JODAH

16

by @sadisakhna


 

 

______👑 *JODA* 👑_____ 

 

            

Na  

 

*Sadi-sakhna* 

 

Ƴar mutan Jama'are 

 

THE TRIO OF TALES  

(3⃣ minds, 3⃣stories,1⃣Journey)  

 

@sadisakhna on Arewapen 

@SAKHNA03 On Wattpad 

*** on Whatsapp 

 

LITTAFI NA 1 

 

👑*Warƙa ta (16)*👑 

 

Kayan jikinsa yake cirewa amma gabaɗaya hankalinsa yana wani waje daban,duk maganar da Fasih yake masa baisan mai yake cewa ba. 

 

"Ranka ya daɗe inata magana tun ɗazu amma bakace komai ba ko baka jina ne?" 

 

Lumshe idonsa yayi tareda yin wani murmushin gefen baki cikeda ƙasaita. Wannan karon yaji muryar hadiminnasa amma bai tanka masa ba sai tashi da yayi ya shiga Zagaye domin wanke jikinsa. 

 

"Jikinsa baƙine lokacin daya shiga amma yana fitowa daga wankan yazama fari mai kalar zinare irin kalar larabawan Masar,amma kuma bai kaisu haske ba,farar riga da aka saƙa da Saƙi mai laushi yasaka,amma bai sunce ɗaurin da Joda tayi masa ba na ciwon da samarin suka ji masa ba ɗaxu. 

 

Man zaitun ya ɗiba yashafawa baƙar sumar kansa,saida yatabbatar yaji sosai kafin ya ɗauko mataji zai taje,daidai lokacin da Fasih ya shigo hannunsa ɗauke da tire na abinci,yana ganin ya ɗau matajin ya ajiye abincin da sauri ya fara gyara masa gashin. Hankalinsa ne yakuma tafiya wani wajen daban,ba ko inaba sai inda Joda tasaka hannunta akan ƙirjinsa ta rufe idonta,yanayin yanda ta maida hankali kacokam akan abinda takexon jiyowa yake tunawa,kuma bazayyi ƙarya ba tabbas yaji tamkar wani zare ya ɗauru a zuciyarsa lokacin data rufe idon,data buɗe idonta cikin razani kuma yaji tamkar wani abu daya fara sakawa zuciyarsa nutsuwa ya fincike daga cikin jikinsa. 

 

"Fasih shin akwai wani salo na magani da mutum yake shigar da tunaninsa cikin jikinka domin yagano mai yake damunka batareda ka faɗama sa ba?" 

 

"Inaa ranka ya daɗe gaskiya bantaba jin salon duba marar lafiya irin wannan ba,saidai idan sihiri shikuma komai sukayi mutum bazayyi mamaki ba" 

 

"Inaa batayi kamada mai sihiri ba,ko ban santa ba zuciyarta tayi farin da baƙin abu kamar sihiri bazai iya shiga ba,saidai idan wani abune na daban a tattare da ita wanda banida masaniyar menene shi" 

 

"Wacece ita ne haka yallabai,ko dai wacce tazo ƙirana ɗazu kan cewar wani abu ya sameta" 

 

Shuru yayi bai bashi amsa ba ƴan mulkin sun motsa,shima ganin haka sai yasha jinin jikinsa. 

 

Bayan sun gama zama yayi ya zuba masa abinci,kaɗan kaɗan yataba,domin abincine dabai kama gwiwar wanda yasaba ci ba,to amma ya zayyi tunda ya fito neman suna da ɗaukaka. 

 

 

A zaune nake ina ta kalle kalle a ɗakin karatun,wani littafi na gano agefen buzunsa babba sosai an ɗaureshi da igiyar fata. Rarrafawa nayi na buɗe ina kallon rubutun bangon. 'AL-HAWI naga an rubuta marubuci Al-razhi ne ya rubuta,babban littafine daya ƙunshi ilimi na Jinya da maganinsa,wani irin kwaɗayin karantashi ne ya taso min, domin idan ba anan wajen ba bana tunanin zanga wani ƙunshin ilimi kamar wannan. Takun sawun tafiyane yasa nayi saurin barin wajen na koma na zauna,amma har sannan idona bai ɗauke daga kallon littafin ba. 

