Pg43
Yadda hankalin Hajiya ya tashi dole ka tausaya mata,gashi bata san dalilin da ya kawowa Ummul wannan ciwon na farar daya ba,kallon hajiyar Sudan ta yi tare da cewa"Hajiya dan temaka ki miko wayar can mu kira mijinta tunda dama shine likitanta"da sauri Hajiyar sudan ta tashi ta nufi inda hajiyar ta nuna mata ,sai dai kuma bata ga wayar ba,dan haka ta ce "a nan dai babu waya ko dai kin manta inda kika barta?"dube dube Hajiya ta fara yi na inda zata ga wayar can ta hangota a yashe daga can gefen inda Ummul ta yi watsi da ita,da sauri ta nunawa Hajiyar Sudan din ta dauko wayar,a dame Hajiya ta kunna wayar ta kawo haske,sai kawai ita ma ta ci karo da sakon da driver ya turo,salati ta shiga yi tana cewa "Hajiya kin ga abinda yaron nan yayi ko?to ai gashi nan shirmen da yayi yana shirin kashe masa mata"ta fada tana mikawa hajiyar Sudan wayar,karba ta yi ta duba sakon, itama dai bata ji dadin abin ba,dan haka sai kawai suka kira driver, basu sanar da baban ba har sai da suka kai Ummul mota sannan Hajiya ta tuna,da gudu ta shiga bangarensa ta sanar dashi a gurguje,sai ga baba da kansa ya fito ya shiga Mota sun tafi kai Ummul asibitin Dr Bilal dan itopia.
Babbar magana ke nan abinda likitocin asibitin Dr Bilal suka fada kenan lokacin da suka ga wadanda suka kawo Ummul asibiti, nan da nan kaf likitocin da suke on duty a ranar suka bayyana akan Ummul tare da bata kulawa ta musamman, wanda hakan yasa a cikin mintinan da ba su wuce ashirin da biyar ba Ummul ta farfado ,sai dai tunda ta farfaɗo take kuka ,hakan kuma zai iya sanyawa ciwonta ya tashi shi yasa suka shiga rarrashinta amma sam Ummul ta kasa fahimtar Yaren da suke mata bare kuma tasan me suke cewa,ko da suka sanar da baba da hajiya halin da Ummul take ciki ba su iya cewa komai ba sai dakin da suka shiga suka samu Ummul din cikin yanayin kuka da damuwa,lokaci daya idanunta sun fada kana kallon ta kasan cewa tana cikin fargaba,daga hajiyar har baba samun kansu suka yi da kasa rarrashinta saboda basu san ta ina zasu fara ba, sai daga can baba ya ɗan numfasa tare da yin gyaran murya sannan cikin kamilalliyar muryarsa ta nagartattun dattijai ya ce"ɗiyata kiyi hakuri kin ji ki bar kuka saboda ba shi zai miki magani ba sai dai ma ya haifar miki da wata sabuwar damuwar dan haka ki yi shiru mijinki zai dawo gareki lafiya,amma dole sai kin kwantar da hankalinki"shiru Ummul ta yi idanunta a rufe amma tana sauraron abinda baba yake faɗa mata,shi kuma ganin ta yi shiru yasa ya mike yana cewa"Hajiya kar ki sanar da ita komai har sai ta yi hakuri ta daina kuka"in Sha Allah Hajiya ta fada tana dawowa kusa da Ummul din bayan baba ya fita daga dakin.
