DU’A (The Unwanted Daughter )

CHAPTER 1: The Girl no one wanted

by @hauwajaywrites

#REPOSTING 2021



بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيمِ


CHAPTER ONE


Around 4:30 a.m…


Cikin tsananin shiru da ya mamaye gidan, ƙofar ɗakin Du’a ta buɗe da ƙarfi.


Without a second thought, Mummy ta ƙarasa bakin gadon da Du’a ke kwance cikin nannauyan bacci. Ta buɗe butar ruwan sanyi da ke hannunta, ta watsa mata gaba ɗaya.


“Ahhh!”


Du’a ta miƙe zaune in panic, zuciyarta na bugawa da sauri yayin da jikinta ke rawa saboda sanyin ruwan.


Kafin ma ta samu damar fahimtar abin da ke faruwa, Mummy ta fara zazzaga mata masifa.


“Kin san ƙarfe nawa ne? Is this the time you’re supposed to wake up? Kin san irin tarin aikin da ke jiranki kuwa?”


Da sauri Du’a ta sauko daga kan gadon, ta haɗa hannayenta cikin roƙo.


“Mummy, I’m so sorry… Please pardon me. Wallahi ba da gangan na yi bacci ba.”


Sai dai roƙonta bai rage ko da kaɗan daga cikin fushin Mummy ba.


Mummy ta nuna mata ƙofar fita da yatsa.


“I don’t want excuses. You have to finish all the house chores before 6:00 a.m. If I come downstairs and find anything undone…”


Ba ta ƙarasa maganar ba, amma yadda ta kalli Du’a ya isa ya bayyana abin da take nufi.


Da rawar murya Du’a ta sunkuyar da kanta.


“In shaa Allah, Mummy.”


A ɗayan side din ɗakin kuwa, Amrah ta ji komai. Sai dai ko motsi ba ta yi ba. Ta ƙara jan duvet ɗinta har ya rufe mata fuska, sannan ta ci gaba da bacci cikin kwanciyar hankali, tamkar babu abin da ke faruwa.


Da Mummy ta fita, Du’a ta sauke wani ajiyar zuciya mai nauyi. Ta share hawayen da suka cika mata ido kafin ta nufi toilet domin yin alwala.


Bayan ta idar da nafila da Sallar Asubah, ta zauna kan sallayarta na wasu daƙiƙu. Hannayenta ta ɗaga sama, idanuwanta cike da hawaye.


“Ya Allah…” ta furta cikin muryar da ke rawa.


“Please help me out. I’m clueless, Ya Allah. Ban san me na yi wa iyayena ba har suke ƙina haka. Ka sauƙaƙa min rayuwa, Ka sa wata rana su daina ganina a matsayin abin ƙyama…”


Hawayenta suka zubo ba tare da ta iya tsaida su ba.


Bayan ta shafe fuskarta, ta miƙe tsaye ta sauko ƙasa without waking Amrah up.


Ko da yake suna da housemaid mai suna Fatima, hakan bai taɓa sa Mummy ta rage wa Du’a aikin gida ba. A ganinta, aikin gidan tamkar nauyin Du’a ne ita kaɗai.


Da ta isa downstairs, ta tarar Fatima ta riga ta fara share falo.


Da murmushi mai sanyi Du’a ta gaishe ta.


“Good morning, Sister Fatima.”


Fatima ta juyo tana murmushi.


“Morning, Du’a. How have you been?”


“I’m fine, Alhamdulillah.”


“Masha Allah.”


Ba tare da ɓata lokaci ba suka fara aikin tare.


Du’a na sharewa, Fatima na gyara kayan falo. Bayan sun gama nan, suka nufi kitchen, suka wanke kayan amfani, suka gyara dining area, sannan suka tabbatar komai ya koma cikin tsari.


Sai wajen 6:30 a.m. suka gama komai.


Du’a ta shirya breakfast a kan dining table cikin nutsuwa, ta tabbatar an jera plates, cutlery da drinks yadda ya dace. Bayan ta kalli komai ta tabbatar babu abin da ya rage, ta haura sama domin sanar da Mummy cewa sun gama.


Da ta shiga corridor ɗin, ta hangi Amrah ta riga ta shiga toilet.


Ta tsaya tana jiran fitowarta.


Bayan wasu mintuna kaɗan, Amrah ta fito cikin wani pink silk robe, tana goge fuskarta da towel.


Ta kalli Du’a daga sama har ƙasa, sannan ta saki wani ɗan murmushin raini.


“Villager.”


Kalmar ta fito daga bakinta a hankali, amma ta isa kunnen Du’a sarai.


Na ɗan lokaci zuciyarta ta cika da zafi.


Sai dai kamar yadda ta saba, ta yi kamar ba ta ji komai ba. Ta ɗauki kayan wankanta ta wuce toilet cikin nutsuwa.


Silence had become her greatest defense


Bayan Du’a ta gama wanka, ta shirya cikin neatly ironed school uniform ɗinta. Ta tsaya a gaban mirror na ɗan lokaci tana gyara hijab ɗinta, sannan ta ɗauki school bag ɗinta ta sauko downstairs.


Lokacin da ta isa dining room, Daddy ma ya fito daga bedroom ɗinsa, sanye cikin wani dark blue suit mai matuƙar ƙayatarwa. Kamshinsa ya cika wajen yayin da yake ƙarasa zama kan kujerarsa.