 

Tsufa yafara zuwa masa,domin har ya durƙusa kaɗan,murmushi yayi daya ganni kafin ya samu waje ya zauna. 

 

"Mai yake tafe da farar tattabara mai neman ilimi da wannan almurun?" 

 

"Baba almahdi barka da almuru ya Lafiyar jiki?" 

 

"Jiki kam gashinan,ya sabon wajen da kika tsinci kanki?" 

 

"Uhmm to gashinan dai Baba,dama wani abu naci karo dashi a ranar yaudin wanda ya ɗauremin kai sosai,kuma nasan babu wani mai wuƙar warware wannan zare saikai Baba......." 

 

Bayan nagama yimasa bayanin duk abinda yafaru shuru yayi yana nazari can sai ya tashi ya nufi wani ƙaramin ɗaki a cikin ɗakin karatunnasa. Ina nan zaune har ya ɗawo ya kuma zama. 

 

"Shin marar lafiyan yanada wani zanen hatimi na zaki a ƙirjinsa?" 

 

Mamaki ne yakamani taya akayi yasani,nidai naga zanen hatimi na zaki a ƙirjinsa tabbas amma dayake bashine a gabana ba ban kawo komai ba,kuma naga dana ɗauke hannuna yayi saurin maida rigarsa ya rufe wajen hatimin,duk da bawai ya fito raɗau bane amma tabbas akwaishi. 

 

"Ehh baba akwai amma taya........." 

 

"Kar hakan ya ɗaure miki kai,nasani ne saboda an kawomin shi a baya bashida lafiya kuma naji ance Uban gidansa yabashi lamuni yashigo gasa,saboda bashida ɗa namiji dazai kawo. Nayi zaton ya warke ashe har yanzu dasaura. Yanzu aikin dazan baki shine kiyi bincike na maganin dayashafi lalurarsa,sannan kiyi masa magani. Wannan shine jarrabawa tafarko dazan baki. Idan har kikayi nasara akwai Wani abu dazan yi miki kyautarsa wanda zai baki mamaki kuma zakiyi farinciki dashi" 

 

Bansan lokacin da murmushi ya subucemin ba,inkuwa hakane zanyi iya iyawa ta,to amma ta yaya zanyi binciken kuma nasamu amsar. 

 

Jimm nayi ina tunani karo na farko danaji ance anyiwa wani bawa magani kuma ma babban mutum kamar Baba almahdi,lallai bawan mai darajane ko shiyasa yake jiji dakai sannan yanayinsa ma bayyi kama da bawan dayake shan wahala ba ,saida baba almahdi ya katseni tukunna. 

 

"Haƙiƙa lallai nayi farinciki kuma nayi matuƙar mamaki da har kika iya amfani da Ruhush-shifa kika gano mai yake damunsa ba tareda yasanar dake da bakinsa ba. Kin cancanta ki zamo Likita a gareshi dan koni Joda nafara ƙalubalantar ilimina a gabanki,Allah yayi miki baiwa mai yawa dan haka karki sare wajen yimasa godiya a koda yaushe" 

 

"Insha'allahu bazan sare da hakan ba. Kuma zan kuladashi da dukkan iyawata wajen ganin nayi nasarar wannan jarrabawa. Bari na tafi kar a gane bana nan,bansan ko suna bari a fita ba amma kuma kada nayi laifi" 

 

Har na tashi zan tafi naji yayimin gyaran murya. Juyowa nayi daidai lokacin daya miƙomin Littafin dana buɗe ɗazun kafin ya shigo,sannan da wani hatimi dayake ɗauke da zanen hatiminsa na sashen magunguna. Daskarewa nasoyi a tsaye,sannan zuciyata ta fara cemin bada gaske bane,konazo zan karba zai fasa.  

