BABI NA ƊAYA.
💎🌹Haula Habeeb 🌹💎
2026 Edition
By
Amdeey Tejj d'Unique.
Gargaɗi
Ba a yarda wani, wata ko wasu gungun mutane su yi amfani da wani ɓangare na wannan littafi ba ta kowace hanya face sai da izinin marubucin. Yin hakan babban laifi ne da ke iya kai mutum ga shiga komar hukuma. A kiyaye.
Jan Hankali
Wannan labari ƙiƙirarre ne. Ban rubuta shi don cin zarafi ko tona asirin kowa ba. Duk wanda ya ga wani abu da ya yi daidai da rayuwar shi, to ya sani arashi ne ba da nufi ne ba.
Jinjina
Jinjina ta musamman ga ɗaukacin membobin Future Writers Association (FUWA) The Rising Star Team. Allah Ya bar zumunci kuma ya ƙara hazaƙa.
Bismillahir Rahmanir Raheem.
*HAULA HABEEB*
BY
AMDEEY TEJJ D'UNIQUE
BABI NA 01
A wayewar garin yau, wadda ta kasance ranar Asabar, daidai da sha takwas ga watan Maris ne ake sa ran wayewar garin da za ta zo wa ahalin gidan da wani irin farinciki na musamman sakamakon abin alherin da za a ƙulla a cikinsa. Sai dai kash! Saɓanin hakan ne ya faru, maimakon farinciki sai ma baƙinciki da ya maye gurbinsa, hakan kuma ya faru ne sakamakon mutuwar ɗaya daga cikin waɗanda za su zama silar ƙulluwar wannan farinciki.
Motoci ne a jere tun daga harabar gidan har waje, kowa idan ka kalli fuskarsa sai jimami yake yi tare da jinjina kai bisa irin wannan iko da ƙudira irin wadda Ubangiji mai yin yadda Ya so, a sa'adda Ya so, ba tare da wani ya tuhume shi dalilin yin hakan ba Ya nuna. To, idan ba haka ba, wa zai ma haka kuma ka yarda? Ai sai dai Shi ɗin mai iko da kowa da komai. Mai cewa kasance kuma ta kasance, ba yadda ka iya ko da ba yadda ka so bane, wato Allah maɗaukakin sarki kenan.
Daga cikin gidan kuwa ban da koke-koken mata ba abinda ke tashi, wasu kuma sai aikin lallashi suke yi, zuciyoyi da yawa sun yi ƙunci babu daɗi, amma duk da haka a wani ɓangare na gidan kuma wasu zuciyoyin cike suke farinciki tamkar an yi musu babban albishir.
A can cikin babban falon gidan, wata mata ce zaune a kan kujera sai kuka take yi, ta ma kasa magana, mutane sai baki suke ba ta, bisa ga dukkan alamu dai ita ce mahaifiyar wadda ta rasun. A zahiri mutuwar kawai take yi wa kuka, amma a baɗini akwai wani ɓoyayyen dalili a bayan wannan kukan. Ana cikin wannan hali ne aka fito da gawar za a kaita makwancinta. Wata daga gefen matar ce ta ce,
"Yaya na yi juyin duniya da ke kan ki je ki yi mata addu'a amma kin ƙi, ga shi har za a fitar da ita. Don Allah ki ƙarfafi zuciyarki, shi fa dama mai rai mamaci ne. Allahn da Ya ba mu ita, yau karɓi baiwarSa. Kuma kin san cewa Ya fi mu sonta. Addu'ar samun rahama da dacewa a makwancinta ya kamata mu yi mata. Don Allah ki daure.''
