Pg46
Hajiyar agades da br sara sune suka maida Ummul gida, sannan suka basu dama suka dan yi bikinsu da ita na sauran lokacin da ya rage musu,daga nan kuma aka kuma shirya Ummul din sannan adda Kulsum wadda take yaya a gurin baffansu ta kaita wajen baffa da ummi,dan su yi sallama, suna shiga Ummul ta rungume ummi tana kuka,haka ta yiwa baffa sai da kyar suka lallameta ta yi shiru,sun ja lokaci me tsayi wajen yiwa Ummul fada me hade da nasiha masu ratsa zuciya, baffa yana gamawa ya tashi ya fice yana share kwallar da ta cika masa ido,to ita ma Ummi da kyar aka raba su da Ummul din, daga nan adda Kulsum da yaya turai suka sakata a gaba sai mota,duk takun da Ummul za ta yi sai ta yi wasu daga cikin tarin addu'o in da baffa da Ummi suka bata har ma da Hajiyar Dr Bilal,daga nan kai tsaye gidan suka kuma komawa da ita a nan suka kara tabbatar da mutunci da karamci irin na ahlin dan itopia, har gaban Hajiya suka kai Ummul, yaya Turai na shirin bata amana bayan sun kammala addu'a Hajiya ta tari numfashi ta,da cewa"kar ki ce komai saboda Ummul ikram 'yata ce Ni ce ya kamata na bada amanarta ba wai ku ku bani ba,dan haka mu yi musu fatan zama lafiya Allah ya kade fitina a tsakani"gaba daya suka amsa da Amin fuskar kowa ka kalla cikin farinciki da nishadi,daga nan Hajiya ta kama hannun Ummul ta kaita wajen baba,a Nan ne suka samu Dr Gen durkushe gaban baban nasa,kansa a kasa yana karbar nasiha irin ta dattijan da suka san martabar mace da sanin ma anar aure da kuma kalubalen da ke cikinsa,zaunar da Ummul Hajiya ta yi a kusa Dr Gen sannan itama ta zauna,daga nan baba yasa mata albarka sannan ya dora musu da nasiha me ratsa jiki daga nan,yayi musu addu'a sannan ya bawa Dr Gen umarnin kama hannun matarsa da su tafi gidan aurensu,hakan kuwa Dr Gen yayi ya kama hannun Ummul da yake ji kamar ya sureta su tashi sama su lume cikin gajimare suka fita bakunan su dauke da addu'ar fatan nasara da alkairi a cikin aurensu.
Dangin amarya dai sai komawa su kayi,gida da kabakin abin arzikin da aka hada musu, sannan Hajiya ta basu hakuri akan in sha Allah zuwa da safe za a zo a kai su su je suga gidan Ummul sannan su yi mata sallama tunda a gobe zasu wuce agadex.
****
A bangaren su zezee kuwa tun lokacin da suka je gidan su Ummul,mommy ta samu kebewa da Ummi su kayi magana cikin mutunci, a nan Ummi take sanar da mommy cewa ai har Dr gen yayi magana da Safwan kuma ya amince dama shima rashin ganin fuska ne yasa bai magantu ba, wannan abu ba karamin farin ciki ya sanya mommy ba,shi yasa ta tafi cikin farin ciki, bata sanarwa da zezee komai ba, saboda ta san Safwan zai kirata, aiko a cikin daren ya kule a dakinsu ya danna mata kira,dakyar zezee ta yi control din kanta ta fuske kamar ba ita ce take kasa bacci saboda shi ba,(su zezee an yi hankali)a daren dai komai ya kammala tsakanin zezee da Safwan.
A ta can gefe kuma A'isha ce da nata gwarzon da ta fidda wato ya Hamza,sai ya zamana an bar mufty da Ali da zare ido, dan su yanzu karatu zasu tafi dan Dr Gen tuni ya gama yi musu shirye shirye,dama bikin su ke jira a kammala kawai su dage.
