THE ENCHANTED KINGDOM

THE UNVEILING HISTORY

by @queenmahirah14

THE ENCHANTED KINGDOM🧚
Story and writing by Queen Mahirah
Marubuciyar...
THE TWO LIGHTS (RIKICIN GIDAN SARAUTA)
KITABUL HUB
LABARIN DR NEELAH
LABARIN BINT ABDULAZIZ


PAID BOOK
FREE CHAPTER
Karku manta wannan littafi na kuɗi ne...
Sai de akwai bononza ga wanda yayi FOLLOWING CHANNEL DINA da GROUP...
Kana da damar samun complete kafin watan June ya kare...
Amma in baka shiga ba har ya kare to be honest asusun ka zai yi kara..ƙiriiiin!!😁
Cos zaka biya 500₦ kafin ka mallaki complete inshallah 🥰
CHAPTER 3
----
Washegari da safe, Maryam ta tashi da wani sabon yanayi a zuciyarta. Ta kasa daina tunanin abin da ya faru da dare. Bayan ta gama ayyukanta, sai ta yanke shawarar fita zuwa gefen dajin domin neman amsar tambayoyin ta.
Maryan Zahrah ta dauki wannan tafiya matsayin karamin abu, hakan yasa ko sanar da Sayyadah Ruqayya bata yi ba ta saci jiki ta fice badan komai ba sai dan yakini da take dashi na cewar ko awa ɗaya baza tayi ba zata dawo...

Ba tare da sanin cewa kana naka Allah na nashi ba...

Dayawan lokaci a rayuwa bawa na nashi lissafin yayin da Ubangijii ya ƙaddara maka wani lamarin da kake tunanin lissafin ka ne ya haifar maka da hakan...

Ba ta san cewa wannan tafiya za ta canza rayuwarta gaba ɗaya ba.

----
Yayin da take shiga cikin dajin, tsuntsaye suka yi shiru, iska ta tsaya, kamar dukkan halittu suna jiran wani abu. Maryam ta ci gaba da tafiya har sai da ta isa wani wuri da ba ta taɓa gani ba.
Hasalima a yau dajin ya sauya ba kamar yadda ta barshi ba jiya...

Sosai abun ke bata mamaki yau dajin bai yi kama da abun tsoro ba kamar yadda yake a jiya hasalima yau cike yake da haske da annuri na ban mamaki...

Ga wassu bishiyoyi masu matukar kyau ga kuma tsuntsaye masu kyau...

Kuka tsuntsayen sukeyi cikin wani salo na burgewa suna shawagi a dajin cikin yanayi na burgewa...

 Wani ɗan karamin Zomo ne mai kyan gaske ya bayyana a gaban ta fari tas mai ɗaukar ido. Cikin wani yanayi na ban al'ajabi zomon ke kallon ta da narkakkun eyes👀dinsa masu matuƙar haske da ɗaukar hankali...

Maryan Zahrah ta gaza jure kallon nasa hakan yasa cikin siririyar Muryarta tace dashi:
''who Are You?
Man - anta?
Waye kai?''

Ta jero masa tambaya daya cikin yare uku data tashi cikin su ko nace ta budi baki dasu...
Kasancewar kauyen da Maryam Zahrah take ya zama tamkar bakin kofa ne hakan yasa kabilu da dama dake zaune a gurin suna jiran ikon Ubangiji.Ma'ana suna zaman jiran wani dama da zasu samu don shiga Ƙasar MADINATUL ALAM... 
Ko motsawa wannan zomon beyi ba sai ma sosa kunnensa da yake yi cikin wani salon burgewa...
Hakan ya kara narkar da zuciyar Maryam Zahrah zuwa ga Zomon...
Hanu ta kai da niyan taba lallausan gashin zomon amma sai ya ji baya yana kifta ido cikin yanayi na burgewa...
Hanu ta kara mikawa amma sai ya fara gudu, wani murmushin burgewa tayi rabi bayan sa shiko sai zunƙulawa yake da ita cikin dajin ita kuma yana binsa a baya...
Baya zata ba bata stamman ya ba taganta a wani tsohon Mashigar wani Daula dake cike da wani tarihi mai zurfi da nauyi..
Wani babban kofa da aka samar dashi da ɗanyen azurfa da lu'ulu'u da murjani...
Cike yake da wasu zane zane-zane masu ma'ana dake nuni da wani tsohon Daula da ƙarni da ya shuɗe...
Zuciyarta ta fara bugawa da sauri.
Ta matso kusa da ƙofar, sai abin wuyanta ya fara haskawa.
Da zarar ta taɓa ƙofar...
Sai wani iska mai karfi ya kaɗa.
Wani haske mai ƙarfi ya rufe idanunta, sannan ta ji kamar an ɗauke ta daga inda take. Lokacin da ta sake buɗe idanunta, ba ta cikin dajin KAINUWA.....