Ba ta motsa ma balle ta sa ran za ta yi abin da ta buƙata, sai kuka kawai take yi. A daidai wannan lokaci ne kuma aka fita da gawar. Sai a lokacin ne ta ɗago ta kalli yadda aka fitar da ita, a lokaci ɗaya take kallon tafiyar cikar burinta, mafarkinta, ginin da ta shafe tsawon lokaci tana ginawa, ta ɓata shekaru da muhimman lokutanta don gina shi, yau shi ne take kallo yake rushewa, koma ta ce ya rushe a gaban idonta. A lokacin da take daf da cin moriyar abin da ta shuka, kuma ba tare da ta yi wani yunƙuri ba kamar yadda ta saba. To ma, ta ina za ta fara idan yin za ta yi? Ko ma ta yi wa za ta kama, to ina ma zata dosa ta fara da shi? Waɗannan ba irin waɗanda ta saba shafe su bane kamar cinnaku, wannan ba faɗan da ta saba da shi bane, a nan ko motsi ba za ta iya ba. Kai Astagfirullah! Don wani tunanin ma idan ka yi kai da kanka za ka ce ko ka yi hauka ne.
Ficewarsu daga gidan ya yi daidai da fashewar wani dunƙulallen abu da ya tokare mata a maƙoshi, wannan karon kukan ya fi ƙarfin ta, babu yadda za ta yi ne, don haka ya ƙwace mata. A zahiri, ganin wannan kukan ya sa mutane ke tausaya mata da tunanin mutuwar ce ta taɓa ta, nan dai aka hau rarrashinta.
A ƙofar gidan kuwa, ana fitowa da gawar dama an riga an taru, ba a jira komai ba aka yi mata sallah sannan aka nufi maƙabarta domin sa da ta da makwancinta.
Bayan Watanni Huɗu
''Nooo! Ƙarya ne wallahi, shirina ba zai taɓa tafiya a banza ba, dole buri da mafarkaina su cika, ba zai yiwu ba.''
Ta yi maganar cikin hargagi tare da wurgi da kofin gilas ɗin da ke hannunta. Ai ku bai jira komai ba ya fashe nan take, yayin da ta ci gaba da huci kamar wata kububuwa.
''Kwantar da hankalinki Ya'ya, burinmu ai dole ne ya cika, idan kina jin dolen-dole to shi ne wannan don babu ta yadda za a yi mu kwashe shekaru muna abu ɗaya lokaci guda ace ya rushe cikin sauƙi, kamar ƙiftawar ido. Haba, ina ma za ta saɓu.''
Samun wuri ta yi ta zauna a bakin rantsatstsen Royal Bed ɗinta wanda ya sha shimfiɗuna alfarma. Haɗe hannayenta ta yi akan ƙirjinta sannan tace,
''Salmai, wannan buri nawa wani abu ne da ban taɓa hasaso wargajewarsa cikin sauƙi haka ba, musamman a lokacin da nake ganin cewa na kusa cim-mashi. Amma sai komai ya lalace cikin ƙiftawar ido. Wannan abin da ya faru kamar ace mai haƙar ramin zinare ne, ya jure dare da rana, zafi da sanyi, rana da iska, yana haƙa sai da ya fara hango zinariya, bayan tulin duwatsun da ya fasa da ƙasar da ya kwashe ya tattara su gefe guda, sai da ya fara hango wannan zinariyar, bai gajiya ba ya ci gaba da haƙa har ya kusan kaiwa ga gaci, sai kurum a ranar da ya zo don kwasar abin da ya daɗe yana wahala akai domin ya ga ya samu, sai ya tarar babu ko alamar wannan dutsen da ya sha fama wajen fasawa ma, balle batun zinariya. Kuma bai tadda kowa a wajen ba balle ya ɗaura alhakin hakan akansa, ko kuma ya yi tunanin ɗaukar mataki. Watau dai wannan dutsen ya koma kamar ma bai taɓa wanzuwa ba.''
Cikin ƙwarin gwiwa Salmai ta dube ta sannan ta ce,
''Ya'ya, kar ki damu, za mu samo mafita, ko ta halin ƙaƙa sai mun mallaki abin da dama can mallakinmu ne.''
