CHAPTER 2
---
🧚THE ENCHANTED KINGDOM🧚
Story and writing by Queen Mahirah
Marubuciyar...
THE TWO LIGHTS (RIKICIN GIDAN SARAUTA)
KITABUL HUB
LABARIN DR NEELAH
LABARIN BINT ABDULAZIZ
PAID BOOK
FREE CHAPTER
Karku manta wannan littafi na kuɗi ne...
Sai de akwai bononza ga wanda yayi FOLLOWING CHANNEL DINA da GROUP...
Kana da damar samun complete kafin watan June ya kare...
Amma in baka shiga ba har ya kare to be honest asusun ka zai yi kara..ƙiriiiin!!😁
Cos zaka biya 500 Naira kafin ka mallaki complete inshallah 🥰
CHAPTER 2
6:8pm
Duk da cewa zuciyarta tana bugawa da tsoro, Maryam ta ɗauki ƙaramin kwando ta nufi daji.
Hasken rana ya fara ɓacewa yayin da ta isa bakin dajin.
Bishiyoyin sun yi tsayi fiye da yadda ta taɓa gani. Iska tana busawa kamar tana faɗin wani abu da ba a fahimta.
Maryam ta tsaya.
Ta kalli hanyar da ta shiga.
"Ya Allah... ka kiyaye ni."
Ta ɗaura hijabinta sosai ta shiga.
---
A cikin dajin, komai ya yi shiru.
Ba a jin kukan tsuntsaye.
Ba a jin motsin dabbobi.
Sai ƙarar takunta kawai.
Maryam tana neman ganyen kainuwa tana ɗuba rassan bishiyoyi.
Sai ta ji wani sauti.
Krak...
Ta tsaya.
"Wa yake nan?"
Babu amsa.
Ta ci gaba da tafiya a hankali.
Bayan wani ɗan lokaci, ta ga wani ganye mai haske wanda bai yi kama da sauran ba.
"Kainuwa..."
Ta durƙusa tana son ɗauka.
Amma kafin hannunta ya taɓa ganyen...
Wani iska mai ƙarfi ya busa.
Fitilar da take ɗauke da ita ta mutu.
Maryam ta ja baya.
"Me ke faruwa?"
Sai wata murya mai zurfi ta fito daga cikin duhun.
"Ba kowa ne yake da damar taɓa wannan ganyen ba."
Jikinta ya yi sanyi.
Ta juya a hankali.
Amma babu kowa.
"Waye kai?"
Muryar ta sake cewa:
"Wataƙila tambayar da ta fi dacewa ita ce..."
"Ke wacece?"
Maryam ta tsaya cak cikin wani yanayin da ta gaza fahimtar mai ne -ne shi guda ɗaya...
Saboda ba ta san dalilin da yasa baƙon murya a cikin daji take tambayar sunanta ba kamar yadda tayi mamakin irin ƙarfin halin ta a yau duba da irin hatsarin da dake cikin dajin, duk da cewa bata taɓa zuwa ba sai yau duk abinda take ji labari ne...
Ajiyar zuciya ta sauke ta furta ''Ya Allah...sa-idnee ...da kai kaɗai na dogara, bani da bangon dogaro daya wuce ka...
Ka taimaki baiwar ka dake cike da sirri da take fatan samun amsar sa...
Ubangiji...
Hummmm''
A hankali ta furta:
"Ni ce Maryam..."
Cikin wani yanayi mai cike da rauni da rashin yadda da kai da kuma sanin asali...
Shiru.
Sai muryar ta ce:
"A'a..."
"Ba ke ce Maryam kawai ba...."
---
A wani ɓangare na dajin, wani saurayi yana tsaye yana kallon komai.
Sanye yake da kaya baƙi, yana riƙe da takobi.
Shi ne Rayyan Al-Hakim.
An aiko shi ne domin binciken abin da ke faruwa a Dajin Kainuwa.
Amma abin da ya gani ya ba shi mamaki.
Yarinya ce kawai.
Ba da makami ba.
Ba da tsoro a fuskarta ba.
Sai dai ƙarfin hali, da wani ɓoyayyen sirri
Rayyan ya yi raɗa:
"Wace irin yarinya ce za ta shiga wannan dajin ita kaɗai?"
