MIJIN ƘANWATA(ƘADDARATA).

25

by @jamilaumarjanafty

*MIJIN KANWATA..*!
_(k'addarata)_


*Wattpad:Jamilaumar315*
*Mallakar:Janafty❤️*


*HIJABS CORNER BY JANAFTY*

*Muna da Hijabai masu kyau da inganci, ɗinki cikin kwarewa da* *mabambanta design,  muna aikawa da kayanmu ko'ina a Nigeria, muna maraba da masu siyan ɗaya ko sari.*
****, tuntuɓa ta wannan lambar*
*KADUNA/ZARIA*


M.A JUMARE FOOD AND SPICES
Pure and Natural hygienic tasty.

Muna da garin Ɗanwake da yaji mai kyau dakan hannu, akwai kuka, tsamiya, garin tamba, kuɓewa da daddawa.
Muna aikawa da kayanmu a ko'ina
Anguwan Ma'aji new millennium city kaduna
Phone number ***

*Page 25*


Sunaima ta gane kuranta a wajen Sulaiman Ranar daya dawo da Daddare,Daman ai ya fadamata Tunda tace yayi abunda yaga dama in sun koma gida aikuwa bakinta ya yankata Domin datace"Saraki..!
Tana kallonsa sai ya Dage mata gira yana Fadin"Ba wani Saraki malama..Kekikace in muka dawo gida in yi abunda naga dama..!
Dole tayi shuru da bakinta Yaran wajen Magajiya yace ta barsu ta kula dasu,Ita abun ma kunya ya bata Suna ganinta ta Haura Dakinsa ta bar musu yaran washegari koda ta fito Magajiya ta gama yi musu shirin makaranta Dayake suna da Wasu kayan makarantar agida bayan na gidan Inna.

Daga ita har Sulaiman shiryawa sukayi ita tayi Shirin zuwa wajen aiki Shima yayi shirin zuwa Office.
Tare suka fita harda yaran bayan sun karya makarantar yaran suka fara zuwa suka ijiyesu,Daganan Suka biya suka ijiye Sunaima ya kuma mata gargadin in tatashi ta kirasa Sani zai zo ya Dauketa bayason Hawa adaidaitan ne in kuma ta hau to ita da Allah.
Kallonsa tayi alokacin Dayake Fada mata haka dukkansu suna Bayan Mota ne Fuska ta Hade tana Fadin"Ni yanzu Saraki sai ka rika min Allah ya isa ko..?
Kai tsaye yace"Ai bakya jin mgana ne..Mgana baya Horar dake sai an bi daake ta haka..!
Yafada Lokaci Daya yana riko hannunta yana yar dariya Kwace hannunta tayi tana kokarin Bude kofar Motar da sauri ya rikota yana Fadin"Afuwan Anty Sunaima..!

Wani kallo tayi mai kafin tace"Sai ka janye mganarka..!
Kai tsaye yace"Kema sai kin janye Taurin kanki..!
Kallonsa tayi tana fadin"Nice ma mai Taurin kai..!?
Kai tsaye yace"Sosai ma..!
Yafada Lokaci Daya yana Taba kan nata kafin ta ankara ya Sunkuya ya Sumbaci bakinta ido ta waro tana Nuna mai Sani Ido daya ya kanne mata yana Fadin"Barsa in ya gano abunda zai makantar dashi ba ruwana..!
Baki ta Rufe da Hannunta tana Fadin"Saraki...!
Da sauri y tareta da Idanuwansa yana Kokarin kashe mata Jiki wata Murya yace"Ki adana kirana da wannan Sunan yanzu..sai an juma in mun hade alokacin sai naji Dadin amsa miki..!
Kai ta girgiza bata da tacewa domin Saraki yafi karfinta Motar ta Bude ta Fita ya bita da kallo Sai da ta fito kana ta Leka tana Fadin"Na manta ban Fada maka ba..Ina so don AllaH in mun tashi naje na gaida Inna..!?
Ido ya sakar mata kafin yace"A"a ba yau ba..!

