Chapter 11
Waheedah tun tana jin dadin tafiyan har ta fara gajiya da zaman motan sai bacci ya dauke ta tana tunanin idan ta farka zata ga sun isa amma ina tana farkawa sai ta sake ganin tafiya kawai suke kasa hakuri tayi ta juya tana kallon Karime dake gefen ta wanda tun shigan su motan wani magana bai hada su ba cikin sanyin murya tace Anty Karime har yanzu bamu isa Habujan ba.
Kallon ta Karime tayi dama tun dazu take mamakin shirun yarinyar murmushi ta mata tace bamu isa ba Waheedah amma mun kusa kin gaji ko?
Gyada mata kai tayi tana sunkuyar da kanta dan ita kam ji take kaman bayan ta zai balle saboda zama gashi tunda suka fara tafiyan sai daya drivern ya tsaya masu cin abinci suka ci masu Sallahn Azahar sukayi.
Sai kusan karfe goman dare suka shiga garin Abuja zuwa lokacin kam Waheedah jin kafafuwanta take kaman ba'a jikin ta suke ba saboda nauyin da suka mata.
A cikin tashan Karime ta tare musu Taxi ta fada masa anguwan Guzape zai kai su kafin suka shiga Waheedah dai ta zama yar kallo dan tunda suka fara tafiya Babu abun da take sai kalle kalle tare da mamakin yanayin garin tun da ta taso a ƙauyensu bata taɓa ganin irin wannan gari ba. Manyan gine-gine ne ke jere a gefen hanya, wasu suna haskawa da fitilu kala-kala. Motoci kuwa sai kai kawo suke yi duk da cewa dare ya riga ya yi amma kuma kowa harkan sa yake kaman safiya.
Plot 12, Guzape Hills Estate
A dai dai bakin Babban gate din Estates din drivern taxi din yayi parking juya Karime tayi tana kallon Waheeda da ta saki baki da hanci tana kallon manya gidajen da ko a farki bata taba kallon kalan su ba a ranta kuma tana tunanin kenan da gsk ne a birni yan kan kai ake yi wannan tunanin da tayi sai da taji yan hanjin cikin ta sun kada.
Riko hannun ta Karime tayi suka fita daga taxi din ta biya sa kudin sa sannan suka karasa bakin estate din wayan ta dake cikin jaka ta ciro tayi yan danne dannenta kafin ta kara wayan a kunnen ta har yawan ta gama ringing ba'a dauka ba sake kira tayi sai da ya kusa katsewa sannan aka dauka.
"Hello" aka fada daga can bangaren.
Numfashi Karime ta sauke kafin tace,
"Assalamu Alaikum. Hajiya mun iso Abuja yanzu, muna bakin gate din estate.
Shiru na dan lokaci aka yi kafin Hajiyan ta amsa,
"Wa'alaiki salam"
Alhamdulillah. Ku tsaya a nan, zan turo security su shigar da ku."
"To shikenan."
Karime ta fada tana ciro wayan a kunnenta tare da katse kiran ta mayar da wayar cikin jakarta.
Waheedah kuwa har yanzu idanunta na yawo kan katafaren estate din. Komai da take gani sabo ne a gareta. Daga security masu shiga da fita cikin estate din, zuwa fitilun da suka kawata ko'ina cikin unguwar.
Bayan 'yan mintuna kadan wani security ya karaso bakin gate din.
"Madam Karima?" ya fada yana kallon Karime
"Eh, ni ce."
Murmushi yayi yana bude karamar kofar shiga.
"Ana jiran ku. Ku biyo ni."
A hankali suka shiga cikin estate din. Waheedah tana tafiya tana kallon gidajen da suka yi jerin gwano a cikin estate din. Kowanne gida a cikin estate din ya hadu matuka. Wasu gidanjen duplex ne wasu kuma bungalow, da manyan balconies da lambuna masu cike da furanni.
Wani katafaren duplex, da aka kawata shi da fitilu masu haske securityn ya nufa Karime da Waheedah da gaba daya ta gama tsorata suna binsa a baya karamar kofan dake hade da gate din gidan yayi knocking gateman ya bude masa kai tsaye hanyar da zai sada shi da babban parlor gidan ya musu jagora suna isa ya danna door bell tare da juyawa ya bar su Karime a gurin.
Ba'a dauki wani lokacin sosai wata wata matashiyar yarinya dake sanye da kayan yan aiki ta bude kofa tana kallon Karime ta saki murmushi tace sannun ku da zuwa Anty Karima ku shigo ta fada tana basu hanya.
Karima dake rike da hannun Waheedah saboda lura da tayi hankalin ta baya jikin ta gaba daya a tsorace take ta shiga janta zuwa cikin parlorn daya gaji da haduwa ga wani kamshi daya ke tashi a kasan lallausan carpet din dake malale a parlorn suka zauna yayi da me aikin ta shiga kitchen domin kawo musu ruwa kamar yadda Hajiyan gidan ta umurce ta.
Sunfi minti talatin a parlorn kafin wata bakar hamshakiyar mata ta sauko daga upstairs cikin takun isa da kasaita a hankali kuma take karewa Waheeda kallo har ta zo ta zauna a kujeran dake nesa dasu.
Cikin girmamawa Karime ta gaishe kafin tace Hajiya wanna ita ce yarinyar da aka samo daga can kauye kiyi hakuri ban kawo ta da wuri kaman yadda kika bukata ba.
Gyada kai Hajiya Jamila tayi kamar baza tace komai ba kuma sai tace Karima ki tabbata yarinyar nan zata iya aiki kuwa naga kamar she's too young infact na fada miki aikin da zatayi bawai na shara ko wanke wanke bane aikin kula da yarinya ne shiyasa nace ki samo wanda at least she's matured.
Murmushi Karime tayi tana sunkuyar da kanta tace Hajiya Insha Allah zata iya kinsan mu yaran mu na kauye komai sun iya wllh.
Tabe baki Hajiya Jamila tayi kafin tace okay tunda kunyi zuwan dare sai ku kwana anan before zuwa gobe sai muje can gidan kawartawa da take son yar aikin idan har ta mata shikenan idan batayi ba kuma sai kuyi hakuri.
Shikenan Hajiya hakan ma muna godiya wallahi Karime ta fada.
Kwala wa housemaid din nata kira bayan tazo tace mata ta kaisu dakin daya ke bangaren su na masu aiki su huta a kuma basu abinci.
Cikin girmamawa me aikin ta amsa da okay ma"
Sannan ta juya tace Anty Karima muje tashi sukayi suka bita yayin da Hajiya Jamila tabi bayan Waheedah da kallon she don't know why but haka kawai taji yarinyar bata mata ba kuma tasan definitely ba lallai ma Hajiya Sarah ta dauke ta aiki ba.
# Waheedah
#***