Pg48
Suna ganin haka kuwa suka mike gaba dayansu suka bar falon,dan su kansu sun ga rashin hankalinsu na zuwa gidan amarya a daidai wannan lokacin,shi kam dr gen ya ma manta da su bare sanin fitar su,cikin lallabawar da bai san ya iya ta ba,ya kama duka hannunta yana tambayarta abinda ya sa ta kuka cikin yaransa da tuni ta gama iya shi,"nace su ci abincin da Hajiya ta kawo mana sun ki ci"ta fada tana waiwayawa dan ta kara tabbatar musu da rashin jin dadin abinda su kayi matan,amma juyawar da zata yi taga wayam,shi kansa Dr Gen sai ya samu kansa cikin jin nauyin abinda yayi bayan ya dawo hayyaccinsa,daga shi har Ummul din tashi suka yi suka fita,lokacin da suka karasa harabar gidan har sun gama shiga mota driver ne kawai ya rage, dan haka da sauri suka karasa bakin motar,Dr Gen dai ya fuske ko a fuska bai nuna wata alama ta kunya ba,wata yar jaka da Ummul bata kula da ita a hannunsa ba ya kikawa adda hasana yana cewa"mun gode Allah ya sauke ku lafiya"Ummul kuwa kukan ta kuma sawa tana cewa dan Allah su dawo su bar tafiyar yau har sai gobe,ganin da gaske take yi ne yasa yayiwa driver nuni da ido da yaja motar kawai,hakan kuwa aka yi driver Yana jan mota ta fara dirdira kafafu a kasa zata tada rikitaccen darinta da baya jin lallaɓa,sanin cewa zata iya zubewa a wajen ta yi darunta yasa shi saurin daukar ta ya yi ciki da ita,yana shiga falon ya hade bakinsa da nata wanda shine ya hanata damar ci gaba da kukan da take yi.
A kan kujera ya kwantar da ita bayan ya sake ta ,kai tsaye abinci ya haɗa mata tare da shayi me lafiya, sannan ya janyo ta jikinsa ya fara feeding dinta kamar wata yar yaye,kasancewar Ummul tana jin yunwa sosai yasa bata yi gardama ba ta ci abinci iya yadda zurfin cikinta yake, sannan ta nuna masa ta koshi,tana kwance a jikinsa ya ci nasa ,lokacin da ya gama har ta fara bacci,ji ta yi kawai ya kuma ɗaukar ta ya shige da ita upstairs,bai kuma dire ta a ko ina ba sai a bathroom tare da nuna mata time din sallar azhar,hakan yasa ta daure ta hakura da baccin, sai dai a tunaninta barinta zai yi ta yi wanka da alwala amma sai taga sabanin haka,dan kuwa da kansa ya cire mata kayanta sannan ya saka ta cikin ruwan kamar dai yadda yayi mata dazu, sai da ya gasata ta gasu har ta kai da cewa bata jin ko wane irin zafi a tare da ita, sannan ya bi bayanta zuwa cikin ruwan,duk yadda ta so ya rabu da ita hakan bata samu ba,sai da suka yi wankan gaba daya, sannan su ka daura alwala, ya kuma nadota a cikin towel suka fito,wata yar doguwar riga me sulbi ya saka mata shima ya sa, sannan ya saka mata hijab suka tada sallah.
Suna idarwa bayan yan addu'a bai tsaya wata wata ba ya dauke ta,sai saman tattausan katifar gadon da take tamkar auduga saboda laushi,duk yadda Ummul ta so da ya barta ta yi bacci hakan ya gagara,saboda kai tsaye ya shiga aika mata zafafan sakonninsa masu rikita ƙwaƙwalwa musamman irin ta su Ummul wadda take cike da yarinta.a hankali a hankali sai ga Ummul na daukar wasu irin darussa masu tsananin zafi daga Dr Gen din nata,ba zan iya tona muku wata irin rayuwa da wadannan ma'aurata suka tsinci kansu a ciki ba, domin nasan kun fi Ni sanin halin da masoya suke riskar kansu a duk lokacin da suka kasance a cikin wannan duniyar,musamman kuma masoya irin wadannan da suka yadda suka amince zasu yi komai saboda farin cikin junansu,kuma suka dauki alkawarin zama da junansu a cikin ko wane irin yanayi dadi ko akasin haka.