****
Tunda suka tafi hanya Ummul take share hawaye tana sakin ajiyar zuciya a kai akai,shi kuma Dr Gen tuki yake kamar baya so dan a hankali yake tafiya cikin nutsuwar sa da take tare da shi a ko da yaushe,sai da ya ji bata da alamun daina kukan ne yasa shi kamo hannunta ya sanya cikin nasa yana dan murza dogayen yatsunta da suka sha ja da bakin lalle, hannunsa daya kuma yana kan sitiyarin yana murzashi a hankali idanunsa akan hanyar,yadda yake sarrafa hannunta cikin nasa hannun ya sa ta yi shiru saboda yadda ya gama kashe mata jiki,kasancewar akwai yar gajiya a tare da ita yasa tuni ta bingirar da kanta a jikin kafadarsa ta kama bacci,hannunsa yasa ya shafo gefen fuskarta tare da lumshe idanunsa yana bude su a lokaci daya bisa kyakkyawar kwaltar dake shinfide saman titin da zata kaika badawa.
Ko da suka karaso tun daga farkon Layin securitys suka san da zuwan su, dan haka tun kafin su kara so an bude musu girkakken gate din da yayiwa kewayayyen gidan nasu kawanya,ba wancan gidan ba ne wannan sabo ne fil ita ce zata fara shiga abinta,ba za a kira gidan da wani mugun kato ba, sai dai muce madaidaici me cike da kayan kawa irin wanda za a kalla a ce eh lallai wannan matar so ce kuma yar gata,fasalin gidan me kyau ne irin na turawa,sai dai kuma a binda zai burgeka a cikin gidan shi ne,daga can baya aka dibi wani bangare guda aka yi masa ginin laka aka yiwa dakunan jere irin na mutanen kauye hatta da randar ruwa a kwai a cikin dakin ga tsakar gida da banɗaki, Dr yayi haka ne saboda kawai ya dinga tunawa da rayuwar da yayi cikin talakawa,dan sosai rayuwar take burge shi,shi yasa yasa a ransa zai yi gini ko da a cikin gidan da zai yi rayuwa da Ummul ne saboda ya koyawa yayansa daraja talaka da rashin kyamar su, sannan zai basu dama su yi hulda da na kasa da su ko dan su fahimci rayuwa.
Yana ajiye motar cikin wadatacciyar rumfar da a ka tanade ta dan ajiye motoci, babu security din da ya zo inda yake saboda wannan babban kashedi ne daga oga mijin sarauniya Ummul Ikram akan muddin yana tare da iyalinsa baya bukatar wani kato ya zo inda yake, wannan dalilin yasa tunda sun san tare yake da amarya basu zo inda yake ba,da kansa ya fita ya zagaya ta bangaren da Ummul take ya bude, sannan a hankali ya rungumota jikinsa ya sabata a kafadarsa,daya hannun kuma ya dauki manyan ledojin da ya kwaso su a bayan mota, daga nan yabi ta wani dogon baranda sai da ya je karshen sa sannan ya taka wasu step basu fi guda biyar ba ya shiga cikin wani babban falo me kyau da tsari babu abinda yake tashi sai kamshin Ummul da hajiyar Sudan ta zamar dashi nata muddin rai kai a komai da ya danganci Ummul wannan tsabtataccen kamshin suke yi,kamshin da baka isa ka ji shi a waje ba tare da ka juya ka ga me yin kamshin ba,a hankali ya ci gaba da taku yana ratsa dakunan da suke cikin falon har ya shiga wata kofa,ashe upstairs ne a cikin kofar nan ya taka da Ummul da take ta sharbar baccinta hankali kwance ,shi kuma yadda yake tafiya ba ka ce mutum sukutum guda kamar ummul ya dauko ba,yana hayewa upstairs din yasa hannu ya janye wata babbar kofar glass wato sliding door ya shige,sai gashi a cikin wani kayataccen falon da ya fi na kasa komai da komai daga nan ya zabi dakin da ya tanada dan zuwan wannan rana ya shige da Ummul dake kafadarsa.