---
Maryam ta sake kallon ganyen.
Sai muryar da ba ta gani ba ta ce:
"Idan kika ɗauki wannan ganyen, ki sani rayuwar ki zata canja, zaki samu sauyi na mafarki, buri da canjin rayuwa."
Maryam ta yi shiru.
Ta tuna da wahalar da take sha.
Ta tuna da yadda take son wata rana ta samu rayuwa mai kyau....wani baƙon al'amari ya bakun ce ta...
A yau a karan farko taji tana buƙatar sauyin rayuwa...amma bata son sauyin mafarki, da burin ta...
''hmmm...
ya Allah da kai na dogara....tabbas na kasance kamar kowa ban cika goma ba...amma ban kasance mai son kai na ba...
Humm Ummi ta rene Ni ma tsawon shekaru ta ci dani...bazan so na barta ba...,
Inason cikar burina, mahaifina na sanshi Ummu na -na ganta ko naji labarin inda take, ta mutu ko tana raye..
Ajiyar zuciya ta sauke tace :
''zan dauki wannan GANYEN badan rayuwa ta ya sauya ba,'''
Wani cute smile ta sake ta ce:'' dan burin Ummi na ya cika, ta samu sauyin rayuwa... Ta samu lafiya...''
Sai ta miƙa hannu da niyan daukar ganyen sai wannan murya yace:
''tabbas kin yi kuskure, burin ta nada zafi ba yadda kike tuanani bane''
Ahankali ta furta: '' koda burin ta na ƙare rayuwa ta cikin azaba da bauta ne, Ni Maryam Zahrah na aminta na kuma yadda, na kare matsayin mai bauta in de har zan saka mata da alƙhairin data mun a rayuwa ...''
Wannan murya ya kuma cewa ''tabbas sauran bayi tara suke basu cika goma ba, amma ke...akwai wani ɓoyayyen sirri tattare dake da ba kowani bawa ke da shi ba...''
Mursmushi tayi ta sanya hanunta don daukar ganyen...
Nan take...
Wani haske ya bayyana a cikin dajin.
Maryam ta firgita.
Amma kafin ta sami damar yin komai...
Wata murya daga bayanta ta ce:
"Kin yi kuskure mai girma."
Ta juya.
A karon farko...
Idanunta suka haɗu da na Rayyan Al-Hakim.
Mutumin da zai zama farkon wanda zai ga abin da babu wanda ya taɓa gani a jikinta.
Ba yar talakawa ba....
Rayyan Al-Hakim yaga wani ɓoyayyen sirri da zai iya canja rayuwar Daular da aka manta dashi tattare da wannan yarinya...
Cike da tashin hankali Maryam ta soma neman hanyar ceton ranta kasancewar Rayyan Alhakim ba gama Garin bawa bane...
Ya kasance bawa mai cike da kwarjini kyan haiba da kamala...
Kallo ɗaya zaka mishi ka shiga rudu koda ko kana da gaskiya...
Maryam Zahrah duk da tayi jarumtar sauraron Muryar dake fitowa daga duhu sai de ta gaza jurar yin ido biyu da Rayyan Alhakim...
Gudu take tamkar zata bar duniya ita kanta bata san ina take takawa ba, cikin ikon Allah ta bar dajin kainuwa ta iso yar karamar kauyen su dake ƙarƙashin MADINATUL ALAM...
Kai tsaye gida ta wuce inda ta samu Sayyidah Rukayya wanda ko kadan bata damu da yanayin da taga Maryam Zahrah ciki ba ita damuwar ta GANYEN KAINUWAR ta...
Sosai Maryam Zahrah ta shiga firkice haka ta ringa aiki cikin razana, lokaci zuwa lokaci takan ji murya sa a kunnenta...
Haka dare yayi duk da irin addu'ar data yi bai hana ta jin muryarsa ba, farin fuskarsa da kuma siren eyes nashi mai ɗauke da sirri...
Ji take tamkar wani abin na fusgarta, Muryar ɗaya fito daga duhu na ƙara mata yawo cikin kwakwalwa...
Ta gaza gane kuskuren da tayi...
