GIDAN YAN KARYA

Pg45

by @zahrawriter12

Har tsawon wani lokaci Alhaji dan gaske ya kai yana murza idanunsa saboda ya tabbatar da abinda yake gani,da ya ga hakan yaki sauya masa komai sai ya fara dukan kansa amma dai duk ya bude idanunsa Dr Bilal yake gani a gabansa,tashi tsaye yake kokarin yi yana cewa "kai wannan ba zai taba yiwuwa ba,Ni za a yiwa tsafi to ai nima shegen kaina ne,"wato kai yaron nan dama abinda kake yi ke nan saboda tsananin hatsabibanci har kamanni kake sauyawa to....ji yayi an kwada masa wani abu a kansa,da sauri ya juya ya kalli bayansa,ai bai san sanda ya dora hannunsa aka ba tare da ware baki zai sanya ihu amma sai wani daga cikin kattin mutanen da ya gani zagaye da shi sanye da wasu irin bakaken kaya ya cusa masa attaruhu cikin bakin ya kuma taune ba tare da ya sani ba,wayyo jama'a kar ku so kuga yadda dan gaske ya haukace duk da yadda yayi saurin furzar da attaruhun, sai dai kuma gwammacewa yayi bai furzar ba saboda yadda laɓɓansa suka dauki yajin taruhun, take ya shiga rawa a wajen yana zagaye mutanen wajen,ga yaransa su killer hannayensu sanye cikin hand cup, saboda tsananin azaba dan gaske ya kasa tantance halin da yake ciki ga zafin baki ga zafin zuciya da ƙwaƙwalwa,suna tsaye suna kallonsa babu kalar rawar da dan gaske bai yi ba saboda tsananin halin da ya shiga,Dr kuwa tuni ya tashi ya maye gurbin Alhaji dan gaske ya zauna a saman kujera tare da dora kafa daya kan ɗaya yana kallon yadda yake tsalle yana rike baki da turo harshe kamar karen da ya ga nama daga nesa.

Sai da ya dauki lokaci cikin azabar da harshensa yake sannan ya ɗan fara lafawa,ya nemi gu ya zauna yana maida numfashinsa ga idanunsa sun yi jawur bayan ruwan da suka yi,a nutse Dr Bilal ya kalleshi sannan ya juya ya kalli wani daga cikin mutanensa ya yi masa alama da ido,take kuwa ya dauko fuskar gentle da ya cire ya bude tare da mika masa,karɓa yayi ya bude ya saka a fuskarsa sai gashi ya koma gentle din da Alhaji dan gaske yake nema,wanda hakan yasa shi zabura cikin matukar mamaki da rudu dan ji yayi tamkar zai zauce saboda tashin hankali,cirewa Dr Bilal yayi sannan ya kara matsowa daf da dan gaske kana cikin kamilalliyar muryarsa ya ce"ka gama naka saura kabarwa Allah,na san kana cikin rudu da tunani amma kar ka damu ga kadan daga cikin abinda ka ke son sani game da ni".

"Dan gaske tun farkon shigowar ka rayuwarmu muka san kai waye amma sai mu kayi maka talala dan mu muga iya gudun ruwanka,mun baka damarmaki da yawa duk dan muga ko zaka gane Allah na nan,amma ina lamarin naka sai karuwa yake, shi yasa muka biyo maka ta inda baka taba zato ba,na farko dai ba dan kai na sauya daga Dr Bilal na koma gentle ba,sai dai kuma hakan yayi min amfani ta hanyar gane kai waye da duk wani shirinka akan mu, sannan ba kowa ce ta turo maka raliya ba sai matarka saboda tasan cewa kaine ka kashe mata iyaye shi yasa ta turo raliya dan ta bincika mata wanda kake son cuta a gaba,dan ta samu hanyar da zata tona maka asiri itama kuma ta samu sassaucin abinda ka yi mata,sai dai kuma abinda bata sani ba, nima na bawa raliya aikin sa maka ido,dan haka ba ita kadai ta yiwa aiki ba har da Ni,dan haka gaba dayanka a tafin hannuna kake,mun san dalilin ka na son bani auren yarka,kai kuma kana shirin auren...sai kuma yayi shuru saboda baya son dan ganta Ummul dinsa da dan gaske dan haka sai kawai ya dora da cewa"daga Ni har mahaifina mun san komai akanka shi yasa mu kayi saurin sanar da baffa mahaifin matata komai dan gane da ni,shi yasa muka rufe ka aka daura aurena da....yaki fadar sunan Ummul, sannan ya ci gaba da cewa"wanda kasa aka kama a Matsayin gentle mutumina ne kuma shine ya fidda raliya daga inda ka ajiye ta, sannan duk abinda ya biyo baya tun daga kan auren zezee da Musa da kamfanoni da cire kudi duk daga nine, dan haka yanzu baka da komai sai iya wannan kangon da wancan da ka boye raliya da mota daya,ragowar kuwa an bawa me hakki hakkinta, ba zan sa a kamaka ba amma ka je matarka ta ce ta barka da Allah shi ne zai saka mata domin duk abinda hukuma zata yi maka ba zata sa ta huce daga fushin kashe mata iyaye da ka yi ba,amma idan aka barka da me duka tasan zata ji dadi akan sakayyar da zai yi mata fiye da hukuncin hukuma dan haka ga hanya ga duniya nan, sannan ba zan ce kar ka fasa ba,ba kuma zan ce ka rabu da duk wani ahalin da ya dangance Ni ba"daga haka Dr Bilal ya tashi ya fice suka take masa baya dama tuni 'yan sanda sun yi awon gaba da su killer.

