BABI NA BAKWAI
💎🌹 Haula Habeeb🌹💎
Story Written By
Amdeey Tejj d'Unique ✍️
BABI NA BAKWAI
Mami
“Hajiya Salamatu, ban san yadda zan yi ba. Hashi ta na son sai na nuna mata asalin iyakarta tukun. Da alama a wancan karon ba ta horu ba, amma wannan karon zan nuna mata ita ba komai ba ce, face ƙaramar alhaki daga ita har mijin nata. Kin san makaho bai san ana kallon sa ba sai an zungure shi.” Ta yi maganar cikin huci da zafi kamar Hashi ɗin ce a gabanta.
Kallonta Hajiya Salamatu ta yi, kallon neman ƙarin bayani, kafin ta ce, “To me ya faru kuma? Kin san ba na ƙasar, tunda na tafi kuma ba mu yi magana ba. Wani makircin ta ta sake yi halan?”
“Batun haɗin auren nan ne. A wannan karon ma ta sake maimaita abin da ta maimaita wancan karon. Wai a gabana, bayan an yanke hukuncin auren Habeeb da Nabila, Hashi ko kunyar idona babu, ta ce wai sai dai a haɗa shi da wannan fanɗararriyar yarinyar, ’yar wajen Ummi. Su kuma da yake munafukai ne, daga mijin nata har ’yan uwan na shi, a rasa mai yi mata musu. Duk sun yarda da abin da ta ce, kamar wata uwar su. To ni wallahi ba zan yarda ba, sai na ɗau mataki.” Ta faɗi cike da ɓacin rai, a ranta tana saƙa irin abin da za ta shirya musu gaba ɗaya su.
Dariya Hajiya Salamatu ta yi, kafin ta ce, “Hajiya Zaina kenan. Ai ba ki ga komai ba tukun. Na gaya miki cewa don kin kulle wancan ƙofar, ba shi yake nufin an gama ba. Don ita ma ba zama za ta yi ta zuba miki ido ba. Ki zo mu koma wurin boka kin ƙi, ke a dole ga ta Allah. Makircinki kawai zai kai ki inda kike so. Kin ci moriyar boka, kin yar da shi a kwandon shara tunda buƙata ta biya, wa ya gaya miki haka ake yi yarinya? Hahaha, hmmm, Allah ya kyauta. Amma ita ɗayar munafukar me ta ce?”
“Wa? Wai Safina. Rabu da munafuka, wannan wa yake sanin cikinta? Ai daga ita sai hanjinta. A fuska kamar Allah, amma wallahi ta ci uwar mu makirci. Ita ma zan biyo takanta, bari in fara gamawa da waccan tukun.”
Sauke numfashi Hajiya Salamatu ta yi. “Yanzu ba waɗannan surutai ba, me ya sa kike yin haka? Me ke tafe da ke? Don wannan zancen ba abin da zai yi mana amfani ba ne. Kar mu yi sanyin yi, mu yi abin da ya dace mu yi. Kin san da zafi-zafi ake dukan ƙarfe, ga shi kuma ba mu da isasshen lokaci.”
“Wurin bokan nan za mu je. Ni idan akwai wanda aikinsa ma ya fi na shi zafi, wurin za mu je. Sha yanzu magani yanzu.”
“A’a fa, ta inda aka hau ta nan ake sauka. Tunda dai mutumin nan bai gaza ba, ke kika gaza, kika guje shi bayan buƙatarki ta biya. Dama ya ce in aure bai kawo ki ba, shi ma zai kawo ki, kuma ga shi.” Hajiya Salamatu ta yi maganar tana watse hannu.
Tsaki ta yi ta ce, “Ke ni fa kada ki dame ni, ba ga shi zan je ba.”
“Dama ya faɗa ai, akwai lokacin da za ki zo.”
“Malama, idan za ki tashi mu tafi ki tashi, kin ishe ni fa.” Daga haka ta miƙe daga bakin gadon Hajiya Salamatu da take zaune, tana saɓar mayafinta. Ita ma Hajiya Salamatu haka, suka fice suna tattauna lamarin.
