CHAPTER 3
by @deejasmah
Sosai jikinta ke ɓari wanda yayi dai-dai da bugawar zuciyar ta. A bakin ƙofar ɗaki suka yi karo da Khaleed da ihun ta ya fito da shi ya yana kiran sunan ta, ganin tana kakkarwa ne ya sanya shi isa gabanta yana maimaita kiran sunan ta. Sai dai ina ta fice a hayyacin ta, don idanun ta sun juye firgici da tsoro sun musu ƙawanya, riƙe ta yayi sai jin ta kuma cewa '' Wayyo na shiga uku'' tana fisgewa a tunanin ta ko abinda ya biyo ta bayi ɗazu ne ya riƙe ta.
''Nana, menene me ya faru?".
Jin muryar shi ya sanya ta duban shi natsuwa tana dawo mata tana nuna masa hanyar kitchen cikin rawar baki tace '' Ki.... Kit......chennnn.....Jiniiiiii''.
Yanda ta ja zancen ba ƙaramin tsorata shi yayi ba, don haka a zabure ya wuce kitchen ɗin. Dube-dube ya fara yi shi bai ga komai ba sai moɗar ruwan da ta yasar a ƙasa garin gudu, kai ya girgiza kawai yana kiran ta. Ko motsawa bata yi ba balle ta amsa masa kiran sai da ya gaji da jira ne ya taho da kan shi ya tisa ƙeyar ta zuwa kitchen ɗin yana duban ta yace '' Ina jinin yake a nan?".
''A nan ne fa, ga shi nan......'' maganar tata maƙalewa tayi ganin wurin wayam babu jini sai ruwan da ta kelayar a ƙasa. Kallon shi tayi bakin ta yana rawa tace '' wallahi fa a nan na gani, yana cikin wancan robar''.
Buɗe robar ruwan yayi babu komai ciki hasalima a bushe yake raƙau,murfin shi ma duk yayi ƙurar ajiya. Duban ta yayi cike da takaici yace '' wai amma akwai abinda yake damun ki ko? Tun jiya sai wani abu kike yi kamar shafin Jinnu. Me ya kawo ruwa cikin nan bayan a sanina ma baki zuba masa ruwa? Infact tun haihuwar ki ma ba'a yi amfani da shi ba''.
Ajiyar zuciya ta sauke tuno haihuwar da yake magana wacce yarinyar kwanan ta biyar a duniya ta koma ga mahaliccinta shekara guda da rabi kenan. Yawu ta haɗiye tana cewa '' Allah fa akwai ruwa a ciki, da kaina na gani fa''.
''To ai sai ki ɗiba ai, kin san dai ana jira na a makaranta''.
''Toh, yanzu zan saka maka ruwan wankar''.
''Yawwa, ki dafa tea ne kawai jira na shigo da biredi kar ki ce zaki yi wani abu rana tayi'' yana gama faɗin haka ya juya ya fita, ji tayi kamar tace ya tsaya amma ta san Khaleed ba zai taɓa tsayawa ya jira ta tana masa soki burutsu ba. A tsorace ta kuma buɗe robar farkon da ta fara buɗewa, yanzu kam kamar almara a cike yake da ruwa sai kawai ta ɗiba ta fara ɗauraye tukunya kafin ta ɗaura kan wuta.
Fita tayi ta fara sharan tsakar gida wanda yake daɗa faɗuwar gaban ta tuno yanda aka dinga yin shara da dare amma ta daure har ta ƙarasa duk da dai ta ƙi yarda ta shiga bayin tsakar gida gudun ta ga wani abun ƙi, komawa kitchen tayi ta juye masa ruwan a bokiti ta ɗaura na shayi wanda ya ji kayan ƙamshi ta sirka masa ruwan ta wuce da shi bayin ɗaki ta kai masa kana ta dawo tana shaida masa ta kai ruwan. Kallon ta yayi yana cewa '' To Allah yayi miki albarka bari in shiga'' ya miƙe zuwa ciki ita kuma ta fara gyaran ɗakin a gaggauce, kafin ya fito ta kammala don dama Khaleed akwai daɗewa a wanka kamar wani mai wankan jego.
Har ta jera kayan shayi kan kafet, kafin ya fito a shiryen shi tsaf cikin jumfa kalar ash na yadin Kashmir. Yayi kyau abun shi don dama Khaleed akwai iya wanka da gayu daidai matsayin shi, zama yayi ta haɗa masa tea a kofi kafin ta haɗa nata. Sai dai duk da yanda take jin yunwa ta gaza cin biredi sai ruwan zafi take ta aikawa cikin ta duk yana hankalce da ita bai tanka ba sai da ya kammala kafin ya dube ta yace ''Hala dai yau ba ki jin cin biredin ne?".
Ajiyar zuciya ta sauke ba tare da ta amsa masa tambayar shi ba sai cewa tayi '' Don Allah Yaya ina son zuwa gidan Uwale yau kar kace a'a''.
Duban tsanaki yayi mata yace '' gidan Uwale kike son zuwa shi ne kike ta yin wani abu haka? To ba yau ba ai na gaya miki ban da gaya min fita a ranar da kike son yin tafiyar in dai ba lalura ba ne''.
''Amma Yaya........''
''Na gama magana Nana, tunda kin faɗi yau sai ki jira in Allah ya kai mu gobe sai ki je'' yana faɗin haka ya miƙe ya suri jakar shi yana cewa '' Ni zan tafi''.