Da sauri Du’a ta ƙarasa gabansa, ta durƙusa cikin ladabi.


“Good morning, Daddy.”


Daddy ya ɗaga idanunsa ya kalle ta from head to toe, kamar mai tantance wani abu. Bayan wasu daƙiƙu kaɗan, ya yamutsa fuska.


“Morning.”


Kalma ɗaya ce kawai ta fito daga bakinsa, ba murmushi, ba kulawa, ba tambayar ya ta kwana.


Du’a ta saba da hakan, amma duk da haka zuciyarta tana ciwo a duk lokacin da hakan ya faru.


Deep down, she wished she could experience what it felt like to be loved by her own parents… even if it was just once.


Mummy ma ta fito. Kallonta kawai ta yi, sannan ta zauna ba tare da ta ce mata komai ba.


Du’a ta ja kujera ta zauna cikin nutsuwa, ta fara breakfast ba tare da ta ɗaga kai ba.


A daidai lokacin ne Amrah ta fito.


Sanye take cikin tsadadden school uniform ɗinta da matching accessories. Da zarar ta iso dining room ɗin, fuskar Daddy da Mummy ta sauya gaba ɗaya.


Murmushi ya bayyana a fuskokinsu.


“Good morning, Daddy. Good morning, Mummy.”


“Morning, princess.” Daddy ya amsa yana murmushi.


Mummy ma ta shafa kanta cikin kulawa.


“How did you sleep, sweetheart?”


“Very well, Mummy.”


Du’a ta kalli yadda suke mu’amala da Amrah na ɗan lokaci kafin ta mayar da kanta ƙasa.


She couldn’t remember the last time they smiled at her that way.


Shiru ya ɗan mamaye dining room ɗin kafin Daddy ya katse shi.


“You two have exactly ten minutes. Finish your breakfast, I don’t want to be late.”


“Yes, Daddy.” Amrah ta amsa da fara’a.


Du’a ma ta amsa a hankali.


“Yes, Daddy.”


Cikin gaggawa suka gama breakfast ɗinsu.


Bayan sun yi wa Mummy sallama, suka nufi parking space.


Kamar yadda ta saba, Du’a ba ta yi yunƙurin buɗe ƙofar gaban motar ba.

She knew that seat wasn’t meant for her.


Amrah ce ta buɗe front seat ta shiga cikin isa.


Daddy ya kunna motar ba tare da ya kalli Du’a ba.


Ita kuwa ta shiga back seat ta zauna kusa da window. Ta jingina kanta a jikin glass tana kallon yadda gari yake


Sometimes, she wondered if she truly belonged to the family she lived with.


Bayan kusan mintuna talatin, suka isa makaranta.


Daddy ya tsaya a school gate.


“Have a nice day.” Ya faɗa yana kallon Amrah.


“Thank you, Daddy.” Ta amsa da murmushi kafin ta sauka.


Du’a ma ta ce,

“Bye, Daddy.”


Amma bai ko waiwayo ya kalle ta ba.


Ta sauka cikin nutsuwa, ta rufe ƙofar motar sannan ta kalli motar har sai da ta ɓace daga ganinta.


Da Amrah ta shiga school compound, kai tsaye ta nufi wajen ƙawayenta.


Firdausi da Rumaisa.


Su ukun suna cikin fitattun ’yan matan makarantar. Ba wai don sun fi kowa hankali ba, sai dai saboda dukiyar iyayensu da kuma yadda suke rayuwa cikin nuna isa.


Expensive phones, designer bags, branded shoes…

A ganinsu, kuɗi ne ma’aunin darajar mutum.


Duk wanda bai kai matsayinsu ba, ba ya cikin lissafinsu.


Du’a kuwa ba ta bi ta kansu ba.

Kai tsaye ta nufi ajinsu.


Kafin ta shiga, sai ta ji wata murya da ta saba ji.


“Hey, friend!”


Ko ba tare da ta waiwayo ba, murmushi ya bayyana a fuskarta.


“Ayesha…”


Ta juya da sauri, suka rungumi juna cikin farin ciki.


Ayesha ta ɗan ja baya tana kallon fuskarta.


Murmushin da take yi ya ɓace.

“Du’a… what’s wrong? You don’t look okay.”


Du’a ta yi ƙoƙarin murmushi.

“I’m fine.”


Ayesha ta girgiza kai.

“No… you’re lying. I know you too well.”


Da jin hakan, idanun Du’a suka cika da ƙwalla.

Ta sauke ajiyar zuciya.


“Ayesha…” Muryarta ta fara rawa.


“When will my family ever love me? What did I do to deserve this? Why do they hate me this much?”


Hawayenta suka zubo.


“Every single day… they make me feel like I don’t belong. Sometimes… I even wonder if I’m truly their daughter.”


Ta kasa ƙarasa maganar saboda tsananin kukan da ya ƙwace mata.


Ayesha ta rungume ta cikin tausayi.

“Shhh… it’s okay. Allah yana tare da ke………


shin mummy da daddy sune parents din Dua? 

Meyasa suka tsane Dua? 


Dan samun amsoshin tambayoyinku ku biyoni a next chapter


kar a manta ayi following acc dina, a danna min gifts sannan a danna like, kuma kar a manta da sharhi


JazakAllah khair for reading this book

Keep reading . 

Remember me in your prayer🙏🏿