Wata irin razananniyar kara dan gaske ya saki har da yin burgima a kasa, sai da ya ji tashin motoci sun bar bakin kangon sannan ya zabura ya tashi ya fita da gudu,motarsa ya fada ya nufi gidan da Allah ne kawai ya kaishi lafiya,ga tsananin mamaki da tashin hankalinsa sai yaga gidan an sanya masa katon kwado ga kuma wasu murtuka Murtukan ma aikata a wajen suna zagaye gate din hannunsu dauke da zungura zunguran bindigu,ai babu shiri yayi ribas ya koma take ya dinga bin sauran gidajensa da filaye amma duk inda ya je sai yaga an rufe an kuma zagaye wajen da jami'an tsaro,wayarsa ce ta yi kara ya daga da sauri, yana sawa a kunnensa manager gidan cacar da yake dashi a boye ya sanar dashi gidan cacar ya kama da wuta shi kadai ba tare da sa hannun kowa ba,"wayyo Allah na" abinda ya fada kenan ya zaburi motar yana kewaya gari kamar tuburarren mahaukaci tuni kansa ya dau caji kwakwalwarsa ta daina aikin komai sai surutai da zage zage da tsinuwa kwando kwando zuwa ga Dr Bilal da kaf zuri'arsa.

***

A bangaren mommy kuwa tuni suka yi kaura daga anguwar gaba daya suka koma saboda gidan da ta siya da yawun Dr Bilal,shi kuma wannan aka saka shi a kasuwa,tuni ta kwashe takardunta da dan gaske yake ta tattalawa yana sauya musu waje ashe duk wayonsa akwai wanda suka fishi,zezee ma tuni ta kara samun kwanciyar hankali saboda yadda ilimin addini ya fara ratsa ta saboda ta bada himma sosai wajen koya,sai kuma wani abun mamaki ga zezee da ta dau kafa takanas ta je wajen Ummul ta roketa gafara, ta jima a gidan suna magana da Ummul, anan Safwan da basu jima da dawowa daga karatu ba ya zo wajen Ummul yaga zezee a gidan, har ya fara bata rai sai Ummul ta yi masa bayanin abinda ya kawo zezeen,to sai kuma ya dan sake kadan da ita,wadda ita kuma a take a wajen ta hadu da soyayyar ta ta gaskiya,sai dai dake yanzu ba zezeen da ba ce tuni ta kama kanta ba ta bari ko a fuska ta nunawa Ummul da Safwan ba.

Ko da taje gida kasa daurewa ta yi har sai da ta sanar da mommy abinda yake zuciyarta, sosai mommy ta yi farin ciki da labarin da zezee ta kawo mata dan haka bata yi kasa a gwiwa ba ta sanar da Dr Bilal ,amma bata bari zezee ta san da haka ba.

