Waheedah

Chapter 10

by @deejarthabdoul12

Kaman yadda suka shirya da asuban fari Dada da jiya bata dawo gidan ba sai karfe Sha daya na dare ta shiga dakin Waheedah a zaune ta same ta hade kanta da kafafuwanta dan ko kadan bata iya runtsawa ba saboda damuwa da kuma tunanin inda Dada zata turata.

Kafa Dada tasa ta bangaje ta tana fadin 
 maza ki tashi ki shirya Karime na nan zuwa tace tafiyan safe zakuyi dan haka kada ki bata mata lokaci Habuja banan kusa bane kafin ku fita daga kauyen nan ma kadai aikine.

A firgice Waheedah ta dago kanta tana kallon Dada Habuja fa taji Dada tace innalillahi shikenan ita kam watakila karshen rayuwan tane yazo baza ta manta ba ta taba jin wasu suna hiran garin a gurin deban ruwa kuma ji tayi suna cewa yan kan kai ake yi a garin da wuya mutum yaje garin ya dawo da ransa kuma shine ita Dada zata turata?
 maganan Dada ne ya dawo da ita cikin hayyacin ta.

Baza ki tashi ba ina miki magana kin wani kuramin ido kaman wata mayyah to ko mayyahn nema kuruwata tafi karfin ki wllh Dada ta fada tana juyawa ta fita daga dakin.

Tashi Waheedah tayi cikin sanyin jiki ta fita a dakin taje ta dauro alwala kafin ta dawo ta tada Sallah.

Dada sai da taji fitan Baba zuwa masallaci kafin ta fito daga dakin tane rike da mayafinta da sauri ta shiga dakin Waheedah a zaune ta same ta cikin sauri tace maza tashi ki dauki buhun ki mu fita daga gidan nan bazan iya jiran harsai Karime tazo ba.

Tashi tayi kaman yadda Dada tace ta dauki buhun kayan nata tana jin yadda zuciyanta yake mugun bugu kaman zai fito daga kirjinta a hankali take takawa tabi bayan Dada data fice daga dakin a tsakar gidan ta samu Dada juyawa tayi tana kallon kofan dakin Baba a ranta kuwa addu'a take Allah yasa Baba ya fito ya hana tafiyan nan.

Wai baza kizo ki wuce ba dan ubanki.

Kallon Dada dake magana tayi cikin sanyin murya tace Dada dan Allah ina so nayiwa Baba sallama ne.

Tsaki Dada tayi tace sallaman uwar me zaki masa zaki wuce ne ko sai nayi kwallo dake.

Sallama akayi tare da shigowa cikin gidan da sauri Dada ta juya jin muryan Karime yauwa Alhamdulillah kinga yanzu nake cewa bari mu tafi can gidan naki kawai saboda naga lokaci ya fara tafiya kar gari yayi haske ku rasa mota.

Murmushi Karime tayi tace kai yaaya mairo karfe biyar da rabi nefa yanzu ta fada tana duba agogon wayan ta.

To naji yanzu dai gata ku tafi Karime ni bana son bata lokacine wllh sanna kuma kudin aikin nata idan an fara biyan nata sai kimin magana naje na karbi lamban bankin Sale me shago na tura miki asa kudin a ciki.

Da to Karime ta amsa tana kamo hannun Waheedah dake tsaye amma ga ba daya tunanin ta baya wajen yanzu shikenan haka zata tafi batayi sallama da Baba yanzu idan ta tafi bata dawo ba fa wannan tunanin ne yasa taji hawaye masu zafi sun cika idanuwan ta juyawa tayi tana kallon Dada so take ta tausaya mata amma ko kadan bata ga alaman hakan a gun Dada ba sai ma wani farin ciki da taga ya baiyana akan fuskan ta.

A hankali Karime take jan hannun ta har suka fita daga gidan hanyan inda ake samun motan fita daga kauyen nasu suka nufa ko kadan Waheedah bata jin karfi a jikinta bayan damuwa harda yunwan data kwana dashi dan gurasan da Baba ya kawo mata ba mai yawa bane kuma bata iya ci sosai ba saboda damuwa lura da hakan da Karime tayi ne yasa ta rike hannun ta da kyau tana cigaba da janta har suka isa gurin hawa motan da baida nisa sosai da gidan.

Suna isa kuwa basu jima ba motan zuwa tashan Bauchi ta cika Waheedah tun da take a rayuwanta wannan shine karo na biyu da ta taba shiga mota dan haka gaba daya a tsorace take.

Around 7:30am suka isa tashan zuwa lokacin Waheedah ji take kaman cikin ta zai hade da bayan ta.

Kallon ta Karime tayi bayan sun sauka a tashan tace kina jin yunwa ne Waheedah?

Gyada mata kai Waheedah tayi tana neman guri a inda suka tsaya ta zauna saboda jirin da yake deban ta.

Juyawa Karime tayi ta nufi gurin da taga wata mata na tuyan kosai ta siya mata na dari biyar da kunun dari biyu a gora kafin ta koma inda take zaune ta mika mata.

Karba Waheedah tayi tare da mata godiya ta fara ci a hankali tana tunanin Baba.

Sai kusan karfe tara motan zuwa Abuja ya tashi a lokacin da motan ya fara tafiya Waheedah ji tayi zuciyan ta na mata wani irin zafi wani alwashi na dar suwa a ranta Insha Allah zata dawo ko dan saboda Baba komin daren dadewa, zata je birni bawai dan cikan burin Dada ba sai dan cikan nata burin da Dada ta hana ta cikawa share hawayen da ya zubo mata tayi tana maida hankalin ta kan hanya.

A can gida kuma sai da gari yayi haske sosai Baba ya shigo gidan yayi mamaki sosai da baiga Waheedah a tsakiyar gida tana aiki ba saboda ya saba a kullum idan ya dawo daga sallahn asuba a tsakar gidan yake samun ta tana aiki tana ganin sa kuma zata tsunguna ta gaishe shi sannan ta cigaba da aikinta.

Tunawa da yayi jiya tace masa kanta na ciwo sai yayi tunanin ko hakan ne ya hanafa fitowa to amma kuma yasan Dada baza ta barta ba ai hanyan dakin nata ya nufa domin dubata harya saka kafan sa daya cikin dakin sai kuma ya janye da sauri yana ja da baya tare da dafe kansa, juyawa yayi ya wuce dakin sa ba tare da ya shiga dakin Waheedahn ba.

Dada dake kallonsa tun shigowan sa gidan ta jikin windon dakinta ta saki wani murmushi a fili kuma ta furta lallai Malam na kan dutse aikin ka na kyau.

#Waheedah
#***