HAZ Mansion
Ihun da ya ji an rafka a cikin kunnensa da kamar za a fasa masa dodon kunne ne ya sa shi buɗe idonsa a zaburre ba tare da ya shirya ba daga baccin da ya fara yi bayan ya gama lazimin safe. Ido biyu suka yi da ita, ta fashe da wata irin dariya tana kallonsa. A fusace ya kai mata wani wawan duka, Allah ya taimaketa ta kauce. S guje ta nufi ƙofa shi kuma ya rufa mata baya zuciyarsa na tafarfasa. Yau kam ji yake idan ya kama yarinyar nan, idan akwai gaba da lahira can zai kaita ya huta, kowa ma ya huta, don yau ta ƙureshi.
Hanyar kitchen ta nufa kai tsaye a guje yana biye da ita. A bayan wata tsohuwar mata da ke aikin abinci a kitchen ɗin ta ɓuya tana faɗin,
''Wayyo Allah Gwaggo wannan mai fuska irinta saƙagon saniyar zai kashe ni."
Turus ya tsaya a bakin ƙofar kitchen ɗin yana huci tare da ƙoƙarin danne fushinsa ganin Gwaggo Gambo a ciki tana aiki. Ga kuma wannan yarinyar mai zubin aljanun duniyar alien a Bayanta. Don shi a ganinsa ko aljanun duniyar mutane ba za su yi abinda take yi ba. Ta wani cukwiwiye mata zani har shirin faɗuwa ma yake yi, ba don ta riƙe da kyau ba. Masu hikima kan ce ko mutuwa ma na kunyar idon mahaifi, Hakan ya sa shi wucewa ba tare da ya ce komai ba, sai cika da batsewa kawai da yake yi. Ga kuma kunyar matar da yake ji saboda kirkinta a gare shi.
Gwaggo Gambo ta kalle ta a kaikaice, ita kuma sai ƙyaƙƙyafta ido take yi kamar wacce ta warke daga makanta.
''Wato ke bakya ji ko Haula? Tun da na dawo gidan nan, bakina bai da aiki face na ban haƙuri. Ba don Allah ya sa Alhaji ƙarami yana jin kunyata ba kuma ina zama da mutanen gidan nan da maƙota lami lafiya kuma ba sun sanni ta daliinki bane, Da an daɗe da korata a gidan nan. Wallahi ki canza hali ko kema kya samu ki huta da maganar mutane. Kowa Haula kowa Haula kamar Haular hauka, Allah ya kyauta.''
daga haka ta juya ta cigaba da aikin da ke gabanta.
Turo baki gaba tayi cikin ƙaramar muryarta ta ce, ''To ba wancan Alhajin mai ɗaki a sama ne ya ce na kira mai shi ba, ,ai ba laifina bane don na tashe shi ya ƙi tashi ne, ni kuma na mai ihu a kunne.''
Ta faɗi iyakar gaskiyarta, dama kuma bata iya ɓoye-ɓoye ba, duk abinda ya zo kanta kawai furtashi take oho in ya ma daɗi ko a'a.
''Kai! Ke dai Haula shegantakarki na da yawa. In ba haka ba ya za ki je mutum na bacci ki yi masa ihu a kunne? Idan ya firgita wani abun ya sameshi fa? ko idan yana da hawan jini jininsa ya hau fa? Kum....''
Katse maganar Gwaggo ta yi da cewa,
''Laaa! Gwaggo idan mutum jininsa ya hau ai ya ji daɗi, idan ya sauka fa babu kenan, kuma malamin bokon mu yace wai mutum baya rayuwa ba jini. Kin ga zai mutu kenan.''
Sai ta zaro ido waje ta sake cewa,
''Ni dai Allah ya sa nawa ya dinga hawa kullum."
Ta faɗa cike da fatan hakan a ranta, don ba ta son ta mutu yanzu.
''Tafi can uwar shiririta! kina yi wa kanki mugun fata ba ki sani ba.''
Ganin za ta sake magana ne Gwaggon ta katse ta don idan ta Haula ne sai a kwana ana maganar nan ba ƙarewa za ta yi ba.