****
Bayan sati biyu da bikin Ummul da Dr gen,duk wanda ya gansu a yadda suke yanzu ba zai ce su ne wadan nan na bayan ba,daga Ummi har baffa yanzu hankalinsu ya kwanta basu da wata fargaba dan duk inda ake tunanin suruki na gari both side to Dr gen ya kai,mufty da Ali suna itopia an fara karatu sai dai mu yi musu fatan nasara,Hamza da Ali kuwa yau yayan baffa ya zo daga agadez saboda za akai kudin aure da sadaki gidan su A'isha da zezee,to zezee dai bata da kowa ta bangaren uba dan haka sai a hannun mijin raliya aka nemi aurenta,gaba daya ba wani lokaci aka sa ba,dan wata daya biyu aka saka shima saboda a bawa zezee damar nemo mahaifinta da ya shiga duniya aka ne me shi aka rasa ne.
Yadda Hajiya da su br sara kannen Dr gen suke yiwa Ummul sai ka dauka sune yayunta, sangarta da tabara a wajen Ummul sai abinda yayi gaba,duk da cewa sosai take zaman aurenta duk wani nauyi da ya rataya akanta kokarin sauke shi take yi,bat dorawa kanta cewa rayuwar aure rayuwa ce ta soyayya da zaka je ka zuba yadda kake so ba,mahaifiyarta da kuma karatun ta na addini ya koya mata cewa ita rayuwar aure duk soyayyar da kuke wa juna dole sai an yi hakuri an kai zuciya nesa, sannan zo mu zauna zo mu saba ce,duk soyayyar da kuke wa juna dole wata rana a sabawa juna,sai dai su ko da sun yi fadan baya zuwa ko ina, domin Dr Gen ya San wace irin mace yake aure,ya san dole sai yayi hakuri da Ummul domin har yanzu tana cikin shekarun kuruciya.
Sannan tun kafin a je ko ina dr gen ya shaida cewa Allah yayi masa babbar kyauta da irin macen da ba ko wane namiji ne yake dacen samu ba,dan duk yadda Ummul takai ga zuba kuruciya da shirme tana matukar yi masa biyayya, wannan musu Ummul bata san ta yi shi ga Dr gen ba,girki kuwa bata da sakaci wajen yinsa shi yasa a cikin kankanin lokaci ta kuma susuta dan bawan Allah,umminta ita ce macen farko da ta fara koya mata yadda zata fuskanci rayuwar aurenta, ta san damuwar mijinta ta san fushinsa, duk da cewa ya kasance mutum mai boye wadan nan yanayin nasa guda biyu,amma Ummul ko motsi ya yi sai ta gane abinda yake nufi,dama yarensa na magana da ido tuni ta yi digiri a ta wannan bangaren,ta san abinda yake so da wanda baya so, tasan abinda yake so a shimfidar aurensu,bata ƙiwa a kome nata,tabbas da ace sauran ma aurata za su dauki darasi a cikin zaman takewar Dr Gen da yar Ummul dinsa da rigingimun da ake samu tsakanin ma'aurata sun ragu, sun koma zo mu zauna zo mu saba,ma ana dai rayuwar farin ciki da zaman lafiya yafi yawan samun sabani yawa sosai a cikin zamantakewa,ya za mana kuma ko da an saba din akwai hanyar daidaitawa ciki lumana ba tare da an ji kan kowanne daga ciki ba.
****
Sosai zezee ta maida kai wajen neman inda zata samu mahaifinta ko da labarin mutuwarsa ne,duk da cewa har yanzu mommy bata wani goyon bayanta akan hakan sai dai bata hanata ba tunda ita duk lalacewarsa ubaanta ne,shi yasa sai dai ta dinga Binta da ido a kan duk shiga da ficen da take yi.