''Toh Yaya Allah ya tsare hanya ya sauke ka lafiya ''.
''Ameen, Jannah'' ya amsa cike da zolaya, wani sanyi ta ji jin sunan da ya kira ta da shi don rabon da ta ji shi a bakin shi tun farkon amarci tun da zama yayi zama shi ma ya koma Nana ko Firdausi kan shi tsaye. Don haka sai taji murmushi tana bin shi da idanu har ya fitar da mashin ɗin na shi ya fita daga gidan, rufe gidan tayi tana juyawa da nufin komawa ta ji ƙirjin ta ya bugi na wani.
Maƙalewa tayi jikin ƙofar gidan tana kallon ƙafafun da ke gaban ta wainda suke zubar da jini, duk da halin tsoron da suka sanya ta amma gwara mata su sau dubu kan ta dubi fuskar ko ma waye. Hannun shi da ke zuban jini ya miƙo yana shafa fuskar ta yana cewa ''Ameen Jannah!!!!!!!!".
Cikin muryar da ta kuma tsorata ta don ba mai kama da ta magen da aka kira ta da shi da dare ba ne, ba kuma shaƙaƙƙiyar murya ba ne ko na wanda ke daka mata tsawa ba. A'a wannan muryar Khaleed ne ba na kowa ba, duk da rawar mazarin da jikin ta ke yi haka ta lallaɓa ta raɓa shi ta wuce zuwa gida cike da jarumtar bata san tana da ita ba tana jin shi a bayan ta yana take mata kamar na sassafiya. Tattara kayan karin tayi ta fita da su waje da na jiya da dare su ma ta ja ruwa a rijiya ta fara wanke-wanke. Sai dai kamar jiran ta ake yi ta zauna masu taya ta aikin suka fara jan ruwa suna yi suna jefa guga kamar irin na rijiyar ƙauyen nan inda kowa ke saka gugan shi ya ja ruwa.
A haka dai har ta kammala ta shige ɗaki, wayar ta ta ɗauka tana kunna karatun Alkur'ani don ta ji an ce in ka ji irin haka ka kunna karatu sai ga shi kuwa yayi aiki don tsit ta ji an watse an bar mata gidan. Hakan ya sanya ta sakin numfashin sukunin da ya riske ta, fita tayi ta ja ruwa ta tara shi a robar kitchen da na bayi ta kuma gyara inda suka karya kafin ta shiga bayin don yin wanka ta bar wayar kan gadon ta.
Ta kammala cire kaya kenan ta ji motsi a bayan ta, dafe ƙirji tayi ta kai hannu ta buɗe ƙofar ko karatun da ake yi zai shigo ciki sai dai ji tayi karatun ya ɗauke sai wata halitta da ta gani ita ba a sama ba ita ba ƙasa ba gashi ya rufe mata fuska tana sanye da wasu fararen kayan da suka rine da jini. Da sauri ta koma bayan gidan ta watsa ruwa jikin ta ba tare da ta sa sabulu ba, ta ɗauro zani sai lokacin tsoron komawa ɗakin nata ya fara kama ta. Sai dai jin da tayi an kama ta ta baya ana shafa mata jiki ya sanya ta janyewa da gudu ta fita zuwa ɗakin.
Sai dai kuma ba'a ɗakin ta take ba, don komai ya sauya mata. Ganin wasu mutane zaune bakin gadon ta sun cike shi tsaf, ga kuma yarinyar ɗazu nan har lokacin tana in da ta bar ta. Suna haɗa Idanu ta ƙwalla kiran sunan ta ''Firdausiiiiiiiiii'' sunan yana amsa kuwa a cikin ɗakin, ƴan bakin gadon na taya ta. Yanzu kam kuka ta fashe da shi tana duƙawa wurin tana faɗin ''Ku bari, ku ƙyale Ni!!!!!!!!".
Amma ko jin ta basu yi sai ƙyalƙyale mata da dariya suke yi suna maimaita duk abinda ta faɗi, a yau kam ba suma take fata ya zo mata ba. Mutuwar ta take addu'ar ya riske ta a yanzu ko zata huta da masifar da yake damun ta amma babu dama sai ficewar hayyaci da ta riski kan ta ciki ta cusa kan ta tayi tsakanin guiwoyinta tana kiran sunan Allah a rai da kan harshen ta.
Sun ɗauki lokaci mai tsayi kafin komai ya ɗauke mata ɗif, da sauri ta tashi ganin babu kowa a ɗakin sai ita ɗaya. Miƙewa tayi da sauri ta buɗe sif ta janyo riga ba tare da ta duba ba ta sanya a jikin ta, ta ɗauko hijabi don ta rantse yau sai ta fita in ya so duk abinda Khaleed zai yi sai dai yayi amma ba zata zauna ta mutu ita ɗaya ba.
Katin ATM ta ɗauka da wayarta ta rufe ɗakin da makulli kafin ta nufi hanyar ƙofar gida sai ji tayi ana bugawa da ɗan ƙarfi, ja baya tayi tana cewa '' waye ne?".
Ba a bata amsa ba sai ma cigaba da buga ƙofar da aka yi, shahada tayi ta kai hannu ta zare sakatar jikin ƙofar tana buɗewa kuma jikin ta ya saki sakamakon wainda ta gani tsaye suna duban ta............