HAZ Group of Company
Habeeb
Iska ya fesar daga bakinsa mai ɗumi. Ya sa hannu ya tattare sumar da ta zubo masa a kan fuska har ta rufe ido. Ya sake labulen da ya yaye yana hangen mutanen da ke yawo a harabar ma’aikatar. Cikin office ɗin ya dawo, ya nemi wuri ya zauna a kan kujerar da ya tashi. Lumshe ido ya yi ya kwanta a jikin kujerar tana juyi da shi sannu a hankali. Shi duk komai ma ya ishe shi. Tun maganar da Daddy ya kira shi a kai last week ya yi masa a kan batun wai sun saka masa rana. Yau ma batun da ya kira shi a kai kenan, wai an buga invitation card, tunda ya ga da alama shi ba ya ɗaukin bikin, ya ga alama ba komai zai yi ba. To idan ya tashi a wurin aiki ya zo ya karɓi nashi, shi y ya rasa dalilin da ya sa ake mai haka. Kuma wai matar ma sai an zaɓar masa. Duk wannan ma ba shi ya dame shi ba. Duka-duka, yaushe aka yi waccan? Har sun sake samo wata, ko da wa kuma wannan karon za a haɗa shi, oho. Shi dama za su bar shi da wani maganar aure da ya fi mishi. Shi bai ga dalilin wannan hanzarin da ake yi ba. Haka kawai su jawo masa raini a wurin yara. Wa ma ya san halin yarinyar? Haka kawai Haula ta faɗo masa a rai. To idan mai irin halinta ce fa? Wani sabon haushi ya sake ƙume shi, ya ja tsaki a fili. Ga shi ba zai iya musu ko jayayya da su ba, don ba su taɓa yanke hukunci a kan sa ya ce musu a’a ga nashi ra’ayin ba. Kawai dai hukuncin da ya yanke shi ne, ba ruwansa da ko wacece aka aura masa. Zai yi huruminsa, tana nata. Idan ma zai kula da ita, sai ya ga kamun kai da natsuwarta tukuna.
Sautin da ya ji a fuskar sa ne ya sa shi buɗe ido. Ya kai dubansa ga wanda ke tsaye gabansa, Salim ne.
Ya ɗage masa gira ɗaya alamar tambaya bayan sun haɗa ido. “Me kake tunani haka har ba ka san na shigo ba?”
“Ouuuufff,” ya furzar da iska daga bakinsa, kafin ya ɗago daga kishingiɗen da yake.
Shi kuwa Salim ya samu wuri ya zauna kan ɗaya daga cikin kujeru biyun da ke fuskantarsa. “Ba ni labari, me yake faruwa?” ya tambaya.
Sai da ya dube shi kafin ya ce, “Ɗan’uwana,” ya kira Salim ɗin da asalin sunan da yake kiransa da shi tun suna yara.
Shi ma Salim ɗin kallonsa ya yi ba tare da ya ce komai ba.
“I don’t know the reason why Daddy wants to get me married. Na rasa dalilin wannan saurin. Duka-duka, yaushe ne aka yi waccan? Yanzu kuma an sake dawowa da wani batun. Gaba ɗaya na rasa ma abin yi. Yanzu fa kirana ya yi, wai idan na dawo in zo in karɓi invitation card.”
Dariya Salim ya yi, zuciyarsa cike da mamaki. Aure kuma? Ya tambayi kansa a cikin zuciyarsa, don shi bai ma san da labarin ba sai yanzu. Shi ma dai abin ya ɗaure mishi kai. Kuma a ɓangare ɗaya zuciyarsa na rawa. Amma saboda ya kwantar wa ɗan’uwansa da hankali, sai ya ce,
“To shikenan, tunda ba ka so, kuma kana jin kunyar Daddy ba za ka iya faɗa masa ba, ni zan faɗa masa. Shikenan ka daina damuwa.”
Wani kallo ya yi masa, shi kuwa me zai yi in ba dariya ba? Dama ya faɗa ne don ya ji me zai ce.
“Hmmm, Bro kenan, ana so ana kaiwa kasuwa,” ya faɗi cikin zolaya.
Banza ya yi masa, bai ce komai ba. Dama shi ma ya san ba wani abin zai ce ba.
“Ka ga Malam, in za ka ware, ka ware ka ba mu hanya. Yauwa don ba za mu zauna zaman gwauranta irin naka ba. Ni ina jira ka matsa ne in yi. Tahir ma haka. Ba kamar ni ba, don ba don jiran yarinyar ta ƙara girma ba, da an wuce wurin. Kwa zo daga baya. Da ni ne Daddy zai min wannan auren, gatan da ka ga kauɗi! Hmmm, ni bari in je in karɓi invitation card ɗin ma duk in raba.”
Kallon sa dai yake yi, bai ce komai ba. Shi haushi ma ya fara ji, yana yi masa magana serious, amma yana mai da ita shirme.