Zata kara mgana ya Dakatar da ita"Nace ba yau ba Sunaima..!
Yafada ba wasa a mganarsa bata kara mgana ba ta mtsa baya Sani ya kallah yana Fadin"Mai idon ganin Mata da miji in kagama kallon mu ta madubin muje..!
Sani na Dariya yace"Afuwan yallabai..!
Kai kawai Sulaiman ya girgiza yana Fadin"Allah ya shiryeka sani..!
Daga haka ya tada Motar suka wuce Lokaci daya yana Daga ma Sunaima Hannu itama ta Dagamai.
Ammh taso ya barta taje su yi mgana da Inna ta Fadamata yadda Hajiya Zabba"u ta karbeta wannan karon sai dai Saraki ya hanata Dole ta Hakura.
Karfe Biyu suka tashi aiki ta kirasa ta fadamai ya turo sani yazo ya Dauketa zuwa Gida
Tana komawa akwai gajiya ajikinta,yasa Wanka kawai tayi ta ci abinci ta kwanta sai la"asar tatashi Tayi Sallar ta fita falo ganin bata ga su Wasim ba tatambayi magajiya tace basu dawo ba abun ya bata mamaki har pass 4 sai ta koma Daki ta Kira Sulaiman.
Yana Dauka tace"Su wasim basu dawo ba..!
Kai tsaye yace"Eh Sani nace in ya Daukesu daga makaranta ya kaisu wajen Inna..!
Cikin mamaki tace"Saboda menene..?
Alokacin suna tare da Saifullahi ne yasa ya mike yadan Mai tazara yana Fadin"Saboda Mganar ki ta yau da Safe..Bazai yuyu inaso naci Amarcina yaran na Takurani ba..!
Sai alokacin ta tuna da korafin da tayimai da safe akan yaran ta barsu su kadai wajen magajiya alokacin bai kalleta ba ammh aransa ya gama Tsara yadda zai yi shagalinsa yaran basu Takuramai ba.
Sunaima ta Shagwabe fuska tana Fadin"Kai Saraki...,!
Da sauri yace"Saraki again.?yau kuwa zaki kira saraki sau Dubu In baki yi wasa ba..!
Cikin kunkuni tace"Ni nagaji..!
Yana Dariya yace"Ni kuma ban gaji ba..!

Bata iya mgan ba ta katse kiran Tana Mmamkin Saraki abubuwansa sun fi karfinta Inna ta Kira sukayi mgana Inna tace taji dadin dawo da su Wasim Daman tunda suka tafi gidan ba Dadi sai ta fara kame kame bata so Inna ta Fahimci wani abu abunda bata sani ba Inna ai ita ta haifeta tasan duk wani motsinta aranta Farinciki take daman Akullum addu"arta Allah ya Daidaita Tsakanin Sulaiman da Sunaima.
Inna sai ta bar mganar ta sako mata mganar sakon da Ahmad ya kawo mata,Sunaima ta fara ma Inna bayani ta karishe da fadin"Inna baki ga yadda suka karbeni ba kannensa da Hajiya,tana kuka tana kara Rokona gafara Inna baki ga abun arziki ba abun sai mamaki yake bani..!

Inna na Dariyan Farinciki take Fadin"ba bu abun mamaki da ikon Allah Sunaima..Fadin Allah ne Hakki ga wanda aka Zalunta in baka da Hakki akan Mutum kana zaune sai Allah ya Fitar maka da Hakki..Abaya ta tsaneki ta so Diyar kawarta yanzu kuma da akayi sai Allah ya bayyana Sakayar..!
Sunaima tace"Hakane Inna..!
Inna ta cigaba da Fadin"Shawaran  da zan baki shine ki kama mijinki Hannu Bibbiyu da Danginsa Musamman Ita Hajiya Domin wannan Damarki ce Allah ya riga ya warware miki Dukkan Matsalolinki Sunaima..!
Da wadanan yan nasihun suka yi sallama da Inna bayan sun gama waya ta Zauna tana Tauna mganar Inna gaskiya ta fadamata Ya kamata ta Shiryama kanta ko sau Daya tayi ma SAraki wani abun alheri cikin Dimbin Alherinsa gareta da iyayenta.