A hankali ya kwantar da ita akan makeken gadon da yake cike da jan furanni da fari a hade ga wani irin kamshi wanda ya bambanta da na falon kasan, wannan kuma kamshin ba na kowa ba ne sai na dr gen ,Yana kwantar da ita ya shige wani daki jim kadan ya fito daure da towel a jikinsa, bathroom ya shiga yayi wanka ya kimtsa, sannan ya fito yana baza sassayan kamshinsa da ya yi sanadin farkawar Ummul daga baccin da take yi,sai dai tana buɗe idanunta tayi arba da Dr gen din nata a yadda ya zo duniya yana kokarin murza turare a jikinsa,ai ko take ta wangale baki ta kurma ihu tare da cusa fuskarta cikin gadon tana yi kamar zata shige cikin katifar gadon,tsaf ya fahimci a binda take yiwa ihun amma dake dan duniya ne sai ya fuske tare da karasowa gabanta yana cewa"idan an yi mafarki addu'a ake yi ba ihu ba"wannan kalmar da ya fada ta mafarki yasa ta yi tunanin mafarkin ta yi shi yasa ta sauke ajiyar zuciya tare da dagowa tana bude baki zata fada masa irin kalar mummunan mafarkin da ta yi,tuni ta bar bakin a bude idanunta kuwa kamar wadda ta yi gamo babu a binda suke sai budewa da rufewa kirjinta kuwa kamar ana dukan sakwara,numfashinta tuni ya fara kaiwa da kawowa, wannan tsoron da Ummul ta shiga yasa shi Jan towel ya rufe jikinsa, amma tabbas ya sa a ransa dole sai yayi maganin wannan tsoron a daren nan,hannu yasa ya kamata tare da dan girgizata wanda hakan yasa ta saki ajiyar numfashi sannan idanunta da suka kafe suka lumshe tare da zubar hawayen da bata shirya musu ba,tsakani da Allah ba karamin firgitata abun nan na Dr gen yayi ba,hakan yasa ta dan matsa daga daf da shi tana satar kallonsa,bai ce mata komai ba ya juya ya koma wajen da ya shiga dazu sai gashi ya fito sanye Da Kayan bacci masu kyau riga da wando sai kuma wasu irinsu a hannusa,zube su yayi a kan gadon tare da hijabi, sannan ya kalleta fuskarsa babu walwala,dan yaga alamun cewa sai yayi mata da gaske zata a jiye taɓara da sakalci,"kije ki yi wanka ki daura alwala ina jiran ki"daga haka ya fice daga dakin,cikin daga murya yadda zai jiyota ta ce"Ni fa na yi wanka dan ina ga wankan da nasha a wajen hajiyar Sudan yafi wanda ka yi a tsawon rayuwarka"yana jinta amma bai ce komai ba,ya dai san cewa nan da dan wani lokaci zai kashe bakin rashin kunyar murus,tura baki tayi tana gunguni sannan ta shige bathroom din,ganin ruwa a hade yasa ta tube ta yi wankan tana mitar ba zata tsaya ta dirje jikin sosai ba dan har yanzu jikinta bai daina radadin durzar hajiyar Sudan ba,brosh ta yi da alwala sannan ta fito, ganin baya dakin yasa ta yi saurin saka kayan da ya ce ta saka tana yi tana kallon hanya dan kar ya shigo Ya ganta a haka, tana gamawa kuwa sai gashi,a gaban mirror ya tadda ita tana ta feshin turaruka bayan wanda hajiyar Sudan ta gama yi mata turarensa,ta bayanta ya tsaya ya kwace kwalbar da take hannunta yana cewa"lallai yarinya kin shirya karbar mijinki irin wannan wankan turaren to amma a yi hakuri haka a bari na ji da na ainihin"ya fada tana kwantar da kansa a kafadarta tare da shigar da fuskarsa cikin wuyanta yana shaƙar nunfashi da mayataccen kamshin da yake neman zautar da shi,dama can yasan Ummul dinsa da son kamshi,dan ko daga nesa ya tsaya sai ya jiyo irin kamshin su na yan agadex a jikinta yana tashi,irin kamshin da suke kira da kabbasa,bare kuma yanzu da ya kuma bin jikinta da hadin kamshi irin na yan Sudan.
