8..
NAZEEFAH SABO NASHE
FREEđ
***
-9
ELEGANT ONLINE WRITERS........
Tana shiga dâakinta hawaye ya fara zubo mata, Tunani take sosai a zuciyarta so take ta hango laifin da takewa dangin mijinta suka tsaneta har haka, mai tayi musu? Shine abinda take tunani a zuciyarta, har ga Allah bata nufin kowa da sharri rayuwarta take free ba tare da kowa a ranta ba amma sun bi sun tsaneta.
A gefen gadon ta zauna, shatu data gefe jikinta yayi sanyi ganin mommah na hawaye, taji duk duniya ta tsani waccan Almasifatun tsohuwar a hankali ta zauna jikin mommah itama ta saki nata kukayi. Momma dafa kanta kawai tayi alamar rarrashi. Daidai lokacin Ammar da Imran suka shigo dâakin jikinsu a sanyaye suka zauna kan cushion chair dâin da take gefe fuskarsu sam ba walwala musamman ammar, sam baya son abinda zai saka mahaifiyarsa a âbacin rai. Ammar yayiâkasa da muryarsa â Momma kiyi hakuri komai lokacine, kuma wata rana sai labari.â Girgiza kai tayi â Na kai maâkura Ammar iya haâkurin da zan iya kenan kun san iya lokacin da nakeâkunsar baâkin cikin hajja tun ranar da na kwana dâaya a gidannan duk a dalilin mahaifinku bai auri zaâbinta ba, kuma ba kowa bace zaâbin nata sai wannan matar da sai da ta san yarda tayi yanzu ta auro masa ita, to lamarin ya isa zan tattara in tafi amma ba zan zauna baâkin ciki ya kashe ni ba just like bani da iyaye, gidan ubanku ne ku zauna, bare shi gashi nan zasu aura masa wacce suke so, tun yaushe nake jan kunmensa ya rabu da yarinyarnan yaâki, saboda kawai kyanta da kwalliyarsa yana rudâarta to yaje ya aureta amma ka san Allah ba hannuna a cikin lamarin aurenka, wanda dama don a gasa min baâkin ciki akaâkirâkiresa.â
Ta saki ajiyar zuciya bayan ta miâke ta shiga hadâa kayanta, Ammar ya riâke akwatin â please mommah kada kiyi abinda baki taâba yi ba da yarintarki balle da girmanki please ki rabu dasu,ko mu kadâai zamu iya share miki hawaye, kuma wallahi at this point sunyi naâkarshe, kaima yaya Imran don Allah kayi hakuri ka kyale musuâyarsu ko don kwanciyar hankalin Mommah â wani kallo Imran ya zuba masa â meye laifin shaheeda da zan rabu da ita, ko kana tunanin a bayansu take? To kullum maganar ta tana jin haushin abinda suke wa mommah.â Wani kallo momma ta wurga masa sai kuma tayi kwafa â mhmn ba dai shaheeda bace Imran ka aureta ban hanaka ba, tunda lokacin da na hanakan ai baka ji ba, sai dai bahaushe yace wanda bai ji bari ba.... kai kuma Ammar kada ka sake masa magana idan ta nice ma barin gidan zanyi ba sai na zauna zanga kayan takaici ba .â Imran shiru yayi yana sake zabgawa Ammar harara sai kuma yayi kwafa ya fice. Mommah tabi bayansa da kallo tana masa adduâar shiriya a zuciyarta ji take kamar ta rusa kuka gaba dâaya sun cusawa Imran soyayyar shaheeda ta âkarfi da yaji da yaudara da komai. â ka rabu dashi Ammar tsakaninka dashi Adduâa ya riga yayi nisa a soyayyar shaheeda ba zai taâba ganin aibunta ba.â Ammar ji yayi ransa ya sakeâbaci idan dai da shine ko da gold akaâkera shahida sai ya haâkura aurenta balle shi dai ban da kyan fuska bai ga mai ya gani tare da shahidan ba tana tafiya kamar sillan kara,sai iyayi da kwainane. Shatu dai tana gefe tana kallon ikon Allah, takaicin Imran kuwa ya gama cikata. Har so take taga wacece wannan da ya fi sonta akanâbacin ran mahaifiyarsa. Ammar ya cigaba da bawa mommah haâkuri ganin taâki haâkura yasa ya fita wajen bayan ya danna kiran hajiya mama mahaifiyar mommah a cikin wayarsa. Basu san me yace ba sun ga dai ya dawo da sauri ya miâkawa mommahn wayar, ya wurga masa harara don ta sanâkara ya kai ta wajen hajiya maman. Tana sallama hajiya mama ta shiga fadâa tuni mommah ta sa kuka ta fara bata labari. Hajiya mama cikin zafi ta katseta â kishiya saboda kishiya zaki bar gidanki akan ki aka fara kishiya?da girman ki da komai kike neman zubar da mutuncin ki to ahir ki kiyayeni kina shirin auren daâkanne da âyaâya, nan gaba su kuma idan sunyi wa zai musu fadâa? To ki saurareni da kyau ki mayar da akwatinnan kafin ma su gani su ji dadâi gobe insha Allahâkannenki sun zo hutu daga turkey zasu zo kanon suyi miki hutu hisham ma dama yana ta son zuwa wajen mutuminsa Ammar. Ina shatu?â Momma ta miâkawa shatu wayar â maza ki masa hajia mama ce â. Shatu ta karâbi wayar cikin rashin sabo ta fara gaisheta â lafiya lau shatu ya baâkunta? Gobe zaki ga aunties dâinki suna ta son ganinki.