Shi kuwa kamar an tsunkule shi, ya sake cewa, “Taɓ, lallai Man, kana so ka yi mana baƙin ciki. A ce bikin C.E.O na HAZ Group of Company gaba ɗaya za a yi a, amma shiru, no event and everything. Gaskiya no, dole mu...”
Habeeb ya katse shi da faɗin, “Hey Mr. man, behave yourself! Ban kira ka nan for all this nonsense ba, so forget about it and get focused on abin da na kira ka a kai.” Cikin kamewa da nuna alamar ba wasa ya yi maganar.
Ɗage kafaɗa Salim ya yi, kafin ya ce, “Okay, ina jinka.”
“Magana ce a kan wannan file ɗin, na ga an kore shi a aiki. For what reason nake son ji? Sai batun wannan ɗagewar, ina so in san waye ya sa aka yi hakan?” Ya haɗe hannayensa a kan teburin gabansa, yana jiran amsar Salim.
“Maganar wanda aka kore shi a aiki ba wani abu ba ne, saboda abin da ya faru ranar ne shi ya sa na sallame shi. Saboda na san akwai abin da ya yi maka ne, don duk da kana cikin ɓacin rai ba za ka ɗau mataki haka kawai ba, shi ya sa na kore shi. Batun postponement kuma, wai umarni ne daga Daddy. Duk da shi ma ba ni da tabbaci a kan hakan, tunda har yanzu ba mu yi magana ba. Ni fa abin ya ba ni mamaki.” Don shi ma ɗin wannan sanarwa ta ɗaure masa kai. Ta yaya za a ce an ba da umarnin dakatar da abu mai muhimmanci, amma shi kansa C.E.O na kamfanin bai sani ba, ba ma hannunsa a ciki.
Ya ɗauki file ɗin wanda aka kora daga aikin ya miƙa masa, yana faɗin, “Wannan ka ga, ka dawo da shi aiki. Ban ce a kore shi ba, don ba mu kama shi da laifin da za mu yi masa haka ba. Sannan ina so zuwa jibi ka haɗa min taron mahukunta kamfani, kuma kowa ya zo, tun daga na cikin garin nan har waɗanda suke wani gari, kowa ya zo.” Yana gama faɗin haka ya fara tattara ƙananan tarkacensa don tafiya zai yi, yanayinsa yana ɗan ciza baki na yadda kansa ya ɗan yi masa ciwo saboda doguwar maganar da ya yi.
Salim ya miƙe tsaye hannunsa riƙe da file ɗin, ya ce, “To, shikenan za a yi yadda ka ce. Duk da ni dai ban so dawowar shi wurin aikin nan ba.”
Bai ce komai ba, don ya gama magana shi kam. Tare suka fito shi da Salim ɗin. A third floor suka rabu, kowa ya kama hanyar inda zai bi..
HAZ Mansion
Yanke kiran aka yi daga can. Sororo ta bi wayar da kallo, jin ya katse kiran. Ta ciza leɓe, a ranta tana faɗin, wato har ni za ka katse wa kira ko? Kada ka damu, lokacin ka ne. Amma za ka yi bayani. Bari amfanin ka ya ƙare, lokacin ne za ka banbance fari da baƙi. Ta yi tsaki, ta wurgar da wayar a kan gado, ta sauka main parlour. Zama ta yi, har ta ɗauki remote ta kunna TV, sai kuma tunanin abin da suka tattauna da Smart ya faɗo mata. Ta yi tsam tana tunani. Ana faɗin saura sati ɗaya aure, ga shi ba ta san inda ta dosa ba. Har yanzu ba wani kyakkyawan sakamako da ta ga yana tunkaro ta. Ta ɗan yi shiru tana tunani. Taɓ, akwai matsala, kada birnin kusa da ya koma nesa, irin nesan da ko gudun jirgi ko mota ba za su cimma mishi ba, bayan ta ci uwar tafiya a cikin duhun dare.
“Kai, never, ba zai yiwu ba,” ta furta a fili. Ta yi shiru, ta hau zagaye a parlour kasancewar ba kowa a ciki. Lallai fa Smart yana da gaskiya. Komawa ta yi ta zauna, ta buɗe wani sabon babin tunani.
Haula ce ta shigo riƙe da kayan tarkacen abinci a hannunta. Ta ƙarasa jikin dining ta hau jera komai a mazauninsa.