 

Ganin ban karba ba yasa yasake miƙomin fuskarsa ɗauke da murmushi. 

 

"Na kulada kallon dakikemasa tun shigowata ai,sannan naganshi ba a yanda na barshi ba,kuma kin taba ganin inda aka bawa mutum aiki batareda an bashi inda zai nemo aiki ba? Wannan littafi ne na babban malami masanin kimiyya da magunguna,zai taimaka miki sosai a bincike,idan bai isa ba ga hatimin neman izinin na shiga ɗakin karatu kowanne a wannan jami'ar amma kiyi taka tsantsan sai bukatar hakan ta tashi gareki." 

 

Karba nayi tareda zubewa akan gwiwoyina,so nake nayi masa godiya amma kuma bakina ya gagara furta hakan,kuka na rushe dashi domin bansan ya zanyi ba. Saida nayi mai isata ina rungume da littafin kafin yayi magana. 

 

"Har kullum shi mai bada ilimi baya kishi idan wani ya iya abinda yakeyi,saidai ma yayi murna da farincikin cewar ko bayanan al'umma zasu cigaba da samun mafita daga wani bashi ba. Tunda na ganki nakejinki a raina tamkar jikata wacce zata gajeni,Allah bai bani ƴaƴa masu baiwar fahimta irinwa ba,mai yasa bazan koya wani ba idan naga ya cancanta koda kuwa shi baya daga cikin ahalina. Dan haka ki kwantar da hankalin ki kicigaba dayin amfani da marki wajen sanin ilimi mai yawa mai amfani,wannan damace dazakiyi amfani da ita kiyiwa aboka karawarki zarrah,ta hanyar bibiyar karatun malamai dasuka gabata sannan da maida hankali akan neman sani komin ƙanƙantarsa,idan kikayi hakan zakiga amfaninsa sosai a gaba. Wannan marar lafiyar kiyi iya yinki akansa sosai,wataƙila wannan shine matakin nasararki ta farko. Kije maza Allah yabada sa'a kinji" 

 

Ɗaga masa kai nayi kana na tashi na fita cikin sanyin jiki,mai nayi Allah yahaɗani da adalin bawa kamar Baba almahdi. Lallai babu abinda zance sai alhamdulillah. 

 

"Kiduba littafin Malami Avicenna wanda ake ƙira Jirgin Magani,yayi rubutu sosai akan cutukan dasuka shafi Jinyar Jini da kuma Garguwar jiki,harma da Guda da dafi. Zaki sameshi a Tsohon ɗakin karatu na cikin Sashen Guru Al-azhar." 

 

Murmushi nayi tareda ɗaga kai kana na fice na tafi sashenmu. A hanya nabi ta wajen masu gadi na saci Fitilar aci bal bal, layin ɗakinnamu naje na zauna tareda fara Duba littafin,kamata yayi na ajiye na kwanta saboda gobe zamu fara karbar karatu,amma kuma ɗokina ko kaɗan bazai barni na jira ba. 

 

Ban ankaraba sai ji nayi ana shambin ƙafata,tashi nayi naga gari yayi haske,da sauri na mike a wajen na shiga ɗakinnamu. Da mata biyun naci karo sun shirya cikin kayan karatun su zasu fita. Gaba na ne yayi rass yaushe nadaina karatun,yaushe nayi bacci sannan yanzun wanne lokacine gabaɗaya bansani ba. Kallonsu nakeyi inaso na tambayesu amma gabaɗaya na kasa,haka inaji ina gani suka fice daga ɗakin. Dabara ce ta faɗomin. Bakin tagar ɗakin naje na ɗauki tsinke na ajiye a ina rana ta hasko. Tsayin Inuwarsa na auna anan nagane rana tayi kusan sa'a Biyu tafitowa wato ƙarfe takwas kenan,cikin hanzari nacire kayan jikina na sauya zuwa na aji,bantsaya yin wanka ba ko asuwaki dakuma neman abinci,domin banma san inda ake wankan ba. Nikaina ji nayi gabaɗaya na muzanta ina ƙyamƙyamin kaina inaga wani kuma.  

