BA SO BANE?

Chapter 2

by @hafsatwaziri1122

BA SO BANE.
Story📃 writing
by

Hafsat waziri

Young talent writer's 

•Yota•


Page 2


Da ƙarfi ta buɗe ƙofar ofishin kamar wacce aka jefo. Sai a lokacin ne ta samu damar sakin kukan da ke cin ranta tun ɗazu. ta fashe da kuka mai tsanani, kamar ranta zai fita.
Suhairat data rakota sai ta taɓe baki. A fili ta ce'' kila budurwar sa ce'' ta juya ta koma bakin aikin ta. 
Yana zaune a kan doguwar kujera, hannunsa riƙe da gorar ruwa yana sha. Ya ji kukan nata kamar a mafarki. Kafin ya gama tantance ko mafarki ne ko gaskiya, sai ya ji ta faɗo jikinsa ta rungume shi gam, tana kuka mai tsanani. 
Bai ma san lokacin da ya mike tsaye har gorar ruwan ta kuɓuce daga hannunsa ta faɗi ba. Ya waro idanunsa cike da mamaki, firgici da tashin hankalin, ganin ta tana kuka haka ba ƙaramin abu bane. 
Karin abun mamakin ma shi ne ganinta anan Nigeria ita kadai. To yaushe ta da wo? Cikin Muryar mamaki ya ce'',.Mommy”
Ya ɗago ta kaɗan yana kallonta. Har yanzu kukan take yi ba ƙaƙƙautawa.
Ya sake cewa cikin matuƙar mamaki,
“Mommyn Daddy, ke? Ke da wa ye? Me ya same ki? Me ya sa kike kuka? Wa ya yi miki wani abu?”
Ya jera mata tambayoyi cikin ruɗani da tashin hankali.
Amma ita sai ƙara manne masa take yi tana ci gaba da kuka. Ya yi ta tambayarta, amma ta ƙi yin magana. Ganin haka, sai ya yi shiru yana shafa bayanta a hankali domin ya kwantar mata da hankali.
Can cikin sanyin murya ya ce,
“A duniya kin san babu abin da muka tsana kamar ganin kina kuka, ko?”
Cikin kuka ta kaɗa kai alamar eh.
Ya haɗiye wani yawu mai nauyi, sannan ya ce,
“To me ya sa kike kuka? Kina so ne ki ɗaga mini hankali?”
Da sauri ta girgiza kai alamar a'a.
Ya sake tambaya,
“To me ya faru?”
Sai dai ta yi shiru.
A hankali ya janye ta daga jikinsa, yana kallon kyakkyawar fuskarta da ta kumbura saboda kuka. Idanunta sun yi jawur, hawayen kuma suna ci gaba da zuba.
Nan take wani mugun fushi ya taso masa.
Cikin kaushin murya ya ce,
“Tun ba yau ba na yi miki alkawari. Ko dan idan uban wanene a cikin ƙasar nan, har ma da wanda ya fi shi iko, duk wanda ya kuskura ya taɓa ko da tsilin gashin kanki ne... Wallahi, wallahi, wallahi, sai dai uwarsa ta sake haifar wani, amma ba shi ba!”
Yana gama faɗar haka, sai ya ɗaga hannu ya share mata hawayen da ke kwaranya a fuskarta.
Daga nan ya kama hannunta na dama.
Nan take ta saki wani ƙara mai cike da azaba.
“Washh!”
Ta sake fashewa da kukan shagwaba.
Da sauri ya sake hannun nata yana kallonta cikin firgici. Sai idanunsa suka sauka a kan hannun. A nan ne ya lura da cewa ya ɗan kumbura kaɗan.
Take fuskar tasa ta sauya.
Idanuwansa suka yi ja ƙur, jijiyoyin kansa suka fito raɗau saboda tsananin fushi. A wannan lokacin, duk wanda ya yi sanadin hawayen da ke zuba daga idanun Mommy, ya riga ya sanya kansa cikin wata babbar matsala.