Ita kuwa kallon ƙurulla ta hau bin Haula da shi, kamar yau ta fara ganinta. Nan wani tunani ya fara clicking a cikin kanta. Ta ɗan yi murmusa duk da akwai sauran doubt a zuciyarta, amma ta samu ɗan sauƙi kaɗan.
Ita kuwa Haula ba ta san ma tana yi ba.
*****
Mami
Durƙushe suke a gaban bokaye, duk sun russuna da kai kamar za su yi sujada, ko masu neman gafara.
Ya bushe da wata irin mahaukaciyar dariya mai amsa kuwwa, kafin ya ce, “Na sani ai, na san za ki dawo. Ke kina ganin kin gama da waccan matsalar ko? Kina ganin shi ke nan amfaninmu ya ƙare ba?” Ya ƙarashe maganar da wannan dariyarsa tasa.
Ta sake gyara zama, ta yi ƙasa da kai tana faɗin, “A yi haƙuri Boka. Mun yi kuskure, amma a yi haƙuri, ba za mu sake ba.”
Ya gyara zama yana dubansu, ya ce, “Kin zo ne a kan batun auren da za a sake yi wa wannan yaro ko?” Ya yi da sigar tambaya.
“Eh, so nake a juya lamarin don in nuna mata iyakarta,” cewar Mami.
Dariyar dai yanzu ma ya yi. “Tun kafin ki zo, na san za ki zo da kuma abin da zai kawo ki. Ki sani, tabbas za a ɗaura auren nan, tabbas ba fashi. Sai dai za a samu matsala, abin zai zo ba yadda aka zata ba. Sai dai na hango matsalar, don an rufe ta. Abu ɗaya na sani, za a ɗaura auren tabbas, amma akwai matsala. Kuma ba za a ɗaura da ’yarki ba kamar yadda kike buri, don ba ta da rabon aure da shi har abada. Sai dai akwai abin da za mu iya yi.”
Mami za ta yi magana, Hajiya Salamatu ta mintsile ta, tana yi mata alamar ta yi shiru.
Hajiya Salamatu ce ta ce, “To Boka, a yi abin da ya dace kawai.”
Sai da ya yi ’yan tsubbace-tsubbacensa, kafin ya ba su wasu abubuwa da layoyi da yadda za su yi amfani da su. Suka zube masa kuɗi, suka fice, Hajiya Salamatu tana yi masa godiya.
Mami kuwa da take cike da shi har wuya, don haushin cewa da ya yi, wai ’yarta ba ta da rabon aure tsakaninta da Habeeb har abada. Ta ja tsaki bayan sun daidaita motar su ta ɗau hanya.
“Ni fa shi ya sa na tsani wannan mutumin wallahi. Na ce miki kada mu je wajensa, ɗan iska kawai maƙaryaci. Idan ba haka ba, ta yaya zai ce mini wai Nabila ba ta da rabon aure da shi har abada? Sai ka ce shi ɗin Allah ne. Ki ji min ɗan abu ta kazan uba ko!” Ta ƙarashe maganar da wata ƙwafa da zagi mai nauyin faɗa a baki.
Dariya Hajiya Salamatu ta bushe da shi har dukan sitiyarin mota. “Ke da kika san shi ba Allah ba ne kuma kika je kika yi masa durƙuso kamar mai neman rahama? Da ƙaryar tasa dai ya yi miki amfani.”
Tsaki ta yi tana harararta. “Dallah Malama, kar ki ɓata min rai. Wai ina kike shirin kai mu ne?”
“Gida mana, ko akwai wani abu ne?”
“Gida kuma? Gaskiya a’a. Ai tunda muka fito, to fa sai mun tarar da sa’a.”
“Kamar yaya?” ta tambaya don ba ta gane ba.
“Kamar yadda kika ji. Wani wurin za mu ai. Ke dama nufinki in koma in naɗe hannu ina kallon su? Taɓ!” Ta yi tana girgiza kai.
Ba tare da ta duni ɓangaren da take ba, ta ce, “To, amma ba ki ji abin da Boka ya ce miki ba ne?”
“Ke dallah, raba ni da wannan tatsuniyar. Wannan zancen ai hankali ma ba zai ɗauka ba.” Ta yi maganar tana taɓe baki.
To kawai Hajiya Salamatu ta ce, tana karya kwana a kan motar zuwa wata kwana.