SAYYADAH RUQAYYA'S POV
Cike da jin dadin tattaunawar su a yau da suka yi da Sahir daya bata yakinin cewa burin su ya cika muddin ta samo sarkar dake wuyan Maryam Zahrah ya bincika ya kuma tabbatar da abinda yake hasashe haka ne, to ba makawa burin su ya cika — yana da yaƙinin cewa cikin daƙiƙa zuwa Sa'a 21 Rayuwar su zata sauya gana ɗaya...

 Cikin takun ta na jan hankali da karairaya ɗaya zama halittan ta take nufar ƙangon ɗakin Maryam Zahrah da bashi da maraba da ɗakin mabaraciya...

Sosai take jinta a ☁️ cloud 9...
She so happy burinta zai cika ba tare da sanin cewa Ubangiji ya tsara komai yadda yaso ba kamar yadda lokaci ALKALIN kansa ne...

Ciki rausaya ta buɗe ƙofar data ke tsammanin zata hango Maryam Zahrah bisa maceceiyar sallayar ta tana sallah ko karatun Qur'anin daya tsufa matuƙa, sai de Ayar Allah dake rubuce a ciki sam bai canja launi ko ma'ana ba, kamar yadda mu'ujiza na Ubangiji ke wanzuwa a wannan ɗakin...

Tamkar ɗakin zai rushe ranar yadda ginin yaji jiki sai de bisa wani iko na Ubangiji babu abinda ke samun sa duk da irin ruwa da iska mai karfi da suke samu a wannan ƙauye na Zan –zabir...
Wulass..!!!
Shine abinda Sayyadah Ruqayya ta gani wato babu Maryam Zahrah cikin dan firkici ta dana zare idonta masu cike da kaifi, ta haɗe girarta...

Soma kiranta tayi cikin ɗaga murya amma shiru...
Tun tana yin hakan cikin izza har ta koma yi afujajan...
Tamakar kanta zai yanke haka take zaga wannan ƙaramin ƙauyen tana neman Maryam Zahrah amma babu labarin ta, kowa yana cewa:
''sam ban ganta ba, ko a bakin rijiyar Ruma''
Inda ta saba zuwa kenan a rana takan zuwa rijiyar Ruma sama da sau 10 don dibam ruwa...
Sayyadah Ruqayya a yau taga ci gaba rashi ta rasa wani alkiblar da zuciyar ta ta dauƙa a yau...
Wani yanayi na tsinci kanta mara misaltuwa abubuwa da dama na dawo mata a brain...
Tana cikin wanan yanayin ne wani haske ya bayyana Sahir dake sanye cikin bakin kaya kamar kullum...
Yau fuskar sa rashin annurin ta yayi muni kamar yadda idonsa yayi matuƙar ja...
Cikin wani murya mai ban tsoro yace: 
''yah Sahiratul Qulub kai con ki...!!''
''a yau kin mana babban asara, sakacin ki ya jawo mun rasa cikan burin mu na tsawon shekaru 20...''
Da wani irin kuka Sayyadah Ruqayya ta fashe ta zuba guiwan ta gaban Sahir, ta gaza gane mai ne–ne abinda zuciyarta ke bege a yau...
Shin tana kuka ne saboda ta rasa cikan burin ta na tsawon shekaru...
Ko tana kuka ne ɗan a yau tayi watsi da alƙawarin data dauka na tsawon shekaru ɗan ta cimma burin ta...
Tabbas yau bata da abin fadi musamman data ji Sahir yayi wannan magana tasan har abada ta rasa Maryam Zahrah ba burin ta kadai ba...
Kansancewar ya sanar da ita cewa kuskure kadan zata yi ta rasa Maryam Zahrah saboda basu kadai ke neman ta ba...
Kamar yadda ta bayyana wani tsohon sirrin dake cikin Dajin kainuwa a jiya...
Hakan yasa har Sarkin yaki Rayyan Al-Hakim ya bayyana don ganin wani mahaluki ne ya karya wannan shingen da akayi tsawon shekaru 20 don lullube tsohuwar Daular da aka ɓoye na tsawon shekaru ɗan wani sirri mai ƙarfi...