Zumbur ta mike ta Fice sai Kitchen magajiya da Samira nata aiki Gaisheta suka hau yi ta amsa tana Fadin"Me kuke Dafawa na Dinner ne..?
Magajiya tace"Farar shinkafa da Miyar kaza Hajiya..sai Ferfesun kayan ciki..!
Fuska ta yamutsa kafin tace"Samira ki karisa wannan girkin..Magajiya fitomin da Naman Dake cikin Fridge ki Tafamin Tuwo zan yi da miyar yauki..!
Tana gama Fadin haka ta fice suka amsa mata Daki ta koma ta kara Kiran Inna tace Ahmad na gida Inna tace yana Shagon dayake koyon aikin kafinta Sai tace bari ta Kirashi ta Fadamai yazo wajen Inna ta bashi Bushasshiyar Kubewa yazo mata dashi Inna tayi Dariya aranta Tana Hamdala ta tuna Farkon Tarewar Sunaima gidan Sulaiman duka wadanan Dake daken Tani tayi mata shi daga Zuntu ta kawo mata sanin Sulaiman ma abocin cin tuwo ne Tun Sunaira nada rai tana yawan Siyansu Musamman Tani ke tada yaro Daga Zuntu zuwa Kaduna saboda kuka,kubewa da su Daddawa.

Alokacin da Inna ta Nuna ma Sunaima Fuska ta bata tana Fadin"Inna da kin bar abunki ko na kaisa gidan nan sai dai ya lalace..Ni dai ba girki zan yi ba..Komai hadiman gidan keyi abunsu..!
Alokacin bata matsa ba sanin Taurin kan Sunaima ammh aranta tasani akwai watan wata rana da Sunaima Zata nemesu ko domin Farantama Sulaiman.
Sunaima ta kira Ahmad ta Fadamai ba Dadewa ya koma gida ya karba Sakon wajen Inna wacce ta juye mata Duka na wajen nata ta hada mata Harda Daddawa Akuma aranta tayi alkawarin Zata Kira Tani duka ta Daka mata saboda Sunaima din Lokaci yayi da komai ya Daidaita Sunaima ta karbi kaddaranta Duk da bata Fito ta mata bayani ba sai dai ance Labarin Zuciya a tambayi Fuska.

Sunaima taji dadin ganin har da Daddawa Ahmad bai zauna ba ta bashi kudin mota ya koma gida,sai ga Sunaima an zage an shiga Kitchen alokacin bata tuna da Mijin kanwarta bace Ita kawai tana Hango yanayin Farincikin da Saraki zai shiga yau yana son Tuwo fiye da kowani abinci kuma hakan ya samo asali ne saboda Zabin Maimartaba ne shima Tuwo yana Daya Daga cikin Abincinsa.
Ana kiran mangariba suna gama Komai Tuwan Semo ne tayi da Miyar Kubewa dataji Daddawa,da Nama har da manshanu sai tashin kamshi take suna gamawa ta hada komai awani Katon Tire Harda Zobon data Hadamai Ta bar su samira suna gyara Kitchen din ta sumgumi Farantin zuwa Dakin Saraki aranta tana jin wannan Lokacin ya zama daga shi sai ita ne.
Dakinta ta koma ta yi wanka tayi sallar sannan ta shirya Cikin Daya Daga Cikin Dogayen Riganun da Hajiya karama ta bata saboda ya gani yaji Dadi tayi rolling din mayafin Rigar Yau har dasu shafa jan baki tayi kyau sosai matuka Tana jiran Dawowar Sulaiman,Dakinsa ta koma ta dan kara gyarawa ta Turara Dakin ta shiga Bedroom din ma ta gyaraahi Tsab yana tashin kanshi Kiran Sallar Isha"i yasa ta fito ta koma Dakinta tayi Sallar Isha"i.

Shuru bata ji Sulaiman ya Dawo ba sai ta fara Damuwa Bini bini ta Dauki wayarta tana Dubawa ta fara Tunanin an ya Lafiya wata zuciya tace ki kirasa kiji ko lafiya Sunaima..?
Batasan ma ta Lalubi lambarsa ba sai jin Mganarsa kawai tayi tana Tsaka da Tunani ashe ta kirasa bata sani ba kunya ya kamata da Sauri ta Datse kiran tana Dafe kanta Afili ta Furta"Kash..Me na ke yi ne haka ni Sunaima..!?
Bata samu mai bata amsa ba Sulaiman ya Dawo da kiran sai da ta kusa katsewa sannan ta Dauka Cikin basarwa Tana Daga Kiran yace"Anty Sunaima How far..?kin ga ban dawo da wuri ba ko..?nima fa inata Sauri ne na dawo afara kirana Saraki Saraki ina jin Dadi..!

Baki ta rike tana Fadin"Saraki..!
Dariya ya kwashe dashi yana kallon Saifullahi Dake Driving yana fadin"Saifullahi ma yace lalle Saraki kai mai sa"a ne..!
Da Sauri Sunaima ta kashe wayarta Kunya ya kamata Saraki baisan kunya ba sam wlh,tana ji yana kira taki Dagawa chan sai ga sakon sa.