Ciran GANYEN, Burin Ummi data sa a gaba ko GUDUWA...?
SAYYADAH RUQAYYA'S POV...
Cikin zallan farin ciki take taku na ƙasaita yayin ta dauki wani madubi dake cikin wani akwatin karfe mai kyan gaske...
Zama tayi bisa royal bed dinta mai shegen kyau da ɗaukar hankali cikin wani yanayi irin na cikakkiyar yar barikin Balarabiya take wani lumshe idonta...
Gashin kanta ya zubo har zuwa bayan ta yayin da kanta ke lailaye da wani head jewelry mai masifar kyau da ɗaukar hanakli...
Wuyanta saƙale da Qidālah (sarkar wuya)...Khawatim (zobba) ne sanye a yatsun ta...
Idonta yasha adon ido irin na Larabawa wato Kuhl...
Hanunta lailaye da Hinna daya matuƙar kara mata kyau matuƙa...
Kallo ɗaya zaka mata ka gano sirri mai tarin yawa tattare da ita...
Yanayin dressing nata da kuma dabi'arta yafi kama da Kawaliyah ko karuwa...
Kamar yadda mursmushin ta ke nuni da wani sirri mai matukar rikitar da brain....
Da narkakkun idonta take kallon wannan madubin yayin da wani haske ya bayyana...
wannan lokacin, muryar Sahir ta fito daga bayan ta:
Sahir:
"Kina neman gaskiya ne, Sahiratul Qulub.... ko kina neman fansa?"
Rukayya ta juya masa baya, idonta ya yi tsauri.
Sahiratul Qulub:
"Duk wanda ya taba min komai ya kamata ya fuskanci sakamakonsa. Amma kafin hakan... zan gano gaskiyar Maryam Zahrah. Domin watakila ita ce mabudin abin da aka boye shekaru da dama."
Sahir ya kalli fuskarta.
Sahir:
"To ki shirya... domin hanyar zuwa gaskiyar ba ta wuce sai an shiga Dajin Kainuwa."
Sahiratul Qulub ta kalli duhun dajin.
Sahiratul Qulub:
"Idan dajin yana gwada zuciyar mutum... to bari ya gwada nata muga ko itace makullin da zai bude Tsohuwar DAUAR NURAYN..."
Ajiyar zuciya Sayyadah Ruqayya ta yi data tuna last convention nasu da Sahir wanda gashi har Maryam Zahrah ta dawo daga Ɗajin Kainuwa ba tare da wani rauni ba, kuma ta dawo da ganyen kainuwa...
Ajiyar zuciya ta sauke a sarari tace :
''lokaci yayi, lokacin da zan dauki fansa...
Tabbas labarin yanzu zai soma...''
Wani weird smile ta sake tana mai lunshe idonta dalla-dalla take ganin abinda ya faru a ranar da aka mata iyaka da Ɗaular Madinatul alam...
FLASH BACK...
Shekaru 20 da suka wuce…
A cikin manyan katangar masarautar Madinatul Alam, an yi wani taro mai cike da tashin hankali. Karar kararrawar fada ta ratsa gari sau uku — alamar cewa an gano wani babban laifi.
A tsakiyar babban zauren sarauta, mutane suka taru. A gefen karagar mulki, Sultan yana zaune cikin fushi, yayin da masu gadi suka kawo wani akwati mai hatimin masarauta.
Sai aka shigo da Sahiratul Qulub (Sayyadah Ruqayya)
Ta shigo cikin nutsuwa, sanye da doguwar kaftan mai launin duhu da zaren zinariya, fuskarta babu tsoro kamar wadda ta san komai zai faru.
Sahiratul Qulub (Sayyadah Ruqayya)
Sultan:
"Rukayya... shekaru da dama muna ganin ki a matsayin mace mai aminci ga wannan masarauta. Amma yau an kawo mana hujjojin da suka sa muka tambayi komai game da ke."
Sahiratul Qulub ta daga kai wani ras taji a zuciyar ta jin yadda Sultan ya ambaci sunan ta ayau kai tsaye, babu salo na kauna, muradi da tsantsan sha'awa kamar yadda ya saba....
Ta kasance MAHAZIYA ( Kwarkwara) data fi kowa matsayi da samun guri...