****
Duk neman dan gaske da zezee take yi a she kusan kullum sai ta wuce ta inda yake zama,amma tsananin dauda da haukan da yake yi tuburan yasa bata taɓa gane shi ba,dan gaske dai har yanzu yana cikin rayuwarsa ta hauka da tunani, wani lokacin idan yayi surutan da zage zagen ya gama sai ya samu waje ya zauna ya yi ta kuka,wani lokacin ma yana ganin zezee amma yana ji yana zata wuce ta gabansa ba tare da ta gane shi ba, haka zai bita da kallo ba tare da ya iya cewa da ita komai ba,har sai ta tafi sannan zai zauna yayi ta kuka yana tuna waye shi a da,tun baya jin nadama a ransa har sai da ya fara kukan nadama a fili da boye saboda tsananin ikon Ubangiji da buwayarsa da yake gani a cikin rayuwarsa tunda gashi kiri kiri ya maida shi abin nunawa a idon duniya kuma ba tare da ya dauke masa hankalin ganewa ba,yana ji yana gani yana so yayi aiki irin na masu hankali amma dake Allah shike da lamarin sai ya ji ya kasa yana ji yana gani zai ta aiki irin na mahaukata,shi yana yiwa kansa kallon me hankali mutane suna masa kallon mahaukaci.
*****
A hankali a hankali sai ga sauki ya fara samuwa a wajen bely, saboda tuban da ta yi da nadamarta sai Allah ya dubeta ya fara kawo sauki cikin lalurarta,abin mamaki wani bawan Allah ne ya kawo ziyara cikin kauyen nasu,sai Allah ya dora masa tausayin bely duk da labarin ta da aka bashi,amma budar bakinsa sai cewa yayi,wai su mutane wace irin zuciya ce da su, me yasa suke jahiltar kansu ne?duk lokacin da bawa yayi laifi tsakaninsa da Ubangijinsa idan ya tuba ya daina da niyar ba zai sake komawa ga aikata wannan laifin ba, Allah zai yafe masa, amma jahilcin da ke cikin kwakwalwar al'ummarmu su da basu bawa yayiwa laifin ba,sai su kasa yafewa ko da kuwa wannan mutumin limamin masallacin Madina zai zama saboda tsananin shiryuwa,dan haka sai kawai ya haɗa mata magani daga horewar da Ubangiji yayi masa ta sanin magungunan irin wannan lalurar,cikin ikon Allah duk maganin da aka yi ba a dace ba karshe dai wannan shine sanadin warakar bely,wani abun burgewa a wajen wannan mutumin me suna Malam kamis shine,neman auren bely da yayi in dai har zata amince kuma a cikin garin Kano yake zaune da iyalansa mata uku,dan haka idan ta amince a Daura musu aure ya tafi da ita,babu wata gardama bely ta amince ,aka daura aurenta da malam khamis,kwana ɗaya suka shirya da yayunta maza da mata suka rakata gidansa dake anguwar dorayi tare da dan abinda Allah ya bawa babanta ya siya mata na gado,babu laifi yana da rufin asirinsa,sai dai matansa basu da kirki, to amma haka ta yi hakuri ta zauna dan ta riga ta sawa ranta ibada zata yi,da kanta ta roke shi ya sakata a wata islamiyyar matan aure da yake karantarwa a cikinta,dan haka sai damuwar cikin gidan ya zama kadan ce saboda ba zama take yi ba kullum tana islamiyya abinta.
****
Yau sauran wata daya babu sati daya bikin su zezee,amma har yau bulayi take loko da sako tana neman Abba dan gaske amma shiru kamar an aiki shurwa garinsu,
A bangaren Ummul kuwa rayuwa ta mika tuni an zama yan gari, rayuwa ake cikin tsafta da kwanciyar hankali, Abuja suke shirin komawa saboda kusan duk harkokin Dr Gen suna can,amma sai sun gama yawan da ya shirya musu zuwa kasashe ko dan cika burin rayuwar Ummul yar karya a baya,idan Ummul ta zauna tana tuna rayuwar da su kayi a baya sai ta dinga jin kunyar Allah saboda gashi dai duk kariyar da su ka yi daga karshe yayi musu ni'imar da basu taba tunani ba ko da a mafarki ne.