''Za ki wuce ki je ki yi shirin makaranta ko kuwa? Saura kuma ki je ki kaini gaba.''
ta ƙarashe maganar cikin faɗa kuma da gargaɗi. Daga haka ba ta sake bi takanta ba, sai ta ci gaba da da aikinta
Duk da haka sai da ta sa hannu a cikin kwandon kayan lambu ta ɗauki karas, ta sa gudu ta yi waje. Gwaggo ta girgiza kai kawai a ranta tana mata fatan shiriya.
Tsaf ya fito a shirye da shirin zuwa office. Har yanzu ran shi zafi yake akan abin da wancan mahaukaciyar yarinyar ta mishi. Fuskarsa sam ba walwala da ma kuma walwala ba adon fuskarsa bane, don ba ya abota da ita. Fitowa ya yi falon daga ɓangaren shi, kai tsaye dinning ya nufa ya ajiye briefcase ɗin hannunsa akan ɗaya daga cikin kujerun dinning ɗin sannan ya nufi kitchen. A jikin coffee maker ya tsaya, ya haɗa coffee ya fito yana kurɓa a hankali. A jikin dinning ya tsaya bai zauna ba har ya kammala sha sannan ya mayar da kofin kitchen ya wanke ya kife. briefcase ɗin shi da ke kan kujerar dinning ya ɗauka ya fice.
Main parlor ya fito, a nan ya tadda mutanen gidan gaba ɗaya sun haɗu a dinning suna breakfast, wajen ya nufa ganin sanyin idaniyarshi a wajen. Bai shiga cikin dinning arean ba ya tsaya daga bakin wajen
Wani ɗan Dattijo ne a wajen ya ce, " Ahh son ka fito kenan! Ƙaraso ka karya ya zaka tsaya a nan.'' Ya faɗi fuskarsa ɗauke da fara'a.
''No Dad, na riga na sha coffee, zan ci abinci idan na je office." Ya ba shi amsa a hanzarce.
''No son. Ka wuce kawai mu je ka ci abinci kafin ka fita, don na san ba ci za ka yi ba ko ka je office ɗin.'' Ya ji an faɗa daga bayan shi. Juyawa ya yi ya kalleta, wata mata ce fara ta yi maganar, itama shekarunta sun ja daon za ta yi shekara 42 zuwa da 45.
Ya wani shagwaɓe fuska kamar yaro ya ce, ''Mommy I have a meeting by 10:30 kuma yanzu about 09:15." Ya yi maganar yana duba agogon da ke ɗaure a tsintsiyar hannun shi.
''Yauwa ka ga akwai sauran awa ɗaya da ƴan kai kenan. A cikin awa ɗaya kuwa ko ɗan yaye ake ba abinci ai ya ci ace an gama."
Zai sake yin wata maganar ta tare shi,
"Kar ka yi musu yaro mu je. Ba ka son cin abinci ni kuma ba na so kana barin kanka da yunwa. '' Ta yi maganar cikin kulawa tana shafa fuskar shi sannan ta ja hannun shi suka ƙarasa zuwa cikin dinning area ɗin. Ta ja mai kujera ya zauna kafin ta ɗau plate ta sa mai abinci ta tura mishi gaban shi. Ba don yana so ba ya fara cin abincin.
"Yauwa ko kai fa son, kana stressing kanka da yawa da aikin nan fa.''
"Yau ba gaisuwa ne son? Ko da yake na ga iyayen naka suna ta shagwaɓa ka kamar ɗan yaye, ina za ka samu damar wata gaisuwa." Cewar uncle Bulama cikin zolaya.
"Ai nima na tsaya ne kawai ina kallon ikon Allah. An mai da yaro kamar wani ɗan yaye.''cewar uncle sammani yana dariya
''Ah! to ya son ranku? Idan ban shagwaɓa shi ba wa zan shagwaɓa? Yi abunka ɗan lele na.'' Cewar Mommy tana dariya.
Nan suka hau tsokanarsa daga iyayen har sauran yaran gidan irin su Salim da Tahir waɗanda suke kusan sa'anni, amma banda ƙannen shi su sai dai su yi dariya idan ta kama. To wa ma ya isa a cikinsu ya fara? Ai ko bakinsa ya yi jini. Abin dai gwanin burgewa.