*****

Hajiya ce zaune a kusa da baba tana waya da Dr da tun jiya ya koma gida amma yaki zuwa gidan duk da cewa zuciyarsa na gidan gangar jikinsa ce kawai take can wani waje daban"magana suke akan maganar bikin,ya ce shi baya bukatar wani biki,Hajiya kuwa ta ce bai isa ba dole su yi biki me kyau da tsafta wanda za a ci asha a yi sadaka,shiru yayi yana son jin ko Hajiya zata ce ya ɗan zo gidan kamar yadda yake so,amma sai yaji har suka gama wayar bata ce masa komai ba,itama ta fuskanci hakan amma sai ta basar saboda bata son ya ga Ummul din har sai an gama gyaran da ake mata,dan ta tabbatar da cewa idan ta bari suka hadu to wallahi dukansu ba za su bari a yi bikin tana cikin gidan ba sai dai abi su can da Gara,shi yasa ta kyale su tun da dai ta samu Ummul din ta daina wannan koke koken saboda hajiyar ta bata labarin yadda Dr suka kare da dan gaske,har Ummul din ta dinga babbaka dariya saboda tsananin farincikin da labarin ya sanyata sai dai kuma ita ma tana cike da kewar Dr gentle dinta.

A bangare daya kuma sun shirya da su umminta har sun zo gidan gaba dayansu ta gansu, har da su Safwan wanda dama su suna zuwa tunda ba da su take fushi ba,hakan yasa ta ɗan samu nutsuwa,har ta bawa hajiyar sudan hadin kan ci gaba da yi mata gyaran da ko mace yar uwarta ce ta ganta sai ta yi sha'awar dama a ce ita ce,ta bangare guda kuma kannen Dr da ita kanta hajiyar suna ci gaba da shirin bikin.

*****

A bangaren Alhaji dan gaske kuma,a ranar da wannan abin ya faru da dare yana cikin zagaye garin masu kwace suka tare shi suka kwace wayoyinsa da motar gaba daya, Sannan suka yi masa duka suka watsar a gefen titi,ko da ya bude idanunsa bai damu ba sai kawai ya ci gaba da tafiya kansa tuni ya juye,babu abinda yake sai lissafin Kudi,daga ya gama sai ya koma tsine tsine ba tare da ya kama suna ba,kana kallonsa dai kaga sabon mahaukaci.

***

Yau dai karshen tukatiki tuk, an shiga gagarumin biki a gidan Alhaji Ahmed dan itopia wanda ya tara yan uwa da abokan arziki biki ne da za ayi na kwana biyu ko kuma na ce walima,dan kuwa babu wasu bidia sai ma karatun alkur ani da addu'a ga ma'auratan, sai kuma manyan kyaututtukan da ake ta mikawa mutane mabukata, sai dai kuma fuskar amarya babu walwala duk irin kyan da ta yi saboda kawai ta gaji da wasa da hankalinta da ake,Hajiya da Ummi duk suna hankali ce da ita amma ba su yanka mata ba, A'ishah ita ce a kusa da ita, dan haka ita take shan korafi da mita kamar ita ce ta hanata ganin Dr Gen din nata.

Ummul ta yi kyau har ta gaji kamar ka sace ta ka gudu,Dr Gen dinta yana daga yana cikin gidan daga can bagarensa kuma yana zuwa ta inda zai iya ganin Ummul ya ganta ya da koma ya kwanta yana ganin kamar ba zai iya ci gaba da danne radadi da ciwon rashin ganin Ummul na tsawon lokaci ba.

A can kuma dakin Hajiya yamma lis zazzaɓi da ciwon kai suka kada Ummul, wanda ko ranta ma babu na rashin Dr gen dinta ne da kuma gajiyar biki,hakan yasa Hajiya ta bawa A'isha key din bangaren Dr Gen wanda yake hannunta akan suje ta Kaita ta kwanta ta yi bacci saboda ta rage hayaniya,Hakan kuwa aka yi A'isha ta kama hannun Ummul Aunty surayya me bin br Sara ita ce ta taka su ta can baya wajen da babu mutane,sai da ta nuna musu bangaren Dr Gen din sannan ya juya ta koma bangaren su Hajiya, Ummul ko ganin gabanta bata yi sosai shi yasa A'isha tana buɗe mata daya daga cikin dakunan da ta gani a cikin falon ta fada ba tare da ta kunna fitilar dakin ba,A'isha ma bata tsaya ba sai kawai ya janyo mata kofar ta juya ta fice daga falon