***
A hankali Dr Gen ya ke bude idanunsa da suke cike da bacci ya sauke su akan Ummul da take zaune a kan ruwan cikinsa tana ta kokarin sanya masa fuskar da bai san a inda ta nemota ba,dan shi kansa ba zai ce kai tsaye ga inda ya ajiye ta ba,hannunta ya rike yana dan yatsuna fuska kafin a nutsensa ya ce"jiya baki barni na yi bacci da rigimarki ta zuwa wajen Hajiya ba, Sannan dai ba zaki tausaya min ba,zaki tasheni da wata sabuwar rigimar,haba oum ki kwanta mu yi bacci kin ji"ya fada yana birkitota kansa,zamewa ta shiga kokarin yi tana cewa"Dr Gen ba Zan kwanta ba kaima kuma ba zaka kwanta ba idan har ba gentle ka koma min ba"zubawa dan karamin bakinta da baya gajiya da yi masa shan alewa yayi Sannan ya ɗan shafa shi da yatsun hannunsa yana cewa"yau kuma matar Dr Bilal,gen take son kasancewa tare da shi?"dage masa gira ta yi ba tare da ta yi magana ba,shi din ma dan murmushin da ita ka dai ce take samunsa a arha yayi Sannan ya karbi fuskar daga hannunta ya saka ,take ya koma gentle me gyaran takalmi,murmushin da ya sa kumatunta suka loba ta yi Sannan ta tashi tana Kama hannunsa,bai Musa mata ba,ya mike da kanta ta saka masa rigar da yake sakawa a duk lokacin da zai fara aikin gyaransa ,Sannan itama ta ɗora katon hijabi akan kayan baccinta tare da jan hannunsa suka fice daga sashen gaba daya.
Wannan bangaren da ya sa aka yi ginin laka irin dai ginin kauyen nan suka zo, sai da suka zo zasu shiga dakin Sannan ta ɗan dakata tare da tare kofar tana cewa"yaya gentle ba zaka shiga dakin nan ba fa har sai ka sayi bakin amarya ,saboda yau Ni ba Ummul din Dr Bilal ba ce ta gentle CE wannan talakan da yake fama da dinkin takalmi da kuma kodaddun kayan da a kullum suke a goge tsaf cikin kamshi da tsafta"hannunsa ya shiga lalubawa cikin aljihun rigar duka biyu, cikin sa a kuwa sai gashi ya samo wata kodaddiyar dubu daya a irin kudaden da yake ajiye wa na gyaran takalmin,mika mata yayi aiko tana kai hannu zata karba ya haɗa da ita da dubun ya rike,bai tsaya wata wata ba yayi sama da ita tare da shigewa da ita cikin dakin, akan gadon karfen da ya sha rumfar gado ya jefata a hankali Sannan ya bita ya kwanta a gefenta suna shaƙar numfashin juna, hannunsa yasa ya janye hijabin da yayi masa katanga da halalinsa tare da hayewa samanta yana kallon cikin tsakiyar idanunta da wannan kallon nasa da yake birkita duk wani lissafinta,hannuwanta tasa ta tokare kirjinsa tana sakin wani dan Marayan numfashi kafin cikin Muryar ta da ta narke ta kuma yin sanyi ta ce"yaya gentle kana da nauyi fa ba zan iya daukar ka ba"ware manyan idanunsa yayi akanta kafin cikin yanayinsa na yin komai cikin nutsuwa ya matsar da fuskarsa daf da tata har hancinsu da bakinsu yana gogar juna, Sannan a hankali ya fara magana da cewa"Ummul ke din duniyata ce,dan Allah ki kasance tare da ni muddin rai,ina sonki ina kaunar ki kaunar da babu iyakarta sai randa numfashina ya yanke ko da ya yanke kuma zan ci gaba da sonki har zuwa rayuwar cikin aljanna da na ke fatan na kasance tare da dakeee"ya karasa furucin cikin wani irin yanayin da ke bayyana gaskiyarsa, Ummul kuwa tsananin shaukin da yaya gentle din ya sanya ta bata san lokacin da hawaye suka fara bin kumatunta ba,bai yi kasa a gwiwa ba ya tarbi hawayen da harshen sa da ya sanya yana tare su suna sauka akai shi kuma yana musu mazauni a cikin cikinsa,daga nan kuma labarin ya sauya Dr gen da gimbiyarsa suka fada wata duniya ta musamman da Allah ya kebancewa ma aurata.