 

Kaina a ƙasa nashiga harabar wani waje ina wasu manyan mata suke raba abinci,Kwano na ɗauka nashiga layin karbar abincin. Ina zuwa wajen wasu mata kusan su Biyar suka mammatsa suna min kallon kaman sunga kashi. Domin ba kayan aji ne a jikinsu ba Kayane irin wanda suka saba sakawa a gida,duk da cewar dama yadin kayanmu da nasu ba ɗaya bane. 

 

Ji nayi kaman ƙasar wajen ta buɗe na faɗa, Bayin mata guda biyun da muke ɗaki ɗaya na kalla,ba laifi sunyi fasali kuma da alama sunyi  wanka,to amma meyasa suna kallona basu tasheni ba,gashi da gangan suka haɗe rai don kada na tambayesu. Murmushi naga ɗayar tanayi itakuma ɗayar tanayi mata magana ƙasa,suna can gefe da kwanon abincinsu a hannunsu. 

 

Wani takaicine naji ya cokemin zuciyata,inajin haushi idan masu ƴanci sukaci mutuncinmu,amma nafi jin haushi idan ya kasance wanda kuke matsayi ɗayane yayi maka. 

 

Akushin hannuna ta ƙarba ta mikawa mai zuba abincin. 

 

"Hungo sakamata wancan tuwon da miya akai" 

 

Karba tayi babu musu tayi yanda tace,sabanin dana ƙariso wajen har ta farayimin ni kallon duk ɗaya muke dake. 

 

Karbar kwanon tuwonnawa tayi a hannun mai zuba abincin kaman ta karbi kashi,miƙomin tayi tana wani shu'umin murmushi,bankawo komai a raina ba na miƙa hannu zan karba,tun kafin kwanon ya taba hannuna naji ta juyemin Tuwon a jikina,ga miyar akwai ɗan zafi,runtse idona nayi inajin abubuwa biyu suna shigata. Zafin miyar da kuma zafin tozarcin da tayimin.  

 

"Ke dabbar inace zaki shigowa mutane nan wajen a hargitse take,ko kazantar da kuke a sansaninku zakixo nan wajen kinyi mana,to yanzu nayimiki mai dalili saikije ki gyara jikinki da kyau,kuma gobema kisake shigowa inda muke a haka" 

 

Taƙarisa maganar tana dunguremin kai,jinayi kamar na rusa ihu,amma nasan ihun bazai taba zuwa ba. 

 

Idona ne ya haɗu dana Mutumin jiya,wani kallo yayimin dana kasa fassara bayanin kan fuskar tasa, daga baya ɗauke kansa yayi tamkar bai taba sanina ba ya cigaba da lamarinsa. 

 

Shin mai yasa ziciyata ta rayamin cewar zai taimakeni,bayan shima bai wuce ya shiga halinda nake ciki ba,ko jiyama yashiga halinda ya ninka nawa muni. Kuma ina kallo ban iya na taimakeshi ba. Wata zuciyar ce tace to ai binciken da kike har kika makara dominsa kikayi. Uhmm ko kuma wa kaina ba,domin zuciyata na kwaɗayin wacce kyauta baba almahdi zayyimin,sannan wacce hanya zanbi nayi masa maganin matsalarsa. 

 

Barin wasiƙar jakin danakeyi nayi na tunani,tsamu tsamu na duƙa na ɗauki kwanon jikina duk miya na bar wajen. 

 

A hanyata ta tafiya ɗakinnamu na haɗuda wata mata,ajiyar zuciya nasake danaga wanda nasani. Iya Ramma ce sansaninmu ɗaya. 