â Murmushi shatu kawai tayi saboda ba âyan hayaniyar a kanta. Hajiya mama ta sake cewa â Ba dai matsala dai ko?â Shatu ta girgiza kai â Bakomai mamaâ To masha Allah sai kin ga saâko â hajiya mama ta fadâa tana kshe wayar. A hankali shatu ta miâka wa Ammar waya, ganin yarda jikinta yayi sanyi yasa Ammar ya shiga janta da wasaâ shatun mommahâkalau kuwa yau na ganki jiki ya mutu? Ko don ki hadâu da Babarki a masifa â harararsa shatu tayi â Ai wallahi ba tsoronta naji ba, don dai kawai mommah ta hana ne amma wallahi da tuni ta dâebi kashinta a hannu yo Allah na tuba wannan âkaramar alhakin, ka san Allah da âkauyenmu ne yau sai na saka yara sun mata kidâan Atire.â Ammar mai zaiyi banda dariya mommah kuwa budâe ido tayi tana kallon shatu yarda take yi da baki â To shatu ba âkauyenku bane kuma anan idan kayi wa wanda ya girme ka rashin kunya kulleka ake a gidan yara don haka be careful.â Ammar ya fadâa fuskarsa dâauke da alamar tsoratarwa. Shatu ta kyaâbe baki â Ai in dai ba kayi a fili ba sai mutum yayi ta bayan fage yarda za âa gane ba.â Ammar girgiza kai kawai yayi yace âAllah ya shiryeki shatu.â â Tashi maza kije kiyi sallah Ayshata ai Na san kina jin maganata ba zaki jawo min abin fadâa ba â.murmushi tayi tana miâkewa dadâin yabon da momma tayi mata da sauri ta shige toilet ta bar momma da ta zuba tagumi tunani yyi mata katutu.
Dahda da daddare da kansa ya shigo dâakin mommah ganin ko nemansa ba tayi ba. A zaune ya sameta kan sallaya da alama lazimi takeyi, jikinsa a sanyaye yake dubanta yana son matarsa shi kadâai kuma ya san irin son da yake mata, ba don komai ba sai don yarda bata tsallake umarninsa kuma iya iyawarta take kyautata masa ba ta son âbacin ransa sam.
Tana ganinsa ta dâan dâauke kai idanunta yana kawo hawaye. A gefenta ya zauna hadâe da riâko hannunta tayiâkoâkarin zamewa ya matse hannun murya a âkasa yaceâDeejah yau mantawa aka yi da abincinka?â Wani kallo tayi masa kafin hawayen idonta su zubo. Hawayen ya dinga bi da ido â kukan na menene?â Murya canâkasa tace â abincinka yana wajen amaryarkaâ fuska ya sake tamkewa kafin yace â wace irin magana ce wannan? Kema kin san sarai ba da amincewata aka yi aurennan ba, to me yasa zaki damu kanki yarda ta shigo haka zata koma, bani da tsarin ajiye mata biyu a gidana, ba raâayina bane tashi muje ki bani abinci kada ki sakeâbata min raiâ Ya jata ya miâkar tsaye suka fita. Hanyar part dâinsa direct suka nufa. Dai-Dai lokacin hafsaâyar hajjan ta ganosu itace auta a dâakinsu da sauri taje ta sanar da hajjan. Hajja kuwa tayi saurin fitowa fadâi take muje ba dani zaâa yi wannan iskancin ba muje da kaina in kai masa amaryar in kuma nuna masa ni Na haifeshi ba shi ya haifeni ba...
A bakin âkofar part dâin nasa ta tsaya tana buga âkofar da âkarfi kamar zata âballe âkofar. Dahda ransa a âbace ya budâe âkofar, murya a sarâke yace âHajja lafiya?â Kallon sama da âkasa ta jefa masa â sannu isashshe har kana da bakin tambayata lafiya to ita lafiyar tana gidan ubanka wuce muje ka taho da amaryarka ita ta cancanta ta kwana a dâakinnan sai an mata kwananta uku rus da bazawara ta bata, kuma ban amince da ko bakinâkofar nan naga sillanâkafafunta ba wuce muje ka taho da matarka.â Mommah da take cikin parlourn tana jiyo duk abinda yake wakana ta miâke zaune zauciyrta na tafarfasa ta fice daga palrlourn.
Shatu dake zaune a main parlour tana jiyo duk abinda yake wakana tayi alâkawarin yau tsohuwar nan ba zata kwana da lafiya ba. Ta shige dâakinta tanaâkissama irin abinda za tayi mata. Da sauri ta shiga tanadin kayan duk da zata yi amfani dasu. Cikin dare ta nufi dâakin da aka sauke hajja, a hankali ta murdâaâkofar Ta shiga, Hajja ta tarar ta saki baki tana barci taci saâa kuwa hajjan ita kadâaice a dâakin tabbas shirinta zai tafi yarda take so, Ta sake kallon shigar da tayi a mudubiâkusumbi tayi sosai a bayanta ga gashinta da ta saka ya rufe mata fuska gaba dâaya sai wani farin hjibin momma da ta sinâkife jikinta dashi, baâa ganin fuskrta Sam, Ta durâkushe sosai kamar wada tana lanâkwashe âkafarta kamar a shanye take. Tsaye tayi gefen gadon hajjan kafin tasa sandar hannunta ta zunguri âkafar Hajjan â Ke tashi ajalinki yau yazo tsohuwar banza mai takurawa jamaâa....... A razane Hajja ta rusa wani ihu fadâi take â ku kuke ganinmu ba mu muke ganinku ba innahu ala rajaâihi laâkadir......