****
Yau sauran sati biyu bikin su zezee,yauma kamar yadda ta saba ta shirya tsaf ta fito dan fita neman abbanta,as usual Mommy da aunty raliya basu ce da ita komai ba bayan ga fatan dawowa lafiya,amsawa ta yi tare da ficewa daga falon, tana zuwa motar ta ta bude ta shiga,sai dai kuma tana kokarin tayar da ita ta hango me gadi da ya bude mata gate yana ta kokawa da wani mahaukaci wai shi a dole sai ya shigo gidan,jan motar ta yi har zuwa inda suke Sannan ta tsaya tare Da leka kanta ta window motar tana cewa da me gadin,"lawan me ye haka ne kake kokuwa da mutumin da ya girme maka ai hakan bai dace ba"sakin mutumin lawan me gadi yayi yana cewa"Hajiya zezee wannan mahaukaci ne idan na barsa ya shigo ba mu san irin bannar da zai yiwa mutane ba"duk da haka dai ka rabu dashi"zezee ta fada idanunta akan mutumin da ya tunkaro ta kai tsaye wanda da ace ba a mota take ba,to tabbas itama zata iya kwasa da gudu saboda tsoron da ya kamata, yana karasowa bangaren da take ya sa hannu yana kokarin bude motar yana cewa"yanzu kema zeezee baki gane abbanki dan gaske ba,kin san tun yaushe na ke so Allah ya bani damar biyo bayanki,ban samu ba sai jiya na samu wannan sa'ar har na samu inda kike?"ai zezee bata san lokacin da ta bude motar ta fito da gudu ba,zubewa ta yi a gaban dan gaske tare da sanya wani irin kuka me taba zuciya,shima durkusawa yayi a gabanta yana taya ta kukan wanda ya jawo hankalin su mommy suka fito a firgice,tsaye su ka yi suna kallon uba da yar bayan sun fahimci abinda yake faruwa,tabbas ba dan zuciyar Musulunci ce da mommy ba da ba zata taba barin zezee ta shigo mata da dan gaske gida ba, Sannan ya ci darajar ita kanta zezeen,amma can boys quarter ta ce ta kai shi ,zeze bata yi musu ba kuwa ta kaishi can din, lawan me gadi ta sa ya temaka masa ya gyara jikinsa,komawa ta yi ta dauko kayan da ta ke ta ajiyar su duk saboda banbanta,to babu laifi ya ɗan yi tsaf amma duk da haka bai dawo daidai ba,dan yanzu kallo daya zaka yiwa ɗan gaske kaji tsoron Allah ya shige ka,saboda ya zama irin matsiyatan nan da ba su da maraba da mahaukata.
Can dare Mommy ta ce da zezee ta kira ubanta tun kafin aje ko ina yanzu ya sauke mata nauyin da yake kanta ma ana ya furta mata saki a gabanta ko ta kara samun sanyi a cikin ranta,zezee din zata fara magiya Mommy ta dakatar da ita da cewa"karma ki fara zezee wallahi na yi rantsuwa ba zan yi kaffara ba sai na rabu da mahaifin ki ko da hakan zai iya kawo wata matsala a rayuwata"zeze na jin haka ta saddakar dan haka ta kira Abba da yake ta wani kalle kalle kamar irin tsohon dan kauyen nan da ko ruwa da wuta babu a garin su,ko da ya zo zama a kasa ya zauna sai dai ya kasa hada ido da mommy, ita din ma fuska a hade ta sanar da shi abinda take bukata,ba tare da wani jan rai ba kuwa dan gaske ya furta mata saki ɗaya,da ga haka ta umarci zezee da ta kaishi gidan da ta bashi a can nesa da su saboda bata son ko wani irin kusanci tsakaninsu.
To zeze dai haka ta dinga shige da fice da mahaifin nata da yanzu hankalinsa ya zama rabi da rabi, dan har mata ta samo masa irinsa ko ma a ce har ta fi shi hankali ta aura masa,sosai zezee ta yi kokarin yiwa mahaifinta gata, to amma dake akwai Hakki akansa sai dai kawai mu ce Allah ya bada lafiya ya kuma yafe masa kurakurensa ya sa rayuwar da zai yi a gaba ta zamar masa kaffara.
****
An yi biki lafiya an gama an kai amarya gidajensu dake Abuja wanda kamfanin dan itopia ya basu tare da motoci saboda aikin da kamfanin suka dauki angwayen,daga nan laila majnun suka dage zuwa nasu cin amarcin.
