Chapter 13
40min Ride ne ya dauke su zuwa Asokoro saboda yanayin traffic din Abuja suna isa Automatic gate din ya bude kansa babban compound din gidan ya baiyana a driver ya nufi parking lot yayi parking mota tare d fitowa ya budewa Hajiya Sarah.
Hibbah da suke zaune a parlor tunda dazu jiran Mom din nasu ta tashi tsaye da sauri tana riko hannun little girl din dake zaune a gefen ta rike da katon teddy bear a hannunta da alama kuma baza ta wuce 5yrs ba.
Cikin sauri ta shiga jan hannun yarinyar tana cewa Baby Zunairah let go your granny is here.
Washe baki yarinyar tayi tare dayin dan tsalle cikin muryan yara tace my granny is back, murmushi kawai Hibbah tayi tare da tsungunawa ta dauki yarinyar ganin tana bata mata lokaci suka nufi fita daga parlor.
Daidai lokacin Hajiya Sarah ta gama fitowa daga motan tana rike da handbag dinta Hibbah na ganinta ta sauke Zunairah kasa ta kwasa da gudu yayin da itama Hajiya Sarah ta fara takowa a hankali wani kyakkyawan murmushi data jima batayi ba na bayyana akan fuskan ta Hibbah na karasowa tayi hugging Mom din tana cikin farinciki.
Hugging nata back Mom tayi tare da cire ta a jikin ta a jikin murmushi sosai a fuskan ta tace Hibbah kekam bakya girma ko kalan wannan gudu haka what if kika fadi fa.
Bata fuska tayi cike da shagwaba tana riko hannun ta tace Mom nayi missing naki ne fa.
Girgiza kai Mom tayi tana kallon Baby Zunairah dake tahowa gurin ta bakin ta a washe, tsungunawa Mom tayi tare da bude mata hannu tana karasowa kuwa ta shige jikin ta tana sakin dariya, ita ma Mom karamin dariya tayi tana shafa kanta tace I miss you Baby.
I miss you too granny Zunairah ta fada.
Dago ta Mom tayi suka nufi hanyan parlor Hibbah na rike da trolleyn data karba a hannun driver.
A Babban parlor nasu Mom ta zauna tana daura Zunairah akan cinyan ta, masu aikin gidan ne da suka kasance su biyu wata dattijuwa da suke kira da Baaba Asabe sai kuma wacce a kallan itama zata kai 30yrs me suna Zulai suka shigo suka gaishe ta tare da mata Barka da dawowa da tambayan ta ya me jiki.
Da sakin fuska sosai Mom ta amsa musu gaisuwan nasu kafin Baaba Asabe ta tambaye ta ko akwai abun da take bukata yanzu tace Aa sai tayi wanka amma ta kawo mata ruwa me sanyi yanzu cikin girmamawa Baaba Asabe tace to tare da juyawa ta nufi hanyan kitchen din dake parlorn.
Hibbah data kagu su gama gaisawa tace Mom how was the Canada ya jikin Bro Rayyan I hope there's improvement before you came?
Ajiyan zuciya Mom ta sauke tace Hibbah babu wani improvement a jikin Rayyan yana nan yadda yake a kwance ba abunda ke motsawa a jikinsa but ina fatan kafin na koma a samu improvement din.
Cikin sanyin jiki Hibbah tace Allah yasa Mom I so much miss him wllh ina so naga ya dawo gida mu cigaba da rayuwan mu kaman da bana son ya tafi ya barmu kaman yadda Dad yayi ta karasa fada tana jin hawaye na ciko idanuwanta saboda tunawa da mahaifin su da tayi.
Insha Allah Muhammad Rayyan bazai tafi ya barmu ba ina ji a jikina kaman wannan ciwon nasa ya kusa zuwa karshe just we should continue pray for him okay?
Gyada kai kawai Hibbah tayi tana share hawayen ta.
Tashi Mom tayi tana sauke Zunairah dake wasan ta a jikin ta tace I need to go and fresh up kice wa Zulai ta hada dinning before na sauko.
