Chapter 14
A kusan tare motar Hajiya Jamila da wanda su Waheedah ke ciki sukayi parking a parking lot din gidan Hajiya Sarah.
Hajiya Jamila na fitowa ta kalli drivern da shima ya fito daga mota tace Bala ka koma gida and kada kamin tukin ganganci da mota.
Cike da girmamawa drivern ya amsa da to Hajiya, kafin Hajiya Jamila ta juya ta nufi cikin gidan su Karime na binta a baya doorbell ta danna,ba'a wani dau lokaci ba Zulai me aiki ta bude kofan ganin Hajiya Jamila ne yasa ta matsa da sauri ta bata hanya tana mata sannu da zuwa ko kallon ta batayi ba ta wuce cikin parlorn abunta su Waheedah ma suka shiga.
Mom dake zaune a parlor tare dasu Hibbah tana ganin kawarta ta ta miki tsaye cike da fara'a tana fadin harkin karaso kenan side hug sukayi kafin Hajiya Jamila ta zauna akan kujera tana kallon Hibbah dake gaishe ta.
Murmushi ta sake tace lpia qlau Daughter ya kika bar Baby tayi bacci da wuri haka ta fada idon ta akan Zunairah dake bacci akan kafan Hibbah.
Mom ne ya katse mata zance nata tace Hajiya Jamila wannan ita ce yarinyar da aka samu din ta fada tana kallon Waheeda da Karime dake zaune a kasa bayan sun gama gaisawa.
Tabe naki tayi tace eh ita ce Karime ta samo na fada mata wannan she's too young baza ta iya aikin kula da yarinya karama kamar Baby ba dan itama wannan ai bata wuce a kula da ita ba amma ta dage zata iya shiyasa na kawota taji daga bakin ki Hajiya Jamila ta fada tana daura kafa daya kan daya.
Murmushi Mom tayi tana gyara zama ta kalli Waheedah da kanta ke kasa sai kuma ta kalli Karime dake addu'a a ranta na Allah yasa kar tace Waheedah bata mata ba itama kamar daga sama taji Mom tace Karima me sunan tane?
Cikin girmamawa Karime tace Hajiya sunan ta Waheedah.
Gyada kai Mom tayi ta maida kallon ta kan Waheedah tana karantar yanayin yarinyar a hankali tace
"Waheedah"
Dago kai Waheedah tayi tana kallon Mom da itama take kallon ta haka kawai Mom ta samu kanta da sakar mata murmushi kuma har cikin ranta taji natsuwan yarinyar ya mata dan haka ta juya tana kallon Hajiya Jamila dake danna wayanta tace I think tunda har an riga da ankawo ta bai kamata ta koma ba idan har Baby ta yarda da ita to ba matsala a hankali zata koyi kula da ita.
Wani irin hamdala Karime ta sake cikin sauri tace Hajiya mun gode Allah ya saka da Alkhairy Allah ya biya miki bukatun ki na Alkhairy wallahi kin gama min komai da kika karbi yarinyar nan dan da bansan ya zanyi na maida ita gida ba.
Murmushi Mom tayi dan sosai taji dadin addu'an da Karime ta mata kafin tace Ameen ya Allah Karima salaryn ta 100k ne every month dan haka sai kiban numbern ki da kuma account number da za'a tura kudin idan wata yayi.
Washe baki Karime tayi tace to shikenan Hajiya.
Hajiya Jamila dai tunda suka fara magana bata ce musu komai ba dan ko kadan batayi tsammanin Mom zata karbi Waheedah ba dan ita fa har cikin ranta taji bata son yarinyar ko kadan.
Hibbah da tun shigowan su Waheedah ta kura mata ido tana kallonta ta tashi ta koma kusa da Mom a hankali yadda Mom din kawai zata ji tace Mom she has a very nice name and I like her tana da natsuwa sosai.
Gyada kai Mom tayi tace I hope that Baby will like her too as you do kinsan rigiman Baby baya kadan.
Hajiya Jamila ta tashi tsaye tana kallon Mom tace to ni Hajiya Sarah zan koma kinsan ba driving din dare nake so ba yanzun ma dan ya kama ne shiyasa na fito.
Tashi Mom tayi ta taka mata bayan ta tafi Mom ta dawo parlon kallon Hibbah tayi tace ta tashi ta kai su Waheedah nan dakin da yake downstairs kafin zuwa gobe Karime ta koma kauye.
*Kauyen Kafin Lemo*
Baba ne zaune a kasan bishiyan da yake gidan ya buga tagumi gaba daya ya rasa me yake damun sa yau kwana biyu kenan baiga Waheedah a cikin gidan ba gashi duk yadda yaso ya tambayi Dada ko Waseelah inda take ya kasa idan yayi niyyan shiga dakin nata kuma saboda ya duba ko tana ciki yana saka kafan sa a bakin kofan dakin sai yaji kansa ya fara juyawa ya manta abun daya kaisa dakin haka zai sake juyawa ba tare da ya shiga ba.
Duk wannan abun da yake yi kuma akan idon Dada kuma ta kudurta a ranta shida Waheedah kuma har abada wllh.
Yanzun ma tana zaune ita kadai a daki saboda Waseelah ba'a gidan ta kwana ba tana gurin Alhajinta tashi tayi ta leka windon dakin nata taga har yanzu Baba yana zaune a in da yake tun safe gashi har rana ya fara fitowa kwafa tayi ta nufi hanyan fita daga dakin akan Baba tazo ta tsaya tana rike kugu cikin masifa tace wai kai Malam ban gane zaman me kakeyi anan tunda safe ba gashi har rana ya fara fitowa baka da niyyan tashi kaje ka nemo mana abun da zamu sanya a cikin mu nifa na gaji da wannan lalacin naka wllh mutum baida aiki sai zaman banza da tunanin banza to gara tun wuri ka tashi wllh.
Dago kai Baba yayi yana kallon Dada jin kalan tijaran da take masa sai faman daga murya take yi makota naji girgiza kai kawai yayi baice mata komai ba ya tashi ya fita daga gidan.
Ah to yafi maka wallahi baza kazo ka zauna kana tunanin wannan shegiyar yarinyar ba mu kuma ka hana mu cin abinci tana gama fadin haka ta juya ta dauko mayafin ta so take taje gidan Balaraba taji ko su Karime sun isa birni dan ita fa ta kosa ta fara rike yan janjuna a hannun ta.
#Waheedah
#***