Dafa kanta hajiya tayi tana cewa"Ummul zan fada miki dalilin da yasa Bilalu yazo miki a siffa biyu idan yaso sai ki yanke masa duk irin hukuncin da kike ganin yayi daidai dashi hukuncin da zai sa ki samu sanyin zuciya daga abinda yayi miki"da sauri Ummul ta fara kokarin tashi, sai da Hajiya ta kamata tana cewa"a'a yi a hankali ki zauna amma ai ba yanzu zan gaya miki ba sai kin ji sauki mun koma gida"girgiza kai Ummul ta yi tana cewa"Hajiya mu tafi kawai ni ba zan wani ji sauki ba in dai ba Dr gen ne ya bar hannun wancan azzalumin ba,kuma fa ba wai dan ina son shi yasa na damu ba sai dan kawai yana musulmi kuma ya taimakeni shi yasa nima bana son wani abu ya sameshi"murmushi ne hade da yar dariya Hajiya tayi Sannan ta ce"to dama na ce son shi kike yi ne?ai ba sai kana son mutum ne kake damuwa da shi ba,ko kin manta Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallama ya ce al Musulmu akul Muslim?"Ummul ta ce"haka ne Hajiya musulmi dan uwan musulmi ne shi yasa nake ji kamar na je na fanshi Dr Gen da abinda dan gaske yake so, dama ni yake so ya aura kin ga kawai sai na hakura na aure shi in dai zai rabu da Dr gen"shafa gefen fuskarta Hajiya ta yi tare da cewa "babu abin da zai faru in Sha Allah,tun da kin dage sai mun tafi mu tafi gidan sai na fada miki abinda kike son ji"ta shi Ummul ta yi ta zura silifas din da Hajiya ta saita mata a gaban kafafunta sannan ta rike hannunta suka fice daga dakin,a mota suka samu driver ya dawo daga maida Alhaji gida.
*****
Cikin kankanin lokaci Alhaji dan gaske ya isa wannan tsohon gidan nasa,yana yin fakin ya fito ya shige gidan,kasancewar gidan ba acikin gari yake ba yasa bai damu da ya tsaya duba inda ya kamata ya ajiye motarsa ba,wata irin mahaukaciyar dariya ya sheƙe da ita har da tafa hannayensa lokacin da yayi arba da gentle cikin wani irin mawuyacin hali dakyar yake motsa idanunsa,da sauri killer ya janyo masa kujerar roba ya zauna a gaban gentle, hannu Alhaji dan gaske yasa ya dago fuskar gentle yana kuma shekewa da dariyar mugunta.
*****
Ko da me gadin bely ya isa kauyen su belyn da ake kira kauyen tofa ba karamar wuya yaci kafin ya gane gidan ba,an yi masa karba ta mutunci har yana mamakin inda bely ta kwaso munanan dabiunta dan sam iyayenta basu da wata suffar da a za'a kira su da mutanen banza,abinda ya kuma burge shi da bai wuce yadda suka karbe shi hannu biyu ba duk da shi din ba Musulmi ba ne,dan ko a ido ka kalle shi zaka fahimci shi din ba Musulmi ba ne,abinci da ruwa aka kawo masa ya ci ya yasha Sannan ya fara kora musu bayani har da karanta musu wasikar da bely ta bayar akawo musu,da farko ma katse shi suka yi tare da yi masa godiya, Sannan babanta ya dora masa da cewa"bawan Allah mun gode da karamci amma mu tuni mun jima da yafe bilkisu daga cikin 'ya'yanmu,dan haka kadaina wahalar da kanka wajen ganin ka sa mun karbeta dan har abada mu da kara zama da bilkisu"kowa dai ya san raunin uwa akan ƴaƴanta shi yasa mahaifiyar bilkisu ta kasa cewa komai amma a ranta tana fatan megidan ta yayi hakuri ta dawo gida su yi mata magani tunda hannunka baya rubewa ka yanke kayar.
To juyin duniyar nan an yi amma mahaifin bely ya kekashe kasa ya ce sam bai yadda bilki ta dawo masa gida ba,daga karshe dai sai da aka dangana ga zuwa wajen me gari wanda shine ya yi sulhu bayan doguwar nasiha da janyo ayoyi da hadissan Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallama,sosai me gadi Ya ji dadi saboda sai da aka hada shi da mutanen da zasu taho da bely, Amma sun sha kashedin cewa kar su taho masa da kayan Haram ko tsinke baya bukata a kawo masa gida da suna shi zai amfana in dai har ba ita ka dai ce zata amfani da abinta ba,kamar dai suttara da kuma kudin da zata yiwa kanta maganin gargajiya.