 

"Iyaa" 

 

Nafaɗa cikin karyayyar murya,ɗagowa tayi tanamin kallon mamaki domin bata taba tunanin ganina a wajen ba. Saurin waigawa tayi ganin babu wanda yake kallonta tajani zuwa wani waje. Tafiya muke batacemin komai ba nima kuma banyi musu ba ina biyeda ita har mukaje kama tafiya zuwa wata hanya,jiya nayi ƙoƙarin wajen ganin nasan abubuwan dasuke ƙunshe a gurin. Dukan da akewa mutumin jiyane ya ɗauke hankalina ban ƙarisa ba. 

 

Rafi muka iso,wanda dukka tafiya yayi ya haɗe da wanda yake bayan sansaninmu. Har sannan batacemin komai ba har saida nagama wanke jikina da kayana na fito tukunna. Lullubin kanta ta cire ta miƙamin nacire jiƙaƙƙun kayana na shanyasu nasaka mayafin a ƙirjina. 

 

A zaune take akan wani dutse tana min wani kallo mai wuyar fassara wanda na gagara fassarashin. 

 

Cikin nutsuwa na iso inda take fuskata ɗauke da murmushi,nayi ƙarya idysan nace banji daɗin yadda ta kula da lamarinnawa ba. 

 

"Aya yadai naga tun ɗazu kinamin kallom tausayi,babu abinda yasameni dai" 

 

"Uhmm ƴar nan bana abinda yasameki nakeyi ba, na wanda zai sameki nakeyi idan ba Allah yabada kariyarsa akanki ba. Wajennan yanada matuƙar haɗari ga mace mai ƴan ci ma ballantana kuma baiwa. Akwai abinda yafaru da wata mai ƴanci amma ƴar talakawa ce,.............hmmm abin babu daɗin ji ko kaɗan" 

 

Shuru tayi kaman bazata ce komai ba,da alama koma wanne irin labarine to lallai mai taba zuciya ne. Kafin nayi nisa a nazari naji muryarta tacigaba da magana.  

 

"Tashigo cikin wannan gasa ta zaban gwarzo wanda yafi kowa ilimi,fikira da fasaha a cikin matasan nahiyar africa, cikin hazaƙa da kuma burin samun nasara domin ta ɗaukaka sunanta da kuma na ahalinta,saidai kash hakan bai samuba sanadiyyar wata jarrabawa data gamu dashi. A lokacin ɗan sarkin Daular ghana na uku shima an turoshi sai ya nemi kebewa da ita taƙi amincewa,ganin bai samu haɗin kai ba sai yasaka yaransa kusan su goma sukayi mata fyaɗe sannan suka kasheta. Kowa yasan mai ya faru amma haka aka rufe wannan kundin da cewar kawai dan taga bazatayi nasara bane tasha guba ta mutu. Bayan wannan akwai abubuwa da dama dasuka shafi wanda basuda ƙarfin ahali a wannan gasa. Maza kansu basa tsira daga ƙakubalen ƴaƴan sarauta to inaga mace hakan ma baiwa. Dan haka tun wuri kafin abu yayi nisa ki janye daga wannan gasa Joda. Wlh ana kashe kashe da baƙar izaya a wannan wajen,tun ba'aje ko ina ba kiga har kinshiga komar wata a cikinsu. Basaso ko kaɗan ɗan talaka kokuma bawa ya rabesu." 

 

Jinjina maganganun nata nayi,tabbas wajennan akwai haɗari,tunda ko sati bamuyi ba nida wancan bawan allah har mun fara karbar rabonmu. Allah sarki shikanma bashida lafiyar Zuciya.....uhmmm nake tausayin wani bayan nima abar tausayince. 

 

"Hakane iyaa nima kaina nasan wasu daga cikin abubuwan da ƴaƴan sarauta ke aikatawa da abokan karawarsu,amma babu komai dama sai an sha wuya ake taka matakin nasara,kedai kawai ki dunga yimin addu'a .....yawwa ya Addah Rahilah ne ina fama da wannan sabon lamarin gabaɗaya na manta da ita." 