****

Unguwar ba ta daɗe da kafuwa ba, saboda haka ba ta cika da jama'a sosai ba. Sai dai duk wanda ya shiga cikinta zai fahimci cewa ba talakawa ko masu rufin asiri ne mazaunanta ba. Manyan gine-gine ne na alfarma ke jere a kowane gefe, wasu har yanzu ana ci gaba da kammala su, yayin da wasu kuma sababbin gidaje ne da ba a jima da tarewa a cikinsu ba. Titunan unguwar kuwa masu faɗi ne, tsaftatattu kuma cike da natsuwar da ake samu a wuraren masu hannu da shuni.
A hankali na ƙarasa gaban wani katafaren gida da ya zarce duk sauran gidajen da ke unguwar wajen haɗuwa. Ginin gidan ta sha fentin ash color mai ɗaukar ido, kuma tun daga ƙofar shiga zaka fahimci cewa an kashe maƙudan kuɗaɗe wajen gina shi. Ginin ya kasance irin na zamani, wanda Shashi ɗaya ne amma babba sosai mai cike da tsari mai kayatarwa da nuna ƙwarewar masu zanen gine-gine.
A tsakiyar harabar gidan har da wata babbar shatale-tale da ruwa ke fesuwa daga cikin wani abu mai kyalli, wacce hasken rana ke bugawa tana walƙiya tamkar madubi. A gefenta kuma motoci ne iri-iri na alfarma kusan goma a jere, kowacce tana nuna darajar mai ita. Wata ƙirar Benz mai launin purple mai matuƙar ɗaukar hankali ce ta fara ɗaukar idona, sai kuma wasu manyan motoci biyu masu launin milk color da suka yi matuƙar ƙayatarwa. Sauran motocin kuwa an lulluɓe su da rigunansu, alamar ba a son ƙura ko rana su taɓa su'' Wasu kyawawan mutane ne su biyar zaune a babban falon gidan, kowannensu zaune bisa kujerar alfarma. A ƙasa kuma, kan wani laushin kafet mai tsada, wasu yara ƙanana biyu—mace da namiji—na ta wasanninsu cikin walwala, ba tare da sun san irin tashin hankalin da ya mamaye manyan ba.
A gefe guda kuwa, wata babbar mata ce zaune cikin nutsuwa. Duk da cewa shekarunta ba za su wuce hamsin ba, damuwar da ke kwance bisa fuskarta ta sa ta yi kama da wacce ta ɗauki nauyin duniya a kafaɗunta.
A tsakiyar falon kuma wani dattijo ne mai cike da kamala da kwarjini yake tsaye. Daga kallonsa ka san mutum ne da ba zai haura shekaru hamsin da bakwai ba. Fuskarsa cike take da tsananin fushi yayin da yake kallon wani saurayi da ke zaune a gabansa. Dattijon yana sanye da fararen kaya garensa ta sha guga sosai haka malum-malum din dake sanya. Yana tsaye, 
Faɗa yake yi sosai kamar wanda zai ari baki.
Shi kuwa saurayin, kansa a sunkuye yake tamkar wani mai laifi da aka kama dumu-dumu.
Dattijon ya zura masa ido na wasu sakanni kafin ya ce cikin murya mai cike da ɓacin rai,
"Wannan ai maganar banza ce, Umar! Babba da kai? Da girmanka za ka aikata irin wannan sakacin? Kuma ka dawo kana tambayata ko ta iso?"
Ya ɗan yi shiru yana huci kafin ya ci gaba.
"Me ya sa ba ka je har Landan ɗin ka dauko ta da kanka ba lokacin da ta nace sai ta zo? Dama akwai wani uzuri da zai sa ka bar min ƴa ita kaɗai a cikin garin nan?"
Ya daga hannu cikin nuna takaici.
"Garin da babu cikakken tsaro! Ina ta sani?"
Umar ya ɗago kansa a hankali. Muryarsa cike da nadama ya ce,
"Don Allah Daddy, ka yi haƙuri. Ita da kanta ta roƙe ni cewa kada na faɗa muku zuwanta. Ta ce tana son ta yi muku bazata ne. Shi yasa ban fada maka ba, Kuma tun kafin jirginta ya sauka a Airport, na tura Ilya ya je ya ɗauko ta."
Kafin ya ƙarasa maganar, Daddy ya katse shi da tsawa.
"Sai na ci mutuncinka yanzu nan!"
Ya nuna shi da yatsa.
"Ni kake gaya wa ka tura Ilya direba ya ɗauko ta? Ina jami'an tsaron gidan? Me ya sa ba ka tura su ba? Me Ilya zai iya yi? Wani kariya zai iya ba ta? Ka kira wayarta yanzu nan mu ji tana ina!" Ya karasa yana jin zuciyarsa kamar zata fito waje,