Dan turesa ta yi tana cewa"Dr Gen yunwa nake ji"ta fada cikin shagwaba ba kuma tare da ta fuskanci inda kalamansa suka dosa ba,kamo kugunta yayi yana wani shige mata kamar cingum, a haka suka taka har falon a inda Ummul ta tarar ya haɗa mata kayan dadi kala kala, da kansa ya zaunar da ita sannan ya zauna ya fara ciyar da ita kamar wata yar jaririya,sai da ya tabbatar ta gamsu sannan ya ci abinda zai iya ci ya ture yana bin Ummul data bi jikin kujerar da take zaune a gabanta ta kwantar da bayanta tana lumshe ido kamar zata yi bacci,zuba mata ido yayi na dan wani lokaci kafin ya yunkura da karfinsa ya sunkuceta kamar wata yar tsana,daga kafa ta shiga yi tana cewa"Ni kam ka sauke ni,haka nan sai ka dinga daga ni kamar wata mara kafa abu kadan ka sure Ni kamar yar tsana"bai kula da mitarta ba har sai da ya ajiye ta a dakin ya tsayar da ita akan kafafunta tare da sanya mata hijab,shi kam sai da ya koma bathroom ya kuma dauro alwala,yana fitowa ya shiga gaba yaja su sallar na fila.
Raka'a goma su kayi suka dora da shafa i da wuturi, sannan suka yi karatu da addu'a,daga nan Dr Gen yayiwa Ummul yan tambayoyi daga cikin addininta wanda dama yasan bashi da haufi dan dai wannan ya zama nauyi a gareshi da ya kuma tabbatarwa da kansa irin uwar da ya samowa yayansa, Ummul kuwa bata dauki sallar da addu'a da suka yi a wani abu ba dan wannan ba sabon abu ne a wajen ta ba,dan haka suna gamawa ta fara sakin hamma duban ta yayi tare da cewa,ta je ta kwanta"tsayawa ta yi tana kallon sa, sai kuma can ta ɗan tura baki tana cewa"amma dai ba a nan zaka kwana ba ko?"a ina kike so na kwana"?ya tambaye ta yana bin ta da wani irin shu'umin kallo da ya fara kassara gabbanta,"a falo zaka kwana saboda kar wani abu ya shigo dakin, ba sai ka canja daki ba,dan Allah ka ji Dr Gen"takarasa maganar cikin sigar lallashi,jinjina mata kai yayi ba tare da ya dauke idanunsa daga kanta ba, a sanyaye ta tashi ta wuce tare da hawa saman gadon ta kwanta ba tare da ta dauke idanunta daga kansa ba,shi din ma ya kula da cewa har yanzu a tsora take da shi kawai karfin hali ne irin nata.
****
Kamar a mafarki Ummul ta ji mutum a kusa da ita, sai dai kamshinsa da yanayinnsa na natsuwa yasa ta fahimci cewa shine ba mafarki take ba,rungume ta ya kuma yi a cikin jikinsa yana bin fuskarta yana sumbata kamar zai cinyeta, a marai rai ce ta rike hannunsa da yake kokarin zame yar rigar jikinta, Sannan ta ce"dan Allah Dr gen ka rike amanar da baffa da Ummi suka baka har Hajiya da baba ma na ji sun ce maka ka rike amana kar ka bari na yi kuka, kuma abinda kake shirin yi min yanzu wallahi idan ka yi min kuka zan yi ina jin ma har suma zan yi,dan Allah dr gen kar ka ji min ciwo da wannan abin naka,ba zan iya ba ka gani karamar yarinya ce ka tausaya min,"bai saurareta ba ya ci gaba da cire rigar ya wurgar da ita a kasa Sannan ya dago fuskarta Yana kallon idanunta ta cikin dan hasken da ya bari a dakin, Sannan ya ce"Ummul dube Ni nan,na san kina da ilmin ki na addini kuma kin san komai a karance,dan haka ina so ki yi hakuri da Ni a wannan daren dai ba zan iya rike amanar baffa da Ummi ba,dama kuma ban dauka ba,ko su san cewa a cikin amanar da suka bani ban da wannan bangaren"a hankali ya hade fuskarsa da tata har bakin su da hancinansu suna gugar juna,Sannan cikin wata irin kasalalliyar murya ya ce"Ummul Ikram in sha Allah yau sai kin san kadan daga cikin irin son da BILALU AHMAD ƊAN ITOPIA yake miki, Ummul am sorry ba zan iya ci gaba da rike tsananin kaunar da nake miki ba,na gaji da boyewa dan haka ki barni na fallasa ta ta hanyar da ya fi dacewa,saboda baki na yayi kadan ya bayyana miki yadda kike a dukkan rayuwata,"ya fada yana hade bakinsa da nata ya shiga yi mata wani irin zazzafan kisess da ya nemi hargitsa karamar ƙwaƙwalwar Ummul ikram.
