mata a rai duk sai ta ji rashin yar wayar ta ya dameta yanzu da ace tana nan ko ba komai da ta kira wani daga cikin yan gudansu ko da bata bari ya ji Muryar ta ba,dan har yanzu tana jin haushin guduwar da su ka yi suka barta,Alhaji dan gaske ne ya fado mata a rai wanda tuna shin kadai sai da ya sanya ta dafe kirjinta, ko ya ya yayi da bai ganta ba,wai shin ko ya san gentle shine Dr ?tunanin da yake neman hanata sakat ne yasa ta ji duk tana son fita ta kewaya ko ta ji iska,hijabin sallarta ta dauka ta sanya a kan riga da sket din dake jikinta na wani lafiyayya leshi mara nauyi dan idan ba tabawa ka yi ba sai ka dauka irin materiyar din nan ne masu taushi,silifas ta zura tana ƙoƙarin fita daga dakin sai kuma ta dakata tana kallon wayar Hajiya da ke kan bed side drower, kafin a hankali ta taka ta dauki wayar ,bude wayar ta yi wadda take ta buɗu saboda babu security, lambar yaya mufty take kokarin sakawa sai kuma ta tsaya saboda wani message da ya ja hankalinta da alama ko bude shi ba ayi ba,hannunta na rawa ta bude sakon,take idanunta suka yi mummunan gani dan ba komai ta ci karo da shi ba sai rubutun da aka yi da manyan baki,kamar haka (HAJIYA GALI DRIVER NE TUN DAZU NAKE NEMAN WAYARKI DAN NA SANAR DAKE ABINDA DR BILAL YAKE SHIRIN YI KO MA NA CE YAYIN,DAN A HALIN YANZU YANA HANNUN YARAN ALHAJI DAN GASKE SUN KAMASHI YANZU,SHI YA CE MIN KAR NA SANAR DAKE WAI AKWAI SHIRIN DA YAKE YI SHI YASA YA KOMA GENTLE DAN YA BASU DAMAR KAMA SHI AMMA FA HAJIYA INA JIN TSORO KAR BILAL YA JE YA KASA FIDDA KANSA, SHI YASA NA GAYA MIKI A SAN ABIN YI )a hankali wayar ta zame daga hannun Ummul kirjinta na wani irin dagawa kamar zai hudo ya fito,babu abinda yake dawowa kunnen ta sai irin alwashin da Alhaji dan gaske yasha a kan Dr Bilal da shirin da yake na son ganin bayan gentle, ke nan idan har dan gaske ya gane gentle shine Dr Babu makawa sai yayi masa kisa dubu idan ana yi,numfashinta ne ya fara wani irin fitar sauri kamar zata hadiye zuciyarta kafin ta yi kasa tana wani irin numfashi me wuyar fita tana juyi a kasan wajen, wanda hakan yayi daidai da shigowar hajiya aiko da gudu ta karasa gaban Ummul din ta dagota jikinta tana kiran sunanta cikin tsananin tashin hankali,hajiyar Sudan ce ta shigo da nata gudun duk da yadda jikinta yake da auki,itama tashin hankalin ta shiga tana tambayar abinda ya samu Ummul din duk sun rude sun rasa abin yi ,sai daga can Hajiya ta tuna da inhelar Ummul din dan haka ta yi saurin daukowa tana shaka mata, a hankali ta fara sauke nunfashi kafin kuma ta tafi luuu ta sume a jikin Hajiyar.......

Zahra✍️

💕GIDAN ƳAN ƘARYA💕

By

FATIMA Y ADAM......

Littattafan marubuciyar.

KUDIRAR ALLAH

KADDARATA SANADIN HASKE

ƁOYAYYIYAR RAIHAN

ƳAR GIDAN YARBAWA

MATAR ƊAN BIRNI

And

GIDAN ƳAN ƘARYA....