Da sauri Umar ya ciro wayarsa daga aljuhu. Yatsunsa har rawa suke yi yayin da yake nemo lambarta ta Naijeria. Kamar yadda ya fada mata ta saka. Ya danna kira tare da ɗora wayar a kunne.
Nan take falon ya yi tsit.
Kowa ya mayar da hankalinsa kansa.
Har yaran da ke wasa a ƙasa sun dakata suna kallon manyan da idanunsu cike da damuwa.
Bayan wasu sakanni, Umar ya sauke wayar a hankali. Ya ɗago idanunsa ya kalli Daddy wanda ke tsaye a kansa yana jiran amsa.
A sanyaye kamar zai fashe da kuka ya ce,
"Daddy... wayarta a kashe, amma ɗazu na kira ya shiga bata ba ta ɗau..."
Kafin ya ƙarasa, Daddy ya fizge wayar daga hannunsa.
Jikinsa har rawa yake yi.
Da kansa ya sake danna lambar.
Sai dai abin da ya ji shi ne abin da Umar ya faɗa.
Wayar a kashe take.
Wani irin sanyi ne ya ratsa zuciyarsa.
Fuskarsa ta sauya gaba ɗaya.
A karo na farko tsoro ya bayyana ƙarara a idanunsa.
Cikin tashin hankali da kiɗimewa ya juya ya kalli Umar.
Muryarsa ta yi ƙasa, amma cike take da razana.
"Umar..."
Ya kira sunansa a hankali.
Sai kuma ya haɗiye yawu da ƙyar kafin ya ce,
"Idan har wani abu ya samu ƴata..."
Ya dakata, zuciyarsa na bugawa da ƙarfi.. Hajiya ta mike da sauri ta zo wajen da su ke cikin kyakkyawar shigarta. Sanye take cikin wata doguwar riga ta shadda mai launin ruwan madara da aka yi wa ɗinkin zubu, yayin da ta ci wani dauri kamar zata wajen biki. Duk da kyan da ta yi, damuwa ce ƙarara ta mamaye fuskarta, har ma hasken murmushin da aka saba gani a tare da ita ya gushe gaba ɗaya.
Ta kalli mijinta da idanun da suka cika da fargaba, sannan cikin sassanyar murya mai ɗauke da rawar damuwa ta ce,
"Alhaji, don Allah ka yi haƙuri. Ka kwantar da hankalinka. In sha Allah babu abin da zai faru da ita. Ai..."kafin ta ƙarasa maganarta Alhaji Umar ya katse ta da sauri. Ya juyo gare ta da idanunsa da suka yi jajir saboda tsananin tashin hankali. Fuskar nan tasa ta sauya gaba ɗaya, a ɗan kankanin lokaci ta rasa nutsuwar da aka san shi da ita. A bayyane yake cewa damuwar da yake yi wa 'yarsa ta mamaye dukkan tunaninsa.
"Na kwantar da hankalina kika ce, Zainab?" Ya faɗa cikin ɗaga murya. "A irin wannan yanayin kike cewa na kwantar da hankalina? Shin kin manta ne ko kuwa baki fahimci abin da ke faruwa ba? Idan shi bai sani ba, ai ke kin sani! Idan kuma kin manta, to ya kamata yanzu ki tuna!"
Ya yi shiru na ɗan lokaci yana jan numfashi da ƙarfi. Zuciyarsa na tafarfasa da damuwa. Duk wanda ya san sa to dams ya san babu abin da yake so a duniya kamar 'yarsa. Ita ce farin cikinsa, ita ce sarkin ƙaunarsa. Saboda haka, duk wani abu da ya shafe ta kan girgiza masa zuciya fiye da yadda kowa zai iya zato.
Nan take ya juya ga ɗaya daga cikin masu aikin gidan da ke tsaye a gefe, wanda tun ɗazu ya kasa ko motsi saboda tsananin fargabar da ta mamaye falon.
"Ka kai!" Alhaji Umar ya kira shi cikin murya mai cike da umarni. "Tashi ka je ka kawo min 'yata. Yanzu nan take!"
Muryarsa ta daki bangon falon kamar tsawa. Nan take mutum ya yi saurin sunkuyar da kai cikin girmamawa.
"To, Alhaji," ya amsa da sauri, kafin ya juya ya fice kusan a guje.
Sauran masu aikin gidan kuwa suka tsaya cikin yanayin damuwa da firgici. Kowa ya san irin matsayinta a zuciyar Alhaji Umar. Sun sha ganin yadda yake sauya gaba ɗaya idan wani abu ya taɓi 'yarsa. Wannan ne ya sa babu wanda ya kuskura ya yi magana ko ya ɗaga kai. Falon ya yi shiru tamkar babu mai rai a cikinsa.
A gefe guda kuma, Hajiya Zainab ta yi shiru. Ta matse gefen mayafinta cikin tafin hannunta yayin da zuciyarta ke bugawa da ƙarfi. Ta yi ƙoƙarin kwantar wa mijinta hankali ne, amma ita kanta zuciyarta cike take da fargaba. Tunani iri-iri suka fara shawagi a ranta, yayin da addu'o'i kawai ke fita daga zuciyarta.