"Don Allah madam ahada mana Dinner tare da Saifullahi kinsan Gauro ne shi a kaduna...gamu nan tafe..!

Tana ganin sakom aranta sai taji Sanyi Tasani yau zata farantama Saraki ransa sosai bazata iya fassara yanayin Datake ji acikin ranta ba sai dai ita kanta ta sani Saraki ya fara zama Jikintan bata sani ba.
Ko minti goma basu yi da gama waya ba taji Muryansu afalo Suna mgana da Saifullahi Tana jin haka ta fara kokarin Raruman Hijabai sai ga Sulaimam ya shigo Dakin ko Dakinsa bai haura ba Harta Yar jakar Briefcase dinsa yana Hannunsa.

Tsayawa tayi daga neman Hijabin tana kallonta Cikin Kallon kurillah Sulaiman ke bin Sunaima dashi Cikin wata irin murya yace"Ya kuma haka..?anyimin kwalliya kuma za"a hanani gani..!
Yafada cikin wani yanayin Sha"aawarta data kamasa,Kamar wata wawiya haka ta juyo da Fuskarta Tana kallonsa ido ya waro yana Fadin"Wow....Beautifull..!
Yafada kamar Miyau zai xubo,Bude mata Hannu yayi yana Fadin"Plz Come Here...!
Nokewa Sunaima tayi kunyar duk ta kamata sosai,ganin taki zuwa yasa ya kariso da Sassarfa ya Rumgumeta sosai acikin Jikinsa yana Shinshinan wuyanta Lokaci daya yana Jan Numfashi,Sunaima ta noke kanta Samam Kirjinsa tana Sauke Numfashi Cikin Salama da wani Farimciki sun Dade ahaka kafin ya Dagota yana kallonta kai tsaye ya Sumbaci bakinta yana Fadin"Ni aka samawa..kuma na tsotseshi..Sauran Dayar kwalliya itama an juma zan Tsotseta. !
Sunaima taji kunya ta saka Hannu ta Daki Kirjinsa tana Fadin"Saraki..!
Hannunta ya rike yana Fadin"Sunaimata..Duniyata..!
Yafada yana Kallon Fuskarta Sunaima ta raba kanta saman kirjinsa tana Dariya shima Dariyan yake yana Fadin"Sako Hijabin ki muje ki gaisa da Saifullahi..!

Yafada Lokaci daya yana Sakinta Hijabin ya Dauko mata dake kan gado ya mika mata yana Fadin"Kinsan Gwauro ne a kaduna..!
Sunaima ta karbi Hijabin tna Fadin"Daman yana da mata..?
Sulaiman yace"Eh mana..Tana chan garinsu Karaye kinsan bakano..Auran gida akayi mai..!
Sunaima tace"Allah Sarki..Yaushe zamu je..!?
Sulaiman na rike da Hannunta yace"Sai ta Haihu..!
Da sauri ta kallesa tana Fadin"Ciki gareta daman..?
Sulaiman na dariya yace"Eh mana..Kinga ke kafar yawo ne sai muje daga suna..mu yi Honeymoon din mu achan kinsan karkara Love yafi Dadi..!
Yafada yana Jan Hancinta Sunaima ta Bigemai hannu tana Fadin"Kargi fa..?
Da sauri yace"Sai kin yi ciki..!
Dakatawa tayi tana kallonsa gira ya Daga mata yana fadin"Ciki kuma..!?
Yace"Yes..kin manta da Sharadin maimartaba wato na kaiki ki kara neman Rabuwa dani ko..?Naki wayon yarinya kiyi Ciki sai muje in takawa yayi mgana na nuna mai sheda shima irin ya fito din nan kina tafiya Dakyar..!
Yafada yana kwantatan yadda Zatayi yana Tura Jakar hannunsa gabansa Dariya ta kamata ta kama kanta tana Fadin"Allah ya shiryeka Saraki..!