*****
Duk abinda ya faru tsakanin zezee da ubanta da kuma yadda takasance tsakanin ta da mahaifiyarta babu wanda bai ji ba,saboda inda asid ya zuba a jikin Moses bai hana shi tafiya ba, kwanciya ce da baya bai isa yayi ba sai dai ruf da ciki haka bai isa ya zauna ba saboda har zuwa mazauninsa duk a kwaye yake babu kyan gani dan wai a hakan ba ana masa magani me kyau amma da tuni ya kuma cin jikinsa, hannu yasa ya ɗan taba kofar tare da sallama,shiru su kayi da ga kukan da suke yi suka zubawa kofar dakin ido cike da tsoron Muryar wanda suka ji, sai da ya kuma yin magana da kara Kwankwasa kofar Sannan Mommy ta tashi ta nufi kofar tare da budewa kirjinta na dukan goma goma saboda basu san da me yazo ba tunda duk jirgin su daya da dan gasken ba maida rai su kayi a bakin komai ba,murmushi yayi saboda ganin yadda suke a tsorace yana shigowa dakin bai zauna ba saboda ba damar hakan, sai samun waje da yayi ya tsaya jikinsa sanye da rigarsa ta magani da ita kadai ce take iya zama ajikinsa dan bashi da halin saka kaya irin namu na gida, Sannan ya dubi zezee da ta kasa kallonsa kanta a kasa tana ci gaba da jan carbin da yake hannunta,numfashi ya fitar Sannan ya fara magana"zezee duk da cewa ina sonki amma ni kaina na san cewa kin fi karfi na,kuma tun a baya son naki kawai nake Amma ko kadan ban taɓa sawa raina cewa zan aure ki ba, Sannan ko da wannan abin ya faru ba aurenki ne na tsara a raina zai zama fansa ta ba,na tsara yi miki abinda kika sa na aikatawa wata ya kuma dawo kaina ne,sai dai kuma lissafi na ya canja saboda wannan "ya nuna mata hoton Dr Bilal da yake sakale a bangon dakinta.
Daga ita har mommy sun shiga mamaki amma sai basu katse shi ba,suka baza kunne da ido dan jin karshen labarin,ya ci gaba da cewa"na fada miki yadda aka yi na samu aurenki,amma ban gaya miki ko waye ba,saboda bai bani damar hakan ba,dan a yanzu ya zama tamkar uban gida na,a yanzu ma ban sanar da ke ba har sai da na samu umarni daga wajensa, wanda shine dalilin da yasa na ji tattaunawar ku da dan gaske, lokacin da ya fita da a ce yana cikin hankalinsa to da tabbas zai ganni,ita ma mamanki bata ganni ba,ganin ta fara shiga ne ya sa na ci gaba da buya har sai da na tabbatar kun gama naku.
A yadda muka tsara da shi Ko na ce a yadda Dr Bilal ya tsara min bai yarda ya yi min hanyar aurenki ba har sai da mu da nayi masa alkawarin zan sake ki a duk lokacin da ya bani umarni,shi kuma ya dauki alkawarin zai dauki nauyin ciwona har na samu lafiya idan Allah ya amince,zezee duk wannan abin da yake faruwa ina yinsa ne a bisa umarnin megida mutum daya tamkar da dubu wamda ya yadda ya shiga matsalar waninsa ko da hakan zai zama wata babbar matsala a cikin rayuwarsa,dan hatta da mahaifiyarki ya jima da shiga cikin matsakarta yayi kane kane yana kuma kan hanyar neman mata hakkinta,tabbas da ace ban dauki darasi a cikin wannan rayuwar ba da ba zan taba rabuwa da ke ba zezee ko dan rama cin amanar da mahaifin ki yayi min a matsayin sa na ubangidana,dan haka na sakeki kuma gashi a rubuce"ya fada yana ajiye farar takarda a gefen ta, Sannan ya ce "wallahi zezee ko da ba mu yi alkwari da Dr xan sake ki ba,to wallahi sai na sake ki darajar abinda kika yi min a yau,daga karshe ina miki Godiya saboda ko ba komai kin yi sanadin shiriyata da kuma haduwata da mutumin kirki kamar Dr ,yanzu ma asibiti zan koma za a yi min aiki, Allah ya shiryi mahaifin ki idan har yana da rabo"daga haka ya juya zai fita, da sauri zezee ta dakatar da shi,wadda tun bayan fara jawabin sakin da Musa yayi mata ta fada wani irin farin ciki tare da yiwa Allah godiya da duk wanda ya kasance ya zama silar wannan saki da ya zo mata a matukar bazata,ta ce"dan Allah Musa ko zaka iya fada mana abinda ya haɗaka da abbana?"