Company 

Tana zaune a kan kujerarsa, shi kuma yana tsugunne a gabanta, riƙe da hannunta mai ciwo yana shafawa a hankali tamkar wani abu mai daraja da yake tsoron ya lalace.
Suna cikin wannan yanayi na ɗan lokaci kafin aka fara knocking ƙofar office ɗin.
Fahad ya ɗago kai, sannan ya miƙe tsaye.
"Yes, shigo."
A hankali aka tura ƙofar aka shiga. Kallo ɗaya za ka yi masa ka gane likita ne. A hannunsa akwai ƙaramin akwatin kayan aiki.
Ya ƙaraso ciki yana kallon hannun mommy da ke zaune kamar wacce aka tilasta wa zama.
Da murmushi likitan ya ce,
Sannu bari in duba hannun."
Shiru ta yi kamar ba da ita ake magana ba.
Likitan ya sake matsowa kusa da ita.
"Ki bani hannun."
Da ƙyar ta buɗe idanunta ta kalle shi. Da zarar ya kai hannu zai taɓa wajen da ya kumbura, sai ta fizge hannun da sauri.
Idanunta na nuni da yadda zuciyar ta ke tafasa"
Ta yi ƙaramar ƙara tare da haɗe gira tana kallon Oga.
"Yana min zafi."
Likitan ya ɗan yi murmushi.
"To shi yasa ma zan duba."
Da ƙyar Fahad ya kamo hannunta ya miƙa wa likitan.
Sai dai da zarar likitan ya taɓa wajen, ta sake fizge hannun tana hararar su duka biyun.
"Na ce yana min zafi!"
Muryarta cike take da fushi da takaici.
Fahad ya lumshe ido na ɗan lokaci, sannan cikin sassanyar murya ya ce,
"Please, mommy. Ki bari ya duba."
A karo na uku ne likitan ya samu damar binciken hannun.
Bayan ya gama dubawa ya gyara tsayuwarsa yana kallon Fahad.
"Ina ganin buguwa ce kawai. Ba wani babban abu ba ne sosai."
Fuskar Fahad babu alamun wasa.
"Zuwa yaushe zai warke?"
Likitan ya buɗe akwatin nasa ya ciro wasu magunguna guda biyu.
"Ta sha waɗannan."
Da ya ga magungunan, Fahad ya yi saurin girgiza kai.
Ya san sarai cewa a duniya bayan kifi da allura, babu abin da take tsana kamar magani.
"Ka ba ni wani abu dabam."
Likitan ya mayar da magungunan, sannan ya ciro wani maganin shafawa.
"To, a riƙa shafawa a wajen."
Nan take Fahad ya karɓa.
Likitan ya yi musu sallama ya fita.
Da zarar ya fita, Fahad ya sake tsugunnawa a gabanta. Ya buɗe maganin shafawar, ya zuba kaɗan a tafin hannunsa sannan ya fara shafawa a wajen ciwon cikin kulawa sosai.
Idanuwanta a rufe suke.
Ba abin da ke zuciyarta sai wutar son ɗaukar fansa.
Fansa a kansa.