Ko matan sarki baza su nuna mata iko a wannan masarautar ba...
Amma a yau taga akasin haka...
Mai ba sarki shawara ya bude akwatin.
A ciki akwai:
wata tsohuwar takarda mai dauke da tambarin masarauta,
wani sirrin da bai kamata ya fita daga fadar ba,
da kuma wani rubutu da ke nuna cewa Rukayya ta yi kokarin gano wani boyayyen asali da aka hana kowa tabawa.
Mai ba da shawara:
"An same wannan a dakinki. Kin yi amfani da haramtacciyar hanya wajen neman sirrin da aka rufe shekaru da dama. Kin karya dokar fada."
Mutane suka fara raɗa-raɗi.
Amma Rukayya ta yi murmushi kadan.
Rukayya:
"Dokar? Ku kira shi doka saboda kuna tsoron abin da zan gano. Amma ku sani... akwai gaskiyar da ba za a iya binne ta har abada ba."
Sultan ya mike tsaye.
Sultan:
"Ba wai neman gaskiya ne ya sa muka hukunta ki ba, Rukayya. Abin da ya sa shi ne yadda kika yi amfani da mutane marasa laifi wajen cimma burinki."
A wannan lokacin aka kawo wata yarinya mai hidima wadda ta durƙusa tana kuka.
Yarinya:
"Ta yi min alkawarin zata kare ni... amma ta yi amfani da ni wajen shiga dakin sirrin fada."
Zauren ya yi shiru.
A karon farko, fuskar Rukayya ta nuna wani abu — ba nadama ba, sai dai fushi saboda an gano ta.
Sultan:
"Daga wannan rana, ba za ki sake zama cikin bangon Madinatul Alam ba. An kwace matsayinki, an cire sunanki daga cikin masu daraja na fada."
Ya juya wa masu gadi.
"Ku kai ta har iyakar masarauta."
Rukayya ta kalli kowa a zauren.
Rukayya:
"Kun kore ni a yau... amma wata rana za ku fahimci cewa abin da kuke kira laifi shi ne hanyar da zan bi wajen gano abin da kuka boye."
Ta cire zoben masarauta daga hannunta ta ajiye shi a kasa.
Sai ta fita daga Madinatul Alam ba tare da ta kalli baya ba.
Amma kafin ta bar kofar masarauta, ta yi alkawari a zuciyarta:
"Zan dawo... ba a matsayin wadda kuka kora ba. Zan dawo a matsayin wadda za ta fallasa dukkan sirrinku."
A hanyar ta na tafiya ne cikin bacin rai ta gamu da wata mata dake cikin wani yanayi na tashi hankali, cike da son ceton gudan jininta ta durƙusa gaban Sayyadah Ruqayya ta haɗa hanunta tana rokon ta data ceci rayuwar yarta, ta nesan ta ta daga Daular Madinatul alam...
Cikin takaici Sayyadah Ruqayya tayi tsawa a matar tana nuna mata irin bacin ran data ke ciki
Sayyadah Ruqayya:
''in ji da kaina ko naji da gunkin diyar ki da baza ta ƙare Ni da komai ba!''
Cikin magiya tace da ita: '' na Miki alkawarin in kika rike yar nan, keda wulakanta har abada...
Keda talauci kun raba hanya...
Nasara zata zama ruwan sha gareki...
Zaki samu daukaka a lokacin da baki zata ba ...
Amma akwai sharadi; zaki kula da ita, ki mata tarbiyya babu ha'incin...
Ki nuna ki koya mata tsarkin zuciya, yadda zuciyar ta zai kasance ba son kai, ta kasance mai sowa dan uwan ta abinda soma kanta...
Ta haka ne zata bude miki kofar sirrin da aka dade da mantawa dashi...
In kika yi haka watarana wannan ƴa zata sa ki zama Malika ba Sultana ba...
----
BACK TO NORMAL LABARI
Ta gaza samun nustuwa kamar yadda bacci ya gaza daukar ta...
Lissafin ta ya zata samu damar gano wannan sirrin, ta gaji da jiran lokaci tana son yin aikin ta da kanta...
Tana son yan ke hukuncin ta da kanta...
END OF CHAPTER 2