Dakatawa yayi Sannan ya juyo yana cewa"zeezee dan gaske ba ni dai yayiwa irin abinda yayi min ba,amma bari na fada muku a takaice".
"Tun ina yaro Alhaji dan gaske ya dauke Ni ina masa kananan ayyuka marasa kyau, kamar irin su kwacen waya yar karamar damfara har zuwa lokacin da na yi wayo ya fara koya min suka da sara sai kuma kayan maye da nake siyar masa a boye,ko lokacin da ya shiga gidan ubangidansa ya kashe iyayen mahaifiyar ki ya tura ni saro kayan maye, a lokacin ban wuce shekara sha biyar ba,amma duk wani waje da yasan zan samo masa kaya kai tsaye yake tura ni,lokacin da na dawo ban san shine ya kashe ubangidansa ba,har sai da ya auri Mommyn ki ya taho da ita nan kano Anan ne da na sani na nuna masa rashin dacewar abin, har mu ka dan yi rigima dashi,to ashe shi ya shiga tsoron kar Na tona amsa asiri shine yasa wani sabon yaronsa killer ya kasheni,to Allah bai yi zan mutu ba,tun da na farka a inda na tsinci kaina, sai kawai na kara gaba, zuwa Legas a nan na cigaba da shanye shaye shaye na, ban kuma kara zama yaro kowa ba,sai dai na daina daba da kwace sai dai na yi yan buga bugata na samu Abinda zan ci abinci da kayan maye na,lokaci daya kuma hankalina ya dawo Kano inda nan ne asalin mahaifata kuma iyayena tubabbu ne sai dai tun ina kan harka da dan gaske suka mutu, Amma ina da yan uwa wasu har yau basu Muslunta ba wasu kuma sun musulunta,kamar wanda kuma gani a asibiti yayana ne amma shi bai musulunta ba.
Bayan dawowata ne ban jima ba Allah ya hadani da zezee, wadda cikin son zuciyata na dinga binta dan ta so ni amma tana wulakantani ,sai na yi mata waya sau goma a rana bata daga ba,idan ma ta daga zafi da cin mutumci ne zai biyo baya,amma duk da haka nan hakura ba,rana tsaka ta kira ni ta bani aikin zubawa wata yarinya asid,ban yi wani tunani Ba na karba saboda na samu damar shiga jikinta,duk da cewa na daina irin wannan ayyukan to ashe tsautsayi ne yake kirana da kuma silar shiryuwa, wannan shine abinda ya hadani da dan gaske, kuma ya shiga tashin hankali ne lokacin da ya ganni saboda yana tunanin zan tona masa asiri wajen mamanki da tunanin zan dauki fansar abinda yayi min dan a tunaninsa moses din da ya sani a baya shine a yanzu "daga haka ya yi shiru yana jiran ko da wani tambayar da za su yi masa,tashi zezee ta yi tana cewa"ban san da me zan saka maka abinda ka yi min ba sai dai na ce maka na gode, kuma in Sha Allah zan neme ka a kusa da komai ya gama daidaita akwai alherin da mommy zata yi maka"Mommy ce ta karba tana yi masa godiya har suka tako masa wajen motar asibitin da ta zo daukarsa.
******
Da kyar da lallashi Ummul ta yadda ta yi wanka da kayan wankan da hajiyar Sudan ta haɗa mata, dan ba dan abinda ya faru ba a yau din ta so ta fara gyare surukuwar tasu,daga nan ta sanya ta a gaba da cimar da aka sauya mata, wadda daga karshe da kuka aka kare dan wannan ba ma su dadi ba ne irin wanda Hajiya take bata,Hajiyan Sudan ta ce"dama dai wannan kukan a kusa yake dan tun dazu nake ankare dake"kama.hannunta hajiyar Dr Gen ta yi tana cewa"ta shi mu tafi dakina mu barwa Hajiya dakin tunda naga alama sanya min ke zata yi a gaba"fita su kayi daga dakin, kai tsaye dakin hajiyar suka koma, ta zaunar da Ummul din a gefen gado Sannan itama ta zauna tare da sanya hannu tana share mata hawayen da suka bata mata fuska,cikin hawayen da suka kasa tsaya mata ta kalli hajiyar tana cewa "wallahi Hajiya kema ki dinga yin kuka dan dai baki san halin dan gaske ba ne, wallahi zai iya kashe Dr Gen dan ba shi da imani"cikin Muryar lallashi hajiyar ta ce"yi hakuri Ummul babu abinda zai samu Bilalu in sha Allah zuwa dare zaki iya ganinsa ya dawo gida,ko ba ki ji sanda ya kirani ya ce mun yana hanya ba?"da sauri Ummul ta share hawaye tana cewa"da gaske ne Hajiya?"au karya zan yi miki?"