Ummul tana zuwa bata tsaya wata wata ba ta fada saman gadon,"ash"Dr Gen ya fada yana sanya dogayen hannuwansa yana tarbarta cikin naked skin dinsa da babu kaya,tun shigowarsu ya ji motsi amma dake muskilin gaske ne sai yayi luf bai motsa ba har ta shigo ta kuma fada kansa,a firgice Ummul ta bude baki zata yi ihu amma sai yayi saurin rufe mata baki ta hanyar hade bakinsa da nata,aiko ta ke ta hadiye ihunta Sannan ta fara kici kicin kwatar kanta,duk da cewa tuni zuciyarta ta sanar mata da kowaye,a hankali ya kai hannunsa ya zame mayafin jikinta tare da dankwalinta wanda take gashin ta ya bayyana, Sannan ya kai hannu ya kunna fitilar dakin da anan take dakin ya haskaka, hasken kuma ya kara haskaka da hasken idaniyarsu da suka haske juna da su,a hankali ya sumbaci idanunta da suke cika da hawayen wata irin kewa da kauna kafin ta kifa kanta a kirjinsa tana dan bugun kirjinsa cikin wata irin sigar da ke bayyana farinciki, dadi, kewa, kauna, shauki, mara adadi ko misalin ganiya, Sannan cikin Muryar ta da ta yi wani irin sanyi ta ce"babu ruwana da kai na yi fushi da kai"tana fada kuma tana kai masa wata irin runguma me cike da shaukin da ita kanta bata san zata iya kasancewa a cikinsa makamancinsa ba,a hankali ya juyo da ita tare dagota sosai ya hade fuskarsu waje daya yana kallon cikin idanunta da har yanzu suke cike da kwalla,hannu yasa ya lakato hawayen tare da yi mata nuni da su,rufe idanun ta karasa yi sai ga hawayen suna saukowa a hankali kamar wanda ake turo su,dumin harshen sa taji ya sauka a saman kuncinta yana lashe hawayen su kuma suna karuwa,da kyar ta iya bude baki cikin Muryar kuka ta ce"Dr gen ka yi hakuri ban san haka ba ne,kuma....hade bakinsa da nata ya sake yi,wanda yasa ta hadiye maganarta,samun kanta ta yi da sanya hannunta cikin tattausar sumar kansa tana wargazata tare da bashi damar yin yadda yaso da harshen ta.

A can cikin gidan kuwa Mommy ce suka zo ita da zezee,sosai Hajiya ta karbe su hannu bibbiyu, ko da mommy ta nemi ganin Ummul Hajiya ta ce mata,ai bata jin dadi tana can bangaren Dr ta kwanta ta ɗan huta ko kan zai saki,zezee kan da ta ji cewar Ummi ma sunan can suna nasu bikin ji ta yi kamar su tafi can din ko dan ta ga Safwan da tun ranar basu kuma haduwa ba,kamar mommy ta shiga ranta sai cewa hajiya ta yi ko za a kwatanta mata gidan su Ummul zasu je su yi Allah ya sanya alheri,babu musu kuwa Hajiya ta kira driver ta ce ya dauko mota ya rakasu,zezee taji dadi har sai da hakan ya bayyana akan fuskarta.hajiya bata barsu sun tafi ba har sai da ta haɗa musu kayan biki kaja guda Sannan suka tafi suna Godiya,

A mota zezee take cewa da mommy"wallahi mommy ni kaina yanzu na fi jin dadin rayuwata,idan mashiga cikin mutane Yan uwana na yi mu mala da su yadda kowa yake yi sai naji farin ciki,yanzu gashi har Kawaye na fara yi masu mutunci ba kamar irin na da ba musamman irin su bely da nake ganin duk abinda take yi ba laifi ba ne,hasali ma a matsayin me yanci na ke kallonta"Mommy ta yi dariya Sannan ta ce"alhamdulillah, zezee abinda zaki yawaita fada kenan tabbas Allah yayi mana babbar ni'ima da ya bamu hanyoyin neman aljanna ya kuma bamu damar neman gafararsa da yi mana alkawarin amsawa, Allah mun gode maka da ka yi mu cikin Musulunci ka kuma tsare mana zukatanmu daga saba maka, Allah ya ci gaba da kare mu da sharrin zuciya"Amin zezee ta amsa tana kwantar da kanta a kafadar Mommy Tana ji a ranta dama mahaifinta shima ya tuba tunda Allah gafururrahim ne,to amma ina, wanda Allah ya shiryar ya shiryar sai dai zata ci gaba da yi masa addu'a idan har yana da rabo zai dawo hanya.

