Chapter 15
Washegari, ranar Saturday, tun bayan da Waheedah da Karime suka yi sallar Asuba, Karime ta fara shirin komawa ƙauye. Bayan ta gama shirye-shiryenta, ta koma wajen Waheedah wadda ke zaune a kan gadon da ke ɗakin.
Ta dafa kafaɗarta cikin sanyin murya ta ce,
"Waheedah, ni yau zan koma gida. Don Allah ki kula da kanki, kar ki yi wani abin da zai sa a kore ki daga gidan nan. Kin san halin Dada. A yadda Yaaya Balaraba ta faɗa min, karuwanci ma ta so ta tura ki. Tun da Allah Ya kuɓutar da ke daga sharrinta, sai ki kiyaye sosai, kin ji ko?"
Waheedah, wadda tun da Karime ta fara magana take kallonta, ta gyada kai kafin a hankali ta ce,
"To Anty Karime, zan kula. Amma don Allah idan kin koma gida, ki samu Baba ki faɗa masa cewa Dada ba ta bar ni na yi sallama da shi ba. Na san hankalinsa zai tashi sosai idan bai gan ni a gida ba kwana biyu."
"To Waheedah, zan faɗa masa. Wannan Dadar taku, Allah dai Ya shirye ta," Karime ta faɗa tana jin takaicin halin Dada. Ta yaya za ta ɗauki yarinya ta tura birni ba tare da sanin mahaifinta ba?
Suna nan zaune Karime na ci gaba da yi mata nasiha da jan kunne, aka turo ƙofar ɗakin. Hibbah ce ta shigo, Zunairah na hannunta, fuskanta dauke da kyakkyawan murmushi.
Ta gaishe da Karime kafin ta kalli Waheedah, wadda ita ma ke kallonta.
Ta miƙa mata hannu tana cewa,
"Sunana Muhibbah, amma Mom da Brother suna kirana da Hibbah. Ke ma za ki iya kirana haka."
A hankali Waheedah ta miƙa mata hannunta tana sakin ƙaramin murmushi. Suka gaisa.
Hibbah ta kalli Zunairah da ke maƙale a jikinta, yatsarta na cikin baki tana tsotsa. Ta ce,
"Baby, here is your new nanny. Go and greet her."
Ta fada tana cire ta daga jikinta ta ɗora ta a kan cinyar Waheedah.
Gyara mata zama Waheedah tayi a jikin cikin kulawa tana kallonta. Wani kyakkyawan murmushi ya bayyana a fuskarta. Ita ma Zunairah kallonta take yi kamar mai son gano wani abu a fuskarta. Can kuma sai ta kwantar da kanta a jikinta tana ci gaba da tsotsar yatsarta.
Waheedah ta shafa kanta a hankali tana cewa,
"Me sunanki?"
Zunairah ta tura baki kaɗan sannan ta ce,
"Granny and Auntie Hibbah call me Baby Zunairah."
"OMG! Gaskiya Sis Waheedah, you're so lucky. Baby ba ta saba zama a wajen wanda ba ta sani ba, balle har su yi hira!" Hibbah ta faɗa cikin farin ciki.
Murmushi kawai Waheedah ta yi tana ci gaba da kallon Zunairah da ke wasa a jikinta.
Juyawa Hibbah tayi tana kallon Karime kafin ta ce,
"Auntie, Mom ne ta ce na zo na duba ko kin gama shiryawa. Idan kin gama, sai mu je ku yi breakfast sannan driver ya kai ki zuwa car park."
Karime ta gyada kai tana cewa,
"Na gama ai. Bari kawai na ɗauki jakata mu tafi."
Hibbah ta yi murmushi tare da cewa,
"Okay Auntie, mu je. Mom tana jiranmu a parlor."
Mikewa Karime tayi tana ɗaukar jakarta, sannan suka fito daga ɗakin tare Waheedah ma ta miƙe tana dauke da Baby Zunairah a hannunta, tana bin su a baya.
A zaune Babban parlorn da sai yanzu Waheedah ta karemai kallon sosai duk yadda taga haduwan parlon Hajiya Jamila wannan ya fisa nesa ba kusa ba suka samu Mom zaune akan kujera tana karanta jarida.
Dago kai Mom tayi idon ta ya sauka akan Waheedah dake dauke da Zunairah murmushi ta sake a ranta tana mamakin yadda akayi Baby taje gurin ta.
Akan carpet suka zauna Karime ta gaishe ta haka ma Waheedah Mom ta amsa da fara'a akan fuskanta.
Ajiye jaridar hannunta tayi a hankali, idanunta har yanzu na kan Zunairah dake zaune a jikin Waheedah.
Ta ɗan yi murmushi kafin ta ce,
"Hibbah, wannan dai Baby ce kuwa?"
Dariya Hibbah tayi tana zama kusa da Mom.
"Mom, ni ma mamaki nake yi. Tun da na kai ta wajen Sis Waheedah ta ƙi dawowa wajena."
Mom ta girgiza kai tana kallon Zunairah.
"Gaskiya abin mamaki ne. Baby ba ta saba sakewa da mutane haka cikin sauri ba.
Mom ta ci gaba da kallon Zunairah cikin mamaki kafin ta ce,
"To Alhamdulillah. Wataƙila Allah ne ya hada jinin su."
Duk suka yi murmushi.
Bayan ɗan lokaci, aka shirya breakfast. Suka zauna suka ci abinci tare cikin natsuwa.
Bayan sun gama, driver ya fito da jakar Karime zuwa mota.
A hankali Karime ta rungume Waheedah dan har cikin ranta take kaunar Waheedah kamar yar uwarta tace
"Ki kula da kanki, Waheedah.
Gyada mata kai tayi tana jin kamar kar ta tafi.
Karime ta juya tayi sallama da Mom da Hibbah, sannan ta shiga mota driver ya tafi da ita zuwa car park.
Tsaye Waheedah tayi bakin ƙofa tana kallon motar har sai da ta ɓace daga ganinta duk da ba dadin zaman gidan su take jiba amma sai taji wani irin kewan gidan ya kamata musamman idan ta tuna batayi sallama da Baba ba
Hibbah data lura da yanayin fuskarta ta dafa ta tace
"Kar ki damu sis Waheedah. In sha Allah za ki saba da kowa a gidan nan."
Waheedah ta gyada kai kawai.
Miƙo mata hannu Zunairah dake tsaye a gefen ta tayi tana cewa,
"Carry me."
Murmushi Waheedah ta sake tare da dukawa ta ɗauke ta a hannta suka koma cikin gidan.
#Waheedah
#***