Shi kuwa ko motsi bai yi ba kai ba ka ce ma da shi ake yi ba. Sai sunkuyar da kai da ya yi murya can ciki ya gaida kawunnan nasa da matansu. Abin mamaki ba wanda ya damu da yadda ya ɗaure fuska ana mai wasa, da alama dai sun saba da hakan.
"Kar ku dame min yaro, ku barshi ya ci abinci ya gangara mai ciki." Cewar Mommy.
Daga haka suka ci gaba da karyawa cikin nishaɗi da barkwanci.
''Yauwa Alhajin sama ina kwana." Cewar Haulat da ke cikin uniform ɗinta hannunta riƙe da lunchbox ɗinta.
"Ah ah Haulat ce lafiya lau, makaranta za a je?"
"Eh amma na kawo ƙara ne, shi ya sa na biyo ta nan. Ka san ai da can hanyar zan bi, tun da ɗazu na gaisheka ko?''
Yadda ta yi maganar kai ka ce da ƙawarta take yi.
"Eh hakane. To amma ƙarar wa aka kawo min?" Cewar Alhajin cikin tambaya.
"Wannan yaron naka mai fuskan saƙagon mana." Ta yi maganar tana wani gatsine fuska tana mayarwa gefe ɗaya, wai ita kar ya rainata.
Salim da ya tura chips a bakinshi ya fashe da wata dariya, dole ya fito da abinda ke bakinshi ba shiri.
" Taɓ! Lallai akwai ƙura." ya faɗa a ranshi don shi tun da ta ce ta kawo ƙara ya san ƙarar wa ta kawo, ga shi yanzu ta ce mishi mai fuskar saƙago, shi har ma ta bashi tausayi.
Ita dai kallon sa kawai ta yi ba ta bi takan dariyar da yakeyi ba ta cigaba da magana. "Daga wai ɗazu na ji ka ce za ka sa a kirashi sai na je ina tashin shi, sai ya ƙi tashi ni kuma na mai ihu a kunne don ya ji ya tashi, amma mutumin nan sai ya biyoni da gudu zai duke ni. Ya sa Gwaggo ta yi ta min faɗa kamar wata ƙaramar yarinya.''
Ta yi maganar wanda yake iyakar gaskiyarta ta faɗa.
Salim ya bita da kallo from head to toe, wata dariyar ya sake fashewa da ita yana mamakin son girma irin na Haula.
"Ayya bai yi daidai ba, amma yanzu dai ki tafi makaranta kar ki yi latti zan mai magana, ba zai sake ba." Cewar Dad, wato Alhaji Salahu, Alhajin Sama in ji Haula.
"Lallai ma samun wurin mutanen na yayi yawa, a ce har da su kaza a cin danƙo? 'Yan aiki suna kawo ƙarar ɗan gida?" Cewar Tahir cike da mamaki.
"Menene haka Tahir, ba ka ga yarinya ba ce?" Salim ya faɗa yana hararar shi
“Ai lallai abun nasu da mamaki, na ga gaba ma yake ƙarawa kullum.” in ji Farida.
Shi kuwa kamar ma ba san da shi take yi ba, ko inda take bai kalla ba kanshi na ƙasa yana juya fork ɗin da ke hannun shi. Sai dai a ranshi ji yake kamar ya tashi ya maƙure yarinyar nan. Da sai abin da Allah ya yi. Shi kaɗai yasan yadda zuciyarsa ke tafarfasa.
Ita kuwa Haula gaba ta yi ta barsu kamar bata ji me suka ce ba, amma sun ci albarkacin Alhajin sama, har ta tafi sai kuma ta dawo ta ce,
''Yauwa Alhajin Sama ka ce mishi ya dinga sake fuska, wannan fuskar tasa idan ka ganta da dare ai sai ka ce gamo ka yi , ka zura a guje.'' Daga haka ta yi gaba ba tare da ta jira ta ji me Alhajin zai ce ba. Ita dai oho tunda ta san ya jita ai shikenan.