Rumgumota yayi yana Fadin"Koda yake ai ko muje yanzu..Bazaki iya mgana ba..!
Hararansa tace"Sabo da..?
Kai tsaye yace"Kin fara jin Dadina...Fadi kike fa Saraki..Saraki..Saraki..kina kara rikeni..!
Bata bari ya karisa ta kwace jikinta ta Fice kamar ta nitse akasa Saboda kunya Dariya yayu ya bi bayanta Kunyarta na Burgesa yana jin Dadin Tsokanarta.
Bayanta yabi ya isketa suna gaisawa da Saifullahi yana ganinsa yace"Me garin kargi nace hala ka manta dani ne..?
Saraki yace"Ta na chan tana tambayana Daman kana da mata ne..?
Nace mata tab har da ma tsohon ciki..nace ta bari matarka ta Haihu zamu je suna dagachan mu yi Yawon Amarci kasan iskar karkara na kara Dankon kauna..!
Sunaima na gefe kai ta Dafe tana Hararansa Saifullahi dayasan Halin yan kayansa yace"Uhm..Sulaiman manya..Kaidai fadi gaskiya..!
Yafada yana mai Dariya yasan meyasa yace haka sai ya ballamai harara yana Fadin"Ban so gulma fa..Zan koreka wlh..!
Da Sauri Saifullahi yace"Yi hakuri..Allah ya taimaki Saraki..!
Sunaima ya kalla yana Fadin"Hada mana abinci muci ya kara gaba..Yana shiga Lokaci kinsani..!
Yafada yana kasheta da kallo Da Sauri tace"Komai yana Dakin ka..!

Cikin mamaki yace"Ke kika Kai..?
Kai ta gyada tana Fadin"Eh..!
Bai ce komai ba ya yi gaba yana Fadin"Taso in fa kanajin yunwar in kuma Daman gulma ta kawoka kaga komai sai ka kara gaba..!
Da sauri ya mike yana Fadin"Inafa..Da Gulmar kuma da Yunwar..!
Sunaima Dariya tayi tana Binsu da kallo Saifullahi yabi bayan Saraki yana Fadin ya Jirasa suna ta Shakiyancinsu.
Dakinta ta koma abunta ta barsu suci abincin,Ba Dadewa sai gashi ya Kirata Tana Dauka yace"Sunaima Inna ta kawo wannan Tuwon..?
Sunaima tace"A"a ni na yi maka..!
Da sauri yace"Wow..Ni kikayi mawa shine kika sakani na gayyato wannan Gardin..?
Sunaima tace"Nidai ba ruwana..!
Tafada tana jin Saifullahi na Fadi daga gefe"Allah na sona..!
Kashe wayar tayi tana Dariya Ita kadai Bata Dauka haka Saraki yake ba ashe ya wuce duk Tunaninta.

Wayarta ta yi ta dannawa har Sulaiman ya kirata yace ta fito suyi sallama da Saifullahi ta fito Sanye da Hijabinta Saifullahi yace"Madam an fa gode..Allah ya bar kauna. !
Kanta na kasa batace komai ba Sulaiman ya amsa da Ameen Ameen..
Saifullahi ya dunguri kansa yana Fadin"Ita tayi shuru kai kuma rasa kunye ka amsa da karfi ko..?
Sulaiman yace"kada na amsa Ubana..!
Itadai gefe ta koma tana kallonsu 5k Saifullahi ya bata Sulaiman ya karban mata yana Tayata Godiya Saifullahi yace"Kai na ba mawa .?
Sulaiman yace"Eh mana Ko Anty Sunaima..?
Yafada yana Tsareta da ido Juyawa tayu tana Yar dariya Saifullahi ya iza keyarsa suka fice sun Dade suna mgana aharaban gidan kafin suyi sallama Saifullahi ya tafi shi kuma ya Dawo Cikin gida a kitchen yaji motsin Sunaima ta maida kayan da sukayi amfani Shigowa yayi yana Fadin"Ki adanamin Sauran Tuwo gobe akwai cin Dumame..!
Yafada Cikin bayyana Murnansa da To ta amsa bayan ya Rumgume yana Fadin"Yau zan bada babban Tukwici..!
Jikinta yam yayi mata yasa ta kasa Juyowa daya Fahimci haka yasa ya saketa yana Fadin"zan je nayi wanka..!