 

"To tana nan da sauƙi inji jinyar bahaushe amma jiki kam saidai alhamdulillah" 

 

Ɗan jimmm nayi kafin naje na duba kayana dana wanke,ba laifi yaɗan sha duk da bai gama bushewa dukka ba. Sakawa nayi na bawa iyaa mayafinta. Kai tsaye hanyar ɗakin magunguna na nufa,akwai abinda nakeson haɗawa a gameda jinyar wancan bawan Allah dako sunansa bansani ba sai gashi an bani shi a matsayin Jarrabawa ta,bansan dalilin baba Almahdi nayin hakan ba,amma koma dai menene zan tabbatar nayi iya ƙoƙarina. 

 

Lokacin dana shiga Ummu hajar bata nan,sai bayi kawai suna ta aikin goge goge da shara. 

 

Teburin na nufa batareda wani jinkiri ba nafara duba abinda nake buƙata,wanda babu kuma sai naje na nemo. 

 

"Hmmm ina mamaki kaza ta dunga cusa kanta a gidan Mikiya,duk tasan komai ƙoƙarinta bazata iya tashi ta bisu ba idan sukayi niyyar ƙaura" 

 

Ɗan murmushi nayi danaji maganar tata,ban ɗago na kalli koma wacece ba amma nasan dani take,budar bakina nace. 

 

"Ai idan da fikafikin koyo da naci zai iya saka na Allah yayi ikonsa watarana ta tashi tabisu koma ta wucesu nisa a sararin samaniya,ballantana ma ko bata tashi ba indai su suka gayyaceta ai zasu iya ɗaukarta su tafi tare." 

 

"Kee lallai ma yarinyar nan dawa kike maida wannan martanin maganar?" 

 

"Da wanda yafara kuma ya tsargu" 

 

Jefar ta tsintsiyar sharar tayi tataho gadan gadan zata dakeni,tun kafin ta iso na ɗauki wata kwalba na buɗe tareda cewa. 

 

"Kinga wannan abun gubace,yana taba fatar mutum a take zata zagwanye,kina matsowa inda nake zan zuba miki shi a fuska,saiki zaba ko ki koma ki cigaba da aikinki kokuma ki ƙare rayuwarki da ƙonanniyar fuska" 

 

Ganin fuskata babu alamar wasa,sannan ga kwalbar na ɗagata sama da ruwan a ciki,yasaka ta tsaya cakk tana nazari,ganin itace zata cutu yasa ta wayance tana zage zage,nidai murmushi nayi kafin a jiye kwalbar wanda babu wani guba maganin zafin jikine ma na yara.  

 

Wata fikira ce tashiga kaina,wato zaka iya yiwa mutum barazana da abinda bai saniba kuma kayi galaba a kansa. Saida suka gama sharar suka fita kafin nasamu hankali na ya nutsu waje ɗaya,kuma na fara haɗa abinda yakawoni. 

 

Tafarnuwa na ɗiba na wanke ta tass,sannan na ɗauki ɗanyar cittama itama na wanketa. Niƙasu nayi a dutsen niƙa saida sukayi laushi sosai sannan na kawo zuma na zuba na garwayasu waje guda. Kallon haɗin maganin nayi kafin na ɗauki kwalba na juyeshi a ciki. Har na gama na fita babu wanda yashigo yasameni.  

 

Sansaninmu na bayi na nufa cikeda ɗokin ganin mutane na Fasihmman ma Addah Rahilah. 

 

Tun a bakin ƙofar na fara jiyo kururuwa na mata,sannan da wani irin nishi mai tsuma zuciyar mai sauraro,ban san lokacin dana runtuma a guje ba zuwa cikin ɗakinnamu. 

 

 

 

 

Sadi-sakhna ce ✍🏼 

 

Comment  

Like  

Share  

Follow