Okay mom.
Wuce wa sama Mom tayi zuwa dakin ta daga gaji da haduwa komai na cikin dakin milk ne a bakin Bed ta zauna tare da bude handbag dinta ta ciro wayan ta numbern Hajiya Jamila tayi dialing ta kara a
kunne ta ringing biyu Hajiya Jamila ta dauka gaisawa sukayi kafin Mom ta fada mata ta sauka Nigeria.
Masha Allah Hajiya Sarah naga da numbern Nigeria kika kira ni ai insha Allah zuwa dare zan shigo saboda an kawo me aikin da kika bukata tana gidana hanzu haka zuwa dare idan kin huta sai na kawota.
To shikenan Hajiya Jamila Allah ya kawo ku lpia Mom ta fada sannan sukayi sallama.
Bayan Mom ta fito daga wanka ta shirya cikin kaya marasa nauyi ta sauka kasa inda aka shirya abinci akan dinning sanin dokan Mom na idan ana cin abinci ba'a magana yasa gurin yayi shiru sai karan spoons kawai daya ke tashi da buruntun Zunairah da take cin abinci tana wasa.
After sun gama cin abinci parlor suka koma Mom na zaune akan kujera Hibbah da Zunairah kuma na kasa suna kallon cartoon da Zunairah ta dage sai ansa a babban plasma daya ke parlon
kallon su Mom tayi kafin tace What about going back to school?"
Ta fada tana kallon Hibbah.
Juyawa Hibbah tayi ta kalli Mom tace next week zan koma Insha Allah an samo me aikin da zata kula da Baby ne?
Yeah Hajiya Jamila tace min an samu zawu dare zasu zo I hope Baby zata yarda da ita karta mana kalan na sauran.
Murmushi kawai Hibbah tayi bata ce komai ba ta juya ta cigaba da kallon ta.
Da misalin 7:30pm Hajiya Jamila na zaune a parlorn ta cikin shiga na Alfarma ta daura kafa daya kan daya wayan ta kiran iPhone 17 rike a hannun ta tana dannawa.
Kwalawa me aikin ta kira tayi bayan tazo ta tsunguna a gaban ta cikin isa Hajiya Jamila tace je ki fadawa Karima su fito and tell them kar su bata min lokaci.
Da okay ma ta amsa tare da tashi ta nufi masaukin su Karime a zaune ta same su Waheedah tayi tagumi yayin da Karime ke danna karamar wayan ta sakon Hajiya Jamila ta fada musu kafin ta juyata ta fita.
Tashi Karime tayi tace Waheedah ta dauki kayanta suje dan tasan tafiya zasuyi.
A zaune suka sami Hajiya Jamila Karime tace Barka da hutawa Hajiya.
Da yauwa ta amsa sannan ta tashi ta kalli Waheedah ganin ba kayan dazu bane a jikinta yasa ta tabe baki ta nufi hanyan fita daga parlorn hannun ta rike da waya da handbag dinta.
Koda suka fita driver dinta na ganin ta ya taso da sauri yana gaishe ta, bata amsa ba sai key din mota data wurga masa kafin ta nuna masa su Waheedah tace gidan Hajiya Sarah zani ka biyo ni dasu bazan iya shiga mota daya da suba tana gama fadin haka ta nufin parking lot mota kiran BMW 7 Series ta shige abun ta.
Juyawa drivern yayi yana kallon Karime yace muje ko.
Murmushi Karime ta kirkiro dan itama ba taji zafin abun da Hajiya Jamila tace, shikenan idan mutum talaka na nema a gun mai kudi walakanci kala kala zai gani girgiza kai tayi ta riko hannun Waheedah suka bi bayan drivern a ranta kuwa tana hamdala da ya kasance Waheedah ba'a gidan ta zatayi aiki ba saboda daga yanda take nuna alamu Waheedahn bata mata ba tana kuma fatan can inda zasu je din a karbe ta dan wllh ita kam bata da kudin motan da zata maida ita gida.