Sai da suka je wurare har uku, amma duk maganar iri ɗaya ce: za a yi auren amma ba yadda aka shirya ba, kuma ba aure tsakaninsa da Nabila. Sai da suka je wurin wani Malami, shi ma ganin idanunta ya rufe, kawai burinta ya tabbatar da za a yi auren. Ya sa ya ce mata akwai hanyar da za ta sa auren ya tabbata. Ai ko ta yi masa ɓarin kuɗi. Ya ba ta wasu ƙulle-ƙulle, ta karɓa, suka fito cike da murna. Ita kuwa Hajiya Salamatu kallonta kawai take yi, don ta san ya ci kuɗinta ne kawai.
Salim
Tare da Habeeb suka dawo. Sai da ya raka shi har side ɗinsa, ya kai masa jakar har parlour. “Man, in za ka nemo sabon P.A, ka nemo. Na gaji da kullum sai na kawo maka jaka.” Salim ya faɗa bayan ajiye briefcase ɗin a kan centre table.
Zama ya yi, ya kalle shi kafin ya ce, “Dama ni na sa ka?”
“Ohh! Haka ma ka ce? Kai fa tsabar samun wuri, ko ka dawo ba ka barin security ya ɗauko ma jaka. Ko ba na nan sai ka jira na dawo in ɗauko. Yanzu kake cewa ba ka sani ba ko? Shikenan, an yi final. Idan za ka nemo P.A ka nemo, idan kuma a’a, ni na gama, tunda dama rawan kaina ya kai ni.” Ya miƙe ya nufi ƙofa.
Shi kuwa ko kula shi bai yi ba, kamar ba da shi yake yi ba. Ya gyara zama ya jingina bayansa da jikin kujerar da yake, ya lumshe ido don a gajiye yake.
Ficewa Salim ya yi, don dama ya san ba kula shi zai yi ba. Ciki ya nufa, kai tsaye ɗakinsa ya nufa, don ta ƙofar baya ya shiga. Sai da ya yi wanka ya fito, jallabiya ya sa don ba inda za shi, yana da aikin da zai yi. Fita ya yi ya nufi side ɗin Daddy. Zaune ya same shi kan kujera yana shan tea yana kallon labarai. Ya ɗago suka haɗa ido, ya sakar mishi murmushi bayan ya amsa sallamar da ya yi.
“Babana kaine?” Daddy ya faɗa fuska a sake yana murmushi.
Wuri Salim ɗin ya samu daga ƙasa gefen ƙafar Daddy ya zauna, kafin ya amsa da, “Eh Daddy, ni ne. Barka da yamma, an wuni ƙalau?” Ya gaishe shi.
Amsawa ya yi, kafin ya tambaye shi, “Ina ɗan’uwanka? Ya aiki?”
“Yana sashensa, tare muka dawo. Aiki Alhamdulillah.” Ya ba shi amsa.
“To, Allah ya taimaka. Na fahimci sam ba ya son zaman cikin gidan nan. Kullum yana can shi kaɗai, ko kewar mutane ba ya yi.” Don abin Habeeb yana ba shi mamaki har yana mamakin yadda yake attending mutane a office, a ce mutum ba ya son zama cikin mutane, yana mamakin yadda mutum zai rayu a haka.
Ɗan dariya Salim ya yi, ya ce, “Daddy, wannan ai ba sabon abu ba ne indai Bro ne. Kuma ka lura, dawowarsa daga ƙasar waje abin ya fi ƙaruwa. Don a da ne ma yake ɗan shiga mutane kaɗan, to da yake can yawanci kowa damuwar gabansa yake yi, shi ya sa abin ya fi ƙaruwa.”
Jinjina kai Daddy ya yi alamar gamsuwa. “Ƙwarai, ni ma na gane hakan.” Hira suka yi sosai, sun jima suna yi, kafin Salim ya shigo da batun maganar auren. Nan ma suka tattauna a kai. Salim ya ce shi za a ba invitation card ɗin ba Habeeb ba. Daddy bai yi musu ba, ya ba shi. Tare suka fita sallar Magariba a masallacin gidan.
A daren Salim ya fara tsare-tsaren biki na dinner da sauransu. Invitation card kuma saboda lokaci ya ƙure, ya san wani ma sai daga baya zai tuna da shi, ya sa ya yi posting a duk social media platforms ɗinsa, tun daga kan Facebook, WhatsApp, Instagram, X (Twitter), Pinterest da sauransu. Daga haka ya taɓa aikin office kaɗan ya kwanta. Ya lalubo hoton abar ƙaunarsa a cikin wayarsa ya kalla, kamar yadda ya mayar da shi al’ada a kowane dare kafin ya kwanta.