Wata irin zazzafar SOYAYYA dr gen ya shiga nunawa Ummul tamkar zai hadiyeta,ji yake duk abin da yayi mata ba zata gamsu da yadda yake jinta a ransa ba,shi yasa har ya nemi rasa ta ina zai fara,yadda yake burkita Ummul din da salo salon da yake mata yasa har ta fara hawaye, sai kuma daga baya kukan ya komawa na tsananin tausayin dr gen din nata,dan tun kan aje ko ina ta fahimci abinda yake son nuna mata,tabbas ko da dr gen ya kasance me baki ba zai iya bayyana mata adadin yadda yake jinta a ransa ba,daga karshe dai sallama masa kanta da komai nata ta yi tare da bashi tallafi ta hanyar nuna masa jarumtarta da kuma kadan daga cikin tata sosayyayyar, dauriya da kuma juriyar ta Sun bada gudunmawa wajen karasa zautacciyar ƙwaƙwalwar da take yi mata SOYAYYAr da babu ji babu gani bata da farko kuma bata da karshe.
Sosai Ummul ta ke kokarin janye tsoro da firgicin da ke tare da ita a yayin da Dr gen yake hanyar kaiwa ga mallakar ta,shi kansa Dr gen neman rasa hayyacinsa saboda tun daga farkon Ummul har lokacin da yake daf da kaiwa makurar kurewa bai ji wani abu da bai sanya shi shauki daga gare ta ba,tun daga kesess ya fara banbance Ummul da sauran mata,bare kuma yanayin halittar jikinta da ƙirar da Allah yayi mata wanda ko ita ce da kanta ba za ta iya yin kanta kamar yadda Allah ya kerata a haka ba,duk wata soyayya da Dr gen ya lullbe a nan take kokarin budewa Ummul ita ta ga kadan daga cikinta ko Allah zai sa ta dinga tausaya masa a cikin mu'amala da rayuwarsu ta aure.
Sai dai kuma duk yadda Dr gen ya kai ga kaiwa kololuwa a cikin tafkin da bai san iyakacinsa ba,hakan bai sa ya kasa tuna wacece Ummul a gare shi da duniyarsa ba,bai manta tausayin da ke cikin kauna mara Algus ba,dan haka bai yi mata danganci ba,ya tafi da ita a hankali cikin wata irin kulawa da kauna bayan ya gabatar da addu'ar kasantuwa da iyali,Ni dai jin kukan Ummul da Dr shi yasa Ni barin maɓoya ta da gudu na yi waje,saboda ba wata mace da ta cancanci jin kukan Dr sai Ummul.....
Zahra✍️
***
💕GIDAN ƳAN ƘARYA💕
By
FATIMA Y ADAM......
Littattafan marubuciyar.
KUDIRAR ALLAH
KADDARATA SANADIN HASKE
ƁOYAYYIYAR RAIHAN
ƳAR GIDAN YARBAWA
MATAR ƊAN BIRNI
And
GIDAN ƳAN ƘARYA....