Fansa a kan duk ma'aikatan company ɗin.
A hankali ta buɗe baki.
"Na kori ma'aikatan wajen nan."
Ta buɗe idanunta tana kallonsa kai tsaye.
"I mean... now."
Mamaki ya bayyana ƙarara a fuskar Fahad.
Ya buɗe baki zai yi magana, amma ta katse shi.
"Now."
Ya kalleta na ɗan lokaci kafin ya ce,
"Okay."
Ya miƙe ya ɗauki wayarsa.
Zai kira ne sai kuma ya fasa.
A hankali ya ajiye wayar.
Sannan ya zagaya zuwa ɗayan gefen table ɗin.
Ya miƙa hannu ya danna ƙararrawar da ke kai.
Nan take wani ƙara ya cika office ɗin.
Ba a wani daɗe ba aka buɗe ƙofar da sauri.
Wata ma'aikaciya ce ta shigo da sauri kamar za ta faɗi.
Fahad bai ko kalle ta ba.
Ya ce,
"Ki tattaro duk ma'aikatan company nan. Ina son ganin kowa a babban hall yanzu-yanzu."
Mamaki ya bayyana a fuskarta.
Sai dai ta amsa da,
"Okay, sir."
Ta juya da sauri ta fita.
Fahad ya sauke numfashi mai nauyi sannan ya juya yana kallonta.
A gefe guda kuma, ita ta miƙe tsaye cikin isa da ƙasaita.
A ganinta ma hukuncin da ta shirya yi musu bai kai girman abin da suka mata ba.
Fahad ya ƙaraso gabanta da murmushi mai laushi.
"Amma dai ba har da ni za ki kora ba ko?"
Ta ɗaga ido ta kalle shi.
Ba ta ce komai ba.
Shirun da ta yi ya fi kowace amsa nauyi.
Ya kamo hannunta a hankali.
Suka nufi babban hall ɗin.
Ita ce ta fara shiga.
Gaba ɗaya ma'aikatan suna ciki.
Ko da suka hango ta, hakan bai hana su ci gaba da hira da dariyar da suke yi ba.
Sai dai da suka ga ba wajen zaman baƙi ta nufa ba.
Ba kuma wajen da aka saba zaunar da ita ba.
Kai tsaye ta nufi kujerar CEO.
Ta zauna a cikinta cikin cikakkiyar izza da iko, tamkar sarauniya da ta hau karagar mulki.
Ta ɗora ƙafa ɗaya kan ɗaya.
Ta jingina bayanta da kujerar.
Ta kuma ɗora yatsunta a gefen bakinta.
Nan take hayaniyar wajen ta mutu.
Hall ɗin ya yi tsit kamar ba kowa a ciki.
Idanuwanta masu cike da tsananin fushi suka ratsa fuskar kowa da kowa.
Babu sassauci.
Babu tausayi.
Babu rahama.
Cikin sauri ta fara kai idanuwanta ko'ina.
Tana neman mutum guda ne.
Shi take son gani kafin komai ya fara.
Amma babu shi.
Ba ta gan shi ba.
Ba kuma ta ga wata alamar zuwansa ba.
Sai zuciyarta ta fara tafarfasa cikin fushi.
Domin mutumin da take nema... shi ne farkon wanda take son fara hukunci a kansa.✍️✍️