Salim kuwa dariya yake tayi ƙasa-ƙasa, gudun kada yayi laifi a wajen shi.
Yinƙurin tashi ya yi mommy ta riƙe hannun sa. Ya kalleta ta girgiza mai kai. Don ta san Alhajin ba zai barshi ya yi wani abu ba, amma za ta yi maganinta da kanta.
HAZ Group of Company
"Wai kai Habeeb me yasa kake min haka ne? Ya zan zo tun ɗazu ina maka magana amma kamar wani dutse ka yi min shiru ka mai da ni ɗan iska, lafiya kake kuwa?"
Bai ko ɗago daga abinda yake yi ba, balle ya sa rai zai ba shi amsa, da alama ma bai shiryawa hakan ba. Wani tunani ne ya gifta a kanshi. "Ooookaaaay, da alama dai yarinyar nan ta yi gaskiya, to ko ka dawo robot ɗin n....."
Wata zabura da yayi tare da dukan table ɗin da ke gabansa ne ya sa sauran maganar da Salim zai yi komawa bai shirya ba, a tsorace yake kallonsa don kam ya tsoratan sosai.
A zafafe ya fara magana cikin matsanancin fushi,
"Kana hauka ne Salim? Ta yaya za ka zo kana min zancen banza irin wannan? Wato haukar da ka manna min ɗazu bai isheka ba Ko? Shi ne ka biyoni nan don ka ƙarasa abinda ba ka gama ba Ko? Oya, stand up and get out!”
Zai yi magana ya katse shi, “I said get out!! I don't wanna see you beside me, so disappear from my face.”
Ya yi maganar a tsawace yana nuna mai hanyar fita.
“Ka ga ɗan'uwa ka saurare ni.”
Da ƙarfi cikin katse shi ya sake dukan table ɗin gabanshi ya ce, “I said get out Salim.”
“I can't.” Shi ma Salim ɗin ya faɗa cikin tsawa. Sai kuma ya nufi fridge da ke cikin office ɗin ya ɗauko ruwan gora, cikin lallashi ya ce, “Ka ga ɗan'uwa, sha ruwa sai mu tattauna.”
Buɗe baki ya yi da niyyar gardama, Salim ya tura mai goran ruwan a cikin bakinshi, ba don ya so ba dole ya sha. Sai da ya fara shan ma kafin ya ji ashe yana buƙata, don haka sai da ya kusan shanyewa kafin ya kau da kai gefe.
Salim ya riƙe shi ya zaunar da shi akan kujera yana faɗin “relax don Allah.” Ya yi maganar cikin tausasawa ga ɗan uwan nashi. Zaman ya yi ba musu ya jingina kanshi da jikin kujera ya lumshe idonsa yana ajiyar zuciya.
"Ka jira ni kada ka je meeting hall ɗin ina dawowa." Daga nan ya fice daga office ɗin, yana share hawayen tausayina ɗan uwan nashi. Ya san dama yana nan cikin tsananin ɓacin rai akan abinda Haula tayi mai, kuma ya san idan ya je wajen meeting ɗin a haka akwai matsala, shi ya sa ya zo shi ya sauke mishi duk fushin da yake ji ɗin shi akan shi. Da ma kuma haka ya ke yi ko bashi ya ɓata mai rai ba. Yakan je ya sauke mai fushin a kanshi, idan ba haka ba akwai matsala. Ya rasa irin wannan fushin, abin ya yi yawa. Tausayi na yake ba shi. Don har asibiti ya kai shi ba tare da kowa ya sani ba, amma haka suka dawo ba wani abu da aka ce shi yake saka shi wannan fushi, amma dai shi ma a lokuta da dama ba son ranshi yake wasu abubuwan ba.
Ya sake shafa kanshi a ranshi yana mishi addu'ar Allah Ya kawo mishi ɗauki akan wannan lamari. A haka nufi office ɗin shi saboda zuwa meeting don lokaci ya kusa 'Yan mintuna suka rage.