Kunya ce ta kamata ta rufe fuskarta tana murmushi.
Gyaran murya hajiyar ta yi Sannan ta fara magana da cewa"Ummul bilalu da kike gani bai taɓa bude baki ya ce yana son wata ya Mace ba a Duniya, shi yasa muke kaunar ki da martaba ki, a matayinki ta wadda ta cinye jarrabawa ta kuma cancanci shigowa ahli irin namu, mafarin abin shine.
Tun lokacin da muka fuskanci cewar idan har ba mu yi da gaske ba, Bilal ba zai taba kawo mana mace da kansa ya ce zai aura ba, wannan yasa muka shiga fafutuka gidan abokan arziki dan neman iri, Musamman ta bangare na,dan na fi babansa zakewa,saboda na samu kwarin gwiwa lokacin da muka rutsa shi akan sai ya kawo mana matar aure sai kawai ya ce ya bamu dama mu nema masa dan shi bai san ta yadda zai ce yana son Mace ba, wannan ya sa na fara binciken da ya kai ni ga dace har na samu wata yarinyar kawata muka hada su suka daidaita amma ba wai dan Bilalu yana son ta ba,yayi biyayya ne kawai dan son farin cikin mu, sai da muka dan fara basu dama suka daidaita kansu, a bangaren yarinya ta nuna tana sun Bilalu dan dama shi ba mijin da mace zata gani ta ce bata so ba ne,sai dai kuma son zuciya wanda shi ne mafarin komai da ya faru,a na i gobe daurin aure aka kira Bilal a waya aka sanar masa da cewa ya je nan babban hotel da ke Abuja ya ga wani abu,kin san halin miskilin mutumin naki sai kawai ya share maganar yaki zuwa,amma sai me wayar da ya boye lambarsa ya takura da kira har sai da ya sa Bilal ya tafi hotel din, bayan ya je ya tambayi lambar room din da aka bashi, Sam bai kawo komai a zuciyarsa ba,har zai Kwankwasa kofar sai ya tuna da abinda mutumin ya ce idan ya zo kar ya buga ya shiga kai tsaye,duk da cewa ya san hakan babu kyau to amma sai ya dubi babban dalilin da zai sa ace yayi hakan,dan haka sai kawai ya murda handle din kofar ya sa kai, kuma yayi mummunan ganin da ya gwammace bai zo wajen ba, ja yayi da baya yana runtse idanunsa tare da dafe kansa da yake wani irin Sara masa kamar zai tsage,rufe kofar da yayi da karfi shi yasa suka zabura daga aikata masha ar da suke yi,cikin rawar jiki Nafisa ta zura kayanta ta fita dan ganin wanda ya shigo, aiko wanda take zaton ne dan kuwa bayansa kawai ta hango yana wata irin tafiya cike da karfin hali da jarumta tamkar babu wani mummunan abu da ya gani.
Da gudu ta bi bayansa ko ganin gabanta ba tayi tana kiran sunansa cikin tsananin tashin hankali mara misaltawa.
Kafin ta cimmasa ya shige mota ya fice daga hotel din da gudu, ya barta tsaye cikin kukan nadama da bakin ciki...
Zahra✍️
***
💕GIDAN ƳAN ƘARYA💕
By
FATIMA Y ADAM......
Littattafan marubuciyar.
KUDIRAR ALLAH
KADDARATA SANADIN HASKE
ƁOYAYYIYAR RAIHAN
ƳAR GIDAN YARBAWA
MATAR ƊAN BIRNI
And
GIDAN ƳAN ƘARYA....