Bai jira amsarta ya fice sai alokacin ta Sauke Numfashi Fridge ta saka Sauran Tuwon da Miyar su magajiya sun gana Tsabatace ko"ina sun ci abinci sun kaima Megadi nashi sun shiga sun kwanta Dakinta ta koma ta shiga wanka,Saboda tasan Saraki sai Allah Tana Fitowa ko mai bata shafa ba Tana Daure da Towel yana ganinta ya Nufeta da Sauri tace"Saraki ban...!
Hannu ya dora saman baki kafin yace"kada kice komai...!
Dole tayi shuru cak ya Dauketa sai kan gado agabanta ya Zare Jallabiyan Jikinsa ya Mata Rumfa,lokaci daya yana Zare Towel kamar yasani ta Fara Kiran sunansa Saraki saraki shi kuma yana ta Bidirinsa yake fadin"Yes Saaraki..Ki karisa Saraki inajin Dadin ka..!
Jin haka yasa ta rikesa sosai Tana jin wani irin yanayi yana ratsa taa batasan sadda tace"Saraki..Sarakiiii....!
Shima yace"Sunaima ta...!
Ahaka suka makale juna cikin muradi mai girma sun raya wannan Daran sosai Sunaina ta bada Halin kai sosai da Sulaiman yaji Dadin haka da asuba sai Tsokanarta yake da Saraki yana Kwakwayon muryanta Kunya duk ya kamata bata da bakin mgana Tunda ya gane Lagonta.
Tundaga Ranar suka Bude Shafin Armaci Ita da Sulaiman su Wasim na Gidan Inna abunsu da safe su fita aiki Tare ya kaita su wuce kamfani in tatashi Sani Direba yaje ya Dauketa zuwa gida kafin ya Dawo Sunaima tamai girki taci gayu tana Jiransa Kwana suke Farantama juna ita kanta bata sanin Tana Sakin jiki da yawa sai bayan komai ya Lafa tayi ta jin Haushin kanta.
Ranar Jumma'a Daddare bayan sun gama Farantama juna rai yake fadamata gobe zasu je Zuntu tana makale dashi tace"Wajen wa zamu je a zuntu..!?
Kai tsaye yace mata"In munje zaki gani..!.
Haka kuwa akayi da Safe suka shirya sai Zuntu a waya ma Sunaima ta fadama Inna da tayi mganar zuwa da yaran Sulaiman yace bai gama cin armarcinsa ba.

Gidan Kawu Jafaru suka fara zuwa yaji Dadi sosai yayi ta saka albarka Sulaiman yayi mai godiya shi kuma ya kara bashi wasu Shawarwarin nan suka dan Dade sukaci Dambun da matarsa tayi da zasu tafi 20k sulaiman ya bassa yace bazai karba ba sai da yacemai ba Ladan aiki bane Kyauta ne Daga dansa sannan ya karba.
Daganan gidan Inna Tani sukaje taji Dadi ta rasa ina zata sakasu gidan ba bakon Sulaiman bane saboda Sunaira akwai zumunci sosai,suna zuwa itana ya bata 10k daganan sai babban Gidansu Inna daman ai chan kowa yasan Sulaiman tun abaya basu jima ba suma yayi musu abun arziki suka kamo Hanya zuwa gida Dare yayi musu suka Tsaya azaria suka kama Hotel suka kwana cikin Soyayya da Farinciki sai da safe suka koma Kaduna da yammah Daganan gidan Inna yakaita suka gaisa suka ga yaran sai bayan Isha"i suka koma gida bayan sun ci Jallof din da Inna ta Dafa da Kifi.

Sunaima ta saki jikinta Fiye da Zatonta Ta kuma Dauki nasihar Inna Duk Safiya sai ta Kira Hajiya da Hajiya karama da Abba ta gaishesu Kuma suma jin dadi suyi ta saka mata albarka,Hakama kannensa suna Kiranta su Safiya Anty sama Anty kasa Lalle rayuwa daman haka ta gada.
Sulaiman ya samu kwanciyar Hankali sosai tunda ya Fahimci Lagon Suunamai tana son soyayya sosai da Rayuwar Masoya shiyasa ya Shagwabata sosai soyayya Salo Salo haka yake mata Shiyasa ta saki jikinta Dashi bata sani ba.

Abu Dayane ke batama Sulaiman rai irin aikin Dare in ta farashi har ta gama yana Kunci yayi ta fada yana ya gaji ita dai bata mgana Saboda tasan Halinsa in ta cika mgana zai iya Botsere mata ita kuma tana son aikinta batasan Rabuwa dashi.




Littafin Mijin Ƙanwata Free book ne yanzu nake reposting, amma ina siyar da document ga waɗanda ba za su iya jira ba 
1k ne ta wannan acct ɗin 5040273639 Moniepoint Jamila Umar
KO tuntuɓa ta wannan lambar ***.



*Janafty*