A can bangaren Hajiya bayan su zezee sun tafi sai shiga neman A'isha akan ta zo ta dauko mata ummul saboda a shirya ta a kaita gidansu,dangin su agades suna can suna jiranta,acewarta ma ai sun yi musu kara, saboda hakurin da su kayi suka bar musu amaryar su kuma suka yi bikin babu amarya,shi yasa take son ta kaita can dan ta basu hakkinsu su kai yarsu dakin miji da kansu,dakyar ta gano aishar Sannan ta ce ta je ta taso Ummul din hajiyar Sudan na jiranta zata shiryata.

Ko da A'isha ta sa kai falon kai tsaye ta nufi kofar har tasa hannu zata bude sai kuma ta yi wani tunani ta dakata ta fara kwankwansawa,sautin kofar ne ya dawo da Dr cikin duniyar da muke,a hankali ya tambayi waye, cikin kunya A'isha ta amsa da cewa"nice Hajiya tana bukatar Ummul"dan jim yayi, bashi da wata mafita sai bada Ummul dan Hajiya bata san yana cikin gidan ba,kuma baya bukatar ta sani din dan haka sai ya dago Ummul din da ta yi lum a jikinsa kamar wata jaririya,bakinta ya sumbata Sannan ya tayar da ita suka mike,gashin ta ya gyara mata ya sanya mata mayafinta yana kallon fuskarta da ta yi wani haske ta yi fresh,hannu yasa ya dan shafa fuskar sannan a hankali ya ce"idan sun gama bikin sun dawo dake ina maraba dake a cikin rayuwata zan yi farin cikin da ban taba riskar kaina a cikinsa ba, Ummul ba zan ce komai ba kuma ba sami fahimci komai ba har sai kin zo gare ni "daga haka yaja hannunta ya fito da ita har falo inda A'isha take tsaye tana jiranta,"A'isha ina godiya da wannan kyauta taki ta bazata,dan haka kina da kyauta a wajena"daga haka ya sumbaci bakin Ummul ba tare da ya ji kunyar idon Aisha ba,sai ita aka bari da saurin ficewa daga falon tana ji kamar ta nutse saboda girman Dr a idanun ta,ko da ta fitan kasa hakuri yayi sai da ya janyo ta jikinsa ya rungume tare da sumbatar goshinta,ji yake kamar Hajiya bazata dawo masa da sarauniyarsa zuwa masarautarsa ba, shi yasa yake kuma jin kewarta na hanashi sukuni,ganin ya kasa rabuwa da ita yasa da kanta ta janye jikinta Sannan ta kai masa sumbatar ba zata a kuncinsa tana mai ficewa da gudu fuskarta dauke da murmushin dariya.

Shafa kuncinsa yayi tare da zubawa hannun da ya shafo wajen idanunsa sai yaki kamar Ummul din yake gani,yadda ta yi din ya tsaye masa a rai kuma ya sanya shi farin ciki dan haka bai san ya saki wani kayataccen murmushi a saman kyakkyawar fuskarsa ba.

***

Ummul tana zuwa hajiyar Sudan ta sanya ta a gaba ta yi mata wankan lalle da na turare sai wasu irin hadin magunguna masu shegen dadi wanda a ka yi su da kayan itatuwa,a cikin kankanin lokaci najiyar Sudan ta gyare Ummul ta fito tsaf cikin shirin Kaita gidansu,duk inda Ummul ta motsa kamshi take,ko waje ta bari sai ya dade bai bar kamshinta ba,shi yasa ko shi kansa Dr Bilal tun da ta bar dakin ya shigar da kansa cikin bedsheet din ya manne fuskarsa yana shaƙar kamshinta da ya kara masa tsananin kewarta da ke tafarfasa masa zuciya da ruhi.....

Zahra✍️

💕GIDAN ƳAN ƘARYA💕

By

FATIMA Y ADAM......

Littattafan marubuciyar.

KUDIRAR ALLAH

KADDARATA SANADIN HASKE

ƁOYAYYIYAR RAIHAN

ƳAR GIDAN YARBAWA

MATAR ƊAN BIRNI

And

GIDAN ƳAN ƘARYA....