A itopia suka fara sauka inda Dr Gen ya kai Ummul cikin family dinsa masu matukar yawa, Ummul bata taɓa sanin haka Dr Gen dinta yake da dangi ba sai da ta shiga cikinsu,tabbas taga gata da kauna dan ji ta yi kamar kar su tafi, sai dai kuma satinsu daya suka wuce bayan sun ziyarci mufty da Ali a makarantar su.
Daga nan ba su tsaya a ko ina ba sai a US,satinsu biyu a nan suka wuce Dubai daga Dubai suka wuce asia daga nan kuma suka sauka Chaina,daga nan suka sauka a katar sai kuma Saudiya da ta kasance kasa ta karshe da suka ziyarta, Ummul kam ta yi kuka har ta gaji saboda tsananin fari cikin ganinta a gaban ka'aba,bata kuma yin kukan farin ciki ba sai ranar da Ummin ta da baffa suka shmmaceta dan bata san cewa Dr Gen ya biya musu zuwan ba sai kawai ganinsu ta yi,wayyo dadi kashe Ummul haka ta dinga shiga jikin Ummi kamar wata karamar yarinya.
Kwanansu goma a Saudiya Ummul ta kwanta zazzaɓi, kar ka so kaga yadda Dr Gen ya rude amma daga karshe da ya gane inda matsalar take sai ga shi yana taka rawa a gaban Ummul yana rausaya saboda tsananin murna, daga nan ya yi sujur shukur,saboda cikin da ya gano a jikin Ummul na wata biyu,Kai hatta da Ummi da baffa ba a barsu a baya ba,bare kuma Hajiya da baba ai ba a cewa komai, tun daga wannan lokaci gata ya nunku a wajen Ummul, kullum Hajiya sai ta yi mitar a dawo mata da Ummul kusa da ita,br Sara kuwa kasa jurewa su kayi sai gasu gaba daya a Saudiya dan kawai suga Ummul sarauniyar su, macen da ta kawo farin ciki cikin ahlinsu,to daga nan ne suka runtsuma gaba daya suka dawo gida nageriya, a Abuja suka sauka, amma saboda kar Ummul tasha wahala sai kawai Alhaji Ahmed shima ya tattaro suka dawo gida abuja dama nan ne wajen zamansu Kano sun je ta ne sanadin Dr Gen da kuma rabon Ummul.
Amma Ummi da baffa suna Kano, sai dai suma kwana kadan Alhaji Ahmed ya basu wani gidan a nan ya ce su dawo saboda baffa zai fara aiki a kamfaninsu na shinkafa dake nan Abujan,matsayi babba aka bawa baffa dan ma bai yi wani karatu me zurfi ba, to amma duk da haka baba ya bashi damar yin karatu na musamman saboda ya mori ƙwaƙwalwar da Allah yayi masa, wannan ci gaba da baffa ya samu ba karamin farin ciki ya sa shi ba, wannan shi ake kira na gaba ya koma baya na baya ya koma gaba, dama haka Allah yake ikonsa, shi yasa ba a son ka wulakanta dan Adam dan babu wanda yasan me Allan zai yi a gaba,to dai gashi baffa ya koma sanya manyan riguna da shiga babban office a maimakon zaman gadi,shi yasa ake so a ko wane rintsi na rayuwa ka rike Allah da kuma gaskiya da amana to tabbas zaka ga ci gaba a cikin rayuwarka, Allah ya bamu ikon biyayya ga Ubangiji da ko yi da ma aiki Sallallahu alaihi Wasallama.
Rayuwar Ummul da Dr gen abar koyi ce, dan rayuwa ce da take cike da soyayya musamman da yakasance dr gen Yana kokarin yin koyi da rayuwar gidan ma'aikin Allah Sallallahu alaihi Wasallama sai zaman nasu ya zama wani na musamman me cike da tsafta.
A bangaren zezee da angonta ma rayuwa ta mika, haka A'isha da nata angon, gaba daya sun hade kansu duk da cewa zezee ta girme musu amma haka suke rayuwa kamar wasu aminai,zezee
💕GIDAN ƳAN ƘARYA💕
By
FATIMA Y ADAM......
Littattafan marubuciyar.
KUDIRAR ALLAH
KADDARATA SANADIN HASKE
ƁOYAYYIYAR RAIHAN
ƳAR GIDAN YARBAWA
MATAR ƊAN BIRNI
And
GIDAN ƳAN ƘARYA....