Chapter 12
Montreal General Hospital Canada
As usual Muhammad Rayyan na kwance akan gadon marasa lafiya dake dakin yayi da nakurorin dake jikin sa ke aiki.
Hajiya Sarah na zaune a gefen Bed din hannunta cikin nasa tana kallon kyakkyawan fuskan sa da gashi ya cika a hakan ma kuma ana gyara masa cikin sanyin murya tace Son I'm going to Nigeria today.
Ina fatan kafin na dawo a samu improvement akan ciwon ka I can't wait to see you wake up from this long sleep Rayyan because I miss you very much. ta fada tana kai hannun sa da take rike dashi bakinta tayi packing din sa a hankali.
Wayan tane ya fara ringing ta ciro shi daga Bag dinta koda ta duba drivern Ubern da tayi booking zai kaita Airport ne flight din karfe goma zata bi zuwa Nigeria gashi yanzu har 9:30am hakan ne yasa ta tashi a hankali tana gyara mayafinta tare da juyawa ta nufi hanyan fita daga dakin sai da taje bakin kofan dakin kafin ta sake juyawa ta kallesa haka kawai ta sami kanta da sakin murmushi sannan ta fita daga dakin.
Cikin 20min drivern Uber din da tayi yayi parking a Babban airport na
Montréal Trudeau International Airport.
Bayan ta sauka daga Uber din kai tsaye cikin airport din ta nufa bayan ta gama duka process din checking da sauran su ta zauna a waiting lounge tana jiran kiran boarding, yayin da gaba daya tunani da zuciyanta suna ga tilon danta da ta bari kwance a gadon asibiti.
Ko 5min batayi da zama ba aka fara kiran passengers zuwa boarding gate saboda dama ba wani time sosai ne ya saura ba.
Ta tashi a hankali ta nufi gate ɗin, tana jan akwatinta, zuciyarta cike da fatan samun cigaba kafin ta dawo Canada.
*Nigeria*
Waheedah da kyar bacci barawo ya sace ta a sabon gidan data samu kanta gaba daya jinta take a takure koda gari ya waye sukayi Sallah ta nemi guri can jikin bango ta makale sai around 11am aka kawo musu breakfast fried yam and egg sai ruwan zafi da kayan tea.
Da kyar Karime tasa ta taci saboda ita kam ba sabawa da kalan wannan ciman tayi ba bayan sun gama karyawa Karime ta dauki kwanukan ta fitar dasu ta dawo dakin.
Sai karfe biyu me aikin gidan ta shigo dakin tace wa Karime suje parlor Hajiya na son ganin su.
Da to Karime ta amsa kafin ta mike tsaye itama Waheedah ganin hakan yasa ta mike tabi bayan ta suka fita daga dakin.
A Zaune suka samu Hajiya Jamila akan kujera ta daura kafa daya kan daya ga kayan fruit a gaban ta tana ci a hankali tana karkada kafa.
A kasa Karime ta zauna Waheedah ta zauna a gefen ta cikin girmamawa ta gaishe da Hajiya Jamila ita dai Waheeda duk abun da taga Karime tayi shi take yi itama.
Sai da aka shafe fiye da minti biyar kafin Hajiya Jamila ta amsa da lpia a takaice cikin takama tace Karima yau kawata take sauka Nigeria dan haka sai zuwa dare zamu je can gidan nata kafin nan ta samu ta huta.
To shikenan Hajiya ba damuwa ai sai mu jira zuwa daren idan Allah ya kaimu Karime ta fada tana sunkuyar da kanta.
Hajiya Jamila bata ce komai ba sai wani irin kallon da take bin Waheeda dashi juyawa tayi ta kalli Karima tace amma Karima kinsan rules dina ko tunda ba yau kika saba kawo min yan aiki ba bana son kazamai amma naga kaman wannan da kika kawo din kazama ce saboda naga kayan da ta shigomin dashi gida jiya shine har yanzu a jikin ta that's means duk zafi da warin hanyan da kuka kwaso jiya dashi ta kwana kuma har yanzu bata yi tunanin yin wanka ba gaskiya Karima bana tunanin wannan yarinyar zata iya aikin nan saboda ko kadan Hajiya Sarah bata son kazanta.
Cikin sauri Karime tace dan girman Allah Hajiya kiyi hakuri wllh zata gyara kuma zan mata fada sosai dan Allah Hajiya kinsan bamu taba samun matsala ba sai wannan karon kuma Insha baza a sake ba.
Tabe baki Hajiya Jamila tayi tace to da dai yafi kam please dauke ta daga gabana saboda naji yanayin dakin ya fara canjawa.
Cikin sauri Karime ta tashi ta riko hannun Waheedah da kanta ke kasa tunda Hajiya ta fara magana kuma ba karamin zafin kiran ta kazama da Hajiya Jamila tayi taji ba, tashi tayi ta dago kanta tana kallon Hajiya Jamila da ta maida hankalin ta kan wayan ta tana dannawa janta Karime ta shigayi har suka fice daga dakin Hajiya Jamila tabi bayan su da harara a ranta kuwa fadi take talaka da shegen kazanta yake.
Suna komawa dakin Karime tasa Waheedah ta tube kayanta ta daura zani ta bata sabulun wanki da soso tace taje tayi wanka sanin ba iya amfani da bathroom din zatayi ba yasa ta bita ta nuna mata yadda zatayi sannan ta fito ta barta tayi wankan.
A cikin bathroom din Waheedah ta jima tana kallon kanta a jikin mirrorn da yake manne a bangon bandakin kalman kazama da Hajiya Jamila ta kira ta dashi yana yawo a kanta, tabbas ita kazama ce sai dai ba ita taso wa kanta hakan ba a gida idan zatayi wanka sai dai in Dada bata gidan nan ma da iya ruwa kawai ba sabulu ajiyan zuciya ta sauke kafin ta fara wankan a hankali ita kanta ba karamin dadin wankan taji ba dan sosai ta dirje jikinta.
Bayan ta fito Karime tsayawa tayi tana kallonta ganin kaman ba ita bace ta shiga bathroom din saboda wani irin haske da kyau da taga ta mata duk da hasken ba sosai bane amma dai kyanta da dauda ya boye yadan fito mayi ta bata tace ta shafa sai ta dauko wani kayan ta in tana jin yadda wani kalan iska me dadi ke shiga jikin ta.
Da misalin 4pm jirgin su Hajiya Sarah yayi landing a Nnamdi Azikiwe International Airport Abuja.
Bayan jirgin ya daidaita passengers suka fara fitowa bayan ta gama duk wani checking ta fito haraban airport din.
Drivern da yazo daukan ta na hango ta yayi sauri ya karasa kusa da ita tare da dan russunawa cikin girmamawa yace
"Welcome Ma" ya fada yana karban trolley dake hannuta kai kawai Hajiya Sarah ta gyada masa da sauri ya karasa inda yayi parking black car kiran Lamborghini Aventador ya bude mata backseat bayan ta shiga ya rufe ya saka trolley dake hannunsa a car trunk. sannan ya zagaya ya shiga mota ya tayar suka bar airport.
A hankali Hajiya Sarah ta jingina kanta a jikin kujeran motan tare da lumshe idonta tana jin farincikin zuwanta Nigeria amma idan ta tuna danta Rayyan dake kwance cikin halin rashin lpia a wata kasar sai ta nemi gaba daya farincikin nata ta rasa cikin sanyin murya yadda ita kadai zata ji tace Allah ya baka lpia Son Allah ya tashi kafadunka.
#Waheedah
#***