----

Tana tsaye ne a gaban wani babban gari mai ban mamaki.
Gidaje ne masu haske, manyan fadoji ne suka bayyana a gabanta, koguna suna gudana kamar azurfa, mutane suna tafiya cikin tufafi masu kyau kamar na zamanin sarakuna.
Maryam ta kasa magana.
"Ina nake?"
Sai wata murya daga bayanta ta ce:
"Kin iso gida, Sultana Maryam Zahra."
A hankali ta juya.
A gabanta akwai wani saurayi mai tsananin kamala, sanye da kayan sarauta masu kyau. Fuskarsa tana ɗauke da nutsuwa da ƙarfin hali. A bayansa akwai masu gadi.
Cike da karfin hali Maryam Zahrah tace :
"Ni ba Sultana ba ce,"
 Maryam ta ce cikin mamaki, bugu da ƙari cikin kaɗuwa ba shakka tana jin tamkar tasan wannan Bawan....
Saurayin ya kalle ta sannan ya ce:
"Sunana Rayyan Al-Hakim, mai gadin Masarautar Nurayn. Mai ɗauke da wani sirri da aka ɓoye shekaru masu yawa... .wanda hallaran da kika yi ya jawo lalacewar shingen da akayi na tsawon shekaru 20"
Maryam ta ja baya cikin rudu ta nuna kanta da yatsa tace ''ni''
"Me yasa kace Ni ce na lalata shingen ?"
Rayyan ya kalli sarƙar dake wuyan ta kafin yace:
"Saboda wannan abin ba kowa ne yake iya ɗaukarsa ba. Kuma dawowarki na nufin cewa lokacin da ake jira ya zo."
Maryam ta ji tsoro da mamaki a lokaci guda....
Ta rasa abin fadi, ta zama tamkar gunki, ƙwaƙwalwar ta ya gaza sarrafa abinda saurayin ke fadi da kuma abinda idonta ke gani..
Wassu kyawawan yan mata ne suka hallara da aƙalla sun kai 7 suna sanye cikin wani kaya mai kyau, wando mai fadi amma ya tsuke daga kasa, sai riga Dan Karami daya bayyana hanunsu da kyakkyawar surar su, wato lafeffen cikin su da kuma madai -dai cin ƙirjin su...
Yayin da fuskarsu sanye da face veil da kuma fore head jewelry...
Sosai sukayi kyau matuƙa cikin fararen kayan nasu kun-kumin su sanye da wani belt mai sheƙi da daukar hankali...
Idon su yasha adon su da suke kirar sa Kuhl, hanunsu ko yasha Hinnā mai matuƙar ɗaukan hankali...
Cike da giramamawa suka sadda kansu gareta cikin wani salo na burgewa suna ce da ita:
''Ahlan wa sahlan ya Sahibatul Sumuw–malaki"
Wani abu Maryam Zahrah ta hadiya tana mai gaza fahimtar yanayin da take ciki a yau..
Kamar a mafarki take ganin komai sai zare ido take ita kadai tamkar mai shirin shigewa cikin ƙasa..
Cike da giramamawa saurayin da ya ƙira sunansa da
 Rayyan Al-Hakim yace:
''Umarni naƙi cikawa namu Sultanah...
Fadi duk abinda kike so, mu kuma a shirye muke da aikatawa koda hakan na nufin karshen numfashin mu ne a doron ƙasa ya SAHIBATUL JALALA...
Yayi maganar ne cikin yanayi na tsantsan giramamawa yayin da ya sadda kansa kasa hanunsa na dama kuwa yana ƙirjinsa...
A lokacin da ya fadi kalmar sa na ƙarshe ne yasa dukkanin halitta da motsin ran dake cikin wannan Daular ya sadda kai cikin salo na giramamawa...
Dukkanin bayi da kuma masu matsayi daga yaro, tsoho matashi, dabbobi da kuma bishiyoyi da koguna sun bata girma matsayin ta na SAHIBATUL JALALA...

----
Cikin duhun wani fada mai nisa, wani mutum yana kallon zuwanta da dukkanin abinda zai iya faruwa nan gaba a madubin tsafin sa.
Mutumin ya yi murmushi mai sanyi.
Ya furta:
"Lokaci yayi... Sultana ta dawo...

— ƘARSHEN CHAPTER 3—